Showing 42001 words to 45000 words out of 201092 words

Chapter 15 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

a tsaye ne."


"Ba zan iya ba, ba zan iya sauri ba Hannah. Kin sani, babu wuya zan iya fad'uwa, a irin saurin nan da kika saka ni."


"Ni ban san irinki ba, Maryam. Yanzu idan bamu samu wuri ba, ya kike so mu yi? Da k'afa kike son mu isa gida?"


"Ni zan kai ku, please ki bi mun ita a hankali. Matata bata son tsanani, kin sani. Komai nata a natse ne, natsatssiya ce."


Kallon mamaki Maryama ta bi shi da shi, tana son sanin yanda aka yi ta zama matarshi, tana son ta san shin a ina ma ya santa? Ita dai ta san bata ko tab'a ko ganin fuskarsa ba, sai yanzu.


"Yes. Ni zan kai ku har gida."


Ya furta cikin halin ko in kula, kamar da gaske dama ya santa.


"Yamma na yi, ku zo mu tafi mana."


Har ga Allah Hannatu ta zata da gaske Maryama ta sanshi, hakan ya sa ta kama hannunta, a hankali suke taku har suka isa bakin motarsa, wadda ya faka a can nesa da gate d'in makaranta, saboda tinted glass da gare ta.


Kamar mutum mutumi haka Maryama ta koma, ta gagara furta komai, mamakinsa kawai take, mamakin samarin yanzu. Tana tunanin a inda ya santa, da kuma dalilinsa na kiranta da matarshi.


Tun da suka kama hanya babu wanda ya furta komai, sai sautin da ke tashi a hankali yana bin wak'ar.


Wayarta ce ta d'auki ruri, ko da ta duba ta ga Mamanta ce ke kira, hakan ya sa ta gaggauta d'auka tare da kallon mai motar. Kallo d'aya ya mata ya gano manufarta, ya gaggauta rage k'arar sautin, ya ringa fita a hankali.


"Mun rasa abun hawa ne, Mama. Amma muna hanya yanzu haka."


Ta tsinke wayar daga nan, ta d'ora kusa da hambrek na motar.


D'aukar wayar ya yi, bai yi wata wata ba ya saka lambarshi a ciki, ya yi dailin take tashi ta fara ringing.


Saving ya mata da Farouk Bobby, sannan ya ajje yana wani shu'umin murmushi.


***


Kin ji yanda muka ha'du da shi. Ban san wani abu sosai game da shi ba, kawai dai na san shi d'in ba mutumin kirki ba ne.


Ya dame ni sosai, Jiddah. Na rasa yanda zan yi da shi."


Ta k'arisa maganar, da damuwa fal a saman kyakkyawar fuskarta.


Murmushi Jiddah ta yi, ta d'an kalli gefen da wayarta take. D'aukowa ta yi a hankali ta bud'e datarta, duk Maryama na kallonta amma ta gagara furta komai.


Ta jima a haka, har 'yan ajin nasu suka fara zuwa, kafin ta mik'o ma Maryama wayar, tana murmushi ta ce,


"Ba wannan ba ne?"


Karb'a Maryama ta yi ta kalli Bobby, su biyu ne a hoton, wani saurayi sanye da k'ananan kaya, jar t shirt da bak'ar pick up, sai Bobby daga gefenshi.


"K'warai kuwa, shi ne."


Ta fad'a cikin rawar lab'ba, kamar wani zai riga ta.


D'an taunar leb'onta ta yi, ta ce,


"Mun samu wata mafitar, akwai wani plan, kawo kunnenki ki ji."


Magana suka yi k'asa k'asa, kafin Maryama ta murmusa, cike da k'warin guiwa take kallon Jiddah.


Murmushi ta mata, wanda ke tabbatar da abin da ta fa'da mata, kafin ta jawo hannunta, ta saka a cikin nata.


Duk chaptern da kuka ga na sako, ku rik'e ta, ku bibiye ta, domin kuwa tana da amfani a cikin wannan labarin.


Kamar yanda na fa'da maku a wancan page d'in, cewa ku d'aure d'amararku, domin kuwa yanzu labarin ya fara.


Shin wace idea ce Jiddah ta fad'a wa Maryama, wacce har ta saka ta murmusawa?


Ko zasu yi nasara a kan wannan plan d'in da suke shirin shiryawa?


Ku dai juri zuwa rafi, da sannu zamu kai ga gaci.


Thanks all.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:44 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣5⃣


Ranar litinin bayan Maryama ta dawo daga makaranta ta kira Jiddah, dama sun yi da ita cewa idan ta dawo zasu haɗu, saboda zasu je gidan su Annur.


A hankali ta taka har bakin ɗakin Mama, ta same ta zaune tana waya, hakan ya bata damar zama bisa sofa, har lokacin da ta kammala wayar.


Da fara'a a fusKarta ta ce,


"Maryama, har kin ci abincin?"


"Ehh, na ci, Mama. Dama fita nake son yi, zan je gidan su Jiddah."


Miƙewa Mama ta yi bisa ƙafafuwanta, wayarta ta ajje bisa mirror, sannan ta tako inda Maryama take.


"Ki kula da kanki."


Kawai Mama ta furta, sannan ta ci gaba da taku har ta fita daga ɗakin.


Murmushi Maryama ta saki. Tana matuƙar son mahaifiyarta, tana alfahari da ita ƙwarai da gaske.


Baro ɗakin ta yi kai tsaye ta nufi nata, tana mai tsananin jin daɗi. A zuciyarta kuwa, zullumi ne fal, wanda ta kasa cire shi, duk kuwa da ƙwarin guiwar da Jiddah ke bata.


Wanka ta sake yi, ta saka baƙar doguwar riga, wadda ta ji ado da duwatsu kalar gwaldin. Mayafin abayar ta yane kanta da shi. Bakin madubi ta tsaya ta dudduba kanta. Ba wata kwalliya ta yi ba sai man baki kawai da ta shafa, ta shafa madarar turaren VIP.


Cikin kyakkyawan takunta ta fito, a hankali ta ƙariso wurin Mama. Bankwana ta mata, ta bata ɗari biyar cewa ta hau napep, saboda drebansu ya yi tafiya tare da babanta, zuwa garin Lagos.


Godiya ta ma Mama, sannan ta miƙe bisa ƙafafuwanta, ta kama hanyar fita, tana jin yanda gabanta yake tsananta faɗuwa sosai ba kaɗan ba.


A Ring road suka yi mahaɗa da Jiddah, a can ɗin kuma ta same ta, a tsaye take, tana kallon agogon hannunta a daidai lokacin, ga kuma waya a hannunta.


Ganinsu da ta yi ya sa ta saki murmushi, ta iso inda suke, haɗe da hawa napep ɗin.


Bayanin inda zasu je ta masa, a ƙarshe ta ce,


"Gidan Alhaji Iqrah Al-Hussain."


"Hajiya ai da haka kika ce tun farko, da baki wahalar kwatance ba. Waye zai ce bai san wannan gidan ba?"


Basu kuma ce masa komai ba, sai fira da ta kaure a tsakaninsu.


"Na ɗan jima a nan tsaye fa, Maryam. Ina shirin kiranki ke nan ma sai ga ku kun iso."


Maryama ta ce,


"Wallahi kuwa, mun ɗan haɗu da hold up ne a hanya."


Ta gyara zamanta, tana son yin magana amma ta yi shiru, tana fuskantar gabanta.


"Ki faɗi abin da kike son cewa." Ta tsinkayo muryar Jiddah, a daidai lokacin da hankalinta ya nemi isa can wata duniyar.


"Zuciyata...zuciyata ta kasa bani ƙwarin guiwa, Jiddah. Ban san me ya sa ba, haka kawai sai gabana yake faɗuwa. Nake ga kamar wata matsala zata gitta a wannan plan ɗin namu."


Tana kaiwa nan ta dakata, tana jin yanda gabanta yake tsananta faɗuwa, zuciyarta na riya mata abubuwa da dama, wanda ta kasa fahimtar komai daga ciki.


"Maryam!" Jiddah ta furta tana kallon Maryama, ta saka ƴan yatsunta a cikin tafukan hannayen Maryama, tana mata kallo mai cike da ƙarfafa mata guiwa.


"Matuƙar baki cire wasi-wasi a kan wannan aikin ba, tabbas za a iya samun matsala. Kin sani, kin san cewa nasara da sa'a suna tattare ga ma'aboci dagiya, juriya da kuma ƙwazo.


Ki ɗauka a ranki cewa wannan wani aiki ne zaki yi, wanda sai mai himma da ƙwazo zai iya yinsa. Ki saka a ranki, cewa ke ɗin mai ƙwazon ce. Hakan ne kawai zai sa ki daina faɗuwar gaba."


Duk yanda take son ɓoye rawar da jikinta yake yi gazawa ta yi, dole sai da Jiddah ta gane.


"Shi ya sa kika ga tun farko na ƙoƙarta hana ki wannan aikin, saboda na sanki, na san halinki, na kuma san wacece ke. Aiki ne wanda marasa tsoro, masu dagiya, wanda suke da ƙwarin guiwa zasu yi. Ba wai ke ba Maryama.


Amma tun da ke ɗin ma kika zaɓa hakan, kike ga kamar zaki iya, sai ki daure, ki daure ki cika wannan aikin ladar da kika yi alwashin yi. Allah Yana tare da ke, insha Allahu zaki dace"


Murmushi Maryama ta yi, tana matuƙar jin daɗin yanda Jiddah ke ƙarfafa mata guiwa. Tana son yanda Jiddah ke goyon bayanta ɗari bisa ɗari, a kan wannan aikin da zata fara.


"Na gode ƙwarai, Jiddah. Ina matuƙar ƙaunarki, ina alfahari da ke, na san kin sani ai."


Kai Jiddah ta ɗaga mata, ita ɗin ma da murmushi a fuskarta, ta ce,


"Yauwa ko ke fa? Ina so ki bani mamaki, ki yi aikin da nake ga kamar ba zaki iya yinsa ba. Na san you can make it, try your best, and make it, Maryama."


"Deal." Maryama ta faɗa haɗe da dunƙule hannunta a cikin na Jiddah.


A ƙofar gidan ya faka napep ɗin, kuɗinsa Maryama ta zaro ta miƙa masa sannan suka fita, suka ƙarisa cikin gidan.


Tun a harabar gida suka ci karo da Annur, wanda ke ƙoƙarin fitowa daga motarsa. Kallo ɗaya Jiddah ta masa ta ɗauke kanta, ta san dole sai ya mata magana, hakan ya sa ta ƙara saurinta, har ta wuce Maryama.


"Jiddah, amma kin san bana son saurin nan ko?"


Ta faɗa cikin wata murya.


Ko waigowa Jiddah bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta, har ta ƙarisa ƙofar da zata sada ta da cikin gidan.


Shi kuwa Annur gaggauta isowa inda Maryama take ya yi, yana son ya mata magana amma bai ga fuska ba, bai san dalili ba, kawai sai ya samu kansa da kasa furta mata komai. Yana ji a ranshi cewa fa yana son yi mata magana, sai dai wani ƙwarjini ya ga ta masa, wanda dole ya wuce ta, ba tare da ya ce mata komai ba.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, a ranta tana hamdala ga Allah, har ga Allah tsoronsa take, bata son ko kallonshi.


Ƙofar da ta ga Jiddah ta shiga ta ɗora ƙafarta a kai, a hankali ta taka sai gata a babban falon gidan, wanda sanyi ya gama mamaye sa, yake fitar da wani ni'imtaccen ƙamshi, mai matuƙar daɗi, wanda ta kasa tantance ko daga ina yake fitowa.


"Maryama."


Ta jiyo muryar Jiddah, wadda ta dawo da ita daga duniyar da ta shagaltu a ciki, take jin ina ma zata dauwama a cikin wannan duniya, mai cike da ƙamshi, wadda irinta ke ƙara wa mutum walwala a duk halin da ya tsinci kansa.


Takowa ta yi cikin natsuwa, a daidaice take ɗore ƙafafuwanta bisa lallausan kafet ɗin ɗakin, har ta ƙariso ɓangaren da kujeru suke.


Zama ta yi bisa kujerar, kusa da Jiddah. Ta ɗora idanuwanta a bisa fuskar dattijuwar matar da ke zaune. Wacce ke cikin shigar alfarma, ta saka wani jan karen miski wanda aka ma ɗinkin doguwar riga, an ƙawata shi da wasu irin duwatsu masu matuƙar kyau.


"Ina wuni?"


Maryama ta buɗe muryarta ta fa, tana mai sakin guntun murmushi, wanda za a iya kiransa da na yaƙe.


"Lafiya ƙalau fa. An zo lafiya?"


Hajiya Suhaila ta furta, tana mai sakin murmushi a saman fuskarta.


"Lafiya ƙalau, Momy."


Maryama ta ce, wanda tana faɗin haka suka jiyo takun Annur, yana ƙoƙarin shigowa ɗakin.


Kusa da Jiddah ya fara ƙoƙarin zama, amma wani wawan kallo da ta watsa masa dole ya tsayar da ƙafafuwansa, yana bin ta da wani irin kallo mai cike da ma'anoni kala daban daban.


Tambayar Jidda Momy ta yi, ya mamarta? Ta shaida mata da tana lafiya ƙalau, ta ma ce a gaishe ta.


Sun ɗan jima a haka, kafin Annur ya miƙe a bisa ƙafafuwansa, a zuciyarsa yana mai son kasancewa shi kaɗai da Jidda, saboda baya jin zuciyarsa zata iya haƙuri da soyayyar Jiddah da take ɗawainiya da shi, wadda ke hana shi saƙat, take takura shi, a duk sanda ya runtse idanuwanshi, yake kallonta, yake kallon kyakkyawar fuskarta.


"Amm...Jiddah, please zan gan ki 2 minutes."


Ya ɗaga laɓɓansa ya yi wannan furucin, yana jin yanda zuciyarsa ke tirsasa shi da bashi yaƙinin yin maganar, duk da shakkun Jiddah da yake yi.


A zuciyarta bata son bin shi ɗin, sai dai kuma yana ɗaya daga cikin plan ɗin da suka shirya, haƙuri da juriyar duk wani abu da zai taso.


Runtse idonta ta yi, tana jin yanda zuciyarta ke ingiza ta, tana mai shawarwarta a kan kar ta je, tunanin da take yi ba zai taɓa zama gaskiya ba.


A wani ɓare na zuciyarta kuwa, ƙaryata wancan sashen yake, yana daɗa bata ƙwarin guiwa kan ta bi shi ɗin, ɗaya daga cikin nasarori ne.


Tashi ta yi jiki babu ƙwari, tana jin yanda idanuwan Hajiya Suhaila ke yawo a duk gaɓoɓim jikinta, duk da bata kalle ta ba, jikinta na bata cewa murmushi ne shimfiɗe a bisa fuskar Hajiya Suhaila, saboda dama ta jima da kawo tayin Annur ga Maminta, sanin halin yaran yanzu ya sa suka watsar da zancen a inda suka yi shi. Ko ba komai Mamin Jiddah ta san Annur, ta san komai game da shi. ba zata taɓa yarda ta sadaukar da rayuwar ƴarta gare shi ba, mutumin da banda neman mata da shaye shaye babu abin da ya ajje.


Bin bayansa ta yi a hankali, basu tsaya ba sai cikin lambun gidan, wanda yake ƙawace da shuke shuke kala kaka, masu matuƙar ƙayatarwa, wanda kallonsu kawai zai iya jefa mutum wata duniyar, mai cike da farin ciki da tarin ni'imomi.


"Zauna, ga wuri nan."


Ya furta yana kallonta, ya ɗan lumshe idanuwansa, yana mai sauke su bisa kyakkyawar surarta, wacce ta sha ado da jan material ɗinkin riga da sket.


Zaman kuwa ta yi babu musu, tana mai ɗauke dubanta daga gare shi. tsarge take sosai saboda yanda ta ga yana binta da wani mayataccen kallo, mai cike da wata ma'anar ta daban.


Bayan ta zauna shima ɗin ya zauna, yana jin wata irin natsuwa a tattare da shi, yana jin yanda soyayyarta ta gama mamaye zuciyarsa, ta sa shi rasa duk wata natsuwarsa, yake jin ina ma zata amince masa, da ya cika burin iyayenshi, ya aure ta, Shi ma ɗin ya zama magidanci. Sun jima suna masa maganar aure, ba wai momynsa kaɗai ba, har da mahaifinsa ma. saboda babu abin da ya rasa komai samu yake. Duk da cewa ya rasa aikinsa, ya ajje sa tun daga sanda ƙwalwarsa ta samu matsala. Babban kamfani babanshi ya buɗe a nan cikin katsina, kamfanin sarrafa ƙarafa ne, wanda ya samu ɗaukaka sosai.


Suɗar laɓɓansa ya yi duka biyun a lokaci guda, sannan ya fiddo su daga cikin bakinsa, ya ɗora idanuwansa a saman fuskar Jiddah. A hankali ya fara ajje kalamansa,


"Jiddah...Jiddah na sani, na san bana sahun irin mazan da kike so, kamar yanda kike shan faɗa min. Amma ki sani, tun da nake a rayuwata, ba a taɓa yin wata ƴa mace wacce nake ma irin son da nake miki ba. Na kasa dakatar da kaina daga sonki, na kasa tsayar da zuciyata daga ƙaunarki da ta jefa ni, wanda ban san sanda na afka a cikinsa ba. Ki dubi girman Allah..."


"Dakata!"


Jiddah ta faɗa haɗe da ɗaga masa hannu.


Miƙewa ta yi tsaye ta fara taku a hankali, tana mai ƙarisowa a gabansa.


"Ko zaka shekara da kalaman yaudararka, ba zasu taɓa yin tasiri a gare ni ba. Ka sani, na san waye kai, na san menene halayenka, na san komai game da kai. A kan me? Me ya sa kake ga kamar zaka iya yaudarata da narkakkun kalamanka, wanda ba zasu taɓa iya narkar da zuciyata ba?


Bayan yaudara da ka ƙware a fanninta, har da ƙarya zaka min, kawai dan na so ka?


Ko baka san na san Amrah ba? Amrah wacce ka so fiye da rayuwarka, ka kula da ita, fiye da yanda ka kula da kanka?


Shi ne dan ƙarya zaka zo min da wata magana, wai baka taɓa son wata mace kamar ni ba?"


Tana kai wa nan ta duƙa ƙasa a gabansa, ta haɗe duka hannayenta a wuri ɗaya, ta kalli cikin idonsa ta ce,


"Dan Allah ka ƙyale ni haka nan, ka je ka nemi wata macen, wacce zata so ka mana. Wallahi baka gabana, bana jin ko darajar takalmin ƙafata ka yi. Na tsane ka, bana ƙaunarka!"


Ta ƙarisa maganar da miƙewa tsaye, tana sake binsa da kallo, zuciyarta cike da fargaba da kuma tsoro. har ga Allah bata so hakan ba, bata so kalaman da ta jefa masa a ce sun fito daga bakinta ba. sai dai kuma bata da yanda zata yi, bata da wani zaɓin da ya wuce ta aikata hakan, matuƙar tana so haƙarsu ta cimma ruwa.


A duk rayuwar da mutum ya tsinci kansa, kar ya zama mai girman kai, ko kuma wulaƙantar da mutane, saboda baka san yanda gobe zata kasance ba, baka san ya rayuwa zata yi da kai a gaba ba.


ka so mutane, kai ma sai Allah Ya so ka. kar ka ƙi mutane, gudun kar kai ma Allah Ya ƙi ka.


Na sani, na san kuna jin labarin wata kala, kamar mun faɗa wata duniyar, ba wacce muke cikinta, ta AMRAH NAKE SO ba. Kar ku damu, muna cikinta, cikinta dumu dumu, mun ɗan leƙa ziyara ne, ziyarar da ke ƙunshe da warwarar zare da abawa.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:44 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣6⃣


Cikin wata irin murya ya fara magana, cike da rauni ya ɗaga laɓɓansa, ya ce,


"Jiddah! Wallahi ina son ki, ina ƙaunarki, har ma ban san ta ya zan kwatanta miki ba. Na san inda a ce zaki leƙa cikin zuciyata, ki ga yanda ƙaunarki ta mamaye kaf tsokarta, da ba zaki taɓa ƙi na ba, ba zaki taɓa jifa na da wannan razanannun kalaman naki, masu razana tunanina ba..."


Ya runtse idanuwansa, yana jin yanda zuciyarsa take masa ɗaci, take rinjayar tunaninsa.


"...na sani, na san cewa ni ɗin ban zama mutumin kirki ba. Ban zama wani abun alfahari, wanda har zaku so ni ba. Amma ina so ki sani, wallahi da zuciya ɗaya nake sonki, da zuciya ɗaya nake da niyyar aurenki, nake son kai ki ɗakina, a matsayin matata.


Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login