Showing 75001 words to 78000 words out of 201092 words
Chapter 26 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
ne garimmu, can ne asalina. Na je wurin wani biki ne na dangimmu, har Allah Ya sa na ga Annur ɗin a can."
"Biki...?"
Maryama ta ambata tana mai ci gaba da,
"Bayan kin gudo kin kama zaman kan ki ne kuma har kika iya komawa wurin wani biki? Kenan hakan ba zai iya zama wani abu ba a gare ki?"
"Tabbas! Hakan ba komai ba ne."
"Anyways, lets back to our business. To ke yanzu ta wace fuska kika kalli abun? A tunaninki tabbas Annur ne kika gani? Idan shi ne, me kike tunanin ya sa ya aikata hakan?"
"Abin da na kasa ganowa kenan. Zuciyata ta kasa tantance min gaskiyar wannan lamarin. Na kasa fitar da abun daga zuciyata. Wallahi a yanayin da na samu Annur abin a tausaya masa ne, abun ya zauna a zuciyarka ne."
"Shi kenan to. Yanzu idan na nemi taimako daga gare ki, za ki iya taimaka min?"
"Me zai hana?"
Hadiza ta gaggauta tambayar Maryama.
"Yauwa to. Ba zan so na zo inda kike ba gaskiya, saboda hakan zai iya zubar da kima ta a idon jama'a, ba za a iya gane dalilina na zuwan ba. Ya kenan?"
Shiru ta yi Hadiza tana nazari, dan ba ta san amsar da za ta ba ma Maryama ba.
"Uuhm..."
Maryama ta ambata.
"Ya kike so a yi?"
"Ko za mu yi mahaɗa?"
"Idan hakan kike so ya yi. Sai ki faɗa min inda za mu haɗu ɗin ina jira."
Za ta kashe kenan Maryama ta ce,
"Wait, a minute please...dan Allah kar ki sanar ma kowa wannan maganar. Ina so ta zama sirri a tsakanimmu, ko Annur ɗin kar ki faɗa ma wa."
"Ba zan faɗa ma kowa ba na miki alƙawari."
Bankwana suka yi daga nan suka kashe wayoyinsu.
Latsa kiran Jiddah ta yi Maryama. Babu ɓata lokaci kuwa Jiddah ta ɗauka. Bayan sun gaisa ne ta kwashe komai ta sanar da Jiddah, har wayar da suka yi da Hadiza yanzu.
"Am totally confused. Baki ɗaya kaina ya ƙulle, na kasa hango komai Jiddah. What can you say? Please hint me, little, Jiddah!"
Kanta ta gyaɗa kamar tana gaban Maryama ne, ta ce,
"Akwai ɗaure kai sosai lamarin. Me ye zai kai Annur Maraɗi cikin awoyin da ba su wuce shida ba? Me zai sa ya ga Hadiza a Maraɗi, kuma ya ƙi nuna ya santa, bayan kuma dadironsa ce? A tunanina ko kaɗan ba zai ɓoye mata kanshi ba, saboda ya san ta san komai game da shi. Ta gama sanin sirrinshi tunda har ya kasance ma'aboci aikata zina da ita."
Shiru Maryama ta yi na tsawon lokaci, kafin ta iya zaƙulo magana daga bakinta, ta ce,
"Ko kaɗan tunanina bai ba ni cewa Annur ne ta gani ba. Saboda a yanda ta siffanta shi, babu yanda za a yi cikin ƙanƙanin lokaci ya yi wanann ɓadda-kamar. Kuma ma idan ɓadda-kama zai yi, sai in ga ai a nan Nigeria zai yi ta. Ban ga dalilin da zai sa ya tafi Nijar ba."
Murmushin takaici ta yi Jiddah, ta ce,
"Ba abun mamaki ba ne dan ta ce shi ne a Maraɗi. Ai kin ga Annur ya taɓa samun taɓin ƙwakwalwa, kuma wanda ya samu matsalar hauka, a kowane lokaci ya kan iya tasar masa. Ta yiu ya taso masa ɗin ne bayan ya je can, tunda mutum kamar Annur dama ba za a raba shi da shiga cikin Nijar ba."
"Jiddah na fara tunanin wani abu. Na yarda da kalaman Hadiza ɗari bisa ɗari. Na fara zargin ƙila dai mai kama da shi ne ta gani. Kin san fa akwai irin haka."
"Haka ne tabbas. Amma yanzu ga shawara ɗaya."
"Ina jin ki Jiddah...Allah Ya sa mai ɓullewa ce."
Jiddah ta ce,
"Kawai ki ma Bobby maganar kai tsaye cewa Annur ya ce yana son ki. Tunda yana yawaita faɗar zai iya ja da duk wanda ya nemi raba ki da shi, a ganina zai iya tona asirin Annur, in ma da wata ƙullalliya da yake ƙullawa ne"
"Good idea."
Maryama ta furta cikin murya mai nunar da ta ji daɗi.
Bankwana suka yi da juna, Maryama ta kashe wayar, tana jin sassauci a cikin zuciyarta.
***
Daga gefensa take zaune, butsu butsu ta ɗaga kanta ta dube shi, cikin tausayi da ƙara jin soyayyarsa a cikin zuciyarta.
"Amrah..."
Ya furta a cikin baccinsa wahaltacce da Dr. Huzaif ya narka masa allurar barci sannan ya samu ya yi.
A hanzarce ta miƙe tsaye tare da isa dab da gadon. Tsura masa idanuwa ta yi, kyam ta ke kallon fuskarsa. Kyakkyawa ne sosai. Hancinsa a tsaye yake siriri, bakinsa ɗan ƙarami wanda ya gama farfashewa, duk ya bi ya lalace tsabar wahala.
Gyaɗa kanta ta yi ta gaggauta dawowa a cikin hayyacinta. Tunanin banza take a ganinta, tunda dai ga shi a kwance yana fama da kansa, me zai sa ita ta zurfafa a begensa?
"Amrah...Amrah nake so!"
Ta sake jin Modu ya ambata duk a cikin barcinsa da yake yi na wahala.
"Modu nice ag gabanka hwa. Buɗe idanuwanka ka gani Fiddou ce hwa ba Amrah ba."
Bai ma san tana yi ba, sai a hankali ta jawo abin rufa ta rufe shi cike da tausayi, ta kama hanyar komawa zamanta za ta zauna.
Jin sallamarsa ta yi ya shigo, hannunshi da leda babba, ya ƙarisa shigowa cikin ɗakin.
Da fara'arta ta amsa masa sallama, ta fasa zaman har sai da ya iso inda take.
"Sannu Fiddou! Ya giɗe yaƙ ƙara ji da jiki?"
"Da sauƙi dai."
Ta furta haɗe da gyaɗa kanta, hawaye na neman fara kwaranya daga idanuwanta.
"Ya isa giɗe ba kuka nat tambaye ki ba. Insha Allahu yana samun lahiya ba da jimawag ga ba. Kuma na tabbata likita zai ba shi kula yanda yak kamata. Ki kwantar da hankalinki."
Shiru ta yi da kukan, sai dai kuma hawaye bai daina fita ba. Tausayinsa take ji. Ko kaɗan ba za ta taɓa iya jurewa ba, ba za ta iya yarda da maganar Dr. Huzaif ba.
"Mahmouda ba na tunanin Modu zai warke. Likita da kai nai yac ce giɗe ga shi yana cikin yanayin matsala. Ka gan shi nan hwa barcin wahala ne yake. Ciwo yad dame shi, likita yai yi mai allurar barci. Yanzu kana ganin wanda zai warkewa ne ba zai taɓa samun sauƙi ba sai idan yana barci?"
Shiru ya yi Mahmouda. Ko kaɗan ba ya son ya ƙara tasar mata da hankali ne. Amma fa ko shi ba ya ba Modu tashi. Babbar matsalar da abin ya shafi zuciya; yana da wuya wanda zuciyarsa ta samu matsala ya tashi, sai dai idan dama ba daga zuciyar ba ne, saboda wasu matsalan ƙirji ne kawai suke fama da shi sai su ce zuciyarsu na ciwo, alhali in zuciya ce ma ba za su faɗa ba, sai dai a gane.
A tsayen da suke suka fara ganin Modu na motsawa, yana ƙoƙarin buɗe idanuwansa da suka gama kumbura tsabar kuka.
Da hanzarinta ta isa gare shi tana ambaton sunanshi,
"Modu..."
Ta zauna a bakin gadon haɗe da taimaka masa wurin tashi.
"Sannu Modu. Yanzu kam nan ɗin ka ya bar ciwo ko?"
Ta gwada masa saitin da tata zuciyar take.
Baki kawai ya washe mata yana bin ta da kallo. Murmushi ta sakar masa sannan ta miƙe tsaye.
"Nurse ta ce idan kat tashi in hwaɗi mata. Za a yi maka gwajin zuciya. (Electrocardiogram (ECG) )"
Barin ɗakin kawai ta yi, ta nufi nurses station.
Bayan ta sanar da nurse ɗin ne ita kuma ta samu likita ta faɗa masa. Izini ya bayar cewa ta je da wasu daga cikin nurses maza, a je da Modu electrocardiograph room (ɗakin da injin ɗin yin ECG yake) don yi masa aikin yanzu.
Hakan ce kuwa ta kasance. Sai da suka haɗa da dabara kafin Modu ya yarda ya ɓaɓɓako daga bisa gadon, jin sun ambaci sunan Amrah; da duk iya taurin kansa in dai aka ambaci wannan suna, to fa tabbas zai aikata duk abin da aka umurce sa.
A bisa ƙafafuwansa yake taku, akasin tunaninsu kenan. Su a tsammaninsu ma ba zai iya yin tafiyar da kanshi ba, dalilin ma da ya sa likitan ya haɗa da maza kenan. Amma da mamakinsu, ambatan sunan wata mace ya saka shi dauriya haɗe da yin tafiya da kansa.
ECG room ɗin suka nufa kai tsaye, a buɗe suka tarar da shi, Technician ɗin da zai masa gwajin suka samu har ya shiga ciki, su kawai yake jira.
A bisa gado suka kwantar da shi, nan take ya fara ƙoƙarin yi masa gwajin, da na'urar yin aikin. Bai fi minti biyar zuwa goma ba ya kammala, saboda dama ba wani ɗaukar lokaci ake wurin yi ba.
Bayan an gama ya je ya ma likitan magana cewa ya kammala, sai ga shi kuwa har room ɗin ya zo ya zauna a bisa kujera, Technician ɗin kuma ya fita ya bar shi da result ɗin a hannu. Shi kanshi ya yi mamakin result ɗin na Modu; yanda ya tsammani ciwon kwata-kwata ba haka yake ba. Ashe ma bai wani ta'azzara sosai ba. Abin da ya sa Modu ɗin yake yawan jin ciwon, saboda abin ya shafi zuciya ne, ita zuciya kau ko kaɗan ba ta son baƙon abu, duk yanda wani abu ya nemi kawo mata tangarɗa, fat ɗaya za ta iya aika mutum lahira.
Hamdala ya yi bayan ya zauna. Kwance yake Modu idanuwansa a rufe, Dr. Huzaif na bin sa da kallo.
Riyawa yake a ransa akwai magunguna manya guda biyu, wanda ya tabbata ko su kaɗai sun isa su kawo waraka ga zuciyar Modu. Bayan haka kuma, zai ƙoƙarta kyautatawa haɗe da faranta masa, zai barsa da zama a asibitin na wani lokaci ba tare da ya ba shi sallama ba, dan ya samu kula mai kyau. Dan da ganinshi an san ba wani galihu ne da shi ba, ita kanta Fiddou ɗin ba lokacin kula da kanta sosai gare ta ba, to bare kuma Modu mai larurin da dole sai an yi taka-tsan-tsan.
Jijiyoyin da suke aika jini zuwa zuciyar Modu ne suka ɗan samu tangarɗa, sai kuma wadda ke kai jini har ciki kidneys ɗinsa. Kuma duk fargabar ko kuma damuwar wani abu ce ta haddasa hakan.
PA ɗinsa ya ƙwala ma kira ya zo, ya aike shi ya kira masa Fiddou. Babu jimawa sai ga ta ta zo, hankalinta a tashe, fargabar abin da za ta ji daga bakin likitan kawai take.
Wurin zama ta nema bayan ta yi sallama ya amsa, ta tsurawa inda Modu yake idanuwa, tana kallon yanda ko motsi ba ya yi.
"Uhm..."
Ta jiyo shi ya yi gyaran murya, alamun yana da buƙatar karkatowar hankalinta gare shi.
"Duk yanda na tsammani ciwon ba haka yake ba. Yau kam za ki ji hwarin labari daga gare ni."
Ya faɗa haɗe da kanne mata ido ɗaya.
Duk da ta ji daɗi sosai a zuciyarta amma ba ta bayyana masa ya gane ba, saboda haushinsa da take ji. Nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke kuwa ita ta tabbatar masa da cewa ta matuƙar jin daɗin furucinsa.
"A cikin kashi ɗari na zuciyar Modu, kashi talatin da biyar za a iya cewa ya gurɓata, ma'ana shi ne yake masa ciwo. Kashi sittin da biyar na zuciyarsa lafiya lau take. Wannan kashi talatin da biyar ɗin ne yake damunsa, shi ne yag gagara daidaita tafiyar numfashinsa, da kuma bugun zuciyarsa yanda ya kamata. Magunguna ne zan rubuta mai, wanda nake da yaƙini da amincewar Allah in dai ya yi anhwani da su tabbas zai samu waraka, zuciya tai za ta koma aiki yanda aka son ta yi."
Ya dakata daga nan, ya ɗan juyar da kallonshi zuwa ga Modu, sannan ya sake kallonta ya ce,
"Matsala guda ɗai ce..."
"Da ma na sani walle. Dole dai sai ka tayar min da hankali. Wai dan Allah kai wane irin likita kake?"
Murmushi ya yi wanda har sai da fararen haƙoransa suka bayyana. Ya ɗan tauni leɓonsa na ƙasa, ya lumshe idanuwansa duka biyun, sannan ya buɗe su a fuskar Fiddou.
Duƙar da kanta ta yi ƙasa, tana mai jin takaicin ha ido da shi, saboda muguwar tsanar da ta masa.
"...matsalar ita ce, magungunan suna da tsada sosai, dole sai an fitar da maƙudan kuɗi wurin siyansu."
Dafe gabanta ta yi da jin kalamansa. Lallai kuwa matsala mai girma. Ita yanzu ya za ta yi ta samu kuɗin siyan wannan magungunan? Ta kanta take.
"Duk kati guda yana kai sefa dubu ɗaya da ɗari biyar, kuma sai ya sha a ƙalla kati huɗu. Gudan shi ne ad da sauƙin kuɗi; yana kai saifa ɗari takwas, kuma shi kati guda ne zai sha. Insha Allahu matuƙar ya sha wannan magungunan a kan tsari, giɗe zai samu lahiya, matsalar zuciya kuwa sai dai wata ta taso, ba dai wadda yake kan yi yanzu ba."
Sosai da ji daɗin maganarsa ta ƙarshe. Har da murmushin farin ciki ta saki. Sai dai kuma ba a nan gizo yake saƙa ba, a ina za ta samu wannan maƙudan kuɗin wanda za ta siya ma Modu magani? Ta dafe kanta, zuciyarta na jefa ta wata duniyar ta daban, ba tare da ta san ta isa ba.
"Jinkirin siyansu kuwa, tabbas zai iya dagula komai, ciwon na shi ya kai inda ba za a ji daɗi ba. A yanzu haka bugun zuciyar Modu a hankali a hankali yake tafiya, saboda wanann jijiyoyin da ba su aika jini yanda ya kamata (blood vessels).
Wannan matsalar da kike ga kamar ƴar kaɗan, tsaf za ta iya dagula komai. Kin ga a yanzu haka yana fama da matsalan ciwon ƙirji, wanda duk waccan matsalar ce sila. Sannan kuma numfashinsa ba ya tafiya yanda ya kamata. Irin wannan matsalar takan haddasa yawan ƙunci, da mutum ya ringa tunanin ya kusa mutuwa, dan ma dai shi ɗin ba hankalinsa ɗaya ba. Tana saka yawan gajiya; ki ji ko ba abun gajiya kika yi kina yawaita gajiya, komin ƙanƙantar abu. Za ta iya saka wa ki ringa jin nauyi sosai a ƙirjinki, kamar an ɗaura miki wani nannauyan abu, wanda ba za ki iya sauke shi ba."
Ya ɗan dakata daga nan, sannan ya ci gaba,
"Dole zai daina cin duk wani abu wanda ya shafi cholesterol (masƙi) na tsawon wani lokaci, har mu ga yanda Allah zai yi da shi. Akwai wani mai na nan na musamman non cholesterol ne, ko abinci zai ci da shi ya kamata a yi amfani wurin girkawa. Kar ya sha madara, gyaɗa, mangyaɗa, manja, nono da sauransu, duka dai zan rubuta miki a takarda idan na koma Office. Magungunan da za a nema shi DIXOGIN yana taimakawa ne wurin aika jini, ya isa cikin gaggawa, kamar yanda ya kamata ya tafi, zai improving blood circulation. Shi kuma DIURETICS yana taimaka ma magudanyar zuciya zuwa ƙoda ne, ya taimaki ƙoda wurin tace gishiri da kuma suga wanda ba a buƙata, it makes it easier for your heart to pump. These medicines are very important."
Ya yi shiru daga nan, yana karantar yanayinta mai cike da tsantsar tashin hankali mara misaltuwa.
Kallonsa kawai take, ba ta san sanda hawaye suka fara wanke mata kumatu ba. Bayanan nasa ma jinsu kawai take, ba wai komai ne take fahimta ba, musamman ma da yake faɗo mata kalmomin da tunda take a rayuwarta ba ta taɓa jin su ba. Ita daga Hausarsu sai French wanda ba za a rasa ba kawai take ji. Shi kuwa dama a US ya yi karatunshi, ba zai taɓa iya magana ba dole sai ya sirka turancin, saboda ba komai ne zai ce ya sani da French ko kuma Hausa ba.
***
Ku ma page ɗin nan kyakkyawar fahimta, wata ƙila zai ma da dama daga cikin masu karatu amfani nan gaba.
Na gode, na gode, na gode ƙwarai masoyana. Har ma ban san da bakin da zan gode muku ba. Ina yin ku, ina son ku, ina ƙaunar ku fi sabilillah.
To Gosties👿 kun san kanku, ehen...kuna discouraging ɗina. Shin aikin wahala ne dan ka danna wannan ƴar tauraruwar kawai don ka faranta min rai? Ina tsananin jin daɗin in ga an yi voting, sai in ji ƙarfin guiwar yin typing kodayaushe😁
Duk wacce ke son na yi posting gobe ta ɗaga hannunta. Idan na ga yawanku zan maku, idan kuma na ga babu votes, alamun dai ba kwa son post gobe ne.😎
Me kuke hasashe? Shin yaya Fiddou za ta yi da wannan bawan Allah, wanda yake da buƙatar taimako a halin yanzu? A ina za ta samu kuɗin siya masa wannan magungunan? Ɓangaren su Maryama kuwa, ko kuna hangen nasara a tattare da lamarinsu? Idan sun yi wancan plan ɗin ya ɓaci, shin kuna tsammanin za su dace a wannan? Drop your comments, and then forward it to family and friends🙌
PINKY DURLING
RAZ 2
[8/30, 3:52 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
4⃣0⃣
Follow me on wattpad: PrincessAmrah
***
Tashi ta yi jiki babu ƙwari, hawaye bai daina kwaranya daga idanuwanta ba, tunani fal a cikin zuciyarta. A hankali take taku har ta isa ɗakin Annur, wanda ta baro Mahmouda a cikinsa.
Ganin yanayinta da ya yi kawai ya tabbatar masa cewa ba lafiya ba. Kuka take wiwi, har da shessheƙa sosai, hannuwanta duka biyu a ka.
A rikice ya miƙe tsaye, ya fara gyaɗa kansa, cike da tausayi ya ce,
"Ki bar kuka giɗe, Allah'n da Ya halicce shi ya hi mu so nai, idan kuma ya tahi ne, to tabbas lokaci nai ne ya yi. Ina gudun kar a yi biyu, ke ma ki kamu da wani ciwon."
Rijif! Ta faɗa ƙasa da ƙarfi ta zauna. Kanta ta haɗe da guiwowinta, tana ƙoƙarin shanye kukanta.
"Ya jiki nai? Halan dai da rai nai? An ƙare wancan awo?"
Duk a jere ya sako mata wannan tambayoyin.
Da ƙyar ta samu ta ɗago kanta, cikin sanyin murya ta ce,
"An ƙare wancan awo yana can yana barci, saboda waccan allura ta barci da aka yi mishi ba ta ƙare saki nai ba."
Da mamaki ya ce,
"Ah, to mi da kike kuka halan?"
Haɗiye sabon hawayenta ta yi, ta ce,
"Likita ya hwaɗi min magungunan da za a sai ma Modu, wanda siyan su ɗai ne zai sa Modu ya samu sauƙi. Suna da tsada sosai, ko ni ban