Showing 195001 words to 198000 words out of 201092 words
Chapter 66 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
dayake nawan sun so su yi yawa, Mama ta siya kuma sai ga gifts da akaita samu na frames ɗin. Sai a ɗauki ko guda uku a tafin mata da su."
Annur ya ce,
"To masha Allahu. Hakan za a yi. Ɗazu a mota bayan an ɗauko mu daga Airport Uncle Marwan ke ce min wai dole sai na miki lefe. Saboda ba wani abun kirki ne a cikin wanda ya yi ɗin ba. To Momy dai ta ce in bari ba sai na yi ba, za su yi komai a kawo miki. Ni dai na ga cancantar na yi miki ɗin, zan kuma yi insha Allahu sai ki haɗa duka. Dady kuma ya ce zai yi ƙoƙari a ci gaba da wannan ginin na jikin namu, part biyu ne a cikinsa, amma da ƴar tazara a tsakaninsu, sai mu zauna ni da Salman idan ya yi aure."
Cikin jin daɗi ta ce,
"Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya. Allah kuma ya bar mu tare har ƙarshen rayuurarmu. Allah ya kawo ranar da zan haifa mana little Amrah."
"Amin."
Ya faɗa a daidai isowarsu bakin gate. Horn ya yi mai gadi ya buɗe musu gate ɗin suka shige.
Dama sun yi sallolinsu. Kai tsaye bedroom kawai suka wuce saƙale da juna.
"Yaya ka samu ka watsa ruwa. Ni ma zan je ɗakina na watsa ko zan ji daɗi a jikin."
"Ki je ina?"
Ya ƙwalalo ido yana kallon ta.
"Dakina mana."
Ta ba shi amsa haɗe da tunzuro baki.
"Ai malama ki ɗauka cewa wanan ɗakin naki ya zama ɗakin baƙi. Kayanki ma duk kwaso su za ki yi ki dawo da su nan. Shara kawai za ta rinƙa kai ki can. Bari ma ki ga."
Ya kama hannunta suka nufi toilet ɗin. Sai ta tuno ranar farko da ta fara yi masa wanka. Ta runtse idonta tana sakin murmushi.
Bayan sun gama suka fito a cikin towel ɗaya. Mai suka shafa sannan suka miƙe a tare ta fitar masa da rigar barci. Sai da ta saka sannan ta ce da shi za ta je ɗakinta ta ɗauko kayan barcin ita ma. Doguwar riga ce ta sako wacce iyakacinta bisa guiwa. Yadinta santsi gare shi irin mai kwnaciya a jikin nan. Ga wata irin humra da ta shafa wacce Islam ta kai mata yau. Sai duk ko'ina ya game da ƙamshin humrar.
Ta same shi ya zauna bisa stool ya dumtse hannunsa na dama. Murmushi ta saki bayan ta iso gare shi. Ya kama hannunta na hagu. Yatsar kusa da ƴar ƙarama ya kama, ya buɗe hannun nasa ashe zoben nan ne a ciki. Ta bi shi da ido har ya zura mata zoben.
"Haƙƙin Amrah ne, amma mahaifiyarta ta ba ni kyautarsa. To ni ma na ba ki kyautarshi da zuciya ɗaya. Ina so ki ɗauka cewa ke kaɗai ce a zuciyata idan har aka cire Amrah da ta daɗe a ciki tun ina yaro. To ki saka a ranki ƙaunar da nake yi ma Amrah ba komai ba ce a yanzu, tunda dai ta tafi babu ita. Ke ɗin dai ce, zan kuma ci gaba da ƙaunar ki har ƙarshen rayuwata."
Tsabar jin daɗi ba ta san sadda ta rungomo shi ba tsam-tsam a jikinta. Numfashi take saki, tana jin yadda ƙaunarsa ke ƙara shiga cikin zuciyarta. A nashi ɓangaren ma haka ne. Daga nan sai suka faɗa duniyar soyayya.
A gida kuwa tun bayan tahowar su Annur Momy ta shige ɗaki tana kuka sosai. Tana jin yadda soyayyar ɗanta da ya rasu ke daɗa wanzuwa a cikin zuciyarta. Dady ke ta rarrasarta yana ba ta baki har ya samu ta yi shiru.
Washe gari
Misalin sha ɗaya na safe Maryama na kitchen ita da Annur suka ji knocking.
"Mallam ka ƙyale ni in dubo mai knocking please, ka wani ƙanƙame ni duk ka hana ni saƙat wallahi."
Annur ya ce,
"Su ma dai baƙin, su rasa lokacin zuwa sai irin wannan da nake jin daɗin kasancewa manne da ke?"
Ta gyaɗa kanta.
"Please mana yah Noor. Babu fa daɗi mutum yaita tsayuwa ba a buɗe masa ba."
"Aunty masifa na ji to. Je ki, amma ki yafa mayafi."
Ba ta ko tsaya saurarar sa ba ta doshi falo. Sai da ta fara saka hijabinta sannan ta isa ta tambaya waye. Muryar mace ta ji ta ce,
"Maƙoftanku ne da suka dawo shekaranjiya."
Da sauri Maryama ta buɗe ƙofar. Kyakkyawar mace ta gani tsaye da mijinta, sai kuma wasu yara guda biyu babba da ƙarama.
Murmushi ta sakar musu haɗe da ba su izinin shigowa har da mijin.
"Sannunku da zuwa. Last week fa na ji ana ta kawo kaya, ashe ku ne kuka dawo gidan."
Matar cikin sakin fuska ta ce,
"Wallahi kuwa mu ne. Yau kwananmu biyu da dawowa ai."
"Ah to masha Allah. Ƴan yara sannunku."
Ta kama hannun babbar.
"Good morning Mama."
Yarinyar ta faɗa cikin ladabi har da rusunawa.
"Morning my dear. Ina zuwa."
Ta miƙe. Kitchen ta nufa ta same shi. Ta ɗika masa duka.
"Mallam ai sai ka fito mun yi baƙi. Sabbin maƙwaftanmu ne har da mijin duk na ce su shigo."
"Ok to bari in je."
Ya fita. Ita kuwa lemuka ta jera a tray ta fita da su.
Hannu ya ba namijin suka gaisa. Sannan matar da yaran duk suka gaishe shi.
"Ga lemu nan ku sha."
Maryama ta faɗa tana murmushi.
Matar ta ce,
"Wallahi mun gode. Ai dayake safiya ce, karyawarmu kenan."
Mijin ne ya yi magana cikin sakin fuska.
"Ni sunana Khalid, matata kuma Ikram (Wanda ya karanta littafin SHI NE SILAH zai san su) waƴannan kuma yaranmu ne, Feenah da Ummu Ruman. Ina so mu ƙulla zumunci, tare da riƙe amanar juna."
Annur ya murmusa.
"Insha Allahu kuwa. Daga yanzu ka zama abokina Khalid. Ikram ma kuma ta zama ƙawar Maryama. Zumunci ya ƙullu kenan har abada."
"To masha Allahu."
Khalid ɗin ya faɗa.
Sun ɗan jima suna taɓa fira kafin Khalid ya ce su tashi su tafi rana ta yi. Sosai Maryama da Annur suka nuna jin daɗinsu, sannan suka yi musu alƙawarin za su shigo su ma da izinin Allah.
Washe gari
Bayan sun gama karyawa Annur ya ce da Maryama ta shirya yau su tafi Maraɗi. Saboda ya fi son a yi komai kan lokaci, duk da dai cewa Hadizar ta ce da Maryama ta amince amma dai ya kamata su yi maganar face-to-face. Tana cikin shiri Jiddah ta kira ta cewa ga ta nan ta zo tana knocking a buɗe mata. Da farin-ciki Maryama ta je ta buɗe mata ƙofar.
Zama suka yi fara'a ƙunshe a fuskokinsu suka gaisa. Ledar hannunta ta miƙa wa Maryama cewa kayan saka ranar su ne ita da Deedah. Tun shekaranjiya Abba da Kawu Imrana suka kai kayan. Maryama ta kumburo fuska.
"Yanzu don Allah sai a kai kayan saka rana amma a rasa wanda zai faɗa min? Ko da safen nan fa sai da na yi waya da Abba da Mama. Dama na ji Hammad na neman faɗa min wani abu kuɗin wayar tawa suka ƙare kuma bai kira ba. Ashe ƙawata amarcewa za a yi. Yaushe ne auren?"
Jiddah ta ce,
"Wata ƙila zance ne bai kawo ba. Yanzu dai ai ga shi nan kin ji daga gare ni."
"Na ji kam. Yaushe za a yi ba ki faɗa min ba."
"Wata biyu ne aka saka."
"To Allah ya nuna mana."
"Amin ya Allah. Ina Yah Noor da jiki?"
Maryama ta yi murmushi.
"Yah Noor kam alhmdulillah. Bari in kawo miki shi ku gaisa."
Ta tafi ɗakinsa. Labari ta ba shi sannan ta kamo hannunshi suka dawo falon.
Tana ganin shi sai ta ga duk ya mata ƙwarjini, saboda duk wannan yaƙen da yake yi a baya babu shi yanzu. Ga kyau da ya yi sosai kamar ba shi ba. Ta gaishe shi. A maimakon ya sakar mata dariya kamar yadda ya saba yi idan an gaishe shi sai ta ga akasin haka.
"Lafiya lau Jiddah. An zo lafiya ya su Mama?"
Cikin mamaki ta ba shi amsa da lafiya lau. Maryama kanta ta san cewa Jiddah mamaki ne ya cika ta. Annur ya kalle ta da murmushi.
"Baby your friend is suprised. Zan shiga ɗaki, explain everything to her."
Ya ba ta peck a hannu, sannan ya nufi ɗakinsa. Jiddah ta bi shi da kallo har ya shige ɗaki.
Maryama ta dawo kan kujerar da Jiddah take, ta zauna bisa hannun kujera. Nan ta labarta wa Jiddah duk yadda abubuwan suka faru. Sai ta riƙe baki cike da mamaki.
"Maryam kina nufin duk zaman nan wai Yah Noor ya warke kallon mu yake kyar?"
Kai Maryama ta ɗaga mata.
"Ba ma wannan ne abun mamakin ba. Wai Farouk Sardauna dai da na sani shi ne ainahin ɗan su Momy? Dama dai gaskiya akwai alamar tambaya. A ce tsakanin Sans da Annur babu wani bambanci kamar su ɗaya. Ba zai yiu a ce coincident kawai ba ne. Dole sai identical twince ne za su yi irin wannan kamar."
"Haka ne kam. Kin dai ji yadda Allah ke tsara al'amarinSa."
Miƙewa Jiddah ta yi.
"Ni zan tafi Maryam, akwai wuraren da zan je idan na koma gida."
"Ke don Allah Jiddah tun yanzu?"
Jiddah ta ce,
"Zan dawo ai kar ki damu. Amma fa ina son jin kyakkyawan labari in the next two weeks."
Harararta Maryama ta yi, ta raka ta har bakin ƙofa, ta shaida mata cewa Maraɗi ma za su tafi yanzu.
"Aikuwa kun kyauta sosai wallahi. Please ki gaishe min da Fiddou, ki ce ina mata fatar alkhairi. Hadiza kuma idan komai ya tabbata insha Allahu da mu za a yi biki."
"To zan faɗa musu insha Allahu. Ki gaishe da su Mami."
*
Misalin ƙarfe biyu da rabi suna cikin garin Maraɗi. Hadiza ta faɗa musu inda za su yi mahaɗa, suka ɗauke ta. Kai tsaye gidan Fiddou suka fara zuwa.
Bayan Annur ya faka motar a ƙofar gida Hadiza ta fita da frames da Maryama ta ce mata ta ɗauka a bayan motar. Kafin Maryama ta fita ya ce
"Ki gaishe ta. Idan kuma mijinta ya bada izini sai in shigo har ciki na musu godiyar da kaina."
Maryama ta ce masa to, sannan ta ɗauki hand bag ɗinta ta fice.
A falo suka same ta kwance ƙasa, Mahmouda na yi mata fifita. Sallama suka yi, ya amsa haɗe da ɗago kai ya kalle su. Bayan sun shigo ciki suka zauna, da sakin fuska ya amsa gaisuwar da ya musu, kasantuwar bai san Maryama ba, Hadiza kawai ya sani.
"Barci ma take yi ko?"
"Walle kam ba ta da lahiya ne. Daga asibiti ma muke."
Hadiza ta yi dariya ta ce,
"Hala dai ta kamu ne."
Dariyar shi ma ya yi,
"Ba ki gajiya Hadiza."
"Aikam tashin ta za ka yi. Baƙi ne ta yi tun daga Katsina. Maryama da kuma mai gidanta Annur yana waje cikin mota shi ya kawo mu."
Ba zai taɓa manta duka sunayen biyu ba. Saboda har gobe suna da daraja sosai a zuciya da kuma bakin Fiddou. Sau da dama takan ambaci sunayen a duk sadda wani abu zai faru mai kama da nasu. Sai ya saki murmushi.
"Ahh sannunku da zuwa. Halan mi da bai shigo ciki ba? Bari in tai in shigo da shi. Fiddou!"
Ya bubbuga ta ta tashi. Murtsukar idanuwa ta fara yi.
"Sahibi mi kuma?"
Murmushi ya sakar mata.
"Baƙi kika yi."
Ta tashi zaune shi kuma ya nufi waje domin kiran Annur.
Tana haɗa ido da Maryama ta ƙarisa murmurewa. Ta saki baki da ido tana kallon ta.
"Wata nake gani kamar dai Maryama."
"Ni ce fa da kaina mai ciki."
Harara Fiddou ta kai mata.
"Babu ko gaisuwa sai tsokana ko?"
Hadiza ta ce
"Babu wani tsokana sai gaskiya. Malama ki ga yadda kika koma, ko mutum bai san mai ciki ba ya gan ki sai ya gane. Mu dai Allah ya raba lafiya mu samu ɗa ko ƴa."
A daidai nan Mahmouda ya shigo riƙe da hannun Annur suna dariya.
Fiddou na haɗa ido da shi sai da ta yi mamaki. Ba ta bar maganar a zuciyarta ba sai da ta tambayi Maryama.
"Halan dai Modu ya warke Maryam?"
Maryama ta ɗaga mata kai tana murmushi.
"Ya warke Fiddou. Hadiza ba ta faɗa miki aurena da shi ba?"
Ta gyaɗa kai.
"Ta dai hwaɗi min ana aurenki rana guda da nawa. Amma ba ta hwaɗi min Annur za ki aure ba."
Maryama ta ce,
"Aikuwa shi na aura Fiddou. Ga shi nan kuma ya warke garas kamar bai taɓa yin wani ciwo ba. Abin da ya sa muka zo dama godiya za mu sake yi miki, shi ma kuma ya miki da kansa."
Annur ya yi murmushi, ya ce,
"Haka ne. Malama Fiddou ya gida ya ƙarfin jiki? Mallam Mahmoud ya ce min daga asibiti kuke."
Cikin kunya ta ce,
"Alhamdulillahi."
"To masha Allah! Duk da dai ban san ta inda zan fara ba, addua ce kawai daidai da ke. Allah ya saka miki da alkhairi Fiddou. Kamar yadda kika taimake ni ke ma Allah ya taimaka miki har ƙarshen rayuwarki. Allah ya dauwamar da farin-ciki a rayuwar aurenku. Allah ya ba ku zuria mai albarka."
Mahmouda ya amsa da,
"Amin. Ai babu komai Annur."
Ruwa ta kawo musu suka sha sannan suka miƙe cewa za su tafi gidan su Hadiza. Bankwana suka musu sannan suka kama hanyar gidan na su Hadiza.
Tare suka fita daga motar, Hadiza na gaba suna biye da ita har suka shiga cikin gidan.
Yayanta suka nemi ganawa da shi. Bayan sun gaisa Annur ya masa bayanin abin da ke tafe da su. Karara ya nuna jin daɗinsa. Saboda yawon ta-zubar ɗin da Hadizar ta yi a baya, amma cikin ikon Allah dama ta nadama ta dawo har ta yi istibra'i, mijin auren ake nema. Don haka duk sadda suka shirya kawai su zo a ɗaura aure, babu buƙatar ɓata lokaci tunda dai ba aure ba ne za a yi kamar irin na ƴan mata.
Annur ya ji daɗi sosai, ya ce insha Allahu iyayensu za su zo bai ɗaya a ɗaura auren a tafi da amarya. Godiya suka masa sosai sannan suka miƙe. Hadizar ta raka su har mota ita da yayanta, suka tafi suna jinjina halin karamci irin na mutanen.
*
Doya da ƙwai take soyawa, amma ji take zuciyarta na tashi, kamar ba ta son warin ta. Famar doɗe hanci ta kama yi, amma sai tsananta abin ke yi. Annur da ke daidai shigowa kitchen ɗin ya ce,
"Baby lafiyarki kike famar doɗar hanci?"
Ba ta buɗe hancin ba ta ce,
"Wallahi ƙamshin doyar ne ba na so."
"To fa! Ko zazzaɓin ne har yanzu?"
"Na ji sauƙin zazzaɓin Baby. Da shirin tafiya lecture ma nake yi wai nan. Tashin zuciya ce kawai nake ji, kuma ƙamshin ne da ba na so..."
Tun ba ta rufe baki ba ta ji amai ya taso mata. Da gudu ta isa wurin sink ta hau kwara amai. Ba wani abun kirki ba ne ba a cikin dama. Guntun doughnut ne da yoghurt da ta yi sammakon sha, saboda yunwar da ta tashi da ita.
Da hanzari ya isa gare ta yana mata sannu. Take daga yin amai duk sai ta galabaita. Ya kamota ya riƙo bisa jikinsa. Yana ƙara ce mata sannu wani aman na zuwa, a jikinsa ta ci gaba da kwara shi. Bai ji ƙyama ba ko kaɗan, sai ma tausaya mata da ya yi sosai, ya hau yi mata sannu.
Ƙauri ya ji alamar doyar ta soye har man ma ya gama yin baƙi. Ga kuma Maryama a jikinsa. Da sauri ya ɗauke ta ɗaf, ɗayan hannunsa ya sa ya kashe gas ɗin sannan ya nufi toilet ɗin ɗakinsa da ita.
Rigar jikinta ya cire mata, ya wawwanke mata baki da wuyanta sosai da sabulu sannan ya ɗauro mata towel ya kwantar da ita bisa gadon sa. Banda sannu babu abin da yake mata. Tausayinta yake yi sosai, yana ji kamar ciwon ya dawo a jikinsa.
Kayan nata ya ɗauka ya fita da su can corridor ya jefa a washing machine ya wanke sannan ya cire rigarsa ma ya wanke.
Dawowa ya yi ya fiddo mata rigarsa long sleeve ya saka mata. Sannan ya ɗauko wani skirt nata na English wears ya saka mata yana yi yana ce mata sannu. Jin wayarsa ya yi tana ƙara. Da sauri ya duba mai kiran ya ga Salman ne.
"Ango lafiya dai ko?"
Ya faɗa cikin muryar gajiya.
"Lafiya ƙalau Annur. Wani aiki ne ya taso a Office yanzun nan Mu'azzam ya kira ni. Ya ce min kuma kai ma ba ka je ba."
Annur ya ce,
"Wallahi na yi shirin tahowa to kuma Maryam jikin babu daɗi. Asibiti ma zan kai ta yanzu.
"Subhanallahi! Me ya same ta?"
"Zazzaɓi ne dai take ta fama da shi kusan five days back, to yanzu dai abun ya yi worst, ba ta da wani ƙarfi sosai."
"Ya salaam! Gaskiya ka gaggauta kai ta asibiti. Bari in kira Mu'azzan ɗin a tsayar da aikin har zuwa gobe idan Allah ya kai mu. Allah ya kyauta ya ba ta lafiya."
"Ameen Salman. Ka gaishe da Hadizar."
"Za ta ji."
Ya faɗa haɗe da tsinke wayar.
Mukullin motarsa ya ɗauka ya je ya buɗe ta ya sa mai gadi ya buɗe masa gate, sannan ya koma ya cicciɓo ta. Wayarsa da tata ya ɗauko sannan ya datse ƙofar bayan ya kwantar da ita a kujerar gaba.
K-Dara Specialist Clinic suka nufa. Sai da aka fara buɗe mata kati sannan aka tura ta layin ganin likita. Har a lokacin tana kwance a jikinsa, sannu yake ta yi mata. Ana zuwa kansu ya kama ta suka shiga. Likitan ya nemi sanin abin da ke damun ta Annur ya masa bayani.
Takarda ya basu cewa a je a yo awon fitsari da na jini. Ganin yadda jikin nata ya galabaita sosai ya sa ya ce dole za a ba ta gado a saka mata drip don walwalarta ta saitu. Nurses ya kira suka kai ta ɗaki, amenity aka kama mata Annur ya biya, aka yi mata duk gwaje-gwajen da suka kamata.
Sai a sannan ya kira gida ya sanar wa Momy, sannan ya kira gidan su Maryama ma ya faɗa ma Mama. Yana gama waya da Mama Salman ya kira ya ji ya jikin? Ya ce da shi ma an kwantar da ita. Fatar samun sauƙi ya mata sannan ya ce anjima za su zo da amaryarsa Hadiza.
Bayan duk results sun kammalu likitan ya nemi ganinshi. A nan ya masa albishir da cewa Maryama na ɗauke da juna biyu na wata guda da sati ɗaya. Hamdala ya yi ga Allah cike da farin-ciki ya baro Office ɗin.
A hanya ya ci karo da Dady da Momy sun zo duk a ruɗe. Ganin sa da suka yi yana murmushi duk sai suka yi turus suna kallon shi. Momy ta ce,
"Ta ji sauƙi kenan ma."
"Ehh alhmdulillah! Mu je na kai ku ɗakin."
Suka bi bayanshi har zuwa amenity