Showing 117001 words to 120000 words out of 201092 words
Chapter 40 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
suka hau kansa, domin ba shi taimakon gaggawa.
***
Wani irin yammaci ne ta yi mai cike da ƙunci da takaici. Rayuwarta take tunani, da kuma makomar Annur. Idan har ta bari ta auri Deedah, ta tabbata ba za ta taɓa ci gaba da taimakon da ta ɗauko ba. Ta sani, Ahmad Deedah mutum ne mai tsananin kishi, wanda ba ma ga budurwarsa kawai ba, har ga ƴan uwansa kishi gare shi. Yana da ƙani mai suna Khalil, haushi yake ji ya ga yadda Maryama ke kula da Khalil, ko da kuwa gaishe shi kawai ta ce ya yi. Mugun kishi ya raba shi da budurwarsa Labibah. Mace mai tarbiyya da girmama na gaba da ita. Ta san darajar duk wani dangin Deedah. Sai da har iyaye suka shiga zancen, amma kawai mistakenly ya gan ta tsaye da namiji a school, zuciya ta ɗibe shi, har ya gaura mata mari. Wannan marin ne ya yi silar rabuwarsu, yanzu haka ma ta yi aurenta har da yaro guda ɗaya. To a haka ne za ta iya auren Deedah? Ina, ba za ta iya ba. Dole ma ta samu Abba da maganar, wala'Allah zai suarare ta, ya kuma dubi lamarinta.
A bisa tafukan ƙafafuwanta ta miƙe. Ji take tamkar duga-duganta za su tsattsarge tsabar gaza ɗaukar gangar jikinta da suka yi. Jikinta ya yi sanyi ƙwarai, ta kowacce gaɓa da ke jikin nata karkarwa take.
Cikin sanyin jiki ta runtse idanuwanta duka biyu, tana mai tsananin jin zafin duniyarta. Lallai rayuwa ta juye mata; daga farin ciki zuwa baƙin ciki. Zuciyarta ta dafe da hannunta na dama, ta ji yanda take duka da sauri da sauri, kamar ma ba daidai take tafiya ba.
Gyaɗa kanta ta yi bayan ta buɗe idanuwan, cikin rawar murya ta furta,
"Ba zan iya ba. Wallahi ba zan iya auren Yaya Deedah ba. Annur nake so, shi nake da muradin aure, koda hankali ko babu shi."
Ta faɗa bisa gadon ta ɗora fuskarta a bisa pillow, ruwan hawayen na sauka a bisa kyakkyawar rigar pillow ɗinta pink colour.
Sallar magrib ake kira, dama dalilin miƙewar da ta yi kenan, amma ta kasa controlling temper ɗinta. Kamar kar a fara mata maganar auren Deedah, ta ƙara jin bunƙasuwar soyayyar Annur a cikin zuciyarta. Ba tausayin Annur kaɗai take ba, sai yanzu ta ƙara tabbatar da hakan, har da soyayyarsa, wacce ke ɗawainiya da dukkan jiki da ruhinta.
Sake runtse idanuwanta ta yi, take hango murmushinsa, kalaminsa, da yadda yake ɗora yalwatattu idanuwansa a fuskarta. Annur bai da matsala ko kaɗan, ta sani. Kyakkyawa ne managarci, cikar zati da tausasshe murmushi. Damuwarsa kawai halin da yake ciki, wanda take sa ran taimakonshi duk tsiya duk rintsi.
Daurewa ta yi ta miƙe ta nufi ban-ɗaki, alwalla ta ɗauro sannan ta ƙoƙarta saita kanta, ta kabbarta sallar magrib. A bisa sallayar take zaune tana adhkar, tana ƙara sanar wa Allah damuwarta, tare da rokonSa mafita ta alkhairi. Sai da ta yi sallar isha sannan ta sauka daga bisa sallayar. Ta faɗa kan gadonta, tana tunanin kiran Dr. Hamdan.
Ba ta jin za ta iya magana da shi a wannan mood ɗin, to ma me za ta faɗa masa? Idan har ya ba ta appointment ɗin, yaushe ne za ta je Maiduguri ta kai masa Annur, bayan kuma ga zaɓin da iyayenta suka mata? Saurin kwaɓar bakinta ta yi, jin yana neman tabbatar mata da zaɓin na iyayenta. Ba fa za ta auri Deedah ba, haka take faɗi a ƙuntatacciyar zuciyarta, mai cike da ƙunci, tashin hankali da kuma fargaba.
Muryar Muhammad ta ji a saitin kunnuwanta yana faɗin,
"Yaya Maryama tun ɗazu nake miki sallama, ban san me ya sa ba ki amsa ba."
Fuskarta a tamke take kallonshi, ta gagara furta masa komai.
"Abba ne yake kiranki dama."
Ya faɗa cikin halin ko'inkula, haɗe da barin ɗakin da gudunsa.
Shi kenan, ta faru ta ƙare, an ma mai dame ɗaya sata! Ta tabbata maganar auren Deedah ce zai mata, dama Mama ta ce idan ya dawo zai tinkare ta da maganar da kansa, kuma idan har tana son farin cikinsu, to kar ta nuna ba ta so.
Wayarta ta jona jikin caji, sannan ta miƙe tsaye, dama ba ta cire hijabin jikinta ba kawai ta fice, ta nufi ɗakin Abbanta.
***
Ƙirjinsa ya dafe da dukka hannuwansa, tari yake iya ƙarfinsa, mai fitowa haɗe da jini. Tun yana yi bai galabaita ba, har abun nasa ya ci tura, ya galabaita sosai.
Sans (Fake Annur) da shigowarsa gidan kenan ya biya ta ɓangaren Mami ya gaishe ta, sannan ya wuto zuwa ɗakin Bobby.
A halin da ya same shi ne ya matuƙar tayar da hankalinsa. Cikin razana ya isa ga Farouk, ya ringa faɗin,
"Guy me ya faru? Jikin ne? Me ya sa ba ka je ka sanar ma su Mami ba? Tana can tana cewa ƙila ma ba ka gidan. Guy dole su Mami su san tsanantar da abun nan ya yi. Dole ne su san me yake damunka, da kuma silar cutar baki ɗaya. Wata ƙila su fidda kai waje. Amma zama haka ai ba zai yiwu ba."
Duk wannan surutan da Sans ke yi ma Farouk bai san yana yin su ba. Saboda tuni ya sume, yana sauke numfashi a sannu a sannu. Fahimtar hakan da Sans ya yi ya sa shi fita da sauri, har yana kai wa bango karo. A gujensa ya isa inda Mami, yana famar shessheƙa, hawaye na zirara daga idanuwansa.
Cikin kiɗima Mami ta ware idanuwanta ga Sans, bakinta na son yin magana amma ta gaza furta komai. Zuciyarta na ƙissima mata lallai akwai abin da yake faruwa.
Dadyn Farouk da ke ƙoƙarin fitowa daga ɗakinsa ne ya ga abin da ke faruwa, cikin tashin hankali ya ce,
"Annur me yake faruwa?"
Muryarsa rawa take sosai, da ƙyar ake iya gane abin da yake faɗi, ya ce,
"Dady...ga...Guy...uhm, Farouk can kwance, jikinsa ya yi tsanani sosai..."
Tun bai rufe baki ba Dady da Mami suka haɗa bakunansa wurin ambatar sunan Allah, haɗe da bin bayan Sans, suka nufi ɗakin Bobby.
A yadda Sans ya bar shi haka suka same shi, light blue shirt ɗin da ke jikinsa ta yi kaca-kaca da jini, ya yi kwanciyar ruf da ciki, saboda galabaitar da ya yi.
"Umar Farouk!"
Dadyn nasa ya faɗa, yana mai jijjiƙa jikinsa.
"Umar Farouk kar ka tafi ka bar ni, don Allah kar ka mutu, idan ka tafi ban san me zan faɗawa mahaliccina ba, na gaza cika alƙawarin Yayana da na yi, ga gaza riƙe amana..."
Kuka sosai yake yi Dady a wannan gaɓar, yana mai gyaɗa kansa, cike da tausayin Bobby.
"A kai shi asibiti Alhaji, ba kuka za mu tasa shi gaba mu yi ba."
Mami ta faɗa.
Cikin kuka Dady ya ce da ita ta je part ɗinsu ta ɗauko mukullin mota, kafin nan su kuma sun cicciɓe shi zuwa bakin motar.
Hakan ne kuwa ya kasance. Bayan sun kai shi mota Sans ya tuka motar, sai Mami a gaba, Dady kuma bayan motar ya ɗora kan Farouk ɗin a bisa cinyarsa, yana kuka sosai na tashin hankali.
Me ya sa ya kasa tarbiyyantar da amanarsa? Farouk amanar Alhaji Usman Sardauna ne. Amma me, ya kasa ba shi ingantacciyar tarbiyya. Ya kasa cika alƙawarin da yayansa ya bar masa.
Da haka suka isa Alheri Clinic, wanda shi ne asibitin kuɗi mafi kusa da gidansu. A gaggauce Sans ya faka motar, ya fito da gudunsa ya shiga asibitin, ya sanar cewa a zo da gado ko kuma keke, ga patient nan uncouncious.
Da gado aka zo aka ɗora Bobby, aka shiga da shi Emergency.
Zazzaune suke su duka ukun, kuka suke sosai, banda Sans da ya rafka tagumi, yana zancen zuci, saboda zuciyar tasa ma har ta bushe da zubda ƙwallan. Tunanin rayuwa kawai yake; duniya ta juya musu baya. Ashe dai haka duniya take? Lallai budurwar wawa. Duniya makaranta, wanda bai zo cikinta ba ma jiransa take. Munanan halayen da suka kasance suna aikatawa kawai yake tunani; mugun shaye-shayensu da neman mata. Hannunsa ya ɗora a ka, yana mai gyaɗa kansa. A zuciyarsa yana fatan kar Bobby ya mutu, kar ya tafi a haka ba tare da ya samu rabauta ba. Ya tabbata idan har ya mutu bai tuba ba, akwai damuwa mai girma. Ya sani, ya san hukuncin abubuwan da suka kasance suna aikatawa, saboda shi ɗin mai ilimi ne, duk wannan abubuwan sai dai ya sanar ma wasu. Amma me ya sa bai yi amfani da su ba? Me ya sa ya kasa zama mutumin kirki kamar yadda iyayensa suka ba shi tarbiyya? Son zuciya. Ya samu wannan amsar daga wani ɓare na zuciyarsa.
Har kusan ƙarfe sha biyu na dare amma ba a fito da Bobby daga Emergency ba, in short, ba ma su ji wani bayani daga gare shi ba. Jugum-jugum kawai suka yi, babu mai faɗin komai, sai zallar tashin hankali a tattare da su.
Wayarsa ce ta yi ƙara Sans. Ya zaro daga aljihunsa, yana gani biji-biji, da ƙyar ya iya gano sunan Momy ne maƙale a screen ɗin wayar.
Cikin saɓular jiki ya ɗaga kiran, yana mai kanga ta a kunnensa.
"Annur lafiya ba ka dawo gida ba har yanzu? Na faɗa maka za mu yi magana amma tun ɗazu nake zarya zuwa ɗakinka ba ka dawo ba. Wannan ƙawar tawa da muka fara maganarta a waya, tana son a ƙera mata kits ɗin nan, kuma sai kirana take, wai kar lokaci ya ƙure..."
Sassarfar kukan da ta jiyo Sans na yi ne ya sa ta dakatawa ba tare da ta kai aya ba.
"Me ya faru da kai?"
Momy ta furta cike da tashin hankali.
"Ga ni a asibiti Momy...Farouk Sardauna ne ba lafiya..."
"Inna lillahi wa innaa ilaihi raji'un! Me ya same shi? Ko tarin da ka faɗa min yana yi ɗin ne?"
Sai yanzu kuka mai ƙarfi ya samu nasarar kufce masa, wanda har sai da hankalin ƴan reception ɗin ya dawo gare shi.
"Shi ne Momy. Shi ne ya galabaitar da shi sosai. Yanzu haka tun ɗazu an shiga da shi, ba mu ji wani labari mai daɗi ba."
"Subhanallahi! Allah ya ba shi lafiya. Wace asibitin kuke?"
Ta tambaye shi cikin zallar tashin hankali.
"Muna Alheri Clinic ne Momy."
"To bari na ma Dadyn naku magana, ga mu nan zuwa yanzu insha Allah."
"To sai kun zo Momy."
Ya furta haɗe da tsinke wayar.
Minti talatin bayan gama wayar Sans da Momy wata nurse ta zo, cewa za su iya shigowa ɗakin yanzu, likita ya gama duba shi.
Da sauri suka mimmiƙe haɗe da nufar Emergency room, gado na biyu suka hango Bobby kwance, an saka masa Oxygen, ga kuma drip an maƙala masa.
Idanuwansa a buɗe suke kyam, yana zuba musu su, ya kalli wannan sannan ya kalli wannan ruwan hawaye ya fito.
Sannu kawai suke masa, Dady na faɗin,
"Ka yafe min Farouk, ni ne silar komai. Dr. Ya faɗa min Smoking ne silar ciwonka, wanda kuma duk ni na jawo. Ni na gaza baka tarbiyyar kirki, tun kana ɗan shekara goma sha huɗu ka fara shaye-shaye, kuma ban iya ɗaukar matakin shiryar da kai ba, duk da yake cewa Allah Shi ke da shiriya, amma mu ma muna iya zama sila. Allah Ya tashi kafaɗunka Umar Farouk. Allah Ya ba ka lafiya ka ji?"
Ya damƙe hannunsa na dama, yana bin sa da idanuwa.
Da tambaya su Momy suka iso ɗakin, su kansu cike suke da tashin hankali. Oxygen ɗin da suka ga an maƙala masa ne ya ƙarisa tayar da hankulansu. Ashe dai ciwon har ya tsananta haka.
Sama-sama suka gaggaisa, Dadyn Annur da Dadyn Bobby suka gaisa, ya masa ya mai jiki.
Haɗa ido Farouk Sardauna ya yi da Dadyn Annur, ya ɗan runtse idanuwansa, sannan ya furzo wasu zafafan hawaye, wanda shi kaɗai ya san raɗaɗinsu.
Ganin haka ya sa Dadyn Annur kama hannun Bobby gam ya riƙe, yana tofa mishi addu'o'i.
"Nas'alullahul-Azeem, Rabbul-arshil-Azeem, an Yashfiyaka."
Ya tofa masa ƙafa bakwai, sannan ya tofa masa
"La ba'sa ɗahuran insha Allah!"
Ƙafa ɗaya. Yana ƙoƙarin zare hannunsa daga na Bobby ya ji ya riƙe shi gam! Ba ya so ya zare hannun nashi.
Wata irin nutsuwa yake ji tana sauka mishi. Ko kaɗan ba ya so Dadyn Annur ya cire hannunshi daga cikin nashi, shi kaɗai ya san daɗin da yake ji. So yake ya yi magana, ya tona asirin ɓoyayyen ƙullin da suka tona rami suka binne, amma ina, abu ya faskara, ya kasa magana, ba ma zai iya ba. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa riƙe hannun wani bawan Allah ya samu irin wannan nutsuwar ba sai yau. Me ya sa?
Bai samu wannan amsar ba ne Malukul-mauti ya zo. Mala'ika Azara'eelu, mai yanke ƙauna, mai raba mutum da mutane, mai kawo ƙarshen zaman mutum da duniyarsa.
Tsayuwar numfashinsa ta yi daidai da tsayuwar ƙwayar idonsa, haɗe da sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, wanda duk sai da suka ji shi, hatta likitan da ke ƙoƙarin shigowa daga bakin ƙofa sai da ya ji numfashin. Zuwanshi ne ya tabbatar musu cewa ba ya numfashi, tashi ta zo ƙarshe, mutuwa ta zo!
***
*My pipu how y'all? Its been a while ban saka wata kuka ba ko? I know, yanzu kam wasu sun koka, ba wai don littafin kawai ba, a'a, tsoron tasu mutuwar. Dole fa za ta zo mana, duk daren daɗewa. Me muka tanadar mata? Shin mun shirya tarbarta? Ko ba mu shirya ba dole za ta zo, ayyukanmu na gari ne kawai za su zame mana garkuwa daga azabar ƙabari. Allah Ya sa mu cika da imani.😫*
*To jama'a! Me kuke hasashe cikin wannan riƙon da Bobby ya ma Dadyn Annur? Kodai kawai yana son tona asirin Sans ne? Ko kuwa dai akwai wata ƙullaliyar da babu wanda ya sani? Alƙalamin marubuciya Amrah ne kawai zai iya warware mana komai.*
*Ina kuke masu mutunci? Ina nufin masu kankaro mutunci, tahm😀 don ku kawai nake posting kullum yanzu, da kuma wasu daga cikin ƴan watsapp masu yawaita comment a kan ANS. Duk ina yin ku sosai kuma ina ƙaunarku fisabilillah. Masu mutunci a ci gaba da kankaro mutunci🤣*
Thanks All
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/3, 1:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
5⃣4⃣
Wattpad: Princess Amrah
This page is in your honour, Hafsy Gusau. Thanks alot for the care nd concern. Amrah loves you so very much, fisabilillah.
***
Hannuwansa duka biyu ya ɗora a ka, kuka yake son yi, amma tashin hankali bai bar shi fasa shi ba. Shin da gaske ne abin da kunnuwansa suka jiye masa? Da gaske Farouk Sardauna ya tafi ya bar shi? Gyaɗa kansa yake, duniyarsa mai cike da ƙunci na riya masa ƙarya ne, Farouk bai mutu ba. Cikin wata irin murya, ya ɗaga sautinshi, ya ce,
"Bai mutu ba! Ga shi nan yana motsi. Wallahi Farouk ba zai tafi ya bar ni ba."
Sai a sannan hawayen ƙunci suka fara saukar masa. Yana kallon sadda likita ya jawo marufi ya rufe Bobby da shi. Jiki a sanyaye ya dafa kafaɗar Sans, ya ce,
"Take heart ka ji? Mutuwa is real, na san ka sani. Kai ɗin ma za ta zo gare ka, ko yanzu ko ba yanzu ba. Ka ɗau haƙuri. Pray for him, ita ya fi buƙata a daidai wannan lokacin. Am very sorry. Sai a nufi ɗaukar gawarsa, idan kuma a nan za ku bar shi ya kwana har safe to."
Dadyn Annur ne cikin ƙarfin hali ya ce za su tafi da shi yanzu.
A cikin daren suka tafi da gawar Bobby, ta kiran waya da kuma text messages aka ringa sanar da mutane, ƴan uwa da abokan arziƙi.
Sans kam tamkar zautacce haka ya koma. Ya yi zaune gaban gawar, shi bai masa addua ba, bai kuma matsa daga gare ta ba. Rayuwa kawai yake tunani. Ya tsura ma gawar idanuwa.
Ƙarfe goma na safe aka yi jana'izar Bobby, aka kai shi tabbataccen gidansa, inda kowa sai ya kwanta a cikinsa, komai matsayi da ikon mutum, dole sai ya kwanta a ƙabari. Ko kaɗan wani mulkinka ko kuma muƙaminka ba zai sa a ƙara ko taƙi ɗaya na girman ƙabarin ba. Kamar yadda aka ma talaka haka za a ma mai kuɗi. Ka saba kwana a bisa lallausan gado da katifa, amma sai ka ji ka kwance, inda ko juyi ba za ka iya ba. Allah ka sa mu cika da imani, mu yi kyakkyawan ƙarshe.
Sans aka bari ƙarshe bakin ƙabarin Bobby. Cikin sassarfar murya yake faɗin,
"Haka mutuwa za ta min? Mutuwa me ya sa za ki tafi da Farouk? Me ya sa za ki tafi da abokina ba tare da kin bar shi ya nadama ba? Allah Ka gafartawa Farouk. Allah ka haskaka makwancinsa. Allah ka yalwata wurin kwanciyarsa. Ya Allah ka gafartawa Farouk kura-kuransa, ɓoyayyu da sanannu..."
Kuka sosai ya ci ƙarfinsa. Da ƙyar ya iya miƙewa a bisa tafukan ƙafarsa, ya taka ya bar wurin. Har ya yi nisa bai daina waigen ƙabarin Bobby ba. Bai daina ji kamar mafarki yake ba. Ina ma dai a ce mafarkin ne, zai farka komai tsawonsa.
Sai da aka masa nisa sosai, mota guda kawai ke wurin, wadda dadyn Farouk ɗin yake cikinta, da wasu daga cikin abokansa. Cikin motar ya shiga, suka kama hanyar gida.
Manya-manyan tabarmu ne aka shimfiɗa ƙarƙashin rumfuna, wanda mutane ke zaune rinkis, suna amsar gaisuwa. Daga jikin bango Sans yake, ya haɗa kai da guiwa, yana jin wasu sabbin hawaye na zo masa. Ba komai ke ƙara tunzura zuciyarsa cikin ƙuncin rashin Bobby ba illa kalaman Dadyn Farouk ɗin, da yake faɗin,
"Allahu akbar! Allah mai iko! Allah mai girma da buwaya. Umar Farouk lokaci ya yi, lokacin tafiya ta yi. Yau dai ka bi mariƙinka na ainahi, ka tarar da shi. Wanda sam! Bai taɓa nuna gajiyawa a gare ka ba, duk da kasantuwarka ɗan tsuntuwa a gare shi. Ya damƙa min amanarka, tare da neman alfarmar kar duniya ta taɓa sanin ba ni ne asalin mahaifinsa ba. Allah Ya rahamce ka Farouk. Allah Ya sada ka da dukkan rahamarSa. Allah Ya yafe maka kura-kuranka."
Shi kanshi