Showing 39001 words to 42000 words out of 201092 words

Chapter 14 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

To wallahi asirinku ya tonu. Baku isa ba"._


_Dariya kawai suka fashe da ita. Suka kalli junansu cikin halin ko in kula. K'ok'arin ruftowa cikin shagon kawai suke._


_Sake dakatar da su ya yi a karo na biyu, yana k'ok'arin ture su da hannuwansa, 'kok'arin fad'uwa suka yi, saboda duk wanda yake cikin maye ba wani k'arfin kirki yake da shi ba._


_Suna cikin haka sai ga Annur ya shigo, a yanayinsa kawai aka kalla za a tabbatar da shi d'in kanshi a buge yake, sai dai nashi mayen ya sha banban da na wancan, saboda shi slow ne kawai yake, hankalinsa bai fita ba._


_Tambayar mai shagon ya yi abin da yake faruwa, nan mai shago ya kwashe komai ya sanar masa, a k'arshe ya ce yana daf da tara masu mutane in har basu fice masa daga shago ba._


_Annurr na jin haka ya dakatar da mai shagon, cike da gadara yake fad'in,_


_"Duka shagon naka tsiyar nawa ce a cikinsa? Ka yo masa ku'di ka ga idan ban siye kaf ilahirinsa ba. Amma ka tasa bayin Allah gaba kana k'ok'arin yin dambe da su, ka ci zarafinsu. To ni d'in nan da kake gani na k'i jinin in ga ana cin zarafin masu shaye shaye, dan duk yanda ban sansu ba sai na yi bakin k'ok'arina na ganin na mayar da martani."_


_kallon junansu suka yi, cikin muryar maye d'ayan ya ce,_


_"Abokina...wannan...wannan ma da alama na hannu ne..." dariya ta ci 'karfinsa har yana dafe cikinsa._


_Ganin haka ya sa Annur ya murmusa, ya kama su a natse ya kai su har bakin motarsa._


***


Kad'an daga halayen Annur Iqrah Al-Hussain ke nan na fad'a miki, Maryama. Yana d'aya daga cikin matasan da suke yad'a fasadi a cikin garin nan. Annur na d'aya daga cikin masu gurb'atar da rayuwar matasan Katsina.


Annur da kike ji da gani, ba wai a shaye shaye kad'ai abun nasa ya tsaya ba, har da neman mata.


***


_wasu y'an mata ne su biyu ke tafiya, su dukansu rik'ak'kun masu zaman kansu ne (Farha da Zee, na cikin *WANDA YA DAKA RAWAR WANI).* Fira sosai suke yi, ko wace na ba k'awarta labarin sabon dadironta. A cikin labarin nasu ne har suka kai ga'bar da Annur ya shigo cikin labarin. D'ayar ke fad'in yanda ya zo har gidanta ya da'uke ta, ya kai ta wani gidanshi da ke unguwar Madawaki. Take fad'in yanda ya kula da ita, ya kuma kashe mata kud'i masu tsoka. A k'arshe ma har da kyautar mota ya bata, saboda Annur matashi ne da ku'di._


_Jin haka ya sa k'awar ta hau kishi, saboda ita d'in ma haka ya kashe mata. Amma a ganinta, ta ya wanda take so zai so k'awarta Farha? Ai ta fi k'arfin nan. Ta fi k'arfi da ajin Farha._


_Hakan ya sa kamar wasa suka hau fad'a a tsakiyar hanya. Abu wasa ba wasa ba fad'a ya yi nisa. To fad'an karuwai dai kowa ya sanshi, hakan ya sa aka rasa mai raba su, aka barsu su kashe kansu._


_Dambe sosai suke yi, cikin dabara Zee ta samu ta zuge jakarta ta fiddo y'ar k'aramar wu'kar da bata rabuwa da ita saboda tsaro. Farha bata ankara ba kawai ta ji wuk'a a kunnenta._


_Bala'i ta ji ita kuma ta ja tsoron gashi guda na Zee, bata sake shi ba sai da ta ciro shi baki d'aya, kan ya d'auki jini. Ita kuwa kad'an ya rage kunnenta guda ya cire, sai lilo yake jini na zirara._


_A daidai lokacin sai ga Annur ya iso. Ganin halin da suke ciki ko kad'an bai sa ya tausaya masu ba. Sai ma rufe su da masifa da ya yi, yana fad'in babu shi babu su, dan haka ko sunansa ya sake ji a bakin d'aya daga cikinsu, sai ya ba'tar da ita._


***


Kinga kuwa, Annur babu ta inda aka barsa. Lalata mata, shaye shaye da duk wani aiki na b'arna yake goyar wa baya. Ko nawa ne zai iya kashewa don ci gaban lalata.


Shi ya sa na yi mamakin jin sunansa a bakinki ai. Nake fatan Allah ya sa ba wani abu ne a tsakaninku ba."


Deedah na kaiwa nan ya dakata, yana kallon yanda baki d'aya reaction d'in Maryama yake.


Suna cikin haka ne Mama ta iso, da plate rik'e a hannunta ta furta,


"Kin ji ni shiru, sai da na d'und'uma miki miyar yanda zaki fi jin dad'inta. Na kuma biya ta d'aki na d'auko miki magani. Ungo gashi."


Ta mik'a mata.


Karb'a ta yi, tana k'ok'arin kaiwa a baki amma tana tuna kalaman Deedah.


Tana cikin haka ne Deedah ya mik'e,


"Ni zan wuce, Mama. Maryama, Allah ya sawak'e."


K'ok'arin kai spoon ta yi bakinta, da abinci a ciki ta furta,


"Ameen, Yaya Deedah. Zan kira ka mu k'arisa maganar a waya."


"To babu damuwa. Mama, a gaishe da Baba idan ya dawo."


Ya tafi.


Tuttura abincin kawai take ba wai dan tana jin dad'insa ba. Kawai dan ta san dole sai Mama ta takura mata sai ta ci.


Bayan ta gama ta b'alli panadol ta sha, sannan ta mik'e ta nufi d'akinta.


Zuciyarta cike take da tunanin yanda zata yi. Tana tunanin mafita, dan a zahirin gaskiya bata jin zata iya barin wannan maganar. Bata jin zata iya barin Annur a halin da yake ciki, wanda take ga kaman soyayya ce ta jefa shi a ciki. Tunani take yi lallai akwai gwagwarmaya babba a gabanta. To ta yaya ma zata fara?


_my exam is around the corner, second to the last semester in the University. Please include me in your prayers. Thanks._


Pinky durling💗
*RAZ 2*
[8/30, 3:43 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣4⃣


Da dare bayan Maryama ta samu natsuwa ba laifi, Muhammad ya shigo ta koya masa karatu. Bayan ya fita ta d'auki wayarta ta latsa kiran Jiddah.


Bata b'ata lokaci ba kuwa ta d'auki wayar suka gaisa ta mata ya jiki?


Nan Maryama ta kwashe komai ta sanar da ita. Daga 'karshe ta ce,


"Jiddah ina son na taimaki Annur. Ina so na fitar da shi daga halaka. Duk ma yanda zan yi, ina son ganin ya fita daga mummunan k'angin da soyayya ta jefa shi a ciki. Sai dai kuma ban san ya zan yi ba. Ban san ta ina zan fara wannnn gagarumin aikin ba."


Ta k'arisa maganar da dafe kanta kamar tana gaban Maryaman ne.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce,


"Na san Annur, na san waye shi. Na san wasu daga cikin munanan halayensa, domin kuwa ni d'in ma ya tab'a gwada min...


***


"Assalamu alaikum." Ta furta a daidai shigarta cikin gidan.


Shiru ba a amsa mata ba, hakan ya bata damar sake yin wata sallamar a karo na biyu.


A nan d'in ma shiru ne, sai ta samu kanta da shigewa ciki kawai, ba tare da ta jira an amsa sallamar tata ba.


Zaune ta same shi a tsakiyar falo, ya tasa shisha gaba sai zuk'a yake, yana fitar da hayak'i daga cikin bakinsa.


Duk'ar da kanta ta yi k'asa, a zuciyarta tana mai tir ha'de da allawadai da munanan halaye irin na Annur. Inda ta san shi zata tarar, da bata zo ba, dan da alama Hajiya Suhailar ma bata gidan.


Mik'ewa ta yi a fusace zata fita, ta jiyo muryarsa ya ce,


"K'anwata, Jiddah."


Samun kanta ta yi da dakatawa, ba tare da ta waiwayowa ba ta ce,


"Momy na ciki ne?"


"Bata nan, sun je dubiya, k'anwar mai aikinta ce bata da lafiya suka tafi tare. Ni kad'ai ne a gidan."


Jin haka ya sa ta ce,


"To bara na tafi. Dama Mami ce ta aiko ni, idan ta dawo ka ce mata na zo, gobe zan dawo idan Allah Ya kai mu."


Tana gama fad'in haka ta fara takunta, taku mai cike da natsuwa, wanda idan tana yinsa dukkan gab'ob'in jikinta sai sun motsa, ba wai kuma da gangan take yinsa ba. Halittar Jiddah ke nan.


Bata ankara ba ta jiyo takunsa, yana ajje tafukan k'afafuwansa a duk inda ta d'auke nata, har ma yana neman wuce ta.


Kamo mayafin da ta yane kanta ya yi, a hankali ta dakata, gabanta sai dukan uku-uku yake, ta gagara furta komai.


"Me ya sa zaki tafi? Lets enjoy together mana, kafin Momy ta dawo. Akwai flavor mai dad'i a ciki."


Ya k'arisa maganar da kwantaccen murmushi bisa kyakkyawar fuskarsa, wadda asalinta jajur take, amma mugun shaye shayensa ya sa ya zama bak'in k'arfi da yaji, lab'bansa su suka fi komai zama bak'ak'e.


A fusace ta d'ora idanuwanta saman nashi, ta fara jefa masa kallon uku saura kwata, a zuciyarta kuwa, tunanin yanda zata yi da shi kawai take. A zuciyarta, ta k'i jinin mugayen halayen Annur. Ta k'i jinin namiji ya tab'a ko mayafinta, ballantana ya yi yun'kurin tab'a fatar jikinta.


"Ka sake ni, Ya Noor..." ta fad'a tana k'ok'arin ci gaba,


"Ka sake ni na fad'a maka. An fad'a maka ni ma irin y'an iskan matan nan ne, wanda kake hul'da da su?"


Ta ci burki a nan, bakinta yana son ci gaba da magana, amma ya gagara furta komai, kaf ilahirin gangar jikinta karkarwa kawai take.


"Haba mana Jiddah! Kar ki gwada min rashin wayewarki mana. Ni a tunanina kin waye, amma zaki watsa min k'asa a ido."


"Wallahi idan baka sake ni ba, zan maka duk abin da nake ga kaman shi ya dace da kai. Ka sanni, ka san wacece ni, ka san bana tolerating nonsesnses."


Sakinta ya yi, yana mai duk'ar da kansa 'kasa, yatsunsa na dama dunk'ule suke, lab'bansa suna rawa, da alama kalamanta sam! Basu masa dad'i ba.


"Lemmi tell you for the last time..." ta murza yatsarta babba da ta tsakiya, ta ci gaba da fad'in,


"Kar ka sake gigin tab'a ni, ko da wasa. Bana jin akwai wani abu da ya rage tsakanina da kai, ka sani. Ka fita daga harkata, ka fita daga rayuwata. An fad'a maka ni ko soyayya zan yi, zan yi ta da mutum irinka ne? An fad'a maka, kana sahun mutanen da nake jin zan iya yin soyayya da su ne? Abeg, Ya Noor, ka rabu da ni, akwai banbancin halaye da dama a tsakaninmu."


Cikin halin ko in kula ya ta'be bakinsa,ya d'aga kafa'dunsa duka biyun, wanda ke nunar da ko a jikinsa, ya koma mazauninsa ya zauna, yana mai ci gaba da zuk'ar shisha, cikin wani salo, mai nunar da k'warewarsa ta wannan fannin.


Ita kuwa Jiddah ta fita, a zuciyarta tir kawai take da halayen Annur, yanda ya yi k'aurin suna a cikin garin, kowa ya bu'de baki baya fad'in abin alkhairi a kansa. Amma a ganinta, iyayensa ne manyan masu laifi, a ce wai kawai dan baka son ganin damuwar d'anka, sai ka kasa kwa'barsa yayin da ya tafka babban shirme? A k'alla, Annur zai yi shekara ashirin da takwas yanzu, ina yake da yarintar da za a ce wai ba za a kwab'e sa ba? Kullum bad'alarsa k'ara yawa kawai take. Gashi abun har ya dawo kanta. Ta sani, ya jima yana sonta, tun kusan shekara d'aya da ta gabata, yake nunar da yana sonta, amma take basarwa, take nuna bata sonshi, ba dan komai ba, sai dan gudun 'bacin suna, saboda duk yarinyar da aka ga tana soyayya da Annur, an san ba ta kirki ba ce, idan ma ta kirkin ce, to zata lalace.


***


Mamanshi k'awar Mami ce sosai, tun suna yara suke tare. Hatta soyayyarsa da Amrah na sani. Na san yanda ya sadaukar da rayuwarsa a kanta, ita ma kuma haka. Na san sanda yake da halayen kirki, yake kyautata wa kowa. Na san lokacin da ya haukace, saboda har gano shi mun yi. Amma daga tashinsa cutar hauka, halayensa suka koma haka."


Jinjina kai Maryama ta yi, cike da damuwa ta ce,


"To yanzu Jiddah, ta ina zan fara? Please ki bani shawara, wace hanya kike ga kamar zan bi, in ceto rayuwar Annur?"


Shiru Jiddah ta yi na wani lokaci, kafin ta ce,


"Da zaki bi ta tawa, Maryama da kin fita sabgar da bata shafi rayuwarki ba. Da kin fita daga rayuwar mutumin da bata cancanci ki shige ta ba. In dan Amrah kike ga zaki taimaka masa, ko kin manta ita d'in ta rasu, tata ta k'are? Kin manta cewa ta yi kyakkyawan k'arshe ita kam? Shi kuma fa, babu ruwan Allah fa. Allah kama Shi zai yi matuk'ar ya mutu da wannan bak'ak'en halayen..."


Bata rufe baki ba Maryama ta ce,


"Saboda hakan nake so na ceto sa, Jiddah. Ina son Annur ya samu rabauta, ina so ya yi kyakkyawan k'arshe, kamar yanda masoyiyarsa ta yi."


Dafe kai Jiddah ta yi, ta san halin Maryama sarai, ta san cewa ba zata tab'a fahimtarta ba, in dai tana son abu, to fa babu wasa.


"Ina ga kamar ki fitar da rana sai mu je gidansu."


"Zuwan gidan nasu zai sama min mafita, Jiddah?"


Maryama ta d'aga lab'banta, ta ajje wannan kalaman, cike da tabbatar da kalaman, a cikin zuciyarta.


"Ehh to, mu dai je. Idan muka je, zan shaida ma Momy ke 'kawata ce. Kin ga daga nan sai mu ringa zuwa akai-akai muna gaishe ta, har mu samu mafita."


"Good idea, Jiddah. Hakan za a yi. Amma gobe idan mun ha'du a Islamiyya, sai mu 'kara tattaunawa."


"To babu damuwa. Allah Ya kai mu."


Daga nan suka tsinke wayar, Maryama na jin zuciyarta na d'an samun sassuuci.


A hankali ta runtse idanuwanta, ba wai bacci take ji ba. Tana tunanin gwagwarmayar da ke gabanta ne. Tana ji cewa ba fa k'aramin risky ba ne zata jefa rayuwarta a ciki. Shiga rayuwar mutum irin Annur, ba abu ne mai sau'ki ba.


A haka b'arawo bacci ya sace ta, bacci mai nauyi ya d'auke ta, wanda ke cike da mafarkai kala kala, duka kuma sun shafi abin da ta saka a gabanta.


Washe gari ta shirya aka kai su makaranta, a mota Muhammad ke mata firar,


"Yaya Maryama, jiya fa Mallam Isma'eel ya sake bani sak'o wurinki, wai in gaishe ki, kuma wai ki bada lambar wayarki a kai masa..."


Bai rufe baki ba Maryama ta d'aure fuska tana kallonsa, tsaki ta fara yi kafin ta ce


"Wai kai ba na ce ka ce masa ya fita harkana ba? Yo wai ina dalili. Malamin Islamiyya amma sai mugun son 'yan matan tsiya. Daga zuwa sau d'aya ya nace ma aiko ka wurina. To ka fa'da masa ni ina da mijina."


D"aure fuska Muhammad ya yi, shi a dole ya ji haushi ta ce bata son malaminsu, murya k'asa k'asa ya ce,


"Yaya Maryama ina mijin naki yake? Ni ai ban san akwai shi ba."


Hannayensa ta ha'de duka biyu, babu annuri ta ce,


"Wai me ke damunka ne? Bana son yawan surutu, kuma ka sani. Ka fa'da masa abin da na fad'a maka."


Bai ce ,komai ba sai zumb'urar bakinsa da ya yi har suka isa bakin makarantarsu, sauke ta aka yi, ta ma dreban nasu bankwana ta tafi, ba tare da sun yi bankwana da Muhammad ba kaman yanda suka saba.


Bayan ta shiga cikin aji ne ta samu Jiddah ce kawai zaune tana maimaita inda zata karanta a saukarsu. Da fara'a ta shiga, ya mik'a mata hannu suka gaisa sannan ta zauna a kusa da ita.


"Bakinki yana motsi, kamar kina son yin magana."


Jidda ta furta tana kallon Maryama da ke k'ok'arin zaro wayarta daga cikin jika, tana jin tana ringing.


"Ina zuwa." Ta fa'da had'e da latsa wayar, ta lumshe idonta, ta bu'de a hankali tana sauraren kalamansa da suke dira a saman kunnuwanta.


"Bobby, na fad'a maka ka fita harkata, na san ka san bana son kirana da kake ko? Please ka daina mana. Ko ana soyayya dole ne?"


Tauna lab'bansa ya yi, cikin wata murya ya ce,


"Ba a soyayya dole, amma dole ki kula ni, Maryam. Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba, na san kin sani, bakya buk'atar maimaici. A ganina kamar kina b'ata wa kanki lokaci ne, kina asarar yawun bakinki."


"Dakata! Bobby. Na san ka san cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne. Me zai sa na so ka bayan halayenka basu kasance na gari ba? A kan me zan so mutumin da bai san darajar mutane ba? Na rok'e ka, Bobby. Dan Allah ka k'yale ni haka nan. Ka bar Maryama ta samu sa'ida mana."


Ta tsinke wayar, zuciyarta sai tafarfasa take, tana mai tsananin jin haushin Bobby.


"Calm down..." Jidda ta fad'a tana dafa kafad'ar Maryama.


"Na san Bobby, ko ba Farouk Sardauna ba?"


Cike da mamaki ta kalli Jiddah, da idanuwa ta bata amsa.


"Abokin Annur ne, ina nufin Ya Noor. Na sha ganinsu tare, wani lokacin idan na je gidansu. Amma ke me ya had'a ki da shi?"


Lab'banta duka biyun ta tura a cikin baki, ta d'an tsotse su kafin ta furzar da iska daga bakinta, ta ce,


"A makaranta muka had'u...


***
Trecking suke ita da 'kawarta Hannatu, tafiya suke suna hirar gajiyar da suka yi, kasantuwar tun daga department d'insu suke tafiya da k'afarsu, har gasu sun iso bakin gate amma basu samu abin hawa ba. Lakcar 'karfe shida ce suka yi, kuma dama sukan samu irin wannan matsalar a duk lokacin da suka yi ta.


Maryama ce ta ce,


"Na matuk'ar gajiya wallahi. Gashi abun hawa ya yi wahala. Idan ma yanzu muka ci sa'a school bus ta zo, hanga ki ga tarin d'alibai, wanda duk abun hawa suke jira fa. Ta ya zamu samu wuri?"


Hannatu ta bud'e baki zata yi magana ke nan suka hangi bus na k'aratowa. A hanzarce ta kama hannun Maryama tana fad'in,


"Ki saki jikinki mu yi tafiya, Maryama. Dan zamu iya rasa wuri."


Saurin da suke yi ne ya sa Maryama ta yi tuntu'be da robar lemo, wadda aka yar a hanya. K'wace hannunta ta yi daga na Hannatu, fuskarta na nunar da damuwa, tana k'ok'arin yin magana.


Kallon da ya ajje a setin fuskarta ne ya dakatar da ita daga maganar da ta yi niyyar yi. Bai d'auke idonshi daga nata ba, haka ita ma bata d'auke nata daga gare shi ba.


"Haba mana Maryama. Dan Allah ki zo mu tafi haba! Ki duba ki ga ko a haka har motar ta cika. Ki saki jiki mu yi tafiya wata k'ila mu samu wuri ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login