Showing 183001 words to 186000 words out of 201092 words

Chapter 62 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

haka kike da kafiya?"


Hanan ta harare ta daidai sadda ta iso ɗakin. Ita kam ta ƙudira cewa ba za ta sake tada ma Momy maganar ba, tunda dai ita ba ta san me kalmar haƙuri ke nufi ba.
Ta je ta zuba wa maigadi kalacinsa ta kai masa da na mai gyaran flowers, sannan ta haɗo nata ita ma. Zama ta yi ta ci ta ƙoshi, ta gyara wurin sosai.


Ƙarfe ɗaya da minti biyar wayar Dady ta yi ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba dai ya daure ya duba, sai ya ga abokinsa ne ke kiransa. Gyara muryarsa ya yi saboda disashewar da ta fara yi. Ya kara wayar a kunnensa.


"To, da wuri haka? Allah ya iso da kai lafiya. Ka yi amfani da address ɗin da na turo maka, babu wahalar ganewa gidan."


Ya tsinke wayar. A daidai lokacin kuma mai gadi ya iso ɗakin, cewa ga ƴan sanda can har mutum uku sun zo. Momy ta gaggauta miƙewa, ko mayafi ba ta tsaya nema ba ta bi bayan mai gadin.


Sai a nan hankalin Dady ya ƙara tashi. Yana ji a ranshi bai kyauta ba. Tabbas ya zama munafuki, saboda rashin cika alƙawari, kuma an siffanta mara cika alƙawari a cikin munafukai. Sai ya tashi ya bi bayan Momy, Hanan da Janan suka bi bayansa. Duk da halin rawar kai irin na Janan, sai ma ta fi Hanan ɗin damuwa. Take jin tashin hankali sosai bisa ga wannan al'amari.


Gaban ƴan sandan Momy ta isa, ta gwada musu ɗakin Sans cewa su shiga su fito da shi. Babu musu kuwa suka shiga ɗin.


Zaune yake ya tasa kwandon kayan kalacin a gabansa, bai fiddo komai ba sai haɗa kansa da guiwa da ya yi, ya yi shiru sai zancen zuci yake yi. Bai ji ƙarar shigowarsu ba sai muryar ɗaya daga cikinsu da ya ji ya ce,


"Hajiya ta ba mu umurnin shigowa mu tafi da kai. Bisa ga babban laifi ba ƙarami ba. Za mu tafi da kai domin ka amsa wasu tambayoyi."


Bai ko musa musu ba ya miƙe, saboda dama abin da yake zaman jira kenan tun ɗazu. Ya bi bayansu.


A daidai gaban Momy da Dady ya rusuna. Cikin muryar kuka ya ce,


"Momy, Dady, please ku gafarta min. Na sani ni mai laifi ne a gare ku. Da ba ni da bakin wanke kaina tunda dai na aikata ɗin. Ba zan taɓa mantawa da halarcinku ba. Ba zan taɓa mantawa da karamcinku ba."


Ya duƙe a nan, yana kuka sosai.


Horn suka ji, hakan ya sa suka waiga ga ƴar ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin suna kallo. Da hanzari mai gadi ya buɗe masa gate ɗin, saboda tun fitowar Dady ya masa bayanin baƙon da zai zo ɗin. Yana shigowa ya masa nuni da parking space, ya faka motar tasa sannan ya fito. Dady ya ƙoƙarta dawo da walwalarsa, ya isa gare shi cikin murmushi yana faɗin,


"Young Dr. Ji nake kamar a mafarki, yau ga ni ga ka."


Ƙam-ƙam suka riƙe hannuwan junansu. Daidai sadda ƴan sandan suka ɗago Sans domin tafiya da shi, daidai lokacin ne baƙon ya haɗa ido da shi. Cikin mamaki ya sake darara idonshi. Ya ce,


"Wani nake gani kamar Annur da na baro yanzu."


Cike da mamaki Dady ya ce,


"Annur kuma? A ina ka gan shi?"


"Yanzun nan fa na baro shi gidan kawunsa, har na duba shi ba shi da lafiya."


Ya riƙo hannun Sans bayan ƴan sanda sun miƙar da shi.


"Annur nan ka kaɗo kuma? Ina Maryamar? Wani abu ya faru ne na ga ƴan sanda za su tafi da kai?"


Momy ta kalle shi. Dady ya ce,


"Dr. Wannan fa tun ɗazu muke nan tare da shi, in fact, a nan ma ya kwana. Ba na faɗa maka jiya muka dawo daga India ba? To ai shi ne Annur ɗin da na faɗa maka ba shi da lafiya ɗin."


Kai ya kaɗa.


"Akwai dai alamar tambaya. Kodai ƴan biyu ne?"


Sai a nan Momy ta samu damar magana.


"Dr. Hamdan a ina ka ga Annur ɗin?"


"Gidan kawunshi mana. Baccin ma na tsaya shan mai ai da sai in ce muku yanzun nan muka rabu da shi..."


Bai gama rufe baki ba. Su Maryama suka shigo. Uncle Marwan gaba, Yamaira biye da shi ta riƙo hannun Yesmeen, sai Maryama da Annur jere da juna.


Dukkansu suka ɗaga kawanansu suna bin su da kallo, musamman ma Momy da ta saki baki tana bin annur da ido. Cikin murmushi Dr. Hamdan ya ce,


"Haba! Ni fa in ce. Annur da alama dai ku ƴan biyu ne ko? Anyways, nan kuka yo kenan. To ga ɗan uwanka mai kama da kai nan ƴan sanda za su tafi da shi."


Ko a jikinsa ya yi wannan maganar. Dama halinsa kenan.


Da sauri cike da mamaki Annur ya isa ga Sans suka rungumi juna, dukkaninsu kuka suke yi sosai, suna jin soyayyar junansu na shiga duk wata kusurwar jiki da zukatansu. Ɗan uwa rabin jiki! Sai ma suka kasa rabuwa, bugun zukatansu na tafiya a tare, kamar yadda ruwan hawayensu ke zuba a kafaɗun junansu a tare.


***


*Bari in dakata a nan yau dai kam. Na gaji. Ba laifi kusan 4k words na yi, kuma a zama ɗaya kawai.*


*Sannunmu dai da jimirin yin comments. Haƙiƙa kuna faranta min rai sosai, inaa jin daɗin hakan. Khairat ta RAZ NOVELLA na gaishe ki. Na ji daɗin kiran da kika yi min tare da nuna farin-ciki da ƙaunarki ga ANS.*


*Masoyana na nesa da na kusa, duk ina jin saƙon gaisuwa da jinjinar ku. Ina matuƙar jin daɗi da hakan. Allahi ya bar zumunci, ya ba mu ikon amfanuwa da darussan cikin labarin.*


*Da alama dai saura ƙiris mu kawo gangara. Kaɗan ya rage in kammala warware ƙullallun abubuwa. Ku dai juri bibiyar alƙalamin Amrah, da sannu komai zai zo muku yadda kuke so.*


*Da gaske saura ƙiris in zubda ma Sans ƙwalla. Sai dai kuma ya za a yi. Dole Momy ta jajirce don ganin ta ƙwatar wa ɗanta fansa. Domin kuwa aika-aika irin wacce Sans ya yi, ba abu mai sauƙin a yafe ta ba ne.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/27, 10:18 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


7⃣3⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Dukkansu babu wanda ya san sadda ƴan sandan suka tafi. Momy ce ta lallaɓa ta musu alama kan su tafi ɗin. Cike da mamaki Dady ke kallon yadda Annur da Sans suka kasa rabuwa da junansu. Hanan da Janan sai murmushi suke saki, duk da cewa su ɗin ma suna al'ajabin wannan tsananin kama da take tsakanin Annur da Sans.


Uncle Marwan ne ya ce,


"Duka sai mu rankaya cikin gida, zan mana bayanin duk yadda abubuwan suka kasance."


Yawu ta haɗiya da ƙarfi Momy. Cikin ƙarfin hali ta matso magana, ta ce,


"Alhaji Marwan kana nufin dama can ka san inda Annur ɗina yake? Me ya sa za ka ɓoye mana?"


Ya yi murmushi.


"Duka wannan tambayoyi ne da zan amsa mana su idan mun samu wuri mun zauna. Ga kuma Dr. A tsaye."


Ya isa ga Dr. Hamdan yana murmushi.


"Ashe dama nan za ka yo Dr."


Dr. Hamdan ya murmusa.


"Shi ne mutumin da na faɗa maka na zo wurinsa ɗin. Da alama ma dai kun san juna."


Dady ya ce,


"Young Dr. Ana ma maganar sanin juna ni da Marwana? Ƙanina ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya."


Da mamaki Dr. Hamdan ya kuma sakin murmushi.


"Allah mai iko! Kuma fa daga gidansa nake yanzu mai kawai na biya na shawo. Ai ni ban ma sani ba."


"Mu shiga daga ciki ko?"


Dady ya faɗa cikin murmushin ƙarfin hali.


Sai a sannan Annur da Sans suka saki juna. Yamaira ta riƙe musu hannuwa su duka biyun bayan ta saki hannun Yesmeen. Maryama kuma ta kama wa Yesmeen ɗin hannu, tana jin tsananin daɗi a duniyarta. Duk wata fargaba da damuwa da take a cikinta sai ta neme ta ta rasa.


Sun kama hanyar babban falon gidan kenan Dr. Islam ta iso. Da sauri ta taddo su, saboda tunda Baban Abdul ya faɗa mata Momy na neman ƴan sanda hankalinta ya tashi. Tana asibiti ne ta duba wasu patients shi ya sa tun ɗazu ba ta zo ba. Ba ta ga fuskokin kowa ba sai Maryama da ta waigo tana kallon ta. Murmushi suka sakar wa juna, duk da yake cewa Islam mamakin mutanen da ta gani a gabanta take yi. Jira ta yi har ta ƙariso kusa da ita. Suka gaisa cikin sakin fuska sannan suka isa cikin falon.


Take mamaki ya kama Islam ganin mai irin fuskar Annur har guda biyu sun zauna kusa da juna. Sai ta saki wayar hannunta ido buɗe ta kasa zama sai bin su da kallo take yi. Babu wanda ya mata bayani, har sai da ta jiyo muryar Momy cikin kuka ta ce,


"Alhaji Marwana ka mana bayanin abin da yake faruwa, don Allah. Ka sa hankalina ya daɗa tashi, gabana ya ƙi ya daina faɗuwa."


Alhaji Marwan ya yi gyaran murya.


"Zan fara da yi mana wata ƴar guntuwar nasiha, game da ɗaukar ƙaddara kyakkyawa da mummuna. Duk abin da ka ga Allah ya tsara ga bayinSa to ka ɗauka cewa dole sai ya faru da su ɗin, duk dabararsu kuwa. Sannan sau da dama abin da ba ka tunanin faruwarsa sai ya faru. Abin da kake da tabbacin zai faru kuwa sai ka ga bai faru ɗin ba. Ina so ku ɗauka cewa dama can Allah ya ƙaddara cewa za ku raini Annur tun yarintarsa har ya girma, sannan kuma a ƙarshe ku samu labarin cewa ba ɗanku ba ne na asali, ba ku ne kuka haife shi ba."


Daga Dady har Momy sai suka miƙe tsaye idanuwansu a buɗe suna bin Uncle Marwan da kallo.


"Yaya Iqra ku koma ku zauna. Yanzun nan zan warware muku zare da abawa."


Dady ne ya koma ya zauna, amma Momy ta gagara zama, Islam ma ta yi tsaye har yanzu ba ta daina mamaki ba.


"Annur ba ɗanku ba ne. Duk ma yadda za a yi to tabbas ba shi ne ainahin ɗanku ba. Ta yiwu a asibitin da aka haife shi ne aka samu matsala aka sauya muku shi. Amma tabbas ɗan uwan Salman ne ga shi nan, ɗan uwan tagwaicinsa. Sannan kuma Yaya ga Yamaira matata ga ta."


Ya nuna musu Yamairah da ta sunkuyar da kanta ƙasa tana kuka.


"Kar ka faɗa mana magana son ranka Alhaji Marwan. Ni na haifi Annur da kaina fa. Ta ya za ka ce wai ba shi ne ɗana ba? Wace hujja gare ka ta cewa an sauya min shi ne?"


"Ba ni da hujjar da zan yi proving zancen nan a yanzu, har sai mun je asibiti an yi gwajin DNA. Amma ina so na miki wata tambaya."


Bai jira ta kuma cewa komai ba ya ci gaba,


"Kin taɓa ganin mutane masu tsantsar kama irin ta Annur da Sans kuma suka kasance ba identical twince ba? Sadda kika haifi Annur ƴan biyu kika haifa aka ce miki kin rasa ɗaya? Salman da Yamaira ƴan Borno ne. A Borno State ke ma kika haihu. Bakya tunanin duk abin da na faɗa zai iya zama possible? I want you to think well, Hajiya Suhaila. Kafin mu je asibiti a muku DNA test."


Dady ya ɗan fara gasgata zancen Alhaji Marwan. Sai ya dafe kansa yana kuka sosai, tamkar ba namiji ba. Shi dama can haka yake da zuciya mai rauni, ƙaramin abu ma sai ya saka shi zubda ƙwallarsa. Bai gama tunani ba ya ji muryar Dr. Hamdan ya ce,


"Yanzu the best solution is that, a yi DNA test ɗin kamar yadda Alhaji Marwana ya faɗa. After that, idan za ku iya to tabbas za ku koma asibitin da aka haifi Annur. Akwai records na komai da ya faru in dai ba za ku iya manta date ɗin haihuwarsa ba. A lokacin har sunan nurse ɗin da ta karɓi haihuwarsa ma ana rubutawa. Sai ku zanta da ita. Ta yiwu a daidai lokacin da aka haife shi an haifi twince, sai aka musanya guda ɗin da ɗan da kuka haifa, aka damƙa muku Annur."


Cikin kuka Yamairah ta ce,


"Babu ko tantama abin da ya faru kenan. Mahaifiyarmu ta faɗa mana cewa ƴan biyu ne ta haifi Yaya Salman, amma ɗayan ya rasu a take."


Sai Momy ta ƙwalalo ido haɗe da zubewa ƙasa rijif. Lokacin da ta haihu ta tuna. Shereefa da ta haihu aka ce mata ɗayan ya rasu. Cikin kuka ta ce,


"Ya sunan mahaifiyar taku?"


Yamaira ta ce,


"Sunanta Shereefah."


Momy ta dafe zuciyarta. Tana ganin yiuwar abin da a tunanin ta ba zai taɓa yiuwa ba. Kafin ta ce komai, Alhaji Marwan ya ce su taso su biyar; Dady, Momy, Annur, Sans da kuma Yamairah su tafi asibiti yanzun nan a yi ta ta ƙare. Yana so ya fitar da su Momy daga wasi-wasi.


Dr. Hamdan ma ya miƙe cewa zai koma Kano yau. Amma Dady ya roƙe shi alfarmar ya jira su dawo. Ko gaisawar kirki ma ba su samu sun yi ba saboda wannan tashin hankalin.


Zaman kuwa ya yi, Maryama da Isam sai kallon-kallo suke, sun kasa cewa ko uffan.


Zaman tsit ne ya biyo ɗakin, sai ɓuruntun Hanan da ke girki a kitchen. Yesmeen kuwa ta yi barci tun ɗazu tunda ba da ita suka tafi ba. Dr. Hamdan latsar wayarsa kawai yake yi, sai ya ɗan nisa ya ce musu sannu.


A asibiti kuwa, bayan an gama duka aka tabbatar wa su Momy cewa Annur ba jininsu ba ne, amma shi, Salman da kuma Yamairah jini ɗaya ne. Hakan ya daɗa tayar musu da hankali. Momy kamar zuciyarta za ta buga haka take ji. Ta rasa yadda aka yi hakan ta kasance. Wane irin daƙiƙanci da rashin hankali ne zai saka ma'aikaciyar asibiti tafka irin wannan babban kuskuren?


A cikin mota kuka kawai Momy ke yi. Dady kuwa kukan zuci yake yi, wanda ya fi na hawaye ciwo. Alhaji Marwan da ke tuƙi ne ke ta tausarsu.


"Shi ya sa kafin na tinkare ku da maganar, sai da na muku nasiha saboda na tabbata sai haka ta faru. Na sani, cewa babu daɗi, kuma dole za ku damu. Amma dole ku daure, ku miƙa komai ga Allah, sannan kuma ku miyar da komai ba komai ba..."


Bai rufe baki ba Annur ya ce,


"Kuma hakan ba wai yana nufin zan bar su Momy ba ne. Ko da a ce iyayena suna raye, na tabbata su kansu ba za su taɓa raba ni da su Momy ba. Raba ni da su kuwa tamkar raba ni da numfashina ne. Sun min abin da ba zan taɓa mantawa da su ba. Matar da ta shayar da ni, ta raine ni irin rainon da mahaifiya ke yi ga ɗan da ta haifa, har kuna tunanin akwai ranar da zan iya butulce ma su Momy? Har abada!"


Nannauyar ajiyar zuciya Momy ta sauke, duk da haka dai hawaye na zuba bisa kumcinta.


Sans bai ce komai ba. Sai jinjina lamarin kawai yake yi. A ranshi yake tunanin ashe ɗan uwansa na jini ne ya wulaƙantar da rayuwarsa. Ashe dai da rabon zai sake haɗuwa da jininsa. Ga shi Allah ya haɗa shi da mutum har biyu, ko ma uku. Tunda dai Yamairah ma kanta ta ajje ƴa, kenan ita ma ta shiga sahun jininsu. Bai san sadda ya saki murmushi ba, murmushin da har sai da ya bayyana.


A haka suka ƙarisa gida mai gadi ya buɗe musu gate suka shiga ciki da motarsu. Dukkansu jiki a saɓule suke banda Sans da Yamairah. Su kam daɗi ne ya turnuƙe zukatansu.


A falo suka yi branching, yanayin fuskokinsu kawai ya sa duk ƴan ɗakin suka gasgata cewa DNA ɗin bai zo daidai da na su Momy ba.


Hannu Dady ya miƙa wa Dr. Hamdan haɗe da sakin murmushin ƙarfin hali.


"Dr. Mun bar ku da jira."


"Babu komai ai. Ga shi har na yi sallah ma."


"To masha Allahu. Abu dai ya tabbata Dr. Ashe Annur ba jininmu ba ne."


Ya goge ƙwallar da ta zubo masa a daidai nan. Haɗe da dakatawa saboda nauyin maganar da ya ji.


Dr. Hamdan ya ce,


"Kar ka damu Oga. Haƙuri za ka yi, haka Allah ya tsara muku tun asali. Yanzu ka ga wani al'amari na Allah, inda za ka san cewa komai rubutacce ne, yaushe rabo na da kai? Shekara da shekaru muka rabu, ko a waya ba mu tare. Amma cikin iko da hikimar Allah, kamar wasa na gan ka a Facebook an sako min kai a People You May Know. Ina ganin sunan na ji daɗi sosai, ban gama tabbatar da kai ɗin ba ne har sai sadda muka yi magana da kai. To ka ɗauka cewa wannan ɗin ma dama can rubutacce ne."


"Babu abin da ya fi damu na irin wulaƙancin da na ma Salman. Na ci mutuncinsa, na ci zarafinsa a kan ɗan uwansa. Ashe ni ban sani ba haukan banza nake, a kan ɗan uwansa ne nake masifar, ɗan uwanshi gudan jininsa..."


Yaimaira ta gaggauta dakatar da Momy.


"Ki daina faɗar haka please. Yadda kika ɗauki Yaya Annur to a yanzun ma haka nake fatar ki ci gaba da ɗaukarsa. Na tabbatar da shi ɗin ma a nashi ɓangaren haka ne. Tunda dai mun rasa iyayenmu, kuma ko suna rayen ma wane irin butulu ne shi da zai bar ku bayan rayuwar da ya yi a tare da ku?"


Sai a sannan Islam ta yi magana.


"Lallai maganar Uncle Marwan gaskiya ce. Cewa so da dama abin da ba ka taɓa tsammani ba yana faruwa. Ga shi nan dai, tunda muke a rayuwarmu ba mu taɓa kawo wa rayukanmu ba cewa Yah Noor ba shi ne ainahin ɗan su Momy ba."


"To ina ɗan namu yake?"


Momy ta tambaya cikin kuka. Ta ji muryar Dady ya ce,


"Ina tunanin shi ne ya rasu."


Cikin takaici Momy ta kalli Dady.


"Ba na tunanin ɗanmu yana raye, kamar shi ne ya rasu sai aka macanza shi a matsayin ɗan uwan tagwaicin Salman."


Ta dafe kanta. Kuka sosai ke sake zo mata. Tana jin takaicin rayuwarta. Komai ganinsa take tamkar a mafarki. Kamar za a bubbuga ta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login