Showing 102001 words to 105000 words out of 201092 words

Chapter 35 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

babu wuya yake shafewa. Yanzu ku ɗauki misali, a nemi hunhun rago a yanka shi manya manya, sai a tsoma shi cikin ruwan mai, wuta ta bige shi. Ya zai yi? Zai koma ya laƙume, tamkar ba manyan yanka aka yanka shi ba. To haka ko na mutum ma yake yi, da zarar ana kai masa hayaƙi, wannan laƙumewar haka zai yi ta, a hankali har ya kai minzalin da zai gama lalacewa.


Ko mata masu amfani da icce wurin girki, ana yawaita faɗakarwa a kan hakan, cewa su daina zama a bakin wutar sosai, matuƙar suka haɗu da icce mai hayaƙi. Saboda wannan hayaƙin zai iya yi musu illa, sosai zai harbi hunhunsu. Su ɗin ma da ya zamewa dole kenan.


Amma ku sai ga shi kuna kai kanku halaka da kanku. Kuna yin abin da ba zai amfane ku da komai ba. Ba za ku ƙaru da komai ba face ciwo mai girma. Why? Me ya sa kuke haka?"


Ya dakata daga nan, yana mai tsananin jin takaicin Farouk Sardauna. A wani ɓangaren na zuciyarsa kuwa, tausayinsa yake, ta yadda yake yaro matashi, amma wannan cutar ta kama shi, wacce ba lallai ma ya ci gaba da rayuwa ba.


Dafe kansa ya yi Dr. Da ƙyar ya iya ci gaba da faɗin,


"Akwai drugs da zan rubuta maka, a dage amfani da su, bayan sati biyu sai ka sake dawowa."


Godiya Annur ya masa, zuciyarsa cike da rauni. Tausayin abokinsa ya gama mamaye duk wata gaɓa ta cikin zuciyarsa. Ƙwaƙwalwarsa yake ji tana juya masa, tana neman dagula duk wani lissafi nashi.


Bayan Dr. Ya rubuta musu maganin ne suka miƙe, jiki ba ƙwari suka bar Office ɗin na shi.


***


My pipu how are y'all? I hope na same ku lapia😍 its been a while ba mu hadu ba ko? Tun kafin sallah. Hidimomi ne suka sha gabana, kun san sallah akwai dadi, zumunci ake sadawa sosai😀 yanzun ma fa kar ku zata an gama. Masoya ANS ne kawai suka taso Amrah a gaba,🤒 don dole na na kokarta taipa muku wannan, ba wani mai yawa sosai ba🤦


To ya kuke gani fans? Waye ne Dr. Hamdan M. Ramat din nan, wanda Dr. Sandra ta ce mento dinta ne? Kamar dai farkon haukar Annur ai Dr. Aqaaq Saifullah ya duba shi ba a dace ba.🤔 Bayanan da Dr. Sandra ta ma Maryama hakan zai iya kasancewa ko ba zai iya ba?


Ina za mu iya gano Sister Rita bare ta warware mana wannan kullalliyar, mai wiyar kwancewa?


Me kuka hasaso ne a wannan ciwon da Farouk Sardauna (Bobby) yake yi? Kar fa ya mutu, ina kaunar Bobby nawa🤧😱


A tabbatar an dropping comments, kafin zuwan next chapter.


Vote, comment and share with your family and friends.


Thanks all


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:56 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


4⃣8⃣


Wattpad me: PrincessAmrah


***


Tun bayan shigarsu mota Bobby ke kuka sosai tamkar ƙaramin yaron da ba ya jin rarrashi. Yana yin kukan yana wani irin tari, wanda da zarar ya tara hannunsa ya fiddo kaki sai ya ga gullamar jini ce. Hakan ba ƙaramin ƙara tayar da hankalin Annur ya yi ba. Ya ma kasa rarrasarshi, shi kanshi ji yake ina ma dai ruwan hawayen ya zo, da bai ga abin da zai hana shi barinsa wanzuwa a saman fuskarsa ba.


Da ƙyar ya iya rintse idanuwansa Annur, ya buɗe su da wani guntun ƙwalla, mai matuƙar zafi a gare shi. Cikin nutsuwa da kwantar da kai ya fara ajje kalamansa, zuciyarsa na ƙuna sosai.


"Ka yi haƙuri Guy, ka kai zuciyarka nesa. Kar ka zata wai don kana cuta hakan na nufin ka kusa mutuwa ne, ko kaɗan ba haka ba ne. Cuta ba mutuwa ba ce..."


Yana neman ci gaba da magana Farouk ya dakatar da shi, cikin sassarfar murya, bakinsa na rawa sosai ya ce,


"Kar ka damu guy. Ka kwantar da hankalinka, na ga ka tasarshi sosai kawai don ba ni da lafiya. Idan ma mutuwar ce ina da maganinta ne?"


Ya saki guntun murmushi, wanda za a iya kiransa da na yaƙe, ya ci gaba,


"Abokina hunhuna fa ne ya lalace, kana sa ran zan ci gaba da rayuwa ne? Na cire rai da rayuwa guy. Ka kai ni gida please!"


Babu musu Annur ya ja motar tashi, suka bar harabar asibitin. Ko a mota babu mai cewa kowa uffan, sai saukar ajiyar zuciya kawai da ke fita. Abun mamaki, su ɗin da suka kasance masu ƙure sautin mota, sai ga shi yau babu. Su ɗin da suka kasance ba a raba su da kayan maye a cikin mota, yau babu. Su ɗin da suka kasance masu raha da shewa a cikin mota, yau babu ko ɗaya. Lallai wannan rayuwar abun tsoro ce. Kana taka Allah na naSa. Kana nan sake da baki kana bankaura, ba ka san ya rayuwarka za ta kasance ba. A duk inda rayuwar ɗan maye take, ba ta taɓa tasiri a ƙarshe, ba zai taɓa aikata abun kirki ba a ƙarshe, matuƙar bai shiryu ba.


A haka suka isa gidan su Farouk ɗin, bayan ya kashe motar ya zagayo ya taimaka masa ya fito, tafiyar kanta a wahalace yake yin ta, saboda cin ƙarfinsa da tarin ya yi. Kuma idan ana kuka dama tari ya fi ta'azzara.


Har ɗakinsa ya kai shi sannan ya kunna masa AC, saboda zufar da yake yi. A zuciyarsa Annur yake tunanin yadda rayuwa ta juyewa abokinsa a tashi guda. Dafe kansa kawai ya yi, yana ƙoƙarin shanye kukan da ke niyyar kufce masa.


***


Cike yake da mutane gidan na su, sai shige da fice ake, ana ta shirye shiryen tafiya wurin walima. Tun bayan da ta yi wanka sam hankalinta ba ya jikinta, yana ga Modu da take tunanin za ta fita ta bar shi yau. Ga shi kuma idan ta tafi wurin walimar, ba da an gama za ta dawo gida ba. Sai sun yi tasu ta musamman a tsakanin ƴan ajinsu.


Tagumi ta rafka, ta rasa uwar ubanta. Ji take kamar ta ɗaura hannu a ka ta yi kuka, sai dai babu dama. A wani sashe na zuciyarta kuwa ji take ina ma a ce an ɗaga wannan walimar, har zuwa wani lokaci, duk kuwa da zakwaɗin zuwanta da ta ringa yi a baya.


Sallamar Muhammad ce ta dawo da ita daga duniyar da ta lula ta tunani. Saurin amsa sallamar ta yi haɗe da ci gaba da shafa powder, tana ƙoƙarin miyar da komai ba komai ba.


"Yaya Maryama, Mama ta ce wai ba ki gama shiryawa ba? Wai kar a makara. Kuma kar ki manta da maganin Yaya."


"Na kusa kammalawa Hammad. Ka ce ina zuwa. Na ba shi maganin tun kafin na yi wanka."


Ficewa ya yi a guje tare da sanarwa Mama saƙon Maryama.


Jiki babu ƙwari ta gama kimtsawa. Hijabinta ta zira har ƙasa sannan ta fito, mutane ta gani dangin Mama da na Abba, zazzaune da yawa, wai a haka ma wasu sun yi gaba tare da Abbah, wasu kuma Mallam Ya'u ya tafi da su, sai ya dawo ya ɗauki Maryama sannan a kwashe sauran mutanen.


Har ƙasa ta duƙa ta gaggaishe su, sannan ta nufi ɗakin Hammad inda Modu yake, ta same shi zaune ya yi tagumi, ruwan hawaye na kwaranya a bisa fuskarsa. Yana ganinta ya yi gaggawar janye hannuwansa daga tagumin da ya yi, saboda ta ce da shi matuƙar bai daina yin tagumi da kuka ba, ba za ta taɓa kai shi inda Amrah ba. Wannan dalilin ne ya sa duk sadda za ta shigo zai kwantar da hankalinsa, ta ci gaba da saka shi cikin farin ciki da walwala.


"Ba ka daina ba ko?"


Ta faɗa tana harararsa, bayan ta ƙarisa shigowa cikin ɗakin.


Kansa ya ringa gyaɗa mata, yana ƙoƙarin yin dariyar yaƙe, wanda a kodayaushe ya yi shi, sai zuciyar Maryama ta sake karaya, saboda ji take ina ma dai ya dauwama a haka cikin walwala, ina ma a ce hankalinsa ya dawo gangar jikinsa.


"Yauwa ɗan albarka. Yau ba za mu samu damar yin wannan darasin ba. Amma dai ina fatar ka haddace wancan ɗin da muka yi."


Kansa ya gyaɗa har yanzu bai daina mata murmushi ba.


"To ɗan tuna min ma, a ina muka tsaya?"


Ta karkaɗe kunnenta haɗe da nuna masa shi da hannunta.


Toshe bakinsa ya yi sannan ya fara magana ƙasa-ƙasa, wacce duk kusancinka da shi ba za ka taɓa gane me ya faɗa ba.


"Ya Noor ba na jin ka fa."


Ta faɗa da wata murya, tana kallon cikin idanuwansa.


Baza mata na shi idanuwan ya yi yana kallo, haka kawai ya samu kansa cikin bege, ya ƙara tuno wasu abubuwa game da Amrarsa. Shiru ya yi, gabansa na tsananta duka, ya kasa koda ƙyafta idonsa ne.


Ganin haka ya sa Maryama ta raina kanta. Ta rasa gano manufarsa, ta kuma samu kanta da faɗuwar gaba.


"Uhm...bara na tafi."


Janye hannuwansa ya yi daga bakinsa, ya ɗan langaɓe kansa, da murmushi ya ce,


"Kin ce wai soyayya da ƙauna suna da bambanci. Soyayya takan ƙare a wasu lokuta, saɓanin ƙauna da babu abin da ke kankare ta. Kuma kika ce...me ma?"


Ya ɗora hannuwansa a kumatu alamun tunani. Sannan ya murmusa ya ce,


"Wai akan yanke soyayya ta wani dalili. Ko mutum ya naƙasa, ko ya haukace, idan soyayya ce ake yi to za ta gushe. Ita kuma ƙauna duk wuya duk rintsi ana tare. Babu abin da ke lalata ta. Kuma a ƙarshe kika ce wai irinta ce nake ma Amrahhhh."


Ya ja maganar a ƙarshe, haɗe da rufe idanuwansa alamun kunya.


Tafa masa ta yi tana dariya.


"Good job Ya Noor ɗina. Lallai kana ganewa sosai, kwanyarka tana ja. Na tabbatar kam ka fahimci wannan darasin, sai kuma gobe insha Allahu za a ƙara maka wani."


Ɓata fuskarsa ya yi alamun jin haushi,


"Ni yau nake so."


Samun wuri ta yi ta zauna a kusa da shi, ta sauke ajiyar zuciya haɗe da faɗin,


"Ka cika rigima Ya Noor. Yau fita zan yi fa. Ranar farin ciki ce a gare ni, kai ma ya kamata ka zama a cikin farin ciki. Walimar saukarmu fa ake yi."


Zullo ya hau yi a saman gadon, yana jin daɗi sosai ya ce,


"Amrata ma an musu walimarsu ta sauka."


Dafe kanta ta yi Maryama, nan ta fara tunowa da kalaman Sandra, inda ta tabbatar mata da cewa losing memory ɗinsa ne ya yi Annur. Kuma dama mutum yakan tuna wasu abubuwa da suka danganci dalilinsa na yin losing memory ɗin. Wanda idan har zai samu mai ɗora shi a saman hanya, sannu a hankali zai fara dawowa hayyacinsa. Zai fara tuna komai na rayuwarsa da ya manta.


"Zan tafi. Anjima Hammad zai zo ya ba ka maganin rana. Kar ka musa masa, da zarar ya ba ka ka karɓa ka sha, idan ba haka ba kuma zai faɗa min, kuma ba za mu sake yin darasi ba."


Kai kawai ya gyaɗa mata, da haka ta fice daga ɗakin, ta samu har Mallam Ya'u ya dawo, wucewa kawai suka yi zuwa Islamiyyarsu.


*


Taro ne na ji da faɗa aka yi. Rumfuna aka kafa manya manya, ga plastic chairs nan birjik an jera. Ga ɓangaren da manyan baƙi za su zauna, da kuma na sauran al'umma. Sai daga can gefe kuma masu saukar ne sai farin ciki suke. Maryama da Jiddah jere suke da juna, komai nasu iri ɗaya ne, hatta da yadin hijabinsu babu bambanci.


Addu'ar buɗe taro aka yi, kafin nan aka kira shugaban makaranta domin yin bayanin tarbar baƙi, da kuma nuna farin cikinsa ga wannan rana. Bayan ya gama kuma ya ɗora da bada tarihin makarantar, kamar yadda kusan kowacce walimar sauka akan yi, shugaban makaranta yana bada tarihin makarantar. A sadda ya kai gaɓar aya a zancensa, ɗai-ɗaikun mutane ne ba su koka ba. Saboda da dama an san labarin Amrah, an kuma san sadda ta rasu. Sai ya zama kamar tsohon tabo ne aka fama musu. Maryama uwar kuka ma dasa nata ta yi, tunawa da labarin Amrah da ta yi, da kuma alƙawarin da ta kasa cikawa na ziyartar Umman Amrah da ta alƙawarta yi a kai a kai.


Kamar an ce ta ɗaga kanta, ta hango iyayen Amrah tafe, fuskarsu ƙunshe da annuri.


Hango shi da shugaban makarantar ya yi ya saka shi faɗin,


"Ga mahaifinta nan ma ya iso, za mu so jin wani abu daga bakinsa."


Da murmushi ya karɓi loud speaker ɗin, ya fara da sallama, sannan ya ce,


"Duk da dai ban san me zan ce ba, kasantuwar mun zo a ƙurarren lokaci, duk da haka ba zai hana ni jawo hankulanmu ba, game da riƙo da Al'qur'ani, musamman ma ku ma su saukar nan..."


Ya fuskanci masu saukar, yana jinjina kansa, sannan ya dora da faɗin,


"Kar ku ga ai kun sauke, sai ku banzatar da karatunku, ku daina yinsa baki ɗaya. Al'qur'ani na da wani abu, da zarar ka bar shi da awa ɗaya, to zai bar ka da yini ɗaya. Idan ka bar shi da yini ɗaya, zai bar ka da sati ɗaya. Idan ka bar shi da sati ɗaya, zai bar ka da wata ɗaya. Idan kuwa ka bar shi da wata ɗaya, shi kuma sai ya bar ka da shekara. Idan ka bar shi da shekara, sai ya bar ka baki ɗaya. Shin za mu so littafi mai tsarki ya bar mu? Za mu so karatun da muka yi ya tashi a iska? Ba za mu so ba. To sai mu dage. Mu riƙe shi ƙyam, sannan kuma mu kiyaye sa. Kamar yadda manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, mafi alkhairinku shi ne wanda ya san Al'qur'ani kuma ya kiyaye shi. Sai mu dage, mu jajirce, kamar yadda na tabbatar iyayenku sun ji daɗin wannan ranar, ina fatar su ci gaba da jin daɗi game da ku har ƙarshen rayuwarsu. Ku dage ku ma ku sanar da wasu, sai ku samu kwantankwacin ladar da za su samu yayin da suka aikata kyakkyawa.


A daidai sadda muke isowa na ji bayanai daga bakin shugaban makaranta; silar buɗe ta, da kuma Amrah baiwar Allah, wacce har yanzu mutuwarta ta kasa kankaruwa daga zukatan dubban mutane. Rayuwarta ta zama abar da kowane uba zai yi burin ƴarsa ta zamto haka, kowacce uwa za ta so ƴarta ta kasance da wannan halayen. Ni ne mahaifin Amrah, kuma har yau har gobe na kasa daina shi mata albarka. Na kasa daina zubda ƙwalla da mutuwarta. Rayuwarta mai shiga zukata, haka kuma mutuwarta mai zama a zukata.


A ƙarshe ina muku addua ya ku wannan ɗalibai, kuma ƴaƴaye a gare ni, da rayuwa mai albarka ta tabbata a gare ku. Allah ya albarkaci karatunku. Allah ya ba ku ikon amfani da shi har ƙarshen rayuwarku. Na gode."


Ya ajje loud speaker ɗin haɗe da barin wurin, ya isa wurin zaman manyan baƙi, inda aka tanadar masa.


Sosai bayanan Mallam Abdallah suka ƙara narkar da zukatan dubban al'umma. Kuka sosai ake yi a wurin.


Daga nan aka ci gaba da gabatar da karatuttuka, yayin da ɗaliban ke fitowa ɗaya bayan ɗaya, suka karɓi kyaututtukansu.


Ƙarfe ɗaya daidai aka kammala. Nan aka fara warwatsewa, yayin da ɗalibai masu sauka suka fara haramar yin tasu gagarumar walimar, ta yasu yasu kawai.


Kafin nan sai da Maryama ta je wurin Umman Amrah, bayan sun gaisa ne Ummah ke mata murnan saukar tasu. Sosai Maryama ta ji kunya, ta ba Umma haƙuri a kan rashin komawarta, sannan ta mata alƙawari lallai za ta zo gobe, saboda akwai gagarumar maganar da take so su yi.


Umma ta ce da ita babu komai ta kwantar da hankalinta, ai ta san yanayin hidimomin ne, bare kuma ita da take ɗaliba.


Bankwana suka yi da Umma ta tafi, Maryama kuma ta nufi inda sauran ɗaliban suke. Amma fa rabi da rabin hankalinta na ga Modu da ta baro yau, tana jin kamar ba ta kyauta masa ba.


***


11th January 2010
Bama, Maiduguri.


Zaune take tana ma wata budurwa wacce za ta kai kimanin shekaru ashirin susar kai. Suna yi suna ɗan taɓa hira, yarinyar na faɗin,


"Aunty jiya Anas ya ce da ni wai ya kamata ya ga Abbu su yi magana. Wai gidansu ana ta masa maganar aure. To ni dai ban san me zan faɗa masa ba, ban kuma san ta hanyar da zan iya tunkarar Abbu da wannan maganar ba."


Mahaifiyar tata ta ɗago yarinyar haɗe da komar da ita zaune. Ta ce,


"Yamaira kenan. Wannan ai abun farin ciki ne, wanda ya kamata a ce kin faɗe shi ba tare da shakkun komai ba."


Kunya ta ji wacce aka kira da Yamaira, ta rufe fuskarta ba tare da ta ce komai ba.


"Yau zan faɗawa Abbunku, insha Allahu idan ya dawo. Duk yadda muka yi da shi zan sanar da ke, sai ki faɗawa Anas ɗin."


Wani matashi ne ya shigo cikin falon, da faraa ƙunshe a saman kyakkyawar fuskarsa, ya ce,


"Sannunku da hutawa Aunty."


"Yauwa Sans. (Sunan da take kiransa da shi kenan, saboda tana kararsa sosai, kasantuwarsa ɗan fari ne. Sans kuma ya samo asali ne daga sunansa Salman Nasir Shuwa. Sai ya zamanto sunan ya bi shi, har ma an daina kiransa da Salman ɗin.)"


"Yaya Sans wannan girl friend ɗin taka ta damen da kira fa. Kullum sai ta min kira aƙalla uku ko huɗu, kawai don a gaisa. Ni na gaji."


Wani kallo Sans ya watsa mata, ya ce,


"Ji min yarinya. Wato daga ma kin samu ana kiranki shi ne har da wani jan aji ko. Sannu kin ji."


Murmushi ta yi haɗe da ɗaukar ribbom ɗinta ta fara faka yalwataccen gashinta.


"Yamaira kamar wayata na ringing. Taimaka ɗauko min da sauri kar ta tsinke."


Da saurin kuwa ta rashi ta ɗauko, sai dai bisa rashin sa'a har ta tsinke a lokacin.


Kafin ta yi dialing mai kiran sai ga shi ya sake kiranta, da sauri ta gaggauta ɗauka da sallama a bakinta.


Miƙewa tsaye ta yi bayan yin sallamar, cike da tsoro da firgici ta dafe gabanta. Zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.


Cikin muryar kuka ta ce,


"Ina za mu tafi mu bar ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login