Showing 3001 words to 6000 words out of 201092 words

Chapter 2 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

Ta gwada masa k'ofa da hannu.


Kama kunnuwansa ya yi ya ce,


"Zan yi yanzu Yaya." Ya fita daga d'akin.


"Assalamu alaikum." Ya fad'a da k'arfi wanda har sai da dariya ta nemi k'wace ma Maryama.


Amsa sallamar ta yi ta ce "Ko kai fa. Ka tafi kawai Muhammad. Ka ce da Baba akwai inda zan biya ne kafin in tafi. Kar in tsaida ku kuma na san tahfiz d'inku babu wasa. Ka ga ko karyawa ma ban yi ba."


"To shi ke nan Yaya. Na tafi." Ya yi gaba.


Addu'a ta masa sannan ta ci gaba da shirinta cike da natsuwa, wanda dama halinta ke nan, komai nata a natse ne, slow d'in nata ma har ya yi yawa kamar wacce k'wai ya fashe mawa a ciki.


Misalin takwas da kwata ta gama shiri ta fito falo, Mama ta samu zaune da littafin hisnul-muslim a hannunta tana karantawa.


Ganin haka ya sa ta nufi kitchen, ruwan lipton ta zubo sannan ta zuba soyayyar doya a plate ta dawo falon.


A hankali take karyawa har ta gama sannan ta fitar da kayakin ta kai su kitchen. Ko da ta dawo har Mama ta gama adhkar d'in.


Gaishe ta ta yi sannan ta ce,


"Mama har an gama?"


Da fara'a Mama ta ce,


"Wallahi kuwa na gama Maryama. Ya aka yi yau kika makara? Na san halin malaman nan naku fa wani lokaci ba sani ba sabo ne."


"Ai da yake yau zamu fara rehearzal ne Mama. Duka d'aliban ma za'a ke fiddowa a fili muna yi a gabansu. Tun daga nan har lokacin walimar." Maryama ta bata amsa tana k'ok'arin zura hijabinta da ta ninke ta d'ora a bisa hannun kujera.


"Af! To masha Allahu! Allah Ya taimaka. Dawowa ba yanzu ba ke nan ko?"


"Gaskiya kam Mama. Wata k'ila ma ta-zarce zamu yi har shida na yamma sannan mu dawo." Maryama ta fad'a, ba kuma 'karya ta yi ba, haka tsarin abun yake, sai dai kuma ita kam ba can zata nufa ba, sai idan ta gama abin da take da wuri ne zata je ko da da yamma ne.


"Bara na tafi Mama." Ta fad'a tana k'ok'arin fiddo hannunta daga hannun hijabin.


"Allah Ya bada sa'a. Sai kin dawo."


"Ameen Mama." Ta fita daga d'akin.


Sai da ta koma d'akinta ta d'auko kud'i sannan ta fita.


A dai-daita sahu ta tsayar ta kwatanta masa unguwar.


K'arfe tara da minti ishirin ta mata a k'ofar gidan su Amrah. Bayan ta sallami mai adai-daita ta shiga gidan da sallamarta.


Amsawa matar gidan ta yi sannan Maryama ta shiga ciki da fara'a.


"Sannu da zuwa Maryama. Iso ciki." Ta fad'a cikin karramawa.


Shigowar kuwa ta yi har falo matar ta kai ta. Wasu irin tsofaffin kujeru ne irin wanda sun ji duniya d'in nan, katifar jiki duk ta gama lalacewa sai zallar katako wanda idan mutum bai kula ba ma tsaf zai iya jin ciwo.


Bayan ta zauna matar ta ce,


"Bara na kawo miki koko. Sai dai kuma yanzun nan na ba almajiri k'osan, saboda kar ya sandare kuma ba cinsa zan yi ba, kokon ma a samus na zuba shi ne."


"Wallahi Mama ki bar shi na gode. Sai da na karya ma sannan na baro gida." Maryama ta fad'a.


"Eyyah! To shi ke nan ai. Ina zuwa." Ta fita daga falon.


Babu jimawa sai gata ta dawo, zama ta yi daga d'an nesa da Maryama san nan ta ce,


"Yanzu zan baki labarin Amrah, Maryama."


Gyara zama Maryama ta yi ta ce,


"To ina jin ki Mama."


"Sunanta ke nan na yanka Amratu. Amrah muke kiranta da shi ni da mahaifinta.


Amrah ita ce 'ya ta uku a gidan nan, sai dai kuma matsayin ita ce babba, kasantuwar duk yaran da muka haifa basa rayuwa.


Tun daga lokacin da muka haifi Amrah, mahaifinta ya d'auki soyayyar duniya ya d'ora a kanta, yake bata kulawa sosai fiye da sauran yaran da muke haifawa basa rayuwa.


Tun Amrah na da shekara d'aya a duniya take da wani laluri, na yawan k'ai-k'ayin tafin k'afa da kuma tafin hannu.


Abin mamamki, yarinyar da bata san wani abu ba a duniya, amma duk lokacin da tafin k'afarta ko hannunta ya dame ta da k'ai-k'ayi, da 'karfi zata kama hannuna ko na mahaifinta tana kai wa a inda yake mata k'ai-'kayin, da nufin a sosa mata.


Tun bamu fahimtar komai har ta kai ga mun fara fahimta, wato dai suna damunta da k'ai-'kayi ne.


A lokacin da ta cika shekara biyu a duniya ne kuma cututtuka suka fara nata yawa, wato yawan zazzab'i, sannan kuma da yawan ciwon gab'ob'i.


Yarinya k'arama 'yar shekara biyu, wacce ko maganar kirki bata iya ba, amma ta san ta ringa gwada duk inda ke mata ciwo tana fad'in,


"Hannu ciwo, cici ciwo, kai ciwo..." da dai sauransu.


Tun bana d'aukar abun serious har na fara damuwa, saboda har cikin dare idan abun ya tasar mata ko kad'an bama bacci, ita kuka ni kuka, mahaifinta ne kawai mai dakewa, yake k'arfafa min guiwa a ko da yaushe.


Ga ta da yawan yin zazzab'i, da zarar sauro ya cije ta sai zazzab'i, idan ta fara zazzab'in kuma shi ne sai wannan ciwon gab'ob'in wanda yake rikita mana lissafi.


Duk wannan abin da yake faruwa, ciwo da yake ta addabar Amrah, ko da wasa bamu tab'a gwada kai ta asibiti ba. Wani lokacin idan zazzab'in ya dame ta ne da kanshi Babanta yake zuwa chemist cewa 'yarsa na zazzab'i, sai a bashi maganin zazza'bin kawai ya zo a bata.


Wata rana, k'anwata ta zo daga Kaduna, ta zo ganin gida shi ne ta zo min wuni, ta samu Amrah bata da lafiya, na tasa ta a gaba ina mammatsa mata duk gab'ob'inta da take gwada min suna mata ciwo.


Cikin tausayi ta ce,


"Wai Yaya Murja me yake damun yarinyar nan ne? Abin tausayi har ta iya fad'in inda ke mata ciwo? Alamun ma ta saba ke nan."


Gyad'a kai na yi na ce,


"Zainabu ni kaina ban san me yake damun Amrah ba. Sai dai kawai na san zazza'bi ne idan ta yi shi yake sakar mata ciwon gab'ob'in nan. Tun da nake haifar yarana suna mutuwa ban tab'a had'uwa da mai irin ciwon da Amrah ke yi ba. Zainabu na fara tsorata sosai wallahi." Ta fashe da kuka tana kallon Amrah.


Ita kam Amrah baki ta wangale tana dariya, shi k'aramin yaro dama babu ruwanshi, yanzu zai gama kukan ciwo kuma yanzu zai kama dariya.


Zainabu ta numfasa sannan ta ce,


"Kuma ku baku tab'a kai ta asibiti ba?"


"Bamu tab'a ba Zainabu. Sai dai kawai Babanta da yake siyo mata magani. Yanzu haka tana da sauran panda yana nan bai k'are ba." Na bata amsa.


"Gaskiya Yaya Murja ku daure dai ku kai ta asibiti. Kar a je ana ciwo daban, magani daban. Likita bashi da halin bada waraka, sai dai kuma yana bada tashi gudunmawar. Ki daure dai a kai ta d'in."


Shiru na yi ina nazari a azuciyata. Na san tabbas gaskiya Zainabu ta fad'a min, sai dai kuma babu hali ne. Abincin da zamu ci ma wahala yake mana. Kuma ba wai zuwan ne nake ji ma ba, a'a, kud'in da za'a caje mu nake ma. Tun da dai komai na yanzu ya koma na kud'i.


"Kin yi shiru Yaya Murja. Gaskiya nake fad'a miki fa. Bai kamata ku zauna kuna ji kuna gani ciwo ya ringa cin yarinya ba. A ce wai yarinya da zarar ta yi zazzab'i sai k'asusuwanta su hau ciwo? Gaskiya akwai dai wata matsalar daban, ba wai zallar zazzab'i ba ne."


Cikin k'arfin hali na ce,


"Insha Allahu ranar litinin zan kai ta asibiti. Ni kaina abin yana damu na bani da yanda zan yi ne."


"To Allah Ya kai mu Yaya Murja. Allah kuma Ya bata lafiya." Ta mik'e.


Bankwana muka yi sannan ta tafi ta bar ni da tunanin kalamanta, hawaye na zirara daga idanuwana zuwa kumcina.




Pinky durling💗
*RAZ 2👌🏻*
[8/30, 3:28 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


0⃣4⃣


Sai dare sannan mahaifinta ya dawo, a gajiye lis yake, wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da baya tattare da walwala.


Duk da cikin halin da nake, na tausayin ciwon Amrah, bai hana ni tashi na tarbe sa ba.


"Sannu da dawowa Mallam. Zauna ka huta kafin na kawo maka abinci." Na fad'a ina mai k'ara dubar yanayinsa.


"To Murja." Ya fad'a jiki a sab'ule.


Kitchen na nufa na zubo masa dafadukar shinkafa da na ajje masa, na d'ibo ruwa daga tulu na kawo masa.


Sai da ya ci ya yi nat, na tabbatar ya samu natsuwa sannan na ce,


"Allah dai Ya sa an yi nasara."


Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce,


"Babu nasara Murja. Abin dai sai hamdala kawai." Ya kalle ni ya gyad'a kai, sannan ya ci gaba da fad'in,


"Duk yinin nan guda da muka sha, wai Alhajin ya fasa zuwa. Har fa lokacin da na ga magrib ta yi na ce ni dai zan tafi, wasu suka ce in dai k'ara ha'kuri, an tabbatar cewa yana gari wai zai zo. 'Yar d'ari biyun da nake da ita, da ita na ci abinci da rana, naira ta hamsin d'aka da waje yanzu haka. Ban san ya zan yi ba Murja. Talauci babbar cuta ce, wacce samun maganinta yake da matuk'ar wahala." Ya dafe kansa.


Cike da tausayi na ce,


"Sai hak'uri Mallam. Ta ko wace hanya Allah Yana jarrabtar bayinSa. Hakan kuma ba wai yana nunar da baYa sonmu ko kuma Ya manta da mu ba ne, a'a, na tabbatar cewa mun fi wasu, tun da mu da wuya mu rasa abin da zamu ci. Wasu kuwa babu, abin da zasu saka ma cikinsu ma wata wahala ne. Fatana dai kawai Allah Ya bamu ikon cinye wannan jarabawar."


"Ameen. Wai duk jiran nan da muka yi, sai bayan isha'in nan wani d'an korensa ya zo yana fad'in mu tafi, wai Alhaji ba zai samu zuwa ba, sai kuma wani lokacin. Dama kyauta ce ya yi niyya ba rok'arsa aka yi ba, kuma wani uzuri ya sha gabansa."


"Shi ke nan ai Mallam. Ka cire damuwa daga ranka. Allah Yana tare da mu..." tun ban rufe baki ba Amrah ta fasa kuka tare da tashi zaune, saboda dama tun d'azu ta yi bacci.


Da sauri na kama ta na d'ora a bisa cinya, ina rirrigarta a hankali had'e da tofa mata addu'o'i, dan a tunanina ko firgita ta yi ne. Abin mamaki sai d'ago min hannunta ta yi, cikin maganarta da bata gwanance ba ta ce,


"Umma hannu ciwo.." ta kuma fashewa da wani kukan.


Gyad'a kai na yi cike da tausayi, na kama hannun nata a hankali ina mammatsawa ina tofa mata addu'a har na samu ta yi shiru.


Bayan kamar mintuna biyar ta ce,


"Umma ya daina ciwon." Ta sakar min murmushi.


"To ki gode wa Allah kin ji 'ya ta? Allah Ya baki lafiya da duk kan 'yan uwa musulmai." Na fad'a ni ma ina mata murmushin.


Bakinta dama ya dad'e da sabawa da furta amin, hakan ya sa ta ce,


"Ameen Umma." Ta sauka daga jikina da sauri ta nufi mahaifinta, saboda sai a lokacin ma ta kula da shi.


Saurin kawar da damuwarsa ya yi ya d'auke ta,


"Amrah 'yata sannu kin ji? Insha Allahu zaki samu lafiya ke ma kamar kowa."


Bata ce komai ba sai lafewa da ta yi a jikinsa, take bacci ya d'auke ta.


Tabbatarwar da muka yi ta yi bacci ya sa a hankali ya nufi uwar d'aka da ita, ya kwantar sannan ya nufi yin sallah.


Bayan ya gama a lokacin nima na shigo d'akin har ma na kwanta a kusa da Amrah, ya hau gadon zai kwanta na yi saurin mik'ewa na ce,


"Ka gaji ko? Da alama kwanciya kake son ka yi. Gashi kuma ina son da mu yi wata magana."


Bayan ya hau gadon ya ce,


"Babu komai Murja. Ina saurarenki."


Saurin share k'wallata na yi sannan na ce,


"Dama gani na yi ya kamata mu kai yarinyar nan asibiti, sam bamu kyauta ba zaman da muke yi haka da ita, ba tare da sanin halin da take ciki ba. Mallam ban tab'a jin yaro mai irin lalurin Amrah ba, rayuwata tana matuk'ar dugunzuma a duk lokacin da ciwon yarinyar nan ya taso, tana matuk'ar bani tausayi. Tun bata san miye ciwo ba har ta kai ga ta sani yanzu. Yarinya 'yar shekara biyu da watanni amma har ta san ciwukanta."


Cike da tausayi Mallam ya ce,


"Haka ne Murja. Ni ma kaina na jima ina wannan tunanin, ina jin tausayinta sosai musamman yanda har cikin dare ba wani baccin kirki take samu ba. Ya kamata mu je asibiti, idan ma wani ciwon ne sai mu sani, mu bi dokokinsa ko ta samu sassauci."


Cikin kuka na ce,


"Haka ne Mallam."


Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce,


"Gashi kuma bani da kud'i Murja. Ban ajje ba ban ba wani ajiya ba. Na abin hawa ma kanshi babu bare kuma na sauran hidindimun asibiti. Wayyo ni Abdallah!" Sai ga hawaye suna zarya a bisa kumcinsa.


Duk da ni ma ina jin hawayen amma a haka na daure, shi ya koma macen ni kuma na koma namiji, na ci gaba da rarrasarsa har na samu ya yi shiru.


"Akwai 'yan samiruna da tasoshi tun na aure, suna wancan d'akin na ajiya tun-tuni. Insha Allahu da sassafe zan je gidan Rakiya Dillaliya, wata k'ila zata siya. Ko nawa ne ma dai ta bamu mu samu a kai ta asibitin. Ai ya fi mu je maula ana wulak'anta mu."


"To shi ke nan Murja. Allah Ya kai mu goben Ya sa a yi nasara." Ya furta a hankali.


"Ameen Mallam. Ka kwantar da hankalinka, Allah'n da Ya d'aura mata wannan cutar shi zai warkar da ita, insha Allahu zata warke, ta murmure kamar sauran yara."


Murmushi ya yi sannan ya ce,


"Ina fatan haka Murja. Na gode k'warai Allah Ya miki al-barka."


Da murmushi ni ma na ce,


"Ameen Mallam."


Daga haka bacci ya d'auke mu.


***


Washe gari kuwa tun da sassafe na fiddo 'yan tarkacen da zan siyar, sun yi k'ura sosai saboda sun kai kusan shekaru biyar a ajiye cikin d'akin ban fitar ba. Bashin omo na ci na wanke su tas, har shek'i suke yi sannan na kife suka bushe.


Buhu na nema mai tsafta na saka a ciki, sannan na nufi gidan Rakiya Dillaliya.


Da yake Allah ya duba zuciyarmu, kyakkyawar niyya ce a ciki, babu ko b'ata lokaci Rakiya ta siyi kwanonin, cas ta cake min naira dubu takwas da d'ari biyar.


Na matuk'ar jin-d'adi, da murna na nufo gida, zuciyata sayau, tamkar an ce min Amrah ta warke ne.


Sai da na fara biyawa na biya ku'din omo, sannan na siyo mana bredi da sauran kayan shayi, sai da dai na kaso dubu d'aya sannan na iso gida.


Ko da Mallam ya ga fuskata ya san akwai nasara, ga uwa uba leda a hannuna cike da karikitai.


"Mallam ta siya har dubu takwas da d'ari biyar." Na fad'a masa ina dariya.


Shi ma dariyar ya yi ya ce,


"Ahh lallai abu ya yi kyau. Ta kyauta sosai wallahi."


Halawartsinke na fiddo daga cikin ledar na mik'a wa Amrah, da sauri kuwa ta karb'a tana dariyar jin dad'i.


Kitchen na je na dafa mana ruwan zafi, na zuzzuba mana sannan na zuba kayan ha'di.


K'arfe goma da rabi muka gama, na ma Amrah wanka muka shirya sannan muka fito, Mallam ya rufe gidan muka nufi bakin titi.


Bamu jima ba muka samu keke napep, asibiti muka ce ya kai mu, ya tambaya,


"Mallam wace asibitin zan kai ku?"


Shiru muka yi mu duka dan bamu san inda zamu je ba, hakan ya sa ya sake maimaita mana.


"Wace asibiti ce ka sani wacce ake kula da k'ananan yara sosai?" Mallam ya tambayi matashin.


Shiru ya yi jim kad'an sannan ya ce,


"Ku je asibitin Turai, dama ta yara da masu ciki ce kawai ai." Ya fad'a yana kallon Mallam.


"In haka ne, ai ga Turai d'in can ma babu nisa sosai ko? A nawa zaka kai mu?"


"Ku kawo d'ari da hamsin." Ya fad'a.


Shiga ciki muka yi ya kai mu har cikin asibitin, dama kuwa babu nisa daga gidanmu, duk cikin unguwa d'aya ne sai dai kuma dole mutum ya hau abin hawa, idan ba haka ba kuma akwai gajiya.


Bayan mun shiga reception, muka tambaya abin da ya kamata mu yi, wata mata ta ce sai mun sai mata kati kafin komai.


Mallam ya je da kanshi ya sai mata katin aka cike, sannan aka d'ora a layin ganin paediatrician (likitan yara.)


Har bayan azahar layi bai zo kanmu ba, kusan k"arfe biyu aka kira sunanta.


Likita ce mace, sanye da lab court da medical glasses.


Kujerar dake fuskantarta ta bani izinin zama, bayan na zauna na gaishe ta da sakin fuska ta amsa.


"Me yake damunta ne?" Ta tambaye ni tare da mik'o hannu ta karb'i Amrah.


"Dr. Tak'amai-mai ban san me yake damunta ba, saboda wannan ne karo na farko da na kawo ta asibiti. Kawai dai na san ta jima tana fama da k'ai-k'ayin tafin k'afa da hannu, daga baya kuma sai abun ya canza, ta koma ciwon k'asusuwa, da zarar ta fara zazzab'i sai ko wace gab'a tata ta ringa mata ciwo, yanzu ko babu zazzab'in ma ciwo suke mata."


Zare glasses d'inta ta yi ta ajiye daga gefe sannan ta hau dudduba Amrah, ta cire mata kaya.


Tana cikin dubawar ba tare da ta d'ago kanta ba ta ce,


"Me nene genotype d'in ki? (Sinadarin jini)"




Pinky durling💗
*RAZ 2👌🏻*
[8/30, 3:29 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


0⃣5⃣


Cikin mamaki na kalle ta, ina k'ok'arin tuna a inda ma na san kalmar, saboda na yi boko bakin gwargwado, sai dai ban yi zurfi sosai a ciki ba, daga JS 3 na tsaya ban samu damar ci gaba ba. Mahaifinta kuma ya gama secondary ne bai wuce ta gaba ba.


"Me nene genotype d'in ki?" Ta sake tambaya ta bayan ta d'ago kanta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login