Showing 84001 words to 87000 words out of 201092 words
Chapter 29 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
kasa yin nasara har yanzu? A yanda mahaifiyar Amrah ta sanar da ita, ko kaɗan Amrah ba ta kasance mai ƙarya ba, komai za ta yi to iya gaskiyarta za ta yi shi, koda kuwa hakan na nufin rashin farin ciki a gare ta. Me ya sa ba za ta zama mai koyi da halayen Amrah ba? Me ya sa ba za ta zama abar alfahari ga nata iyayen, kamar yanda na Amrah suke alfahari da Amrah ba?
Share hawayenta ta yi ta jawo wayarta, ta latsa kiran Jiddah. Bugu biyu ta ɗauka tana faɗin,
"Su Mama sun amince ko? Ai dama na san ba za su ƙi amincewa ba."
Shessheƙar kukan da Jiddah ta ji Maryama na yi ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi. Cikin lallausar murya ta ce,
"Maryama kar dai ki ce min ba a dace ba."
Cikin kuka Maryama ta ce,
"Ba a dace ba Jiddah. Sam! Wannan shawarar ba ta ɓullar da ni ba. Jiddah ban taɓa yiwa Mamana ƙarya irin haka ba, na tabbata Allah ba zai ƙyale ni ba. Ba zan taɓa samun nasara ba matuƙar ina ci gaba da yi ma iyayena ƙarya."
Cike da damuwa Jiddah ta ce,
"To fa! Abu bai yi daɗi ba kuwa. Kuma yanda na faɗa miki ɗin haka kika yi?"
"Haka na yi Jiddah. Abba dai ya turo min kuɗi wai na tura musu, in faɗa musu ba zan samu zuwa ba. Ita mama cewa ta yi ma na fita daga ƙungiyar baki ɗaya."
Ta sake fasa wani kukan, zuciyarta raunane, tana mai neman mafita.
Cikin kwantar da hankali Jiddah ta fara mata magana, a yadda take maganar, tamkar ta na a gaban Maryama ɗin ne.
"Ya isa haka please! Kukan ai ba zai amfana miki komai ba, dan Allah ki daina."
"Jiddah ban san ya zan yi ba, zuciyata ta riga da ta kamu da son ganin wancan bawan Allah'n. Ban san dalili ba, amma nake ji a jikina akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare da shi. Jiddah ko kin san cewa zargin da nake shi..."
Dakatar da ita ta yi Jiddah, ta ce,
"Na samu shawara, amma fa mai haɗarin gaske, ba lallai ba ne ta zama hanyar ɓullewa."
Maryama ta gaggauta faɗin,
"Allah sa dai ba wata ƙaryar za ki saka ni yi ba, dan wallahi na riya a raina ba zan kuma yi wa iyayena ƙarya ba, sai dai in komai zai lalace."
Ajiyar zuciya ta sauke Jiddah, ta ce,
"Ni kaina na gano babban kuskuren da muka tafka a karo na biyu, wanda duk hakan ne yake jawo tangarɗa a plans ɗinmu. Shi ya sa dama na faɗa miki, wannan kam ba lallai ba ne a yi nasara."
"Ina jin ki Jiddah, go on."
"Me zai hana kawai ki tunkari Mama da maganar, ki faɗa mata gaskiya? A gani na hakan kawai zai iya zame mana mafita, idan ta amince shi kenan, ida ma ba ta amince ba sai mu haƙura, kawai ki fita daga al'amarin, duk yanda Allah Ya tsara daidai ne."
Cike da yaƙini Maryama ta ce,
"Haka ne Jiddah, tabbas na yi wannan tunanin ni ma. Kawai mu daina ɓoye ɓoyen."
"Tabbas kuwa. Yanzu yadda za a yi, kawai bari gobe da safe idan na yi shirin islamiyya in biyo ta nan, ni zan tinkari Mama da maganar, na san ta sigar da zan mata, kuma insha Allahu za ta amince."
"I trust you Jiddah. Allah Ya kai mu goben."
"Ameen. Sai da safe. Please ki cire damuwa daga ranki, Allah Ya na tare da mu, kuma Ya ga zuciyoyinmu taimako muke son yi."
"Na gode ƙwarai. Sai da safe."
Kashe wayoyin suka yi su duka. Duk da damuwar da Maryama take ciki, haka kawai take jin nutsuwa a cikin zuciyarta. Hankalinta ya ɗan kwanta yanzu kam. Tabbas ƙarya fure take ba ta da ɗa. Mai gaskiya ba ya taɓa shiga shakku, a duk inda zai je.
***
Tun daga lokacin da boka ya lalata true love ɗin da Annur ya faɗa, sai ya samu sauki, hankalinsa ya kwanta sosai, yanzu kam ba shi da sauran fargaba, tunda ya ga Dady'nsa ya koma yanda yake masa a baya. Ko ya je aiki ko bai je ba, iyayensa ba sa masa faɗa, ko kaɗan ba sa takura shi. Sai wata irin ƙauna da take ƙara shiga a tsakaninsu. Mugun halinsa kuwa ƙara ta'azzara kawai yake. Shaye shaye da mugun bin matansa, sai abin da ya ci gaba. A wannan lokacin kam babu soyayyar Maryama ko kaɗan a zuciyarsa. Sam! Ya ma manta da ita a doron ƙasa. Dama tuni aka fidda masa Jiddah daga zuciyarsa, Maryamar dai ce abun ya gagara, har sai da boka ya yi aiki a kanta.
Sigari yake zuƙa, yana jin yanda zuciyarsa ke masa daɗi, rayuwarsa na cikin kwanciyar hankali. Sosai yake jin duk wata gaɓa ta jikinsa na ƙarfafa masa guiwa wurin aikata alfahsharsa, ta hanyar ingantacciyar lafiya da yake da ita.
Wayarsa ce ta yi ƙara, ya ɗan karkaɗe tokar sigarin, haɗe da jawo ta a jikinsa, yana duba mai kiran nasa.
Sunan da ya gani ne ya sa shi gaggauta ɗauka, yana murmushi ya ce,
"Abokina ya dai?"
"Normal guy. Kana ina ne?"
"Ina gida. Akwai damuwa ne?"
Daga ɗaya ɓangaren Bobby ya ce,
"Babu damuwa. I just wanna see you right now."
"Akwai damuwa kenan."
Annur ya faɗa.
"Ehh to, wata damuwa ce a tattare da ni, tun ina ɓoyo dai na ga ya kamata ko kai na sanar da kai, gudun samun matsala."
Ajje karan sigarin ya yi a bisa ɗan ƙarfen da yake ɗorawa, cike da damuwa ya ce,
"Me yake faruwa da kai guy?"
"Tarin nan dai da nake yawan fama da shi ne, ka sani ai. To abun yake damu na sosai, ba kaman da ba, yanzu fa har da jini nake fitarwa daga maƙoshina. Na rasa ta ina matsalar take."
Zaro idanuwa ya yi Annur, tamkar yana gaban Bobby ɗin ne, ya ce,
"Matsala fa babba ba ƙarama ba guy. Me ya sa kake zaune da ciwo ba ka faɗawa kowa ba? Ai ya kamata a ce an je asibiti."
Bobby ya ce,
"Dalilin da ya sa na faɗa maka ɗin kenan. Na tabbatar idan na tinkari Abbana da maganar, ba zai tsaya saurare na ba, zai ce shegen shaye shayen da nake ne na jawowa kaina masifa. Ka san halin dai Abba sarai."
Dafe kanshi ya yi Annur, ya ce,
"Ka kwantar da hankalinka. Na tabbata ba wani abu mai girma ba ne. Gobe da safe zan zo in ɗauke ka, sai mu je asibiti a duba ka. Ka kwantar da hankalinka, everything will be okay."
"Thank you very much guy. Am very grateful."
"You are always welcome. Amma ka kiyaye guy, don't drunk today, har sai an gano ta inda matsalar take."
"Ok guy."
Suka yi sallama.
***
kallon sa ta yi da murmushi ta ce,
"Zan tai gida in dawo, mi kake so in taho ma da shi?"
Hannunsa ya ɗora bisa haɓarsa alamun tunani, ya kuma sauke hannun, ya yi dariya sosai haɗe da faɗin,
"Alawa mai tsinke."
Ya ɗan karkace kansa, hannuwansa duka biyun ya rufe fuskarsa, wai shi a dole ya ji kunya.
"Aikam zan taho ma da alawa mai tsinke. Bari in tahi, ka yi min addua ka ji?"
Ta nufi barin ɗakin. Har ta kai bakin ƙofa ta ji muryarsa ya ce,
"Idan an dake ki ki rama. Kar kuma ki ma kowa kuka, ni ne nan zan shigar miki. Ni jarumi ne."
Ya jinjina hannunshi alamun shi ɗin mai ƙarfi ne.
Murmushi ta yi ta ce,
"Banda abunka Modu, halan wa zai bugu na?"
"Yo su mana."
Ya marairaice mata fuska tamkar ya ga ana dukanta ɗin ne.
Da fara'a a fuskarta ta ce,
"To jarumina. Duk wanda yab buge ni ina tahowa in hwaɗa maka, Moduna jarumi."
Sosai ya ji daɗin ɗorasan da ta yi. Ta fice daga ɗakin murmushi shimfiɗe a saman fuskarta.
Koda ta isa gida da ɗar-ɗar ta shiga. Tsoron shiga gidan take, gudun tashin hankali. Duk da yake dai yanzu ta ji huɗubar da Hadiza ta mata, sam! Ba ta jin za ta iya haƙuri da abubuwan da Aunty Sahiya ke mata. Ta gaji, haƙurin da take ne ya sa take mata yanda ta ga dama, har ƙannenta ke taya ta.
Cikin wata irin murya ta yi sallama. Tun a zaure ta gane Yayanta ya dawo, saboda mashin ɗinsa da ta gani ya faka.
Farin ciki ta ji ya ziyarci zuciyarta, gani take tamkar baƙin cikinta ya zo ƙarshe, a tunaninta zai ba ta kuɗin da za ta siyawa Modu magani, koda ba duka ba ne.
A tsakar gida ta same su, ya zauna bisa tabarma, ga kular abinci a gabansa yana ci. Da murmushinsa ya kalle ta, ita ɗin ma ta sakar masa. Ɗan uwa rabin jiki. Take ta ji wani irin daɗi ya lulluɓe ta. Duk da dai yana biyewa matarshi suna ƙin kyautata mata, hakan bai hana shi nuna yana ƙaunarta.
Sunkuyawa ta yi har ƙasa ta gaishe shi. Ya amsa sannan ya ba ta izinin zama a bisa tabarmar.
"Giɗe zuba abinci ki ci. Halan daga ina kike? Tun ɗazu ina ta ma Sahiya magana ta ƙi hwaɗi min inda kika tahi. Sai dai ta ce wai in bari har in kin ga dama kin dawo, sai ki hwaɗi min."
Babu haufin komai Fiddou ta hau ba shi labarin duk abin da ke faruwa. Da zaman da take yi asibiti tare da shi Modu ɗin.
Sosai ya tausayawa Modu. Ko kaɗan ba ta tsammani hakan daga gare shi ba. Ba ma ta zaci zai yarda da ita ba.
"Wayyo bawan Allah! To yanzu halan ya ake ciki? An samu kuɗɗin maganin?"
Daɗi ta ji sosai, ta yi tsammanin ko kuɗin zai ba ta, hakan ya sa da sauri ta ce,
"Ba a samu ba Yaya. Do Allah dai ka taimaka muna idan kana da hali."
Mamaki ƙarara a fuskarsa ya kalle ta. Lallai ma Fiddou. Shi ɗin ta kanshi yake. Biɗar kuɗi ya je kuma ba wani abun kirki ya samu ba. Jarinsa na takalmi tuni ya karye, saboda rayuwar yau da gobe.
Ban so tsayawa a nan ba, dole ce ta sa; ina fama da mura da ciwon kai, zazzaɓi duk a lokaci guda💆 da ƙyar ma na samu yin wannan ɗin. Please include me in your prayers. I love y'all fisabilillah.
Da gaske ne fa, duk abin da aka saka ƙarya a cikinsa ba ya tasiri ko kaɗan. Musamman ma kuma a ma iyaye ƙarya, duk yadda ake ganin kamar an yi nasara, tabbas a ƙarshe za a ga akasin haka. Ramin ƙarya ƙurarre ne. Bari mu gani, ko za ta dace a wannan karon? Ku dai cigaba da bibiyar marubuciyar, sannu a hankali za a zo wurin.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:53 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
4⃣3⃣
follow me on wattpad:
PrincessAmrah
***
Sanye take da doguwar hijabinta mai hannu, ta uniform ɗin Islamiyyarsu. Sannu a hankali take taku, tana jin yanda gabanta ke tsananta duka, fargaba ta dabaibaye mata kaf illahirin jiki da ruhinta.
A hankali ta yi sallama, cikin raunanniyar murya, mai nuna zallar damuwar da take cikinta.
Amsa sallamar ta ji an yi, aka ƙara da faɗin,
"Shigo ciki ina zuwa."
Bisa ɗaya daga cikin kujerun da ke jere a falon ta zauna, ajiyar zuciya take saukewa, lokaci zuwa lokaci.
"A'aha a'aha! Yau Hauwa Jiddah ashe ke ce."
Murmushi ta ƙirƙiro da faɗin,
"Wallahi kuwa ni ce Mama. Allah sa dai Maryama ba ta riga da ta tafi ba."
Bayan Mama ta zauna ta ce,
"Duk yau ko motsinta ban ji ba. Na rasa me yake damun wannan ƙawar taki, shez not in her mood, tun jiya."
Shiru Jiddah ta yi tana taunar leɓonta na ƙasa, sai rarraba idanuwa take, ta sunkuyar da kanta ƙasa.
"Ta zo min da wani batu ne jiya, wanda sam! Hankali ba zai iya ɗaukarsa ba. Ban san me ya sa yarinyar nan baki ɗaya ta sauya min ba, duk wasu shawarwarinta ta daina tunkarata da su, damuwarta ba ta tinkara ta da ita, tun wasu makonni da suka shuɗe."
Cikin ƙarfin hali Jiddah ta ɗago kanta a wannan karon, ta samu zaƙulo sanyayan kalamai daga bakinta.
"Mama dan Allah idan na ce zan miki wani bayani za ki fahimce ni?"
Gyara zamanta ta yi Mama, ƙyam ta ɗaura idanuwanta ga Jiddah, ta ce,
"Zan saurare ki Jiddah, zan kuma fahimce ki insha Allahu."
Ƙasa ta dawo ta zauna Jiddah, ta ajje jakarta daga gefe, ta ce,
"Mama na san Maryama ta ba ki labarin Amrah ko?"
"Tabbas ma kuwa. Labarin da ya girgiza ni, ya taɓa zuciyata, ya zauna min a cikin zuciya har yanzu."
"Mama akwai abubuwan da Maryama ta yi kuskuren ɓoye miki, ba ta sanar da ke su ba, dangane da labarin Amrah."
Ko kaɗan Mama ba ta ɗauke idanuwanta daga fuskar Jiddah ba, hankalinta da komai nata ta tsayar da shi ga Jiddah, sosai take neman ƙarin bayani.
"Mama akwai Annur..."
Ta kwashe komai ta sanar da Mama; tun daga farkon soyayyar Annur da Amrah, har zuwa lokacin da Amrah ta rasu, Annur kuma ya haukace. Ta faɗa mata kaf munanan halayen da Annur ya faɗa, tun bayan sanda ya warke daga hauka, har zuwa wannan lokacin. Ba ta ɓoye mata taimakonsa da suka yi attempting yi a karon farko ba, da kuma silar ƙaryar da Maryama ta musu jiya. A ƙarshe ta fasa kuka, tana ƙoƙarin yin magana Maryama da ke laɓe bakin labule ta fito daga ɗakinta, ta ce,
"Mama ina zargin ba ainahin Annur ba ne a gidansu, wallahi wannan mahaukacin ne real Annur, shi ne masoyin Amrah!"
Ba mama kaɗai ba, hatta da Jiddah sai da ta ɗago kanta da mamaki ta kalli Maryama, ko kaɗan ba ta yi wannan zaton ba. Sai yanzu ma abun ya zo mata. Haƙiƙa biri yai kama da mutum. Ita sai ma yanzu zahirin labarin Amrah ke dawo mata. Cewa tana ganin wani mai kama ɗaya da Annur, wanda har ya taɓa sace ta. To ko dai da gaske shi ɗin ne? Kenan bai warke daga haukan da yake tun bayan mutuwar Amrah ba? Ko kuwa dai ya warke wata cutar ce daban?
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke Mama. Baki ɗaya ma kanta ya ɗaure. Wani ɓangaren zuciyarta tausayin Annur ne ya gama mamaye ta, wani ɓangaren kuwa tunanin mafita kawai take. Shin za ta amince ma ƴarta tarar wannan riskin ne, ko kuwa za ta hana ta aikata taimako?
Hannunta ta sa ta dafe kanta. A hankalin ta shafo shi har bisa fuskarta, ta ce,
"Maryama ta yi kuskure tun farko, na rashin sanar min da wannan al'amarin. Ba a ɓoyewa iyaye matsala irin haka, abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa. Kin sani, daga ni har Abbanku ba za mu hana ki taimako ba, musamman ma ga mutum irin Annur, wanda yake da buƙatar taimakon. Yanzu da kika ɓoye mana halin da kike ciki, inda a ce shi wancan mugun ya miki wani abu, ya kike gani? Dan Allah Maryam kin mana adalci kenan? Yanzu za ki so a ce 'yarki ta cikinki ta miki haka? Ya za ki ji idan hakan ta kasance a gare ki? Sam! Ban ji daɗi ba Maryam, ban taɓa tsammanin akwai abin da zai rusar da alƙawarin da ke tsakaninmu, na sanarma juna damuwarmu ba."
Kneel down ta yi Maryama, hawaye take sosai, ta matso kusa da Mama, cikin muryar kuka ta ce,
"Na sani, ni ɗin mai laifi ce Mama. Dan Allah ki gafarta min, wallahi na rasa ta inda zan fara faɗa miki aikin da nake shirin yi ɗin ne, gudun kar ki hana ni. Amma wallahi na nadama, yanzu kam na gane kurena, na tabbatar cewa ashe dai ƙarya fure take ba ta da ɗa. Duk wanda ya kasance yana aikatata, to tabbas babu shi babu cin ribar komai na rayuwa. Duk wasu tsare tsare na shi za su lalace. Allah Ya sani na nadama, na yi da na sani Mama, wallahi ba zan kuma yi ba. Amma dan Allah ba dan halina ba, ki taimaka ki bar ni na ci gaba da wannan aikin ladar da nake son yi. Insha Allahu babu abin da zai faru sai alkhairi..."
Ba ta kai iya inda take son ta tsaya ba, kuka ne dai kawai ya ci ƙarfinta, ya hana ta ƙarisa zancen nata.
Ganin haka ya sa Jiddah ta ɗora da,
"Kin ga Mama ita kanta waccan Hadizar sai da Maryama ta shawo kanta, yanzu haka ta alƙawarta bin Maryama, su je har can Maraɗin tare, su taimaka ma bawan Allah'n, sannan su tabbatar da gaskiyar lamarin. Yanzu mama idan har Maryama ba ta samu zuwa ba, muna tsammanin Hadiza ma za ta je? Mama dan Allah a dubi wannan lamarin, taimako ne, jihadi nn mai girma, kuma mai matuƙar lada. Allah ne kaɗai Ya san ladar da za mu samu, daga mu har ku."
Datse haƙoranta ta yi bayan ta kai nan, alamun dai ta kai aya a nata zancen kenan, wanda shi ne Maryama ta so ta ƙarisa faɗi, sai kuka ya ci ƙarfinta, wanda ya gagare ta ƙarisa zancen.
Murmushi Mama ta yi, ta gyaɗa kanta cikin barkwanci ta ce,
"Wani abu sai yaran zamani. Ku fa a dole wayo kuke son ku min ko?"
Jiddah ma murmushin ta ƙirƙiro, ta ce,
"Mama ba wayo ba ne, neman taimako ne kawai."
"To na ji. Sai ku tashi ku tafi makaranta kar ku makara."
Maryama ba ta miƙe daga kneel down ɗin da ta yi ba, a hakan cikin kuka ta ce,
"Mama ai ba ki faɗa mana kin amince ko ba ki amince ba. Na tabbatar Hadiza na son jin wani abu daga gare ni, ina gudun kar ta ji ni shiru ta canza ra'ayinta."
"Ya isa haka to daina kuka. Tashi ku tafi na ji, zan ma Abbanku magana."
Murmushi sosai Jiddah ta yi a wannan karon, ba tun yanzu ta san rayuwar gidan su Maryama ba; sosai babansu yake da sauƙin kai da bin ra'ayin yaransa, musamman ma idan abin da ya shafi farin cikinsu ne, matuƙar dai bai saɓawa sharia ba. Dama Mama ce kaifi ɗaya, idan har ta ce haka to hakan, yana da wuya ta kuma canza magana, saboda ita ɗin ko kaɗan ba ta wasa