Showing 93001 words to 96000 words out of 201092 words
Chapter 32 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
ce ta yi wannan maganar bayan ta karɓi ledar, tana fiffiddo magungunan a hankali.
"Babu komai ai, kuma ai ban ga kin yi canjin kuɗinki zuwa Sefa ba, ni kuma akwai su a jakata."
Sai yanzu ma Maryama ta tuna fa ashe ma ba ta yi canjin kuɗi ba. To inda a ce Hadiza ba ta siyi maganin ba da ya kenan? Sai dai ta canza su inda za a karyarsu, tunda sun baro Boarder.
Wani iri take ji a cikin zuciyarta. Sosai take jin ƙaunar Hadiza a ranta. Mace ce mai kirki, mai tausayi, mai matuƙar haƙuri. Sai a yanzu take jin haushin kanta na yanda take yawaita jifar Hadiza da kalamai marasa daɗi. Sam! Ba ta cancanci haka ba. Kamata ya yi ta ja ta a jikinta, cikin kalamai masu daɗi ta ringa nusar da ita illolin bariki, ta ringa kwatanta mata abubuwan da suka dace da rayuwarta. Wannan taimakon da ta ma Modu ya sa ta daɗa jin ƙaunar Hadiza a zuciyarta. Me ya sa za ta zaɓi zaman kanta a rayuwarta? Sam! Karuwanci bai kamace ta ba. Zuciyarta mai kyau ce, sosai ta yaba da karamcin Hadiza.
Ba ta san sadda ruwan hawaye ya fara wanke mata fuska ba. Da sauri ta miƙe tsaye, ta rungume Hadiza, sosai Hadizar ke jin saukar ruwan hawayen Maryama a kafaɗarta.
Ɗago kanta ta yi bayan ta ɗan raba jikinta da na Maryama. So take ta san dalilin da ya sa Maryamar take kuka. Tana son sanin dalilin da ya sa Maryama ta rungume ta, runguma mai nuna zallar soyayya.
"Hadiza ban taɓa sanin cewa karamcinki har ya kai haka ba. Ashe haka zuciyarki take? Na yi da na sani, na yi nadamar abubuwan da na ringa yi miki a baya. Haƙiƙa na gasgata, cewa komai na duniya yana da advantage, haka kuma yana da disadvantage. Hausawa suka ce; ko kare yana da ranarsa. Kin kyauta sosai Hadiza, kin yi ceton rai matuƙa. Ladarki tana ga Allah maɗaukakin sarki, shi kaɗai zai iya biyanki wannan jihadin da kika yi Hadiza."
Rungumar Maryamar ta yi ita ma tana hawayen, ta ce,
"Babu komai Maryama, yi wa kai ne."
Jin muryar Jiddah suka yi ta ce,
"To miye abun kukan tunda dai ba wani abu ba ne? A ganina ai farin ciki ya kamata mu yi baki ɗaya, mu kuma ƙara roƙon Allah ya ba Annur lafiya."
Fiddou ta ce,
"Ameen hwa. Yanzu tahiya za ku yi da shi kenan?"
Tana sharar ƙwallanta.
Maryama ta raba jikinta da na Hadiza, ta ɗan tauni leɓonta na ƙasa, ta saka hannunta na dama ta share ƙwallar da ke malale bisa fuskarta.
"Dole tafiya za mu yi da shi Fiddou. Amma kar ki zata wai Annur ya tafi ya barki kenan. Insha Allahu zai dawo gare ki, da ƙafafuwansa. Zai dawo gare ki, a cikin hankalinsa. Zai miki godiya, zai jaddada miki darajarki, martabarki da kuma begenki. Ki cire damuwa a zuciyarki, addu'a Annur ke buƙata, ita yake da muradi a wannan lokacin ba kuka ba."
Duƙawa ta yi ƙasa Fiddou, daidai saitin Modu ta saki murmushi, wanda tana yinsa ruwan hawaye na zurara daga idanuwanta. Ta ce,
"Annur..."
Ita kanta ta ji daban, shiru ta yi ba tare da ta shirya ba, saboda yanda ta yi furucin sunan nashi, har cikin zuciyarta.
"Annur tahiya za ka yi ka barni yau kam. Zan yi kewarka sosai ba kaɗan ba. Don Allah ko kaɗan ne ka ba ni gurbi a cikin zuciyarka. Ka min so ko da kaɗan ne, wanda bai kai rabi rabin wanda kake ma Amrah ba. Na maka alƙawarin jiranka, har ranar da za ka dawo bisa ƙahwahuwanka zuwa inda nake. Ina maka hwatar alheri. Allah Ya baka lahiya, Allah Ya kawo ƙarshen haukan da kake yi..."
Ta yi shiru daga nan, sanadiyyar kukan da ya ci ƙarfinta.
Bayan ta samu da ƙyar ta haɗiye kukanta ta ci gaba,
"Allah Ya haɗa ka da Amrarka, Allah Ya sa ka same ta cikin ƙoshin lahiya."
Ta duƙar da kanta a wannan karon, tana gyaɗa kanta. Sosai take kishin Amrah, kawai dauriya take. A wani ɓangaren na zuciyarta kuma tana jin wani yanayi game da Amrah, burge ta take, ko ba komai ita ɗin masoyiya ce ga masoyinta, wato mace ce da Modu ke mutuwar so, wadda da alama ya rasa hankalinsa ne saboda ita. Sosai take jin haushin kanta, na haushin Amrah da ta ringa ji na tsawon shekaru, tun daga sanda ta fara jin Modu ya ambaci sunanta.
Kamata ta yi Jiddah ta miƙar tsaye. Dafe kafaɗarta ta yi cike da kulawa. Tausayinta take, sosai take jin Fiddou har cikin ranta.
Cikin raunanniyar murya ta ce,
"Amrah ba ta raye. Amrah ta mutu, tsawon shekaru kusan huɗu da suka gabata..."
Guntse bakinta ta yi a daidai nan saboda kukan da ya zo mata, na tuno Amrah da ta yi.
Tsayawa ta yi da kukanta Fiddou, ta ɗora idanuwanta da ta buɗe tsabar mamaki a fuskar Jiddah, tana neman ƙarin bayani na kalaman da suka fito daga bakin Jiddah.
"Kwanan Amrah ɗaya da rasuwa Annur ya haukace. Mutuwar Amrah ce sila Fiddou, mutuwarta ce silar haukacewar Annur."
Gyaɗa kanta take yi Fiddou. Ya mutuwa za ta mata haka? Me ya sa za ta ɗauki masoyiyar Annur, wacce ya fi so fiye da komai nasa? Wannan wace irin ƙauna ce Annur yake ma Amrah? Cikin kuka ta ce,
"Biri yai kama da mutum..."
Ta koma bakin gadon Modu, ƙirƙiro murmushi ta yi ta ce,
"Ka kwantar da hankalinka Modu. Insha Allahu Amrarka tana can cikin aminci, tana zaman jiranka. Amrah taka ce, kai za ta aura, ita za ka aura a cikin Aljannah, da yardar Allah"
"Yeee yeee! Na ji daɗi. Ke ma kina sonta ko? Ai na san dole ki so Amrah. Amrah ba ta da maƙiyi, duk wanda zai zauna da ita sai ya so ta. Shi ya sa ta siye min zuciya, muka yi alƙawarin aureee!"
Ya ringa wasa da yatsun hannunshi, kanshi sunkuye a ƙasa ba tare da ya ɗago ba yake wannan maganar.
"Ƙwarai ma kuwa. Ina son Amrah sosai, musamman ma da kake sonta. Amma ka san ina sonka ni ma?"
Sai a sannan ya ɗago kansa, ya harare ta sake da baki, wani irin kallo yake mata.
"Ke ni Amrah kaɗai nake so. Ai ita ta ce min kar in yaudare ta, kar in so wata macen bayan ita, kuma na mata wannan alƙawarin. So kike na zama mai cin amana? Amrah ta sha faɗa min babu kyau cin amana, ko kaɗan kar na zama mai cin amana ga kowa. Dan Allah ku kaini wurinta, ku kai ni inda Amrata take, na shaida mata ina riƙe da alƙawari, tana cikin zuciyata."
Kuka sosai yake, ya dafe zuciyarsa.
Sosai Fiddou ke mamakin Modu. Wani lokacin idan ya yi magana tamkar mai hankali. Duk maganar da zai yi game da Amrah ta hankali ce, babu sokana a ciki. Yana yawaita tuno abubuwan alkhairanta; nasihohin da ta ringa yi masa. Hanya ɗaya ce tal za ta yi saurin dawowar hankalin Modu, a ce Amrah na raye, ya yi tozali da ita. To matsalar wanda ya mutu ba ya dawowa. Amrah ta tafi, su da haɗuwa kuma sai a lahira.
"Ka daina kuka Mod...Annur. Da kai za su tahi yanzu, za su kai ka inda Amrah."
"Ka sha magani tukuna, za mu tafi ba da daɗewa ba."
Maryama ta faɗa bayan ta ɓallo mishi magungunan, ta duba ƙa'idar shan kowanne, sannan ta miyar a cikin ledar, ta tura a cikin jakarta ta hannu.
Robar ruwa ta ɗauko daga can bisa wata loka, ta buɗe ta, sannan ta miƙa wa Modu magungunan.
"Ungo Annur, ka jefa su a baki sannan ka bi da wannan ruwan ka haɗiye."
Bayan ya karɓa ya tura duka a bakinsa, ya ci gaba da tauna ko a jikinsa, kamar mai cin wani abu mai zaƙi.
Gyaɗa kanta kawai ta yi, sosai take jin tausayinsa.
Bayan ya taune duka ya ce mata,
"Kin ga bakina, na shanye duka. Mu tafi inda Amrata."
Ya wangale mata bakinsa, mai cike da zallar ƙazanta a cikinsa.
Murmushi ta yi Maryama, ta ce,
"Na gani to rufe bakin. Bari mu je wurin likitanka ya baka reffer, sannan mu tafi."
Bai ce mata komai ba, ta juyo ga Fiddou ta ce,
"Mu je wurin likitan ko?"
Kama hanyar barin ɗakin suka yi, suka bar Hadiza da Jiddah a tare da Modu.
A lokacin da suka isa Office ɗin Dr. Huzaif akwai patient a cikinsa, hakan ya sa suka zauna a kujerun da ke jere, na masu jiran layi ya zo kansu, na ganin likita.
Ba su wani jima da zama ba patient ɗin ya fito, hakan ya sa suka roƙi alfarmar wanda zai shiga next, cewa ya musu uzuri ba jimawa za su yi a ciki ba, magana kawai za su yi.
Bayan sun shiga suka zauna, Fiddou ta ɗauke kai daga dubansa, Maryama kuma cikin girmamawa ta gaishe shi.
"Sannu hwa. Mun wuni lahiya?"
Ya tambaye ta yana murmushi.
"Alhandulillahi, Dr. Sunana Maryam, ni ƴar uwar Annur ce."
"Modu?"
Ya tambaye ta a daidai lokacin da yake ɗora dubansa ga Fiddou, da ke ta faman haɗe rai, ita a dole gaba take da shi.
"Fiddou baby."
Ya furta yana ajje wani sassanyan murmushi, mai nuna zallar tsokar da yake mata.
Ba ta kalle shi ba, haka kuma ko uhm ba ta ce ba. Dama shi kanshi bai sa ran jin wani abu daga gare ta ba.
"Fiddou sarkin hushi. Halan dai ba za ki huce ba haka nan? Haba mana yi murmushi Fiddou Baby. Ok ok, bar fuskar ma a haka kin hi yin kyau, sosai rashin hwara'a yake kyau a fuskar Fiddou baby."
Dariya Maryama ta guntse. Wannan wane irin likita ne? Shi dai ga shi nan kamar mai tambotsai, kamar ba shi ba ne suka tarar a ɗakin ɗazu suna masifa shi da Fiddou, amma ga shi ya dage sai faman tsokanarta faɗa yake.
"Fiddou baby yi haƙuri kin ji? Ɓacin rai ne hwa, amma yanzu na huce."
"Kar ma dai ka huce."
Ya jiyo muryar Fiddou ta faɗi haka, cikin halin ko'inkula.
"Uhm...ni dai ba wannan ba Dr. I'm Annur's Sister, blood Sister."
Cikin mamaki ya kalli Maryama. Blood sister? Ya maimaita a ƙasan zuciyarsa.
"Wannan baiwar Allah'r da kuka tafi ɗazu har ta siya masa magani, ita ta zo wurinshi tare da Fiddou, a lokacin da ta ganshi ta gane shi, saboda an jima ana nemansa a gida har ma an gaji an haƙura, to bayan ta kai mana labarin ne muka yi waya da iyayenmu cewa ga abin da yake faruwa, Abbanmu ya ce mu ƙoƙarta zuwa mu tafi da shi."
Gyaɗa kansa ya yi Dr. Huzaif. Sosai ya jiye ma Modu daɗi. Ko ba komai zai koma cikin rayuwar ƴanci, zai koma a gaban iyayensa, su kula da komai nasa. Ya tabbata za su tsaya tsayin daka wajen ganin ya samu lafiya, bakin ƙarfinsu za su nema masa lafiya.
"Reffer muke so ka ba mu, don so muke mu tafi yanzu, kar mu yi dare a hanya."
"Allah sarki! Amma na jiye masa daɗi sosai. Allah Ya sa hakan ya hi zama alkhairi."
"Ameen Dr."
Ta furta haɗe da gyara zamanta, tana sake kallon Fiddou da ke ta faman hura hanci, wai ita ta tabbatar ma Dr. Fa ba ta son raini.
File ɗin Modu ya sa aka ɗauko masa, ya harhaɗa duk wani abu da ya dace, sannan ya yi short note a kan wata takarda, ya jefa ta a cikin file ɗin na Modu.
"Fiddou baby halan ya za ki yi? Ko binsu za ki yi?"
Banza ta masa ba tare da ta kalle shi ba. Sosai take jin haushinsa.
"Fiddou baby na san hwa kina iya mutuwa idan aka tahi da giɗe. Yi haƙuri kin jiya, ke ma hwa da gangan, haka kawai ki kama son mahaukaci, wanda kika san dole ko ba daɗe ko ba jima danginsa za su zo? Idan ma danginsa ba su zo ba, bakya tsammanin duk ranar da ya dawo cikin hankali nai ya nuna bai san ki ba? Hahaha! Yi haƙuri Fiddou baby. Amrah yake so!"
A wannan lokacin kam dubarsa ta yi cike da ƙuluwa. Ta kasa shanye baƙin cikin da yake guma mata. Inda a ce ya san cikin halin da take da sam bai dame ta da magana ba. Ita surutun ma duka ba ta jinsa. Ba ta jin yin masifa, amma dole ta sa ta sai ta mayar masa da martani.
"Halan wai mi ruwanka da rayuwata? Ehh na ji ina son Modu, ko kana hana ni? Kuma ko abin da ya hi mutuwa zan yi ina ruwan mutum da ni?"
"Babu."
Ya faɗa haɗe da gwada masa tafukan hannayensa duka biyu, alamun babu ɗin.
Da murmushi ya miƙawa Maryama file ɗin duka, yana faɗin,
"Allah Ya ba shi lahiya giɗe."
"Ameen Dr. Mun gode ƙwarai da taimakonka. Fatan alkhairi a kodayaushe."
Miƙewa ta yi ta ce,
"Idan kun gama kya same ni."
Miƙewar ta yi ita ma Fiddou, ta buga uban tsaki haɗe da bin bayan Maryama, suka bar ɗakin.
Bayan sun ƙarisa ɗakin Modu, nan Maryama ta shaida ma Jiddah da Hadiza cewa an gama komai, tafiya kawai za su yi.
Raunukan da ke ƙafar Modu har yanzu ba su gama warkewa tas ba, hakan ya sa Maryama da Hadiza suka taimaka masa wurin tashi, suka saukar da shi daga bisa gadon.
Fuskarsa cike take da annuri, bakinsa ya ƙi rufuwa, daɗi yake ji sosai a cikin zuciyarsa.
Kallonsa ta yi Fiddou, da sauri kuma ta sunkuyar da kanta. Wani irin raɗaɗi take ji a zuciyarta. Tana jin wani sauyi a tattare da ita. Sosai duniyarta ke cike da tsantsar damuwa. Ba ta san sanda ta isa gabanshi ba, ta haɗa jikinta da nashi, duk da ƙazantar da ke tattare da shi. Rungumarsa ta yi tsam a jikinta, tamkar kar su rabu haka take ji. Bugun zuciyarsa take ji a saitin tata zuciyar, a hankali ta fara saukar da ruwan ƙwalla a bisa kafaɗarsa.
Cikin taku mai sanyi Maryama ta iso gare su, gaggauta janye Fiddou ta yi daga jikin Modu. Hakan bai kasance halal ba, ba muharraminta ba ne Fiddou, dan haka bai kamata ta masa irin wannan rungumar ba.
Bai ma san abin da take ba Modu, tuni hankalinsa ya kaɗu da tafiyar da za su yi. A ganinsa yau ce ranar da zai ga masoyiyarsa, wacce suka jima ba su ga juna ba.
"Wata ƙila daga yau ba zan sake ganin Modu ba, wata ƙila ba zan sake saka shi a idona ba, wata ƙila ba zai sake dawowa gare ni ba. Ta yiu kallon ƙarshe nake ma Modu, sai a lahira in da rabo..."
Ta saka kuka sosai, bayan ta duƙe ƙasa.
"Mu je ko?"
Jiddah ta faɗa tana kallon Hadiza da Maryama.
Ɗaga mata kai Maryama ta yi, Fiddou ma ta miƙe duk da kukan da take, ta tattara yanata-yanata da ke ɗakin, suka fita tare, a ƙofa suka yi kiciɓus da Dr. Huzaif zai shigo, domin su yi bankwana da Modu.
Gaisuwa da fatan alkhairi a gare ku. Ba zan taɓa gajiyawa da nuna muku farin cikina ba, ku ɗin nawa ne, kuna raina, ina kaunarku all fisabilillah.
Wattpadians sam! Ba na jin daɗi fa. Wai sai mutum ya karanta, amma ya tsallake ɗan alamar tauraron nan ba tare da ya dangwala shi ba. Shin wani aikin wahala ne?
To fa!
Maryama ta sadaukar da lokacinta ɗungurugum don ganin ta taimaki Annur, ta fitar da shi daga rayuwar da yake ciki. Sosai ta hana kanta walwala da farin ciki, kawai don dawowar farin cikin Annur.
Ga kuma Fiddou, wacce komanta na Annur ne. Ba ta damu da haukan da yake ciki ba, a haka take ƙaunarsa, har ba ta son rabuwa da shi.
Hadiza fa? Ita kanta masoyiyarsa ce, ta ƙaunace shi, a ƙarshe ga shi ta siya masa magungunan da ake ta tsumayen samun mai siyansu. Ta zama silar samuwar wani farin ciki na daga rayuwar Annur. Ko kun san cewa zuciya ita ce jigon komai na rayuwar mutum? To Hadiza ta siya masa maganin da zai warkar da zuciyar Annur.
Ya abun zai kaya?
Ku juri bibiyar labarin, sannu a hankali duk za a samu mafita.
Thanks all
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:55 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
4⃣6⃣
follow me on wattpad:
PrincessAmrah
Ba ta ko kalli inda yake ba, ta ƙoƙarta bi ta gefensa ta wuce, kasantuwar ita ce a gaba, su Maryama biye da ita.
"Ba dai har kun hito za ku tahi ba."
Suka ji muryar Dr. Huzaif ya faɗa, yana binsu da kallo.
Da murmushi Maryama ta ce,
"Wallahi fa Dr. Tafiyar kenan."
"Allah sarki!"
Ya furta haɗe da gyaɗa kansa yana kallon Modu. Sosai yake tausayin Modu. Hannunshi na dama ya haɗa da na Modu shi ɗin ma na dama, suka gaisa, ba tare da ya saki hannun ba ya ce,
"Allah Ya baka lahiya abokina. Ina hwatar tahiyar nan ta hiye maka zama alheri hiye da nan da kake. Sai wata rana ka ji."
Ya sakar masa hannun nasa, yana ƙarisa maganar da faɗin,
"Allah haɗa ka da Amrarka."
Sai a sannan Fiddou ta iya kallonsa, yanzu kam ba haushi ya bata ba, burge ta ya yi.
Cikin dakiya da nuna jarumta ta ƙoƙarta shanye ruwan hawayenta, ta ce,
"Amrah ai ba ta raye, ashe ta jima da mutuwa."
Kansa ya dafe Dr. Huzaif, ya runtse idanuwansa na kusan sakan goma, sannan ya buɗe su cike da tausayi.
"Lallai kuwa akwai matsala, dole ne Modu zai kamu da ciwon zuciya. Ashe shi ya sa kullum yake yawaita ambatar sunanta?"
Kai ta ɗaga masa Fiddou, ba tare da ta faɗi komai ba.
"Allah Ya ji kanta da rahama. Allah Ya ba Modu lahiya."
Sam Fiddou ba ma ta kula da mugun kallon da Modu ke binta da shi ba. Haushinta ya ji a lokaci guda. Don me za ta ce Amrarsa ta mutu? Me ya sa za ta so raba jini da hanta?
Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa, ba ta sake haɗa ido da Modu ba, saboda har ga Allah kallon da yake mata ba ƙaramin tsorata ta yi da shi ba.
Fita suka yi daga nan, suka kama hanyar barin asibitin, Jiddah da Hadiza tallabe da Modu. Sai Maryama da Fiddou biye da su a baya. Dr. Huzaif kuma