Showing 144001 words to 147000 words out of 201092 words
Chapter 49 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
ni zan wuce. Office ma nake son wucewa kai tsaye, akwai aiki da ya taso min. Tun jiya da na bar nan gidan na kira wani abokina da yake da babban shago, na mishi bayanin abin da nake so. Sai ga shi yau da sassafe ya kawo kaya, kuma ni kaina na ga ba laifi sun yi kyau sosai. Iya dai wanda suka samu kenan, kasantuwar abun na gaggawa ne, kuma dai duka ba shi ake ma ba. Zaman lafiya tabbatacce ne babban abun so."
Bayan ya miƙe tsaye shi ma Kawu Imranan ya miƙe, yana faɗin,
"Wannan gaskiya ne Alhaji Marwana. Babu abin da zan ce da kai face na dad'a jaddada maka godiya. Allah ya saka maka da dukkanin alkhairanSa. Su kuma yara Allah ya ba su zaman lafiya, ya ba Annur lafiya."
"Ameen ya Rabbi. Ni ina ji sai kuma Ranar Jumu'a ɗin. Da an sauko masallaci da izinin Allah zan ƙoƙarta zuwa, tunda dai sai ƙarfe uku za a ɗaura. Ga wannan."
Ya zaro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa wa Kawu Imrana.
"Sadakin nata ne."
"To masha Allahu! Allah ya nuna mana da rai da lafiya. A gaida iyalin."
*
Wuraren ƙarfe huɗu sai ga Kawu Imrana ya zo gidan su Maryama. Bayan ya shigo ya zauna ne mai gadi ya shisshigo da akwatunan. Bayani ya ma Mama cewa lefen Maryama ne, daga Alhaji Marwan. Sannan kuma ya labarta mata duk yadda suka yi da shi jiya da suka haɗu.
Ta matuƙar jin daɗi, tunda dama a waya ne suka yi magana, cewa ranar Jumua mai zuwa ne ɗaurin auren. Abba ne ya dawo a daidai lokacin. Da faraa suka tarbi juna. Sannan kawu ya koma ya zauna.
"Baban amarya."
Kawu Imrana ya faɗa, yana murmushi.
Tsuke fuskarsa ya yi Abba, bai kuma faɗin komai ba, har Maryama ta wanzu a gabansu, ta ajje musu lemuka da cups a tray.
Har ƙasa ta duƙa ta gaishe da su. Ta juya za ta tafi kenan ta jiyo muryar Kawun cike da wasa, yana faɗin,
"Amarya ga lefenki nan fa. Surukinki da kanshi ya kawo min su har gida. Ga kuma sadaƙi da kuɗin neman aurenki."
Kunya ta ji sosai, ba ta iya furta komai ba, sai kama hanyar barin ɗakin da ta yi.
"Zo mana ƴata."
Ba musu ta juyo ta dawo, ba ta ɗago kanta ba har ta duƙa a gaban kawun nata.
"Ungo wannan."
Ya miƙo mata bandir na ƴan ɗari biyar har guda biyu, dubu hamsin hamsin kenan.
Cikin alamun tambaya ta miƙa hannu biyu ta karɓi kuɗin. Ba ta samu damar tambayarshi ba, ta ji ya ce,
"Dubu hamsin kuɗin neman aurenki ne. Dubu hamsin kuma sadaƙinki. Haƙƙinki ne, ki yi duk yadda za ki yi da su; ƴan hidindimunku na amare, tunda dai angon babu lafiya. Komai naki insha Allahu gobe zuwa jibi za su iso, na yi odarsu daga Dubai, wani abokin kasuwancina da ke can na tura ma. Amma ki yi haƙuri fa, ban tambaye ki irin wanda kike so ba, kuma ƴan matan yanzu na ga su ke faɗin kala ko?"
Ya murmusa.
"Na tabbata ba zai min zaɓen banza ba. Za ki ji daɗinsu ƙwarai."
Hawaye ta ji suna wanke mata kumatu Maryama. Har ma ba ta san ta yadda za ta gode ma bawan Allah'n ba. Mutumin na da kirki sosai, bai taɓa bambanta su da yaran da ya haifa da cikinsa ba. Shi ya sa take jin wata irin kunya na daɗa lulluɓe ta, ta ƙin amincewa da auren ɗanshi.
"Insha Allahu zuwa dare, Ahmad zai kawo miki invitation cards, naku na ƴan mata. Sai ku gayyaci duk wanda za ku gayyata, tunda dai biki ne na budurwa ba bazawara ba. Ko zawarawan ma dai ai sun waye yanzu, bikinsu suke yi kamar ƴan matan. Sai dai na canza sunan angon, Muhammad Nuraddeen na ce a rubuta, duka har na ɗaurin aure ma."
Gyaɗa kai kawai Abba ya yi. Shi kanshi yana jinjina halin karamci irin na yayanshi. Ba dukkanin yayye ne ke da irin halin Kawu Imrana ba. Bai ma nemi shawararshi ko kaɗan a duk hidimar ba, shi kaɗai ke abin shi.
"Ku yi bikinku hankali kwance, kar ki ji komai ƴata. Ai dama ba kowanne biki ba ne ango ke halartar hidimomin, ɗaurin aure ne dai dama ake zuwa, to don wannan mai sauƙi ne, zan iya cewa bai da lafiya ne yana asibiti a kwance."
Mama ta duƙa har ƙasa, ta ce,
"Allah ya sani, bani da bakin gode maka. Haƙiƙa kai mutum ne na gari, da ke da kyawawan halaye. Allah ne kaɗai zai iya biyanka. Allah saka maka da alkhairi. Allah ya bar zumunci."
"Kar ku ji komai fa. Yanzu don na ma ƴata abu har sai an min godiya? Tamkar kaina fa na ma. Yanzu dai, a kaini inda ɗan nawa yake, in gan shi, in masa albishir cewa ya kusa angwancewa."
Ya ƙarisa maganar da sakin murmushi mai faɗi.
***
*Na gaji.🤣😅*
*Na cika alƙawari ko ban cika ba?😀 Na cika. Duk dayake cewa akwai wanda ba su canko daidai ba. Ba zan faɗo ainahin amsar ba, har sai mun zo wurin. Wanda suka canka daidai za su gani, su kuma tabbatar da cewa daidai suka amsa.*
*Masu karatu, sai a shirya shan casu, domin kuwa, an kusa zuwa wurin.*
*Ba lallai a ji ni gobe ba. Fatan za ku min uzuri.*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/13, 8:20 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
6⃣2⃣
Wattpad: Princess Amrah
***
Wannan shafin sadaukarwa ne ga Hajiyata Matar Sarki. Fatar dai an haɗa kuɗin ashoben mutane da yawa, don ya kusa ƙarewa...lol. ina yin ki sosai Hajiyata. Allahu ya bar zumunci da zaman tare. Ƙaunarki nake yi fisabilillah.
***
Muhammad ne ya musu jagora zuwa ɗakin da Annur ɗin yake. Da shigar su suka same shi zaune ya takure kanshi, yana kallon wuri ɗaya. Ko tunanin me yake oho. Sallamarsu da ya ji ce ya gaggauta ɗago kanshi yana kallonsu. Kyakkyawan murmushinsa mai daɗa fiddo kyawunshi ya sakar ma Muhammad. Shi ma Muhammad ɗin ya sakar mishi murmushin, sannan ya ƙariso daf da shi ya zauna.
"Ka ga Kawunmu nan, wanda zai ɗaura muku aure kai da Yaya Maryama. Ga kuma Abbanmu, ai ka san shi ko?"
Bai ba Hammad amsar ba sai dariyar yaƙe da ya saki yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Bayan kawu Imrana ya zauna, ya ce,
"Ɗana sannu ko? Ya ƙarfin jikin?"
A nan ɗin ma Annur bai ce komai ba. Ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana kallon wuri guda.
"Insha Allahu yau saura sati guda a ɗaura muku aure da Maryama. Ai kana so ko?"
Bayan ya rufe fuskarsa ya ce,
"Ai Amrah ta ce da ni in so ta, kuma ina son ta ɗin. Ita ma ta faɗa min tana so na."
Dariya suka saki su duka, har Abba sai da ya yi dariyar. Saboda yanayin yadda Annur ya yi maganar, dole sai an yi dariya.
"Ai haka nake so dama. Insha Allahu za a ɗaura muku aurenku kai da ita. Kana so ka ci gaba da zama a nan ko kuwa dai a fitar muku da gidanku daga kai sai ita?"
Shiru ya ma Kawu bai ba shi amsa ba. Don bai ma san inda maganar tashi ta dosa ba.
"Tunda ba za ka min magana ba, bari ma in tashi in tafiyata."
Jawo rigar Kawu Imrana ya yi, ya ce,
"Zan maka magana. Allah kuwa."
"To to to na ji. Yi min maganar in ji."
Ya dawo ya zauna Kawu Imrana.
"Uhm...Amrah fa ba ta da lafiya tun wancan lokacin. Ni ma sai gobe na tuna da haka. Har ma an kai ta asibiti fa. Allah kuwa da gaske nake muku ba ƙarya ba."
Gyaɗa kansa ya yi kawu, ya ce,
"Allah sarki! To amma dai ta ji sauƙi ai ko?"
Ɓata fuskarsa ya yi yana kallon kawu, kafin ya harare shi, ya ce,
"Wa ya faɗa maka ta ji sauƙi? Ba ta ji sauƙi ba fa. Haka ma wai aka ce wai ta mutu. Daga farko ban yarda ba. Amma sadda tai min zuwan ƙarshe a mafarki ta sanar da ni hakan, cewa ba za ta sake dawowa ba. Kawai dai in riƙi Maryama a madadinta."
Duk da cewa a shirme ya yi maganar, hakan bai hana Kawu Imrana tausaya masa sosai ba. Haka ya ɗan rinƙa jansa da fira, har suka ɗauki tsawon lokaci, kafin ya miƙe, ya ce da su Abba su taso su tafi, yana son tafiya gida, kasantuwar magrib tana gabatowa.
*
Kamar wasa haka shirye-shiryen aure suka ci gaba da kankama. Ranar litinin ɗin da ta rage kwana biyar aure, Alhaji Marwan ya kira Kawu Imrana a waya, cewa akwai gidanshi da ke nan cikin road K, kusa da nashi gidan. Ba wani babba ba ne sosai, sai a kawo amarya a cikinsa. Sosai kawu Imrana ya yi na'am da hakan. Sannan a ƙarshe suka yi sallama.
Lambar wayar Mama ya kira, bayan ta ɗauka suka gaisa, yake yi mata bayanin yadda suka yi da Alhaji Marwan, sannan a ƙarshe ya ce
"Kayan Maryama dama sun iso, yanzu haka suna cikin store a ajjiye. Idan an tashi zuwa jere, kawai sai ku faɗa min, zan kira Alhaji Marwan ɗin na sanar da shi."
Mama ta ce,
"Idan haka ne kuwa ai sai a sanar da shi cewa ranar Laraba za a zo jeren. Gudun kar abun ya cunkushe cikin hidimar biki."
Kawu Imrana ya ce,
"To madalla. Insha Allahu gobe zan umurta da a kwashe kayan nan ɗin duka a kai su can gidan nata. Kin ga idan an tashi jeren kawai zuwa za a yi."
"To babu damuwa Yaya. Ni ɗin ma nan akwai ƴan karikitai da za a kwasa. Su kayan kitchen da bedsheets da labulaye. Jiya muka je da ita duk muka siye su. Goben sai masu kwasar kayan su biyo ta nan su tafi da kayan."
"To babu damuwar Hajiyar Maryam. Haka za a yi da yardar Allah."
"Na gode ƙwarai Yaya. A gaishe da iyali. Su Hajiya Rakiya dai ai ba sai an kai musu IV ba, saboda su ma masu gayyatar wasu ne."
Kawu ya ce,
"Wannan gaskiya ne. Za su ji duka insha Allahu."
Suka yi sallama. Tana ajje wayar ta ƙwala ma Maryama kira.
Bayan ta zo ta ce,
"Ga ni Mama."
Mama ta ce,
"Cikin kayan nan da Hassana Gusau ta kawo miki. Akwai wani na gari na nan a wata roba, ki duba yoghurt na nan cikin fridge, ki tabbatar kin sha fa. Cokali guda za ki zuba garin a cikin rabin cofin yoghurt ɗin. Ki ɗaga kanki ki shanye duka."
Cikin jin kunya ta amsa da to, sannan ta juya za ta tafi. Sake kiranta Mama ta yi, bayan ta dawo ta ce,
"Matar Sarki ta kira ni ɗazu, ta ce wai ta harhaɗa kuɗaɗen ashoben ƴan RAZ NOVELLA 1&2. To wai tana so ne ki je ki karɓa ki ɗora a motocin haya da za a kai musu. Ita ayyuka sun nata yawa ne. Ga shi kuma jibi ma jere za su je su miki."
Duk da dai bakinta cike yake da son yin tambaya amma ba ta yi ba. Haka ta koma ɗakinta tana mai nazartar kalaman Mama. Kenan har an fitar musu da gidan da za su zauna?
Zama ta yi a bisa sofa. Ta jawo lakar madubinta, ta ci karo da tarin magungunan da Hassana Gusau ta kawo mata kyauta. Murmushi ta yi, a ranta tana tunanin wanda ake mata shirin domin shi. Mahaukaci ne fa ba mai lafiya ba. A bayyane ta furta,
"Allah ya ba ka lafiya ingantacciya Yaa Noor ɗina."
*
Washe gari misalin ƙarfe huɗu na yamma motar kwasar kayan ta iso ƙofar gidan su Maryama. Baki ɗaya kayan da ke nan ɗin aka kwasa sannan suka wuce kai tsaye GRA, tare da bin kwatancen da Alhaji Marwan ya musu.
Suna barin wurin Sans na isowa da motarshi. Ya yi mamakin kiciɓis ɗin da ya yi da motar kaya. To sai ya ƙoƙarta kawar da komai, duk kuwa da cewa zuciyarsa ta ɗan fara kitsa mishi wani abun na daban.
A ƙofar gida ya faka motarshi, yana nazarin miye next. Ya ciro wayar Bobby daga jikin chaji, ya latso lambar Maryama, sai dai kuma ya ji ana faɗin babu kuɗi a wayar.
Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya jawo tashi wayar da ke jone sautin karatun Qur'ani na fita daga cikinta, ya fara ƙoƙarin kwafar lambar.
Babban abin da ya ɗaure mishi kai, sadda ya fara rubuta lambar sai ya ga yana ma da ita, har ya rubuta mata Maryam. Mamaki ya cika shi, nan fa ya fara tunanin inda ya samu lambar.
Shiru ya yi na ɗan lokaci, kafin zuciyarshi ta tunasar da shi abubuwan da suka faru kwanaki, da kuma ta yadda aka yi ya samu lambar tata.
"Kar dai tunanin da nake yi ya tabbata fa. A ce ita ce Maryama da boka Gagarabadau ya fitar min da soyayyarta ta ƙarfi da yaji daga cikin zuciyata."
A bayyane ya yi maganar. Mamaki na daɗa yawaita a zuciyarshi. Me hakan ke nufi? Dama da yarinyar ne Bobby ya yi soyayya kafin ya mutu? Ya aka yi duk ba su sani ba?
Kanshi ya jingina jikin sitiyarin motar, yana jin duniyarsa na masa zafi. Raɗaɗi da zugi zuciyarsa ke masa. Ta yaya zai iya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa Farouk Sardauna, cewa zai aikata buƙatar tashi ya auri Maryama? Kamar ya saɓa ma zancen boka ne. Dama da ƙyar aka samu aka fitar da soyayyarta daga cikin zuciyarsa. Yana ga matuƙar ya aure ta, lallai soyayyarta za ta ci gaba da haɓaka a cikin zuciyarsa. Duk da dai cewa a yanzu ɗin babu ko kaɗan.
Cike da takaici ya tada motar, ya bar harabar unguwar, zuciyarsa na masa zugi. Yana mai tsananin jin haushin dokar da boka Gagarbadau ya gindaya masa, kan cewa babu true love gare shi har abada.
*
Waya suke da Jiddah, faraa sosai bayyane a saman fuskarta.
"Jiddah yanzu don Allah duk irin gajiyar nan da na yi, kuma kina nufin gobe ma sai mun fita?"
A ɗaya ɓangaren Jiddah ta ce,
"Abu dole. Yo to me muka yi ma? Daga rabon IV fa babu wani abu da muka aikata. Yau fa saura kwana huɗu biki Maryama. Dole gobe mu samu mu rage aiki, ko Salon ne mu fara zuwa. Jibi sai a yi lalle."
Ajiyar zuciya Maryama ta sauke. Ta ce,
"Oh ni Marryam! Wannan abu ba ya ƙarewa wai?"
"Ina fa zai ƙare? Auren kenan ai. Ɗazu ƙawarki Saudat ta kira ni. Take faɗa min wai akwai sauran ƙawayenku na jami'a da ba a kai ma IV ba. To ni dai na ce mata gobe idan mun gama wankin kai, daga can za mu wuce gidansu mu ɗauke ta, sai a kai musu."
Guntun tsaki ta saki Maryama. Ta ce
"Ni wallahi na gaji da wannan hidimomin. Kuma wai yanzu da zarar an gama, ranar Monday mai zuwa in fara exams."
Jiddah ta ce,
"To ya za ki yi. Sai haƙuri. Ni dai don Allah gobe ki fito da wuri, yadda za mu yi komai a kan lokaci."
"To Allah ya kai mu. Bari in tafi in duba Yaa Noor, duk yau da Hammad kawai na bar shi."
Dariya Jiddah ta yi,
"Hammad manyan mutane, ƙanin amarya. Sun fa yi hutu ko?"
"Ehh mana, sun yi hutu ran Friday ɗin nan. Sai farin ciki yake wai za a yi biki suna hutu."
"Gaskiyarsa ai. Biki daɗi gare shi."
Daga nan suka yi sallama.
Ajje wayar ta yi kan gado, sannan ta nufi ɗakin Annur, zuciyarta cike da ɗokin ganinshi.
Bayan ta shiga, ta samu sai yaƙe baki yake, shi kaɗai, yana kallon wuri guda.
Gyaɗa kanta ta yi tana murmushi, sannan ta ƙariso gabanshi ta zauna, tana tafa hannuwanta a daidai fuskarsa.
Zabura ya yi ya kalle ta, sannan ya kuma sakin murmushi, idanuwansa a kanta.
"Sai dariya kake kai ɗaya Yaa Noor. Ba ni labari, me ya faru?"
"Hammad ne."
Kawai ya faɗa, yana ci gaba da murmushi.
"Me ya yi Hammad ɗin?"
"Ya ce wai gidanmu daban za a fitar mana, daga ni sai ke idan an mana aure."
Gyaɗa kanta ta yi. Ta ce
"To kai ka ji daɗin hakan ne?"
Harararta ya yi, ya ce,
"Ehh mana. Na ji daɗi sosai."
Sai kuma ya ɗaure fuska, hawaye na ƙoƙarin saukowa daga idanuwanshi zuwa kumatunshi.
Ganin yadda idonshi ya cika taf da ƙwalla ya sa hankalinta ya tashi. Ido a buɗe take tambayarshi,
"Me ya faru kuma don Allah? Na rasa me ya sa sam kuka ba ya maka wahala."
Hannunshi na dama ya sa ya share hawayen. Ya ce,
"Don Allah kar ki tafi ki bar ni, duk wuya duk rintsi. Kin ga Amrah ma sai da aka kusa bikinmu sannan ta tafiyarta ta barni, ta bar rayuwata baki ɗaya."
A daidai wannan lokacin sosai kuka ya ci ƙarfinsa. Ya haɗa kansa da guiwa, yana mai shessheƙar kuka.
"Yah Noor ya akai ka san haka? Ta ya aka yi ka san cewa sai da kuka kusa aure sannan Amrah ta tafi ta bar ka? Kenan hakan na nufin ka fara tuno wasu abubuwa na rayuwarka?"
Bai ce da ita komai ba, kamar yadda ba ta tsammani zai ce ɗin ba. Sai dai kuma mamaki take. Tana kuma ƙara tabbatar da lallai sauƙi na zo mishi. Duk wasu shirme da yake yi a baya sun sauƙaƙa. Wani abun ma idan ya yi shi ba za ka taɓa cewa shi ne ba. Ga kuma yanayin kayan da mai gadi ke saka mishi. Tsafta sosai.
*
Tun daga sadda ya kula da fitar Maryama. Ya lallaɓa a hankali ya shiga ɗakinta. Cikin nasara ya samu wayarta a kan gado, ba ta fita da ita ba. Da sauri ya ɗauka. Ya ja pattern ɗin da ta saka, babu ɓata lokaci wayar ta buɗe.
Neman lambar Maman Abdul ya hau yi, amma bai gani ba, saboda bai san sunan da ta saka mata ba. Hakan ya sa ya koma a farkon contacts ɗin, ya rinƙa bi a hankali ɗaya bayan ɗaya, har ya zo kan lambarta, ashe Dr. Islam ta saka mata.
Lallaɓawa ya yi ya fice da ɗakin, yana tunanin yadda suka yi da Maryama jiya. Ya same ta da IVs a gabanta, yake tambayarta ta gayyaci Maman Abdul kuwa? Ta ce da shi ba ta gayyace