Showing 126001 words to 129000 words out of 201092 words

Chapter 43 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ba, bai taɓa ganinta ba, amma ya ci gaba da rayuwa a idanuwan duniya a matsayin shi ne asalin masoyinta. Sau da dama shi kanshi yakan zauna ya yi tunani; makomar rayuwarsa a duk sadda wancan ƙullin ya kwance. Ga shi abokin shawarar nashi babu shi a yanzu, ya kwanta damarsa. Kodai zai fito ya fallasa kanshi ne? Ya tambayi kanshi. Da sauri wata zuciyar ta inigiza shi haɗi da kwaɓar kanta, cewa kar ya yi. Ta ya zai ci gaba da rayuwa a duk sadda asirinsa ya tonu? A ina zai ci gaba da zama? Dama Allah ne gatanshi Bobby ne gatanshi, tun ma kafin ya dawo gidan su Annur ɗin. To babu Farouk yanzu, ya zai yi? Zai rufe bakinshi salin-alin ya ci gaba da rayuwa a gidan. Sai dai ya tsara ma kanshi, cewa babu shi babu kayan maye har abada. A duk sadda zai ga mai yi ma zai Ƙoƙarta kwaɓarsa, saboda shi ya ga illarsa, a zahiri ba nesa da shi ba.


***


Cike da ƙarfin hali take taya Mama aikin haɗa kalaci. Raba-da-rabi take jin daɗi a zuciyarta. Nan daɗi, can kuma haushi; Auren dole da ake son a mata. Daɗin kuwa na kalaman da suka fito daga bakin Annur ne, masu cike da zallar nishaɗantar da zuciyarta, da duk gaɓɓan jikinta.


Bayan sun gama duka ta kai a ɗakin Abba, ta samu har ya gama shirin fita Office, kalacin kawai yake jira.


Gaishe shi ta yi cikin girmamawa, banza ya mata, ko kallon inda take bai yi ba.


A zatonta ko bai ji ba ne, hakan ya sa ta sake ɗaga sautinta, ta gaishe shi.


Bai mata magana ba, sai ma Hammad da ke daidai shigowa ɗakin da ya ma magana, cewa ya je ya kira Mama.


Jiki babu ƙwari ta fice daga ɗakin, wasu irin zafafan hawaye na fita daga idonta. Tun daga jiya take kuka, babu ci babu sha, sai famar ciwon kai, wanda panadol ya kasa saukarwa.


A bisa faffaɗan gadonta ta faɗa. Haushin kanta take ji sosai, ta yadda zuciyarta ta kasa aminta da zaɓin iyayenta. Ba ta ga laifin Abba ba, ko kaɗan. Da gaske ko ita ce ba za ta taɓa aikata abin da take so Abban nata ya yi ba. Bai kamata ba, a yadda kawu Imrana ya yi hidima da Abbanta, kuma ya iya ya tinkare shi da zancen wai ba ta amince da auren Deedah ba.


Muhammad da shi kanshi bai ji daɗin abin da ya faru ba, bayan ya kira Mama zuwa ɗakin Abba, ya lallaɓa ya shiga ɗakin Mamar da shirinsa na makaranta, ya ɗauko wayarta, ya ɓoye a cikin rigarsa. Da sanɗo da sanɗo yake tafiya, har ya fita daga part ɗin nasu, ya nufi wani part da ke can baya, inda babu kowa.


Lambar Kawu Imrana da aka rubuta ma Yaya Imran ya gano, babu shakka bare tsoro, ko kuma tunanin wani abu, ya latso kiranshi. Har ta tsinke bai ɗauka ba, ya sake kiransa, tana daf da tsinkewa Kawu Imrana ya ɗauka.


Sallama ya yi, haɗe da faɗin,


"Hajiyar Maryam barka da safiya. Ya tashin iyali?"


Sai a yanzu Muhammad ke jin faɗuwar gaba duk da kasantuwarsa ƙaramin yaro. A haka ya daure, ya ce,


"Kawu ina kwana? Ni ne Muhammad."


"To to to madallah da Muhammadu. Ya kuka tashi da iyayen naka?"


"Suna lafiya."


Ya faɗa a hankali.


"Lafiya dai ko ɗana?"


Kawu Imrana ya faɗa, cike da mamakin kiran da Muhammad ɗin ya masa da sassafen nan.


Magana Hammad ya hau yi masa ƙasa-ƙasa, yana yi yana waigen gefe da gefensa, gudun kar a kama shi yana yi.


Sai da ya yi kusan wayar minti bakwai, kafin suka yi sallama da kawun nashi, haɗe da lallaɓa komawa ɗaki.


Ya ci sa'a kuwa har yanzu Mama tana tare da Abba, hakan ya sa ya lallaɓa ya miyar da wayar. Sai dai kuma ya manta shaf, domin kuwa yarinta ba ta bar shi ya tuna goge kiran ba.


Fitowa ya yi fuskarsa a sake, haɗe da nufar ɗakin Maryama.


A kwance ya same ta, tana ta faman kuka mai sauti.


Ƙarisowa ya yi ya zauna a bakin gadon, cike da tausayin tilon ƴar uwarsa, mai ƙaunarsa, mai son farin cikinsa fiye da nata. Riyawa yake a ransa, duk yadda zai yi dole ya yi, don ganin ya kuɓutar da ita daga wannan mawuyacin halin da take ciki. Ya fara hawa hanya a yanzu kam, yiwuwar abun kawai yake jira.


Bubbuga ta ya yi a hankali, yana faɗin,


"Yaya Maryama..."


"Leave me Muhammad!"


Ta faɗa da ƴarfi, cike da takaici.


Duk da ya ji haushin tsawar da ta masa, amma bai yi zuciya ba, ya sake faɗin,


"Na miki alƙawari in dai ina raye to babu wanda zai miki auren dole. Wanda kike so shi za ki aura."


Tashi ta yi zaune tana kallon shi.


"Ta yaya?"


Ta haɗa wannan kalaman biyu, da ƙyar da jibin goshi, duk da ba ta san ta yadda ta tsamo su daga cikin bakinta ba.


"Just wait, you'll see."


"Kar ka yi koma menene Hammad. Kar ka ja min, ina zaman zamana. Ka bari kawai, mu barwa Allah lamurranSa, Shi ne kawai zai iya magance mana."


Kanshi ya gyaɗa mata, da murmushi ya ce,


"Ba zan ja miki komai ba Yaya Maryama, I promise you."


Kanta ta gyaɗa da hawaye kwance a bisa fuskarta, ta ce,


"Allah ya tabbatar."


Kafin ya sake faɗin komai ya ji muryar Mama na kiransa, cewa ya fito Abba ya wuce da shi makaranta.


Tashi ya yi, ya mata ba-bye, sannan ya fice daga ɗakin, yana jin zuciyarsa wasai, tamkar babu wata damuwa a cikinta.


***


A yi maneji da wannan, iya wanda ya samu kenan.


Do comments
Do votes
and then share with your family and friends.


Thanks all


Pinky Durling
RAZ 2
[9/7, 12:29 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


5⃣7⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Tun daga sadda Fiddou ta karɓi soyayyar Mahmouda yake duk iya ƙoƙarinsa na ganin ya koya mata son shi. Ya ɗan samu nasara kaɗan ba mai yawa ba. Domin kuwa a yanzu har murmushi takan yi duk sadda suke tare. Ko a gida ma yakan faɗo mata a rai har ta samu kanta da murmusawa. Sai dai kuma murmushin yakan gushe daga saman fuskarta, idan ta tuno da Modunta, wanda take ma mutuwar so.


A tsawon wannan lokacin, har manya sun shiga maganarsu, an tsaida zancen auren nasu, wata ɗaya mai zuwa.


A yanzu ne Aunty Sahiya ke nadamar abubuwan da ta kasance tana ma Fiddou. Ta tabbatar cewa cin amana ne fa take yi, kuma ba za ta so wata ƙanwarta ta faɗa tarkon matar yayanta ba, kamar yadda ta ringa cutar da Fiddou, ƙanwar mijinta uwa ɗaya uba ɗaya. Duk wata biyayya da ya kamata ƙarama ta ma babba, haka Fiddou ke ma Aunty Sahiya. Amma ita ta kasa karɓarta a matsayin ƙanwarta, ta kasa kyautata mata kamar yadda ita Fiddou ɗin take ƙoƙarin kyautata mata.


Zaune take a ɗaki Fiddou ɗin. Ta rafka tagumi tana mai tunano tsawon lokutan da suka shuɗe, na zamantakewarta da rayuwarta da Modu. Shirmensa kawai take tunawa, da kuma sunan Amrah da ke yawan fitowa daga bakinsa.


Sosai ta yi zurfi da wannan tunanin, hakan ya sa ruwan hawaye ya fara sauka a bisa kumcinta.


Gyaran murya ta yi Aunty Sahiya, bayan ta ƙarisa shigowa ɗakin ta nemi wuri ta zauna, a kusa da Fiddou ɗin.


Zabura ta yi Fiddou, ganin Aunty Sahiya ta shigo ɗakinta, kuma har ta nemi wuri ta zauna. Ta tabbata ba alkhairi ne a tattare da zuwan nata ba, sai tarin wulaƙanci da take tunanin zai fito daga bakinta.


Da dukkan hannuwanta ta sa tana share hawayen, haɗe da furta,


"Sanu da shigowa Aunty Sahiya."


Abin da take tsammanin faruwarsa sam! Ba shi ne ya faru ba. Sai saɓanin haka da ta gani. Murmushi ne shimfiɗe a fuskarta, tana mai ƙara kallon Fiddou, cike da yanayin tausayi.


"Yauwa Fiddou. Kukan ne halan har yanzu ya ƙi ƙarewa?"


Mamaki bai bar Fiddou ta iya furta komai ba, sai kallon al'ajabi kawai da take bin ta da shi.


"Ki yi haƙuri Fiddou, komai yai yi hwarko yana da iyaka. Kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi."


Ba ta taɓa tsammanin Aunty Sahiya ta san hakan ba, haka kuma ba tai tsammanin akwai ranar da Aunty Sahiya za ta iya fuskantarta da irin wannan kalamin ba.


"Fiddou magana nake son yi da ke, ta fahimta. Hwatar za ki mallaka mini dukkanin nutsuwa da hankalinki."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta ce,


"Insha Allahu. Ke nake saurare."


Matsowa ta yi daf da Fiddou, ta ce,


"Gahwara zan nema a wurinki Fiddou. Na sani, na san ni ɗin ban zama ta gari a gare ki ba. Tunda na auri Yayanki Labib ban taɓa yin wani abu da nuhin hwarin cikinki ba, duk da kuwa naki ƙoƙarin na ganin kin ba ni girmana.


Ki sani Fiddou, na yi da na sani, da na sani mara misaltuwa. Sai yanzu nake jin haushin kaina; rashin kyautata mikin da na yi, duk da kuwa ke ɗin kina da buƙatar mai kyautata miki.


Don Allah Fiddou ki yafe min, wallahi na yi alƙawarin hakan ba za ta sake hwaruwa ba."


Tana dakatawa a nan, da sauri Fiddou ta tsugunna a ƙasan Aunty Sahiya, tana kallon yadda take kuka, kuka mai tabbatar da ta nadama.


Hannunta ta saka Fiddou, ta ringa share mata hawayen, tana faɗin,


"Ki daina kuka Aunty Sahiya. Wallahi komai ya wuce. Allah Ya yahe muna baki ɗaya."


Da haka suka rungumi juna, cike da ƙaunar junansu, tamkar babu wani abu da ya taɓa shiga a tsakaninsu.


***


Sosai rayuwar Sans ta sauya, daga baƙin ciki zuwa farin ciki. Duk wani abu da zai nema yana samu, tamkar sadda yake gidansu. Kulawar da su Yax ke ba shi, ko shi ne Ogan nasu iya wanda za su ba shi kenan. Sosai suke girmama shi, duk da kasantuwarshi gurgu, ba ya neman komai ya rasa a rayuwarsa.


A lokacin da Sans ya cika wata guda a gidan ne, Bobby ya fara ƙoƙarin karkatar da shi, ta hanyar koya masa shan cyrup, da niyyar duk wata damuwa da yake cikinta za ta gushe, izuwa wata duniyar ta daban.


Daga farko sam! Sans bai yarda da hakan ba. Dalilin da ya sa ya butulce ma Bobby kenan, ya kuma ƙi karɓar wannan tayin nasa. Sai daga baya ne sadda damuwar tunowa da iyayenshi ta addabe shi, ya ringa tunanin tilon ƙanwarsa Yamaira, kwatsam Bobby na zaune da shisha a gabanshi, da kuma karan sigari a hannu yana zuƙa, sai tarin kwalaban cyrup a gabanshi, ya shanye wasu, bai fasa wasu ba.


A zaune ya same shi ya yi mankas, amma bai fara fita daga hayyacinsa ba.


Ƙoƙarta sauka daga keken nasa ya yi, saboda a tsawon wannan kwanakin har asibiti Bobby ke kai shi, inda yake da wani nurse abokinsa, yake ma Sans treatment.


"In har da gaske kake cewa wannan abun zai gusar min da damuwar da nake ciki, shirye nake da ɗanɗanawa, a karon farko na rayuwata. So da dama nakan tuno da rayuwata ta baya, in tuno da kyautatawar da na samu daga wurin iyayena. To kuma lokaci guda na rasa su, sun tafi sun bar ni ni kaɗai a duniyata. Don haka dole in fantsama wata rayuwar ta daban, saɓanin wacce nake a kai sadda suke raye."


Hannu ya ba Sans suka tafa Bobby, yana faɗin,


"Ko kai fa abokina. Yanzu na ji magana. Ungo wannan. Ina mai tabbatar maka da zarar ka fara shan shi yau, to gobe kai za ka kawo kanka da kanka cewa in ƙara maka."


Karɓar kwalbar ya yi Sans. A daidai zai kai kwalbar bakinsa, wani tunani ya faɗo masa a rai, cewa kar ya sha, ya yi ƙoƙarin kwaɓar zuciyarsa, da kuma ta abokinsa, a kan wannan mummunan halin. Wani sashe na zuciyarsa ne ya gargaɗe shi, kan cewa matuƙar fa bau aminta da wannan tayin ba, lallai zai dauwama a cikin damuwa, kamar yadda Bobby ya faɗa masa a baya.


A bakinsa ya kai kwalbar, bai sauke ba har sai da ya shanye ta tas, har yana suɗar baki-bakinta. Ya ajje ƙasa, yana mai kallon yadda Bobby ke sakin murmushin jin daɗi.


Tun daga wannan lokacin ne Sans ya ƙware a harkar, har ma ya nemi ya zarce Bobby. Suka ɓaci kuma da mugun son mata, da neman mata. Har a gida ake kawo musu matan. Yax da Esien ne suka koma tuƙin napep, duk don su ringa kawo ma su Sans mata suna musu fyaɗe. Idan sun yi fyaɗen kuma sai su sa su kai su can su yar, duk sadda suka farfaɗo su nemi hanyar tsira.


Da wani yammaci ne, daidai irin ƙarfe shida na yamma, babban titin ring road babu kowa a kai, babu giccin ko babur bare mota.





Bobby na tukin mota sai Sans kujerar zaman banza. A tsayin wannan lokacin kam sosai Sans ya ji sauƙi. Baki ɗaya ya ma daina hawa kujera, saboda kyakkyawar kula da ya ringa samu daga wurin wannan nurse ɗin da ke asibitin Turai.


Man motarsu ne ya ƙare, hakan ya sa Bobby yai yai ya tada motar amma ta ƙi tashi.


"Oh Gosh! Guy man motar nan fa ya ƙare."


Cikin takaici Sans ya ce,


"Damn it! A tsakiyar dajin nan da babu giccin kowa ne mai zai mana haka?"


"Ka dai gani ai."


"Guy wats the solutuon?"


"Don't really know abokina. Sai dai ko in kira Yax ya ɗauko jarka ya siyo ya kawo mana. Idan ba haka ba za mu shekara a nan, ba tare da kowa ya gitta ba. Kuma ga shi Saleem ya ce zuwa magrib za ka koma. Likitan ƙashin ya zo. Duk da dai ka samu sauƙi sosai, amma dai yana da kyau a ƙara tabbatar da lafiyarka."


"Haka ne. Just give him a call to. Allah sa akwai kuɗi a hannunshi."


"Ameen."


Bobby ya faɗa, haɗe da zaro wayarshi daga jikin chaji yana mai ƙoƙarin kiran Yax ɗin.


Kusan mintina arba'in suka ɗauka a wurin, kafin Yax ya iso, suka fita da nufin zuba mai a motar.


Wani mahaukaci ne suka gani yana tinkaro inda suke, hakan ya sa suka firgita su duka, suna ƙoƙarin guduwa saboda yadda yake ƙara tinkaro su.


Duhu ya fara a daidai lokacin, sai hasken wayoyinsu da suka dalle mahaukacin, wanda ya iso daf da su.


Ido buɗe suke ƙare mishi kallo su duka ukun, kallon yadda kamanninsa suka zo ɗaya da Sans, babu ko bambanci.


Sake kallon Sans suka yi Bobby da Yax, sannan suka sake dalle mahaukacin, don su sake tabbatarwa. Shi kanshi Sans ɗin mamaki yake. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin tsananin kama irin wannan ba.


***


Misalin ƙarfe sha biyu na dare ne Mama na zaune falo ta ji sallamar mace. Amsa sallamar ta yi tare da ba ta izinin shigowa cikin falon.


Bayan ta zauna ne suka gaisa, duk da cewa Mama ba ta san matar ba, amma hakan bai hana ta sakar mata fuska ba.


"Ya su Maryama? Ko ana makaranta?"


"Maryama na ɗaki. Maryama!"


Mama ta ƙwala mata kira.


Da hanzari Maryama ta share hawayen nata, sannan ta fito cikin wani taku a nutse, da mutuwar jiki a tattare da ita.


Murmushi ta saki a lokaci guda ganin wacce ta zo ɗin, zaune bisa kujera.


Bayan ta ƙarisa shigowa ɗakin ta zauna ƙasan matar, haɗe da faɗin,


"Umma ashe ke ce."


Ta saki sassanyan murmushi.


"Ni ce fa da kaina Maryama. Kin gan ni da rana tsaka ko? Ya na same ku?"


"Lafiya lau Umma."


Maryama ta juya ga Mama, ta ce,


"Mama ita ce Umman Amrah. Dama na faɗa miki za ta zo ai."


Faraa sosai a fuskar Mama ta ce,


"Allah sarki! Ai ban gane ki ba."


Umma ta ce,


"Haka ne. Ko ranar walimarsu ba mu samu damar gaisawa ba. Yau ai ga ni na zo har gida."


"Mun kuwa ji daɗi ƙwarai da gaske."


Mama ta fada. Ta kalli Maryama ta ce,


"Maryama kawo mata drink ko. Abinci ma na daf da sauka ai."


Bayan Maryana ta miƙe ta ce,


"Ehh Mama. Miya ce kawai ba ta ƙarisa dahuwa ba. Bara na kawo drink ɗin."


Ta doshi hanyar Kitchen, tana mai jin wata nutsuwa sosai a tattare da ita. Damuwar da take ciki na ɗan raguwa, duk da dai akwai ta ɗin fanjam a cikin zuciyarta.


Lemon five alive na roba ta sako guda biyu a plate, sannan ta ɗora cup a kai, ta nufi dawowa falon.


Fira ta tarar Mama da Umma suna yi, tamkar dama can sun san junansu.


A gaban Umma ta ajje, sannan ta koma kan kujera ta zauna, tare da faɗin,


"Umma don Allah ki sha lemu kafin a gama abinci."


Ɗaukar lemun ta yi Umma, ta fasa ta zuba kaɗan a kofi ta sha. Bayan ta shanye ne ta ce,


"Ina Annur ɗin yake?"


"Yana can ɗakin. Mu je ko?"


Maryama da Mama suka miƙe, Umma ma ta miƙe.


Sai da ta fara rufo ƙofar falon don kar a bar shi haka babu kowa, sannan suka nufi ɗakin da Modu yake, Maryama a gaba sai su Umma biye da ita.


A zaune suka same shi, yana ta faman jeren alphabets, sai ha haɗa sunan Amrah da Maryama ta koya mishi, sannan ya haɗa sunanshi, sai kuma na Maryama a gaba.


Kallonshi Umma ke yi cike da mamaki. Tabbas babu ko tantama Annur ne wannan. Real Annur, na Amrah.


Ido buɗe suka ƙarisa shigowa cikin ɗakin, suna kallonshi.


Ganinsu da ya yi ne ya sa Modu murmusawa, yana faɗin,


"Maryama kin gani na iya? Kalla ki ga. Ga Amrah, ga Annur, ga ki."


Ya saki murmushi yana gwada musu jeren da ya yi.


Idonshi bai ankare da Umma ba har sai sadda Maryama ta mishi nuni da ita. Take gabanshi ya hau faɗuwa, ya ringa nuna ta da yatsa, bakinsa ya gaza furta komai.


'Hakan na nufin ya gane Umman Amrah kenan?' Maryama ta tambayi kanta. Da alama ana samun nasara, ana samun ci gaba sosai. Tunda ga shi har ya fara tunowa da wasu abubuwa na rayuwarshi. Ya fara tunowa da wasu mutanen da suka dangance shi.


"Ka san ta ne?"


Maryama ta gaggauta tambayarshi, tana ƙura masa dukkanin idanuwanta.


"Ni ma ban sani ba. Kin san ni?"


Ya tambayi Umma.


"Ƙwarai da gaske kuwa Annur, na san ka, farin sani ma kuwa. Ni ce Umma, Umman Amrah. Ka tuna ni?"


Dafe goshinsa ya yi alamar tunani, kafin ya ce,


"Idan kin san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login