Showing 159001 words to 162000 words out of 201092 words
Chapter 54 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
da ya sa su Momy ɗin ba su koma gidan su Maryama wurin biki ba kenan a ranar.
A yadda Momy ta ga Habu ne ya tabbatar mata da ba lafiya ba. Miƙewa ta yi cikin kiɗima, ta ce,
"Habu me ya faru...?"
Bai ko jira ta dire tambayar tata ba, ya ce,
"Hajiya babu lafiya. Annur ga shi can kwance cikin jini, kamar ma ba ya numfashi ko kaɗan."
Ido buɗe momy ta dafe kanta, da sauri da sauri ta ji gabanta na faɗuwa. Ta ce,
"Habu me kake faɗa ne haka?"
"Hajiya ba wannan ba ne ya kamata ki yi, sai an gaggauta kai shi asibiti, domin a ba shi taimakon gaggawa, idan ma yana raye kenan."
Shi kanshi kuka yake sosai, su Hanan ma hankalinsu ya tashi, Janan ta nufi ɗakin Dady ta sanar masa. A kiɗime Dady ya fito shi ma, ko riga babu a jikinsa sai singlet, yana faɗin
"Ku ba ni mukullin mota."
A hakan ya fice zuwa ɗakin Sans, ya tarar mai gadi sai famar kuka yake, ya kasa zaune ya kasa tsaye.
"Ya Salaam! Annur me ya faru haka? What's wrong with you? Cakar ka ta yi wuƙar? Sai dai haka kam. Mallam Ya'u ku taimaka ku kamo min shi a kai mota, insha Allahu Annur ba zai mutu ba, zai tashi da kafaɗunsa."
Cicciɓarsa suka yi suka kai mota, a lokacin har su Momy da ke ta ruzgar kuka sun isa bakin Prado ɗin. Bayan an saka shi suka shisshiga ciki, kai tsaye suka nufi Nadda Hospital.
*
Sai shida da rabi ya samu damar tashi, kasantuwar hidimar biki akwai gajiya sosai. Da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta, ta sauko daga bisa gadon a hankali, sannan ta nufi toilet. Alwalla ta ɗauro sannan ta fito tana tsane ruwan hannunta a jikin rigar barcinta ta silk.
Hijabinta ta ɗauko ta saka sannan ta tada sallar, a lokacin har gari ya fara yin haske-haske. Bayan ta sallame ta yi addu'o'i sosai, sannan ta fara niyyar tashin Annur. Har ta ɗaga hannunta za ta ɗan bubbuga shi, sai kuma ta tuno cewa, psychologically ba a son tayar da mai mental illness daga barci. Sosai hakan ke ƙara rikita ƙwalwarsa, saboda an dakatar da wani jin daɗinsa. Fasawa ta yi, ta jawo blanket ta rufe shi, saboda sanyi-sanyin da ake yi, kasantuwar an kwana ana shara ruwan sama.
Komawa ta yi ta kishingiɗa bisa tafkeken kafet ɗin da ke baje daga gefen gadon, sannan ta zaro wayarta da ke jikin caji. Text take son ta tura ma iyayenta na godiya, da kuma sauran mutanen arziƙi da ƙawayenta na ban-gajiya. Iyayen nata ta fara tsara ma text mai matuƙar ma'ana, ta musu godiya na hidima da ita da suka yi tun haihuwarta har izuwa girmanta. Sun ciyar da ita, shayar da ita, suturtar da ita, sannan kuma suka ilimantar da ita ba tare da gajiyawa ba. Sun ba ta duk wani farin ciki da ya kamata iyaye su ba ma yaransu, har ma sun zarce. Sun ba ta tarbiyya mai kyau, wacce ta zam abar alfahari ga kowa, ake son koyi da duk halayenta. Sannan a ƙarshe suka ba ta farin cikinta, ta hanyar aura mata mutumin da take da muradin taimaka masa, da kuma tsantsar ƙaunarsa.
Tana gama rubuta text din ta sharr hawayen da suka sauko mata. Ta ɗan yi jim! Ba tare da ta sake kallon wayar ba, saboda jikinta da ya yi sanyi, iyayenta da kuma Hammad ƙaninta, kuma abokinta ta tuna, cewa ta rabu da su kenan fa sai dai idan ta je ganin gida.
Ta daɗe a haka kafin ta wartsake, ta musu sending message ɗin a tare. Kawu Imrana ta fara rubuta ma nashi, na tsayuwar da ya yi ga rayuwarsu, tun ma kafin su zo duniya. Sannan a ƙarshe ya goyi bayanta ɗari bisa ɗari, ta hanyar tsayuwa tsayin-daka ganin an aura mata farin cikinta. Ba ta da hanyar biyansa, addua ce kawai za ta masa. Ta nemi gafararsa a kan butulce ma zaɓinsa da ta yi, ya yi haƙuri ya gafarta mata.
Text guda ta rubuta na ban-gajiya, ta yi sharing ɗinsa ga duka contacts ɗinta. Datarta ta buɗe saboda ta jima ba ta hau charting ba. A hankali charts suka ringa shigo mata, wasu daga ciki na taya ta murna ne, mafi rinjaye dai groups ne da take, saƙuna da yawa saboda jimawar ta ba ta hau ba. Kamar wasa ta ga shigowar saƙon Dr. Hamdan, tamkar a mafarki haka ta shiga cikin saƙon nasa, ta hau karantawa.
Ce mata ya yi ya ji ta shiru, kuma ya kira ta tun ranar da suka yi magana amma ba ta ɗauka ba. Tun bayan da suka yi maganar nan bai san dalili ba ya ji abun ya masa tsaye a rai, ya ji tausayin mara lafiyan sosai. Idan har za ta samu lokaci, to ta daure ta kawo shi Maidugurin, ya mata alƙawarin duba lafiyarsa sosai. Idan kuma tana ga kamar abun da sauƙi sosai, to ta jira shi, akwai Seminer da zai je Kano nan da sati uku, in ya samu yadda yake so zai zo Katsinar wurin wani abokinsa. Idan kuma bai samu zuwa ba, to sai su same shi a Kano ɗin.
Sosai Maryama ta ji daɗin hakan, farin ciki ya kasa ɓoyuwa daga fuskarta, gani take kamar ma har Annur ɗinta ya warke ne. Saboda yadda Dr. Sandra ta rinƙa ƙawata Dr. Hamdan ta tabbatar cewa gwani ne.
Miyar masa da saƙon ta yi, cewa za ta jira shi ɗin har ya zo, tunda dai ta bi shawarwarin Dr. Sandra sosai, ta kuma ga ci gaban hakan.
Kashe datar ta yi bayan ta tabbatar saƙon ya je masa, sannan ta miƙe bisa ƙafafuwanta, tana jin yadda daɗi ke ziyartar zuciyarta. Kallon Annur ta yi a karo na biyu, ta saki murmushi, ganin yadda ya haƙiƙance barcinsa yake.
Falo ta nufa kai tsaye, ta hau dudduba yadda komai na falon ya tsaru, sai ta ji ya ƙara birge ta sosai. Daga nan ta wuce ɗayan bed room ɗin, wanda ya kasance nata, shi ma ta sake duddubawa, komai ya yi tsaf gwanin ban shaawa. Ta fito kuma ta nufi kitchen. Haka ta zagaye gidan tsaf tana duba tsaruwarsa, kafin ta koma ɗakin Annur. Har a lokacin bai tashi ba, a bayyane ta furta,
"Sai sharar barcinsa yake yana morewa. Kai ma kenan da babu gajiyar biki a tattare da kai."
Ta cire hijabinta sannan ta shiga wanka. Bayan ta fito daga wankan ta wuce ɗakinta. Mai ta shafa sannan ta yi light make_up. Ta feshe jikinta da body spray lungu da saƙo, har a bayan kunnenta. Bayan ta gama ta ɗauki cotton bud ta goge bayan kunnen nata da shi. Bakin wardrobe ɗinta ta isa, ta fiddo wata atamfa kalar light blue, da aka ƙawata da manyan flowers kalar pink. Ɗinkin riga da skirt ne da suka bi jikinta, suka bayyana shape ɗinta sosai. Bayan ta saka ta ƙarisa gaban madubi, ta kalli kanta sosai sannan ta ɗaura ɗankwali. Turarukan oud kala kala ta feshe jikinta da su, ta saka takalma high heels ta bar ɗakin.
Isar ta ɗakinsa ta same shi ya tashi, sai famar dube-dube yake, da alamu ita yake nema. Yana ganinta ya saki tattausan murmushi, yana motsa bakinsa.
"Mi Amor ka tashi?"
Bai san me take nufi da kalmar da ya ji ta kira san da shi ba, sai dai kai kawai da ya ɗaga mata, fuskarsa har yanzu ƙunshe da faraa.
"Then, mu shiga toilet ka yi alwalla ko?"
"Ban iya ba."
Ya faɗa yana gyargyaɗi da kansa.
"Mu je zan yi maka ne. Daga yanzu kullum zan rinƙa koya maka sallah. Insha Allahu sannu a hankali za ka iya. Mu je."
Miƙewar kuwa ya yi, ya bi bayanta suka isa ban-ɗakin. Sai da ta matsa masa toothpaste a brush ta goge masa lungu da saƙo na bakinsa, sannan ta wanke mishi tas, ta masa alwallar. Tare suka fito, ta ce ya hau bisa kafet ɗin, duk abin da ya ga ta yi shi ma ya yi, ta saka hijabi.
Raka'a biyu kuwa suka yi, sai famar waige-waige yake yi, sai ya saki murmushi, sai kuma ya ɗaure fuska, har suka ƙarisa sallar. Addua ta saka shi ya ma kanshi sosai, sannan ta ce,
"Yanzu sai wanka ya rage ko?"
Ya ɗaga mata kai.
"To ina zuwa. Ban kunna heater ɗin ba ma."
Ta shiga toilet ɗin.
Knocking ta ji ana yi daga bakin ƙofa, ta gaggauta fitowa daga toilet ɗin ta isa ƙofar falo. Tana buɗewa ta ga Hammad ne da wata cousin ɗinta Aysha, hannuwansu riƙe da basket mai girma, sun kamo su biyun. Murmushi ta sakar musu, ta ce,
"Sannun ku da zuwa ƙannena. Ku shigo."
Ta yo gaba suka biyo bayanta. Zama suka yi bayan Aysha da Hammad sun azzo basket ɗin a bisa dinning table.
"Ina kwana Yaya?"
Suka faɗa a tare.
"Lafiya ƙalau. Ya gida ya su Mama?"
"Sun ce ma a gaishe ku."
"Aikuwa muna amsawa."
Ta isa gaban electronics, dama jiya su Jiddah sun haɗa mata komai, kunna musu kallo ta yi, African Magic Hausa ta kai musu, ana yin film ɗin Maula.
"Ku yi kallo Sholie. Zan je in dawo. Idan ba ku karya ba ku ɗiba ku karya."
Hammad ne ya ce,
"Mun karya Yaya. Naku ne ku kaɗai ke da Yaya Noor."
Dafa kansa ta yi sannan ta ce,
"To shi kenan. Ku yi kallo kafin in dawo."
Ta nufi ɗakin Annur ɗin. A yadda ta bar shi haka ta same shi, ya yi zaune a takure bakin gado, yana jiran ta.
"Am sorry na bar ka Mi Amor. Su Hammad ne suka zo. Mu shiga ko?"
Ta jawo light blue towel ɗinsa jikin ƙofa, ta riƙe a hannunta.
Bayan sun shiga toilet ɗin ta rufe ƙofar, nan fa ake yin ta. Samun kanta ta yi da jin kunyar ganin tsiraicinsa, sosai ba kadan ba. Shi kam ko a jikinsa, ya hunce sannan ya tsuguna. Idonta ta rinƙa rurrufewa, sai idan za ta shafa sabulu take buɗe su, da haka dai aka yi wannan wanka, da ƙyar da jiɓin goshi. Idon a rufe ta ɗaura masa towel ɗin sannan suka fito. Ɗan ƙaramin towel ta ba shi cewa ya tsane ruwan jikinsa da shi, sannan ta ƙarisa gaban wardrobe ɗinsa ta fito masa da wani baƙin yadi mai matuƙar kyau. Feshe kayan da turare ta yi, har da boxer ɗinsa. Ta shafa masa mai, da mayukan turare a jikinsa, ta fara ƙoƙarin saka masa kayan. A nan ma an sha wata dagar, da ƙyar dai ta samu ta gama shirya shi, sai famar dariyar yaƙe yake yi, yana kallon kayan jikin nashi, yana tattaɓa su yana motsi da kai.
"Kayanka ko? Suna da kyau sosai Mi Amor. Sun kuma karɓi jikinka. Amma ka san me? Ka fi kayan kyau. Sirrin kyawun kayan ma daga kai ne. Inda a ce wani namijin daban ne ya saka su to ba za su yi kyawun haka ba."
Ta kama hannunsa suka ƙarisa falon, cike da ƙaunarsa, tana jin duniyarta na mata matuƙar daɗi.
***
*My pipu ku yi maneji da wannan. Na san ya yi kaɗan, amma dai ku min uzuri. Kuma sai da na yi 1k words duka suka goge sai da na sako sabo.*
*Ya kuka ji wannan shafin? Kun ga soyayyar Marnoor ta fara ƙarfafa sosai ko? Irin hakan shi ya fi komai daɗi.😍😘*
*A wani ɓangaren kuma, mun ga yadda Sans ya luma ma cikinsa wuƙa, da nufin kashe kansa.* *Wanann wace irin damuwa ce mutum ke gare shi da har zai gwammaci ya rasa rayuwarsa? Duk wanda ya kashe kansa fa ya mutu kafiri, wutar Jahannama ita ce makomarsa.*
*Ko Sans ɗin ya mutu? Alƙalamin Amrah kawai zai warware mana.😥😪*
*My Sister na gode ƙwarai da haɗaɗɗiyar video da kika haɗa ma wannan littafin. Video fa ta yi kyau masha Allah! Kowa ya yaba. Allah ya saka miki da alkhairi ya bar zumunci.❤💃*
*Kar a manta a rinƙa yi ana tunowa da danna ƴar tauraruwar nan mai kyau da daɗin taɓawa.😀*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/21, 12:06 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
6⃣7⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Emergency aka karɓi Sans, aka shiga ciki da shi domin tabbatuwar yana raye ko ba ya raye? Idan yana raye to sai a ba shi taimakon gaggawa.
Tun sadda aka shiga da shi hankalin su Dady bai kwanta ba. Momy sai zirga-zirga take, ba ta nan ba ta can, tana ta aikin zubar da ƙwalla. Sosai suke son sanin halin da Sans yake ciki. Hakan ya sa Dady ya kasa daurewa, bai jira an ba shi izini ba kawai ya afka cikin ɗakin.
Ganin ya yi malaman asitin sun yi cincirindo a bakin wani gado, duk da bai ga wanda suka zagaye ɗin ba, amma ya tabbatar da cewa Annur ɗinsu ne. Hakan ya sa ya gaggauta isa inda suke, hankalinsa a tashe. Kallo ɗaya za ka ma Dady ka tabbatar cewa ba ya cikin nutsuwarsa. Saboda yadda duk ya bi ya koma tamkar zararre, rigar jikinsa ma a birkice ya saka ta, saboda har ma ya shiga mota daga shi sai singlet da gudu Janan ta koma ta ɗauko masa rigar ya saka.
"Ya za ku bar ni a cikin duhu ku kasa fa min haƙiƙanin abin da yake damun yarona?"
Ya faɗa a fusace, yana kallon yadda suke aiki bakin ƙoƙarinsu domin taro numfashinsa, kafin a fara yi masa ɗinki a cikin nasa.
Babban likitan da ke wurin cikin tattausan lafazi ya dafa kafaɗar Dady, ya ce,
"Ka kwantar da hankalinka Alhaji. Insha Allahu yaronka zai ci gaba da rayuwa kamar kowa, zai tashi da kafaɗunsa. Akwai bayanin da ya kamata na maka, amma ka yi haƙuri ka fita har mu shawo kan babban lamarin, sannan zan buƙaci ganawa da kai. Kar ka ji komai fa, da yardar Allah komai zai daidaita."
Sai a sannan Dady ya ɗan samu nutsuwa. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, ba tare da ya furta komai ba ya nufi barin ɗakin.
Da sauri su Momy suka ƙarisa gabanshi, suna tambayarsa halin da Sans ɗin yake ciki.
"Da ransa bai mutu ba. Suna can suna aiki a kansa sosai. Mu taru mu saka Annur ɗinmu a addua, ita ya fi buƙata daga gare mu a daidai wannan lokacin ba wai kuka ba."
Yana gama faɗin haka ya koma bisa teburin da aka jera a reception ɗin ya zauna haɗe da rafka uban tagumi, yana ta famar ambaton sunan Allah daga bakinsa.
Jin hakan ya sa su ɗin ma suka ɗan samu kwanciyar hankali. Amma duk da haka ba su daina yin kukan ba.
Hanan da Janan suka zauna kusa da Dady, momy kam zaman ya gagare ta, zirga-zirga kawai take hannunta tallabe da bayanta tana hawaye tana addu'a a bakinta.
*
Kanta ta ɗora a saman cinyarsa. Fuskarta ƙunshe da fara'a, ta jawo hannunsa saitin kanta tana faɗin,
"Mi Amor kai fa nake jira don Allah. Ka ringa bubbuɗa tsakiyar gashin kana duba inda ke da dandruff sai ka kankare min."
Saurarenta kawai yake, amma fa ba ya fahimtar komai, sai murmushin da yake saki shi ma ɗin. Ta san da hakan sarai, ta san cewa ba ya gane abin da take nufi, amma da gan-gan take komai, tana son ƙara kusancin zukatansu ne.
Tashi ta yi zaune haɗe da girgiza kanta, gashinta da ya barbazu bisa fuskarta ya koma ya kwanta har bisa gadon bayanta. Ribbon ɗinta ta sa ta ƙulle gashin, sannan ta shafa mai a gaba-gaban ya ƙara kwanciya, kwantaccen gashin goshinta ya kwanta luf.
"Yah Noor ka san me?"
Ya girgiza mata kai.
"Ina ƙaunarka sosai."
Ta saki sassanyan murmushi.
"Kai ma ba za ka ce kana ƙaunata ba?"
Ta ɗan turo baki alamun shagwaɓa. Kallon ta kawai yake tana daɗa birge shi. Sai dai kuma bakinsa ba zai taɓa iya furta yana son kowa ba face Amrah. Duk yadda ya buɗe baki da nufin faɗa wa Maryama cewa yana son ta, sai bakin ya gagara faɗi, ya ambaci sunanta da Amrah.
"Kana jin kunya ta ne? Well. Zo ga kunnena ka raɗa min a ciki. Don Allah for once dai ka furta min cewa kana so na. Zan ji daɗi sosai Mi amor"
Ta kanga masa kunnen nata, tana sauraren abin da zai faɗa mata. Ji ta yi ya yi murmushi a kunnen nata, ya ce,
"Amrah nake so!"
Janye kunnenta ta yi a fusace, ranta in ya yi dubu ya ɓaci. Ta fara jin haushi sosai, da kuma kishi da ke nuƙurƙusar zuciyarta. Ita kanta ba ta san yadda akai ta kamu da kishin matacciyar da ba ta duniyar ba ma.
"Yah Noor ba zan ƙara cewa ina son ka ba tunda har yau na gagara ka ambata kana so na. Haba don Allah! Kullum dai Amrah! Amrah! Amrah!? Ya kamata by now a ce ta fita daga ranka. Matar da ba ta duniyar baki ɗaya, amma ta gagara fita daga bakinka. Haba mana ka samu ka fitar da ita daga ranka ko za ka samu dawowa a cikin hankalinka..."
Ta kwantar da muryarta a daidai sadda hawaye ke fita daga idanuwanta, ta ce,
"Don girman Allah Yah Noor ka so ni koda rabi-rabin ƙaunar da nake maka ne. Ya kamata a ce ka farga, ka fitar da Amrah daga zuciyarka. No more Amrah in your life yah Noor. No more Amrah in this world. Amrah ta tafi inda ba a dawowa. Ta tafi inda mu ɗin ma za mu je mu same ta, amma ba dai ita ta dawo ta same mu ba. Na sani, cewa Amrah masoyiyarka ce ta gaske. Ka ƙaunace ta, kamar yadda ita ma ɗin ta ƙaunace ka. Kun yi soyayya ta tsakani da Allah, mai cike da tsafta da yarda da juna. Amrah was your first love, amma kar ka ɗauka cewa ita ce last love ɗinka. Saboda har yanzu kana da masu yi maka irin ƙaunar da Amrah ke maka."
Ta dakata daga nan, tana kuka sosai mai cike da tashin hankali, duniyarta na mata juyin waina, kamar yadda zuciyarta ke juyewa daga farin-ciki zuwa baƙin-ciki.
Kanta a duƙe yake ƙasa, tana sakin kuka mai cike da tashin hankali, kamar wasa ta ringa