Showing 132001 words to 135000 words out of 201092 words
Chapter 45 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
tsaida Annur, duk tarin mazajen da ke duniyar nan? Ki dai canza tsari, ki canza zaɓi, wallahi ba ki cancanci auren fasiƙin namiji irin Annur ba."
Yana kaiwa nan ya dakata. Yana sauraren abin da zai biyo baya.
Kawu Imrana ne ya yi gyaran murya, ya ce,
"Duk wani halin hauka da yake ciki, mai sauƙi ne, mafi tsananin dai wannan halayen nashi da Ahmad ya faɗa."
Mamaki sosai Deedah ke yi. Hauka? Ya tambayi kanshi. Kenan Annur ya koma ruwa? Ya taɓa sanin sadda ya haukace, wanda tun bayan nan ne ya warke baki ɗaya ya canza halayenshi.
"Maryama. Dole za ki canza tsari. Duk da na miki alƙawarin aura miki duk wanda kike so, hakan ba yana nufin wai zan yarda ki auri kowanne irin mutum ba ne. So nake na gina rayuwarki. Ki auri mutumin kirki, wanda zai kyautata miki, ki ji daɗinsa, ko muna raye ko kuma ba mu raye."
Cikin ƙoƙarin shanye kukanta ta ce,
"Kawu, wanda Yaya Deedah ke magana fa ba shi ba ne Annur. Ainahin Annur ɗin yanzu haka yana gidanmu, cikin halin taɓin hankali..."
Ta kwashe komai da ta sani, tun daga farko har ƙarshe, a taƙaice ta sanar da shi.
Abba da ke zaune bai musa ba, saboda ya san yadda komai ya faru.
"Kawu wallahi in dai don hauka ne, ni na amince a hakan zan aure shi. Adduarku kawai muke da buƙata."
Gyaɗa kansa ya yi kawu Imrana. Ya ce,
"To shi kenan ai. Tunda dai kin zaɓi hakan, kuma ya kasance mutumin kirki ko kafin haukan nasa, babu komai. Allah ya tabbatar mana da dukkanin alkhairanSa. Yanzu ai dole za a kai shi gidansu ko? Tunda ai ba zai yiu ai aure ba tare da wani nashi ba."
Ɗago kanta ta yi, ta ce,
"Wannan mai sauƙi ne Kawu. Akwai ƙawata Jiddah, Mamanta ƙawar maman Annur ce, zan mata magana, mu nemi kawunshi mu yi maganar, in masa bayanin komai, sannan in haɗa ku. Ba na son Annur ya koma gidansu a cikin ƴan lokutan nan, saboda wancan fasiƙin da ke zaune gidan a matsayin Annur ɗin, kar ya ɗauki wani mummunan mataki a kanshi."
"Babu damuwa to. Ki dage da addua. Insha Allahu komai zai zo yadda ake so. Ku tashi ku tafi kawai, dare na yi."
Godiya sosai Maryama ta masa. Zuciyarta na mata daɗi sosai, ta ƙara da faɗin
"Kawu don Allah ka nema min gafarar Abba. Ya yafe min. Wallahi ba haka na so ba ni ma, ni kaina ban san yadda aka yi ka san wannan zancen ba."
Murmushi ya saki kawun, ya ce,
"Kar ki damu. Fushi ne ya yi, kuma na tabbata zai yafe miki. Ku je kawai. Hajiya sai da safe ko?"
Jiki a sanyaye Mama ta ce,
"Mun gode ƙwarai Yaya. Sai Allah ya tashe mu lafiya."
Ba su ko shiga sauran parts ɗin gidan sun gaisa da matan nashi ba, suka zarce inda motarsu take, Mallam Ya'u ya tayar, suka nufi gida.
*
Da isarsu gida ta faɗa bisa kujerar falo tana kuka sosai, kukan da ita kanta ta rasa gane ko na menene. Kuka sosai take, mai haɗe da ƙara da shessheƙa.
Ji ta yi an dafa ta. Ba ta ɗago kan nata ba bare ta nemi sanin wanda ya dafa ta ɗin. Sai ƙarfafa kukan nata ma da ta yi.
Muryarshi ta ji ya ce,
"To ai kuma ta kuka ta ƙare ko Yaya? Ina don za a miki auren dole ne ya sa kike kuka? To ai an fasa. Kawu da kanshi ya miki alƙawarin ba ki auren wanda kike so. Dama kuma ai na miki wannan alƙawarin ko?"
Sai a sannan ta ɗago fuskarta da ta gama kumburewa don kuka. Idanuwanta baki ɗaya sun rine, sun zama jajaye.
"Hammad dole ne na yi kuka. Yanzu da wane ido zan ci gaba da kallon Kawu? Na rasa ta yadda aka yi ya san cewa ba na son Yaya Deedah, tunda dai na tabbata Abba ba zai taɓa faɗa masa ba, kamar yadda ya ce ɗin. Na rasa a wanne babi zan saka rayuwata a daidai wannan lokacin. Shin farin ciki ne ko kuwa baƙin ciki?"
Guntun murmushi ya yi Hamnad, haɗe da sassauta muryarsa, ya ce,
"Ni ne nan na kira kawu ɗazu da safe."
Ya kuma sakin sassanyan murmushi, wanda ke ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa.

Cike da mamaki ta kalle shi.
"Kai ne?"
Kai ya jinjina mata.
Sai yanzu ta gama gane komai. Saboda ɗazu da rana Mama ta ɗauko wayarta ta ga sunan Kawu a dials ɗinta. Har ta tambaye ta ko ita ta kira shi? Amma ta ce ba ma ta ga wayar tata ba tun safe. Mama ta ce to ƙila Abba ne ya kira, duk da dai ba ta tsammanin shi ɗin ne.
Muhammad ya buɗe bakinsa ya ce,
"Abin da ya faru shi ne, bayan mun gama gaisawa da Kawu, ya nemi sanin dalilin da ya sa na kira shi. Cikin rawar murya na ce,
"Kawu dama so nake in faɗa maka wani abu. Ka kuwa san cewa Yaya Maryama ba ƙaunar Yaya Deedah take ba? Wallahi Kawu yanzu haka tana can tana kuka. Damuwa ta taso ta gaba, tun daga jiya ba ci ba sha. Kuma Abba ya ce ba ta isa ba! Dolenta ta auri Yaya Deedah ko tana so ko ba ta so. To Kawu ni kuma ba na so a ma Yaya Maryama auren dole. Ina son ta fita daga cikin wannan damuwar da take."
Kawu Ya yi shiru jim! Kafin ya ce,
"To kai waye ya faɗa maka haka? Ita Maryamar ce ta saka ka ka kira ka sanar min?"
Na ce,
"Ko kaɗan Kawu, Yaya Maryama ba ma ta san zan kira ka ba. Ita dai kawai ta sanar da ni cewa ba ta da ra'ayin auren Yaya Deedah. Kamar yadda ta ɗauke ni ɗan uwanta na jini to haka ta ɗauke shi. Kuka kawai take ta famar yi tun jiya, har wayewar garin yau. Ni Kawu abin da ma ya fi ba ni tausayi shi ne, hatta da gaisuwarta yau Abba bai amsa ba. Kawai don ta nunar da ba ta son Yaya Deedah da aure, shi kuma ya ce ba zai iya tinkararka da wannan zancen ba."
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce,
"To shi kenan Muhammad. Insha Allahu za a duba, za kuma a yi duk abin da ya dace. Kar ka faɗa ma kowa ka ji? Ni ma babu wanda zai ji daga bakina. Na maka alƙawari."
Daga nan na mishi sallama sannan na tsinke wayar, na lallaɓa na dawo da wayar zuwa ɗakin Mama."
Ba ta san sadda ta saki murmushi ba Maryama. Ta miƙa masa hannu suka kashe, ta ce,
"Good and talented boy. Who teach you all these?"
Murmushin ya yi shi ma. Ya ce,
"My brain."
"I have trust on it."
Ta kuma sakar masa murmushi. Tana jin ƙaunar ƙanin nata na daɗa yawaita a cikin zuciyarta. Wani abu sai jininka. Ranar naka kuwa sai naka. Yanzu idan ba Muhammad ba waye zai iya yi mata haka? Don ma dai yaron yana da ƙarfin hali. Yadda suke girmama Kawu Imrana, ko ita da take babba ba za ta taɓa tunanin ta tinkare shi da maganar ba, amma shi har ya yi wannan tunanin.
"Around of applause for yourself."
Ta faɗa tana taya shi tafa ma kanshi.
Mama da tun ɗazu take tsaye tana saurarensu mamaki ya gama kashe ta. Har ga Allah zuciyarta ta gama tunzura ta da ta yi fushi da ƴar tata, saboda kunyata su da ta yi. Sai dai yanzu ta saduda, ta roƙi ƴarta a cikin zuciyarta, cewa ta yafe mata, ta nemi ɗaukar alhakinta ba tare da haƙƙinta ba. Ashe ita kanta ba ta san abin da ke wakana ba, aikin Muhammad ne duka.
Gyaɗa kanta ta yi tana mai share dukkanin ƙwallan da suka gama kwarara bisa fuskarta. Soyayyar ƙani da yayarsa ta burge ta, yadda ƙaramin yaro ɗan shekara goma sha biyu kamar Muhammad ya ɗauki damuwar yayarsa a matsayin tashi. Ya gusar mata da damuwarta ba tare da shakkun komai ba. Lallai ƙauna ta yi ƙauna. Shaƙuwa iya shaƙuwa.
Ɗakinta ta nufa domin gabatar da sallar magrib, da kuma ta isha'i da ake kan kiranta.
Miƙewar ta yi ita ma Maryama, ta ce da Muhammad za ta fara shiga ɗakin Annur ta ga lafiyarsa, kafin ta nufi nata ɗakin ta yi sallah, shi ɗin ma ya je ya sauke tashi.
A zaune ta same shi, yana aikin wasa da alphabeat kamar yadda ya saba kodayaushe.
"Ya Noor barka da dare."
Ta furta bayan ta ƙarisa shigowa ɗakin.
"Me ya sa kika yi kuka?"
Kawai ta ji ya faɗa, bayan ya gama nazartar yanayin fuskarta.
Saurin share fuskarta ta yi, da ƙirƙiro murmushi ta ce,
"Waye ya faɗa maka na yi kuka? Ni ban yi kuka ba. Ciwon ido ne fa nake yi."
"Amrata ba ta ƙarya. Ba ta ɓoye min dukkanin damuwarta. Ki yi ƙoƙarin zama kamarta."
Tamkar ba shi ya yi maganar ba, ya ci gaba da wasan shi.
Kallon shi kawai take, mamakin kalamansa take sosai. Wurin zama ta nema, ta ce,
"Ya Noor magana za mu yi."
Shiru ya mata, ba tare da ya furta komai ba, sai dai murmushi kawai da yake saki.
"Ya Noor, aure Abbana ya ce zai min."
Ɗago kansa ya yi cikin kiɗima, idanuwansa a buɗe, ya gagara furta komai.
"Ka san wa na ce masa zan aura?"
Ba ta jira me zai ce ba, ta ci gaba da faɗin,
"Na ce masa kai nake so, kai zan aura."
Dariya ya saki mai nuna zallar nishaɗin da kalaman nata suka saka shi.
Ta ci gaba da,
"Za ka amince ka aure ni ko?"
"Ehh mana. Ba na faɗa miki Amrata ta ce na aure ki a madadinta ba? Na ji daɗi, za a mana aure."
***
*Na gaji. A yi haƙuri da wannan, tunda dai jiya na muku posting.*
*Sannu a hankali na fara warware muku wasu abubuwa ko? Kun dai ga mahaukaci mai kama da Sans, wanda ba kowa ba ne face Annur. Haka kuma mun ga yadda ake nemansa ruwa a jallo, da kuma ƴan sanda da aka baza domin neman shi. To sai dai abin da ba mu gama sani ba, me ya sa Sans ya gaggauta guduwa ba tare da ya ƙarisa wurin ƴan sandan ba? Hakan na nufin yana da wani ƙudiri ne? Me kuke hasashe? Drop your comments.*
*Masu mutunci kar ku manta dai, ku cika aikinku na kankaro mutunci.😀*
Thanks all
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/8, 11:31 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
5⃣9⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Mamaki fal ya kama Bobby a lokacin da Sans ya gama yi masa bayanin abin da yake faruwa.
"To me kake tunanin yi yanzu?"
Ajiyar zuciya ya sauke Sans, ya ce,
"Ina tunanin komawa gidansu a madadin mahaukacin da na ga an maƙala sunanshi Annur. Tunda dama ka ga nan ɗin da nake zaune ba a kowa nake ba. Ba zai yiu rayuwata ta dauwama a gidan gona ba, kuma a ƙarƙashinka. Nan gaba zan iya zame maka wani nauyi. Gwara dai tunda ga mafita ta zo, a sauƙaƙe kawai in koma gidan nasu, ba za a samu matsala wurin canje canjen halaye ba, tunda dai ka ga shi ɗin mahaukaci ne, da hauka ya baro gidansu."
Hannu Bobby ya ba shi suka tafa. Ya garƙame hannun gam-gam yana faɗin,
"Guy kai shege ne fa. Ka san hanyoyin ɓullewa da dama. Amma ka san me? Akwai wani Boka da nake zuwa wurinshi, duk sadda wata matsala za ta taso min. Kawai za mu je wurinsa, sai ya ɓatar mana da wannan mahaukacin, a masa kurciya koma ina ne ya tafi. Sannan kuma a kashe bakin iyayen nashi, kar su taɓa ɗago ka, kar kuma su taɓa yin shakku kan cewa Annur ɗin su ne ko ba shi ba ne? Kamar hakan zai yi ai ko?"
Jinjina kansa ya yi da sauri Sans, ya ce,
"Good idea. Yanzu yadda za a yi, a mishi dabara a raba shi da kayan jikinsa, su dawo a jikina. Sannan in fita cikin daren nan, ba na so a kwana. Ba kuma da yanayin hauka zan koma musu ba. Cikakken mai hankali zan koma, saboda kar abun ya yi tsayi, in rinƙa yin hauka saɓanin wanda shi ɗin yake yi, har wata maganar ta ɓullo, a samu matsala mai girma. Ko ya ka ce?"
"Hakan ya yi daidai Sans."
Ƴan yatsunshi biyu ya ɗora a laɓɓanshi haɗe da faɗin,
"Shshshsh! Kar in kuma jin Sans a bakinka. Annur nake a yanzu."
Ya ƙarisa maganar da sakin tattausan murmushi.
"Amma fa guy har yanzu ina mamaki. Kodai asalinku twins ne wai?"
"Kai share kawai. Kamanni ne kawai aka samu. Kodayake dai Aunty ta taɓa faɗa min cewa mu twins ne, amma ai ka ga ba a gari ɗaya ba ne. Kuma ainahin twin brother ɗina ya rasu tun sadda aka haife shi, kafin ma ni in fito duniya. So, ka daina wannan tunanin. Its just a coincidence."
Kafaɗunsa ya ɗaga duka biyu Bobby, ya ce,
"Shi kenan ai. Yanzu me ya kamata a yi?"
"Kawai tare za mu tafi. Idan mun haɗu da ƴan sanda sai ka ce tsinto ni ka yi a galabaice, shi ne na ce ka taimaka ka kai ni gida. Idan kuma ba mu haɗu ba, kai tsaye mu ɗauki address ɗin gidan su Annur ɗin, mu nufi can. Na san me zan yi daga nan."
Bobby ya ce,
"Yadda ka ce a yi haka za ai. Sai dai kuma abu ɗaya."
"Mene ne?"
Sans ya tambaya.
"Ba ka yi kama da wanda ya galabaita ba."
Ya saki murmushi Bobby bayan ya yi wannan maganar.
"Kar ka damu, na san me ya dace. Yanzu dai kai snapping gashinsa, yadda askin kanshi yake, daga nan idan ba mu haɗu da ƴan sandan ba sai mu samu mu nufi wurin mai askin nan ya miyar min irinshi. Idan kuma mun haɗu da su shi kenan. Na tabbatar in dan aski ba za su taɓa kawo komai a ransu ba. Nan da kamar kwana biyu ko uku sai mu je wurin bokan."
"Guy kana tunanin daga tasowarka hauka za su bar ka ka fita ne? Ba na jin za a tama barin ka. Gobe da sassafe na maka alƙawarin zuwa wurin bokan da kaina. Zan mishi bayanin komai, duk yadda aka yi zan zo har gidan na sanar maka."
Daga nan suka nufi Annur gadan-gadan, suka yi musayar kayan jikinsa, Sans ya miyar a nashi jikin, sannan suka kama hanyar tafiya.
Sun ci sa'a kuwa ba su haɗu da check point ko ɗaya ba har suka isa wurin mai askin. Bayan an gama suka karanta address ɗin su Annur a wani round about da aka maƙala hotonshi. Gidan babu wahalar ganewa sosai, hakan ya sa ba su wani ɓata lokaci ba suka isa.
A yanayin yadda Sans ya koma, tsaf za a iya cewa lallai Annur ne. Kominsu iri ɗaya. Askin kanshi irin na kan Annur ne. Dama kuma tafiyarsu da komai iri ɗaya ne. Ya ƙoƙarta miyar da kanshi tamkar wani galabaitacce, wanda ya tashi daga cutar hauka.
A ƙofar gida Bobby ya faka motar. Ya zagaya ya buɗe ma Sans gefenshi, sannan ya tallabo shi a hankali yake taku, har suka isa bakin gate.
Knocking ya yi har sau biyu, sannan mai gadi ya zo har da gudu-gudunshi yana faɗin,
"Yi haƙuri fa, na ɗan zaga ne."
Fuskarsa ta rikiɗe da mamaki lokaci guda, sadda ya haɗa ido da Sans. Idonshi a buɗe yake faɗin
"Annur! Kai ne? Ina ka shige ana ta nemanka? Alhaji da Hajiya sun damu sosai da rashinka. Amma kwa na ji daɗi da Allah ya sa ka dawo lafiya. Ku shigo daga ciki Mallam."
Bobby ya koma tamkar wani mutumin kirki. Mai gadin ya musu jagora har suka isa cikin gidan.
A falo suka tarar da Hajiya Suhaila sai famar kuka take. Islam ma na yin nata, Pharm IA sai famar rarrashinsu yake.
Sallama mai gadin ya yi, sannan Bobby ya biyo bayanshi har yanzu bai saki Sans ba.
Zabura Pharm IA ya yi a daidai sadda ya ɗago kanshi ya ga Sans. Ido a buɗe yake faɗin,
"Shi kenan ma, sai ku daina kuka ai. Ga Annur nan Allah ya taimake mu ya dawo, ko kwana ma bai yi ba, Allah ya dubi duminiyarmu."
Ya saki faffaɗan murmushi, yana ƙarisa isowa a gaban su Bobby. Kama hannun Sans ya yi, yana faɗin,
"Annur me ya sa ka tafi ka bar mu? Ka fa san cewa ba za mu iya rayuwa ba tare da kai ba. Mahaifiyarka ta shiga tashin hankali sosai, kalli ka ga, ƙanwarka ma kuka take tun daga sadda aka fahimci ba ka nan, ka bar gidan nan."
Zaunar da shi Sans ya yi, ya ce,
"Ku ɗaga hannunku ku gode wa Allah Alhaji. Domin kuwa a wani irin mugun daji na haɗu da wannan bawan Allah'n, a sadda motata ta dakatar da ni, sanadiyyar ƴar matsala da ta samu."
Momy ta iso gaban Sans, ta dafa cinyoyinshi, tana kuka mai haɗe da murmushi, ta ce,
"Na ji daɗi sosai da ka dawo gare mu Annur. Sannu ka ji?"
"Ina Amrah take?"
Ya buɗe bakinsa ya faɗa, duk da cewa bai san ko wacece ita ba, kawai dai ya fahimci cewa tana da matuƙar daraja a rayuwar wancan mahaukacin ne.
Hajiya Suhaila ta ce,
"Amrah ta rasu Annur, ka sani fa, sai dai idan mantawa ka yi."
Kuka Sans ya fasa mai razanarwa da ƙarfi, tamkar da gaske ya shiga damuwar. Yana faɗin,
"Me ya sa za ta tafi ta bar ni? Amrah na da matsayi mai girma sosai a zuciyata. Ina ji da ita fiye da duk tunanin mai tunani. Me ya sa za ta tafi ta bar ni? Me ya sa ta zaɓi barin duniya ta bar ni? Mutuwa ya za ki ma Annur haka? Da kin sani ki ɗauke ni ni ɗin ma, da zan fi samun sassauci a cikin zuciyata."
Bai san ko wacece Amrah a rayuwar Annur ba. Bai sani ba, shin ƙanwarsa, yayarsa ce, ko kuma budurwarsa ce? Kodai matarsa ce? Shi ya sa ya yi wannan maganar, ya kuma dakata daga nan.
Mamaki suke yi sadda Sans ya yi wannan maganar. A zukatansu suke tunani, kodai Annur ɗinsu ya warke daga haukan da yake yi ne? Mahaukaci ba zai taɓa