Showing 147001 words to 150000 words out of 201092 words

Chapter 50 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ta ba, ba kuma za ta gayyace ta ɗin ba. Ya roƙe ta kan ta taimaka, amma ta ƙiye masa. Ita kuwa tana gudun tonuwar asiri ne kawai, ko kaɗan ba za ta so Dr. Islam ta san da zancen auren ba, don kar ta zo ta nemi sanin mijin. Kuma ma ta san halin Hammad da surutu, da kanshi zai iya jan ta ya kai ta har ɗakinshi, inda Annur ɗin yake.


Gatsine ya yi haɗe da latsa kiranta, bugu biyu kuwa ta ɗauka, da sallama ƙunshe a bakinta.


Amsa sallamar ya yi da murmushi ya gaishe ta.


"Muhammad yarona ya kake?"


"Lafiya lau Aunty. Ya Abdul?"


"Abdul na lafiya Hammad. Ya Mama da Maryam?"


"Suna lafiya duka Aunty. Dama kiranki na yi na ba ki wani labari."


Murmushinta ta faɗaɗa, sannan ta ce,


"To ina saurarenka yarona."


Sai da ya lelleƙa ko'ina irin yadda magulmata ɗin nan suke yi. Kafin ya ce,


"Ko kin san kuwa an kusa yin auren Yaya Maryama?"


Da mamaki Dr. Islam ta ce,


"Aikuwa dai ban sani ba. Amma yaushe ne auren da Maryama ta gagara ta sanar min?"


"An kusa fa Aunty. Na ji an ce wai ranar Friday ne ɗaurin auren. Amma dai ranar Alhamis za a yi Get Together a gidan Kawunmu."


Mamaki sosai Dr. Islam ta yi.


"Muhammad kodai wasa kake min? Ta yaya Maryama za tai aure har ma a ce kwanaki huɗu kacal suka rage kuma ba ta sanar min ba?"


Ɗan taɓe bakinsa ya yi Hammad. Ya ce,


"Allah kuwa da gaske nake yi Aunty. Amma ki kira ta anjima sai ki tabbatar. Kar fa ki faɗa mata na kira ki."


Dariya ta yi sosai. A ranta tana mai jinjina wayo irin na Muhammad. Idan ya yi wani abu sai a ce ya zarce shekarunshi.


"Ba zan faɗa mata ba insha Allahu. Kai ma kuma sai ka kame bakinka to. Zan san yadda zan yi."


"Yauwa Aunty. To ki gaishe min da Abdul. Idan za ki zo bikin don Allah ki zo min da shi. Zan yi party ni ma ɗin ranar Alhamis."


"To na maka wannan alƙawarin, insha Allahu. Ai har ma da Momynmu za mu zo da yardar Allah. Sai anjima ko."


Ta katse kiran. Har zai koma ya miyar da wayar kuma sai ya tuna da ranar da ya kira Kawu Imrana ɗin nan fa ya manta bai goge ba. Don haka yanzu kam dole sai ya goge. Ya sakar ma kanshi murmushi, haɗe da yin delete na kiran.


Har ya miyar da wayar Maryama ba ta dawo ba. Sosai ya ji daɗi, koba komai zai ga Abdul ɗinshi, zai zo wurin partynshi.


*


Tun sadda ya koma gida yake jin zuciyarsa na masa zafi. Ya ma rasa me zai yi ya ji daɗi? Baki ɗaya duniyarsa ta juye masa. Babu ko kaɗan ɗin farin ciki a cikinta. Ga shi dai bai rasa komai na game da dukiya ba. Gadonshi da yake kwance a kai, babba ne sosai, mai ɗaukar aƙalla mutum uku ko huɗu. Sanyin AC ya gama garwaye ɗakin, ga wani irin ƙamshi da ke fita ta kowacce kusurwa. Bai rasa dukkanin kayan more rayuwa ba, amma kuma farin ciki ya masa ƙaura. Lallai ya yarda, cewa dukiya da kayan more rayuwa ba koyaushe ne suke zama dukkanin farin cikin mutum ba. A cikin ɗan taki kaɗan, komai ya juye masa. Kullum cikin ƙunci da baƙin ciki, tun daga mutuwar babban abokinsa. Sosai yake tunowa da iyayenshi, da kuma danginshi; na uwa da na uba. Ko ya suke yanzu? Ya dai tabbata cewa iyayensa basa raye. Amma kuma ya san ba lallai ba ne a ce duka har danginshi babu su ba. Dole za a samu wanda suke raye. Tunani yake a ransa, shi yanzu a haka rayuwarsa za ta ci gaba, ba tare da wani makusancinshi na tare da shi ba? Ya sani, ya san cewa babu abin da ya rasa a gidan da yake. Haka kuma ko sau ɗaya ba su taɓa yin wani abu wanda zai nunar da cewa sun gane cewa ba shi ne ɗansu ba. Amma kuma yana ji a ranshi, lallai duk daren daɗewa sai asirinsa ya tonu. Sai sun fahimci cewa ba shi ne asalin ɗansu ba.


Juyi ya sake yi, yana jin yadda ruwan hawaye ya wanke masa dukkanin fuskarsa. Me ya sa rayuwa za ta masa haka? Mafita yake nema daga wurin Allah, yana fatan Allah ya kawo masa ɗoki, ya fitar da shi daga wannan damuwar da yake cikinta. Duk yadda yake son cika alƙawarin da ya ɗaukar ma Farouk Sardauna dole hakan ba zai yiu ba. Zai haƙura, ba zai taɓa kai kanshi ga auren Maryama ba, gudun faruwar wani abun.


Har aka fara kiran assalatu ko kaɗan Sans bai runtsa ba. Ya ma gaji da kwanciyar, a ƙarshe ya tashi zaune, yana kuka sosai, wanda har muryar kukan ma ta disashe. Da na sani kawai yake daɗa yi, wanda ya zame masa tamkar abinci. Tun daga sadda Bobby ya rasu kullum cikin takaicin rayuwarsa yake. Munanan halin da suka aikata, har Bobby ɗin ya rasu a cikinsu.


Tashi ya yi jiki babu kuzari, ya nufi ban-ɗaki. Alwalla ya ɗauro sannan ya dawo, ya shimfiɗa dardumar sallarsa, ya fuskanci alƙibla, haɗe da kabbara sallah.


Ya daina wasa da salla, kwata-kwata. Sosai yake kasƙantar da kanshi ga mahaliccinshi, yana mai neman yafiyar Allah, tare da roƙawa abokinsa gafarar Allah.


***


*Da gaske Sans na ba ni tausayi, har cikin zuciyata. Idan na tuno da yadda ya yi rayuwarsa a baya, da kuma yadda ƴan ta'adda suka salwantar da rayuwar makusantanshi, sai in ji duk wata tsanarsa da nake tana wucewa. Akwai wasu daga cikin masu karatu, wanda suke cewa wai bai kamata Sans ya tuba ba, sai dai ƙarshensa ya yi mummuna. Ba zan faɗi komai a yanzu ba, don kar na ba ku satar amsa. Sai dai kuma ina so ku sani, komai na duniyar nan yana da sila. Idan Farouk Sardauna ya yi silar lalacewar Sans, to kuma ga shi mutuwar Farouk Sardauna ta yi silar shiryuwarshi. Abu ɗaya tal ya rage na rayuwarshi, wanda sannu a hankali duk zan warware muku. Da ni da ku duka, babu wanda ya fi ƙarfin faɗawa a irin halin da Sans ya faɗa, domin kuwa babu wanda ya fi ƙarfin ƙaddara. Addua dai ce takobinmu, ita za mu riƙa, muna fatar Allah ya tsarkake mana zukatanmu, mu kasance masu kyautata rayuwarmu, har sadda mutuwarmu za ta zo ta ɗauke mu.*


*Daga nan kuma sai ku taya ni wangale baki, na jeren da za a je gidan Marnoor. Abun fa da gaske ne, biki sai daɗa kusantowa yake. Abun ya zo, inji mai tsoron wanka.😁🤣*


*Me za ku ce game da wannan surutu da Hammad ya yi? Shin ya kyauta ko kuma bai kyauta ba? Akwai fa ƴan bayan Hammad, masu yin ƙani da shi, wanda na san kai tsaye za su ce ai Hammad ya musu daidai😀. Yaro mai surutu fa haka yake. Akwai sadda yake yin mai maana, kamar sadda ya kira kawu Imrana. Akwai kuma sadda yake yin mara maana, wanda shi ne ma ya fi rinjaya. Ga shi dai Hammad ya kwafsa, ya kwaɗawa Dr. Islam kira ya sanar mata auren Maryama. Ko ya abun zai kaya? Za ta zo ko ba za ta zo ba? Akwai fa cakwakiya.😊😅*


*Nagode ƙwarai masu bibiyar wannan labarin. Har ma wasu lokutan nakan rasa abun faɗe, tsabar faranta min rai da masoyana suke yi. Wasu groups ɗin da bana ciki ma, ina jin labarin yadda suke ƙaunar ANS. Akwai lokutan da ake min Copy and paste na yadda ake hirar ANS. Ban san da bakin da zan gode muku ba. Sai dai addua da fatar alkhairi. Allahu ya bar zumunci, ya saka muku da dukkanin alkhairanSa. I love y'all, fisabilillah.*


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/14, 5:33 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣3⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Washe gari tun da safe misalin ƙarfe tara na safe ƴan jere suka tafi domin aiwatar da aikinsu. Maryama kuma dama mukullin ɗaya motarsu a hannunta yake. Tare da Hammad suka tafi, bayan ta shiga sun gaisa da Annur, ta ba shi duk abin da ya dace na kalacinsa.


Kai tsaye gidan su Jiddah suka dosa. Daga nan suka wuce wurin Salon. Ba su wani tarar da layi ba. Mutum baiyu ne a gabansu. Hakan ya sa misalin biyu na rana an gama musu duka.


Daga nan suka wuce gidan su Saudat. Sun samu ta shirya su kawai take jira, da yake sai da Jiddah ta kira ta ce ta zama cikin shiri, sun kusa zuwa su ɗauke ta. Sai da suka yi sallah, har abinci Saudat ta zubo musu sannan suka bar gidan, suka nufi kakkai ma wanda ba su kai ma kati ba. Har kusan biyar na yamma sannan suka gama. Bayan sun kai Saudat gida sannaam suka wuce kasuwa domin yin siyayyar da ba su kammala yi ba, ta Get Together.


*


Tun sadda Kawu Imrana ya kira shi cewa ƴan jeren sun isa gidan, yake tunanin yadda zai yi da su ta ɓangaren abinci. Ga shi kuma ba ya son iyalinshi su san da zancen auren ko kaɗan, kamar yadda ya yi ma kawu Imrana alƙawari. Hakan ya sa kawai ya yanke hukuncin zuwa Restaurant ya musu odar abincin komai yawan shi.


Falon nata ya shigo bai same ta ba, hakan ya sa ya gyaɗa kanshi haɗe da hayewa sama. Ya rasa ko wace irin mace ce ita ɗin. Sam ba ta son mutane. Ko a falonta ba ta cika zama ba bare cikin masu aiki. A ranshi yake cewa dama haka Shuwa suke, ko kuwa dai ita ɗin ce haka?


A kan Sofa ya same ta riƙe da wayarta, ta miyar da dukkanin hankalinta ga wayar. Har ya ƙariso ya zauna a gabanta ba ta san ya iso ba, sai da ya yi gyaran murya sannan.


Da murmushi take kallonshi, bayan ta saka wayar a duhu.


Murmushin ya sakar mata shi ma, ya ce,


"Wane irin littafi kuma ake karantawa yau?"


Cike da soyayya take kallonshi, ta ce,


"Har ma ka san littafi nake karantawa kenan."


Hannunta ya kama ya riƙe, ya ce,


"Dole in sani ai, saboda aikinki ne. Ya sunanshi, faɗa min? Wata ƙila idan sunanshi ya min ma kin ga kawai sai ki karanta min."


Sai da ta ɗan yi far da ido kafin ta ce,


"Sunanshi WANDA YA DAKA RAWAR WANI...Labari ne a kan wata yarinya Farha, wacce ta shiga gararin rayuwa, ta dalilin ƙawa da kuma namiji. A ƙarshe ta faɗa harkar karuwanci, inda tun a duniya ta girbi abin da ta shuka. Marubuciya Maimuna Bashir Miemie Queen ce ta rubuta shi."


Gyaɗa kansa ya yi, ya ce,


"Allah sarki! Har na ji ta ba ni tausayi. Yo wannan rayuwar ta yanzu ka ɗauke ta da sauƙi ma ya ka ƙare bare kuma ka zafafa ta? Allah dai ya shige mana gaba, ya yi mana jagoranci a dukkanin lamurranmu."


"Ameen."


Ta faɗa tana kallonshi.


Yarinyar da ke kwance bisa gado tana barci ya kalla, ya bi a hankali ya cire mata takalmin ƙafarta, ya ce,


"Wani abu sai Shereefa. Wato in dai ba barci ta yi ba ba a taɓa raba ta da takalma."


"Kai ma dai ka faɗa. Ai ni kam ban san kalar Yesmeen ba. Sosai ta gado Yaya Salman. Aunty ta sha ba mu labarin yadda ya yi yana yaro. Ko kaɗan ba ya yarda a raba shi da takalma. To ga mai gadon shi nan ya samu ai."


Miƙewa ya yi tsaye, ya ce,


"Ni zan fita, wata ƙila daga Office akwai inda zan wuce. Ban ma dai yi niyyar zuwa Office ɗin ba gaskiya, saboda na tashi jikin ba daɗi. Wani dalili ne mai girma zai fidda ni."


Miƙewa ta yi ita ɗin ma, suka ci gaba da taku tare, har suka sauko daga bisa bene. A falo ta mishi sallama da fatar alkhairi, sannan ya fita, ita kuma ta nufi ɗakinta.


*


Wuraren ƙarfe shida na yamma ƴan jere suka koma. Fuskokinsu a sake, dangin Mama ne da kuma na Abba, da yake kansu a haɗe yake, akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu.


Da faraa Mama ta tarbe su, ta ce,


"Sannunku da dawowa. Har an gama kenan. Sannu, sannunku da aiki."


Amsa mata suka yi, wata babbar mace daga cikinsu, wacce ta kasance Yaya ce ga Mama, ta ce,


"Gaskiya ba laifi Maryama ta yi sa'ar dangin miji. Domin kuwa wani mutumi yadda ya rinƙa hidima da mu abun sai godiya. Akwai kirki sosai wallahi. Gaskiya ki ce da Alhaji Balarabe ya jaddada mana godiya a gare su, domin kuwa ba kowa ba ne zai iya yin wannan hidimar."


Mama baki a sake ta ce,


"Aikam zan faɗa masa insha Allahu."


Daga nan suka fara haramar tafiya. Da zummar wasu idan suka zo gobe sun zo kenan har sai bayan biki.


A gajiye Maryama ta dawo gida ita da Hammad. Sai da ta fara zuwa inda Annur ta ɗan jima kafin ta dawo ɗakinta, ta watsa ruwa sannan ta saka kayan barci, a daidai sadda ake kiran sallar magrib. Zumbuleliyar hijabinta ta zumbula, sannan ta kabbara sallah.


*


Tun da sassafe mai lalle ta iso. Ƙarfe goma na safe ne dama aka saka za a yi sa lalle. Daidai lokacin kuwa gidan ya fara ɗaukar harama. Ƴan mata duk sun zo domin gabatar da sa lalle. Wanda shi kanshi ɗin akwai wani ɗan guntun casu da za a yi bayan laasar, a lokacin an gama yi ma kowa lallensa, tunda ita amarya dama sai da dare za a mata, sadda duk aka warwatse. Jiddah da Saudat kuwa gidan suka dawo da zama daga yau, saboda za su fi jin daɗin hidimar, da kuma aiwatar da komai a kan lokaci.


Da yamma kuwa aka ƙawata gidan da simple decoration, kalar Pink and gold. Wurin ya yi kyau sosai, aka jera kujeru, da kuma gefe guda da aka ajje royal chair, wacce amarya za ta zauna a kai.


Ƴan RAZ NOVELLA da kansu suka ɗauko Ado Gwanja, wanda musamman saboda ranar yau zai zo ya nishaɗantar da su. Har Gwanja ya iso harabar wurin amarya da ƙawayenta ba su fito ba. Bai damu da hakan ba, kawai ya fara sakin kiɗa. Sautin na tashi tamkar an tsakuri ƴan Nagarta Fans Group ne. Ummu Aysher ba ta ko ƙarisa naɗin ɗankwalinta ba ta fito, gyale a hannunta tun daga bakin ƙofa take rawa, har ƙasa-ƙasa take yi. Mienerh ce a bayanta, sun haƙiƙance tsakaninsu da Allah rawa suke, har suka iso harabar da Gwanja ɗin yake. Aikam yana ganinsu ya canza salo, aka sako wakar A sha rawa rawa. Kafin ka ce kobo fili ya cike da ƴan mata, ƴan group group sai cashewa ake, har lokacin da Jiddah da Saudat suka fito da amarya. Aunty Maijiddah Musa ce biye da su a baya, sai famar sakin murmushi take, tana ɗan taka rawar dattako, irin ta manyan mutane.


Amarya ta sha gayunta, cikin dressing kalar golden.





Da haka dai Ado Gwanja ya nishaɗantar da su, ƙarfe shida da rabi na yamma aka gama. Cike da nishaɗi aka warwatse.


*


Da dare mai lalle ta hau zana ma amarya nata lallen, inda Maryama ta ce ita kam ba ta son mai yawa, ta fi son kaɗan irin wanda ake yayi yanzu.












Sai kusan sha ɗaya na dare sanann suka sallami mai lallen ta tafi.


*


Ranar alhamis da safe aka fara shirin yin walima, inda aka gayyaci Malama Zulaihat Rano da aminiyarta Khadija S Mohd suka gabatar da waazi mai ratsa zukata. Sosai suka jawo hankalin amarya a kan ladabi da biyayya ga mijinta.


Amarya ta sha kyau sosai, inda ta sha bakin dressing abunta.




















Sosai aka ci aka sha a wurin wa'azin. Ba wai amarya kaɗai ba, har ma da sauran mutane sai da suka girgiza da yadda malaman suka rinƙa tsoratar da amarya daga zaluntar mijinta. Suke hasasho mata rahama matuƙar ta kyautata ma mijinta. Sai sha biyu na rana sannan aka gama wa'azin, saboda da yamma kuma za a yi Get Together a gidan Kawu Imrana.


Wanka ta yi ta saka wata ƴar ƙaramar riga iya guiwa. Rijif! Ta faɗa bisa gado, tana faɗin,


"Kuma wai fisabilillahi anjima wani abun za a sake yi. Ni wallahi in da za ku bi ta tawa da an fasa. Na gaji sosai."


Harararta Jiddah da Saudat suka yi, Jiddah ta ɗika mata dukan wasa, ta ce,


"Lallai ma yarinyar nan kin raina mutane. Ai in Allah ya yarda Party an yi shi an gama. Gwara ma ki saka a ranki cewa babu fashi, da izinin Allah. Bari ma ki ga in kira matar nan mai make up, kar ta ɓata mana lokaci, shi ya sa na so kar ta tafi ɗazu amma ta nace wai da wuri za ta dawo."


Ta latsa kiran mai kwalliyar. Bugu biyu kuwa ta ɗauka, Jiddah ta ce,


"Dama ce miki zan yi don Allah ki taimaka mana ki zo da wuri. Wallahi ba ma so a yi dare ne. Get together ne fa har da iyaye duk za su je. So muke amarya ta shirya da wuri, in ya so duk wacce ba ta shirya ba sai a yi babu ita."


Mai make up ɗin ta ce,


"To insha Allahu da an yi sallar azahar zan zo. Kar ki ji komai."


"To shi kenan, sai kin zo."


Ta tsinke wayar tana faɗin


"Oya tashi ki yi alwallah, yadda idan lokacin sallah ya yi yi kawai za ki yi. Ni fa kin san ni da uzurta mutum, don ba na son ɓata lokaci a komai nawa."


Tashi ta yi Maryama, ta ce,


"To Aunty Masifa."


Ta nufi ban-ɗaki.


"Na dai ji koma me za ki ce da ni ki ce. Ni ma wankan zan yi yanzu. Bara na je na fara faɗa ma dattawan can, su taimaka su shirya da wuri su ma. Don na yi waya da Yaya Deedah, ya ce ƙarfe biyar daidai za su zo da motocin kwasar mutane."


Saudat da ta miƙe kan gado ta ce,


"Ai kin san su manyan mutane ba su cika ɓata lokaci da yawa ba. Matsalar dai dama daga ƙawaye ne. Amma da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login