Showing 162001 words to 165000 words out of 201092 words
Chapter 55 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
jiyo shessheƙar kukansa, ta gaggauta ɗago da kanta, ta ɗora idanuwanta a bisa kyakkyawar fuskarsa da ruwan hawaye ya gama wankewa.
Kallon sa take cike da mamaki. Me ya sa shi kuka? Ta tambayi kanta. Ganin yadda bil-haƙƙi yake kuka ne ya daɗa tayar mata da hankali. Kuka yake mai cike da tashin hankali, jikinsa na karkarwa, idanuwansa sun kaɗa sun yi jajur a cikin ɗan taƙi kaɗan. Ƙasa ya ƙura ma ido yana kallon wuri guda, hannunsa ɗaya dafe da kansa, ɗayan kuma ya ɗora a bisa cinyarsa, ya dunƙule shi.
Gyaɗa kanta ta hau yi, tare da ƙarfafa kukanta, tana faɗin,
"Ni ce? Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min. Ban san cewa abun zai maka zafi har haka ba. Ba zan so Allah ya rubuta min zunubi ta dalilin saɓa maka ba. Wajibi ne a gare ni na faranta maka, na ba ka duk wani farin-ciki kamar yadda na yi alƙawari."
Ta dakata daga nan, ta ci gaba da binsa da kallo. Ji ta yi cikin sanyin murya ya fara magana,
"Amrah nake so! Amrah ce kaɗai a cikin zuciyata. Amrah me ya sa za ki min haka? Me ya sa za ki tafi ki bar ni? Ina ƙaunarki Amrah. Ke ce rayuwata. A kullum da ƙaunarki nake kwana nake tashi. Soyayyarki ke ɗawainiya da duk wata gaɓa da ke cikin gangar jikina. Ki dawo gare ni Amrah. Ki zo ki tallafi rayuwata Amrah. Ki zo ki bayyanawa duniya cewa ke kaɗai nake so, kamar yadda ke ma ni kaɗai kike so..."
Kuka sosai yake yi, a hankali yana tuno wasu abubuwan, wanda dama yakan tuno su, sai dai wasu lokutan da zarar ya tuno su, sai kanshi ya hau sarawa, tare da manta komai da ya fara tunowar.
Sosai take mamakin Annur. Sau da dama yakan yi abubuwa irin na masu hankali. Yakan yi kalamai masu sanyaya zukatan ma'abota soyayya. Duk yadda yake gwada yana son ta, lokaci kaɗan zai birkice mata, tamkar ma bai taɓa ganin ta ba. Abun nan yana ci mata tuwo a akushi. Tana shiga tsantsar damuwa a duk sadda irin hakan ta faru. Sai dai kuma tun da ta san shi, daga lokacin da ta ɗauko shi daga Maraɗi ta dawo da shi gidansu, ba ta taɓa ganin shi ya yi irin wannan kukan ba. Tabbas kalaman ba baƙi ba ne a gare ta, to sai dai abin da ya tayar mata da hankali yadda yake kuka riris, jikinsa na ta famar karkarwa.
Hannunsa ta kama duka biyun, ta damƙe su a cikin nata. Sosai take jin nutsuwa na saukar mata. A duk sadda za ta taɓa shi, sai ta samun sauyin yanayi irin haka. Sai ta ji yadda ƙaunarsa ke ɗaukar ta tana kai ta can wata duniyar ta daban, duniyar da masoya ne zallah a cikin ta.
Ji ta yi hannunsa zafi rau, saɓanin yadda ta taɓa su ɗazu sadda tana kwance a cinyarsa. Cikin damuwa ta ce,
"Ka gani ko? Ga shi nan wannan kukan da kake ya sakar maka zazzaɓi. Ka ji yadda jikinka ya yi zafi sosai Yah Noor. Don Allah ka daina kukan nan. Wallahi ba zan sake tayar maka da irin wannan maganar ba. Na maka alƙawari."
Bai daina kukan ba, sai dai ya rage ƴarfinsa. A hankali ta isar da gangar jikinta gare shi, ta haɗa jikinsu, tana jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya. Hannuwanta ta zira ta rungumi bayanshi, ta ɗora fuskarta a bisa kafaɗarsa. Ji ta yi nutsuwa na saukar mata, kamar yadda shi ɗin ma a nashi ɓangaren hakan ne. Shiru ya yi da kukan da yake yi, bugun zuciyarsa na daidaita, yayin da yake jin duniyarsa ta damuwa na rikiɗewa izuwa ta farin-ciki.
Jin ya dakata da kukan ya sa cikin saukar da murya ta ce,
"Ka san yadda zuciyata take ƙuntata a duk lokacin da zan ga ɗigar hawayenka ɗaya a bisa kumatunka? Ka san irin halin da nake shiga a duk sadda kake cikin halin ƙunci? Sosai nake shiga tararrabi a duk sadda zan gan ka takure alamun rashin walwala. Ka taimaka ka daina, matuƙar ba so kake a zo a kwashi gawata daga gidan nan ba."
Saukar ajiyar zuciyarsa kawai take ji. Tana jin yadda ya langaɓar da kansa a tata kafaɗar, ya sadaukar da kaf gangar jikinsa gare ta. Sun jima a haka, har sai da dukkaninsu suka samu wadatacciyar nutsuwa, kafin ta raba jikinsu da juna, ta ɗora idanuwanta a kan rinannun nashi idanuwan, tana bin sa da kallo.
Murmushi ta ƙirƙiro kafin a hankali ta ce,
"Ya isa to ai, komai ya wuce. Bari in tashi in kawo maka abinci."
Kanshi ya ɗaga mata.
"To ai ban ga ka yi murnushi ba."
Muenushin ya saki wanda har sai da hakoransa suka bayyana. Sosai ta ji dadi, wani sanyi ta ji ya dira a cikin zuciyarta. Kai tsaye ta nufin kitchen domin ta kawo masa abincin.
Vegetable noodle ce ta dafa, kasantuwar ta dawo exam ne a ƙurarren lokaci, saboda yau suka fara kuma da guda biyu suka fara. A plate ɗaya ta zubo musu, ta duba pepper soup ɗin da ta ɗora a wuta saura ƙiris ruwan ciki ya ƙare. Da sauri ta gaggauta kashe gas ɗin, sannan ta zuba ruwa madaidaici ta motsa, ta kuma kunna gas ɗin amma ta rage ƙarfin wutar.
Fork guda ɗaya ta saka a plate ɗin, sai kuma ta ɗora spoon ɗaya, ta nufi fitowa. A gabanshi ta ajje, sannan ta ce,
"Bari in kawo mana drink."
Ta koma ta ɗauko kwalbar blue cocktail guda da cups guda biyu, ta fito.
A baki ta ringa ba shi abinci a hankali yana ci. Sai ya ringa kallon ta yana murmushi, tamkar ba shi ne ya gama rusar kuka yanzu ba.
Da haka har suka ƙoshi, ta zuzzuba drink ɗin a cup, da kanshi ya kai baki ya sha nashi, sai da ya shanye duka sannan ya ajje cup ɗin. Ita ma ta sha. Kwashe kayan ta yi duka, kafin ta dawo kusa da shi, ta gyaggyara wurin ta feshe da tangerine freshner. Bayan ta gama duka ta jawo handout ɗinta da take dubawa tun sadda take kwance a cinyarsa, ta hau dudduba kaɗan-kaɗan, shi kuma ta kunna masa kallo, tashar Zee World.
***
Kakkausan murmushi ta sakar masa a lokacin da ta same shi a ɗakin. Da nashi murmushin ya tarbe ta, cikin idanuwansa nata idon suke, har sadda ta iso gare shi.
"Har bakin sun tahi?"
Ya tambaye ta, bayan ya haɗa jikinsa da nata.
"Uhm sun tahi. Sun ce ma in gaishe ka."
Ta ƙoƙarta ɓamɓare jikinta da nashi.
"Mi halan rowa za ki yi mini?"
Gyaɗa kanta ta yi ta murmusa.
"Lokacin sallah dai yak kusan yi."
Ɗan taɓe bakinsa ya yi, ya ce,
"Hakanan hwa. Bari in nuhi masallaci to."
Ya miƙe haɗe da ɗaukar hularsa daga bakin gado ya saka.
"A yi min addu'a."
Hannunsa na dama ta kama ta saka a cikin nashi, ta ce,
"Allah ya sa a dawo lahiya. A yi mana addua."
"Insha Allahu. Amma wace iri kika son na yi miki?"
Sai da ta ɗan yi shiru alamar tunani, kafin ta ce,
"Zaman lahiya da zuri'a mai albarka."
"To na yi alƙawarin zan yi. Amma hwa ni ma ina da buƙatar wani abu."
"Mi halan?"
Ta tambaye shi cikin yatsinar fuska.
"Kawo kunnenki ki jiya."
Ta kanga masa kunnen nata. Magana ya mata ƙasa-ƙasa, wadda duk iya ƙwa-ƙwar mutum ba zai taɓa jin abin da ya faɗa mata ba. Da alama dai zance ne na ma'aurata. Murmushi kawai ta saki haɗe da gyaɗa masa kanta, ta ce,
"To na jiya. A dawo lahiya."
Ya fice daga ɗakin yana dariya, haka ita ɗin ma dariyar take.
Kitchen ta nufa, farar shinkafa ce take dafawa, koda ta duba har ta dahu, ruwa kaɗan ne kawai bai tsane ba. Ta duba miyar ita ma ta dahu. Ta sauke sannan ta kashe reshore ɗin. A flask ta juye miyar sanann ta bar ta buɗe don ta ɗan sha iska. Kafin nan har ruwan shinkafar ya tsane, ta sauke shi ma ta kashe ƴar bouncing burner ɗin, ta kwashe shinkafar a food flask babbar ta miyar.
Kafin Mahmouda ya dawo daga masallaci Fiddou ta gama shirya komai ta kai falo bisa kafet ta ajje. Dama ta yi wankanta, kaya kawai ta sauya, daga atamfa zuwa wata doguwar rigat roba, wadda ta kame jikinta. Kanta babu ɗankwali, sai yalwataccen gashinta da ta faka ya zuba har bisa gadon bayanta. Tana fitowa ta same shi ya dawo yana jiran ta. Da sauri ta ƙarisa gabansa tana masa sannu da zuwa.
"Madem ke yi kyau sosai hwa. Irin wanann kwalliya ai sai ki saka na kasa cin abinci."
Harararsa a wasa ta yi, ta ce,
"Aikam ba zan so mijina ya zauna da yunwa ba. Saboda haka bari in hanzarta zuwa in cire kayan in sako wanda ba za su hana maka cin abinci ba."
Ta nufi barin jikinsa. Jawo ta ya yi da hanzari, ta faɗo bisa jikinsa.
"Wa ya hwaɗi miki irin haka nake nuhi? Ai wannan kaya irinsu ne nake so ki rinƙa saka min duk sadda nake gida."
"To na ji. Ga abinci nan."
Ta ƙarisa bisa kafet ɗin, shi ma ya iso kusa da ita ya zauna. Serving ɗinsu ta yi. Ciyar da junansu suka hau yi cike da soyayya da ƙaunar juna, sai da suka ji su sun yi jim sannan ta kwashe kayan haɗe da dawowa.
"To kyan alƙawari cikawa. Na yi miki addua don haka ke ma sai ki cika naki alƙawarin."
Maficin hannunta ta duke sa da shi, ta ce,
"Halan dai ba ka gajiya?"
"Har abada! In dai da ke ne."
Miƙewa suka yi suka nufi bedroom maƙale da junansu.
***
Cike da shauƙin ƙauna take waya, tana yi tana ɗan lumshe idanuwanta, tana sakin wani tausassan murmushi. Tsabar jin daɗin wayar da take ya sa ta ringa tsigar stones ɗin lace ɗinta da aka ƙawata shi da su. Ita kanta ba ta san tana yi ba, har sai daga baya ta ankare. Cikin mamaki ta ce,
"D me ka san me ka ja min kuwa?"
"A'a J me sai kin faɗa."
"Uhm. In faɗa maka kaf stones ɗin da aka ma kayan jikina ado da su na bi na cire du, duk ban san na yi ba sai yanzu na ankare."
Dariya sosai ya yi mai sauti. Ya ce,
"Ah to komai ya yi daidai. Hakan ya tabbatar min da cewa kina jin daɗin wayar da muke yi ɗin."
"Uhm, to ni dai sai ka biya ni, tunda dai kai ne silah."
Cikin shagwaɓa ta yi maganar, har can cikin kunnuwansa ya ji dirar sautin nata.
Ya ɗan lumshe idanuwansa, cike da bege ya ce,
"J me kin cika rigima. Na ji to zan biya ki. Just count, in the next 2 or 3 months zan ninka miki wannan ɗin ma."
Tamkar tana a gabanshi haka ta harare shi, ta ɗora hannuwanta a daidai saitin zuciyarta, ji take yadda rijiyar ƙauna ke gudanya a cikin zuciyar tata, tamkar ta sa hannu ta yakito ta, ta gan ta da ido, ta yadda za ta ƙara azama wurin ƙaunarsa.
"D me ka san me?"
"Sai kin faɗa dai tukuna zan sani."
"Jiya bayan ka tafi Abbana ya kira ni. A gaban Mami ya ce wai ya ji daɗi sosai ta yadda ya gan ka mai ladabi da girmama na gaba da kai. Ya ce wai ya tabbatar ba zai yi asarar aura maka ni ba."
"J me am so much happy. Ashe har haka nake da daraja a wurin Abbah?"
"Ehh mana. Amma don Allah D me kar ka watsan ƙasa a ido. Kamar yadda kaken nan a yanzu, ina so ka ƙara azama wurin darajta iyayena. Sosai za ka ƙara siye zuciyar Jiddah..."
Bai bari ta ƙarisa ba da murmushi ya ce,
"Na riga da na gama saye zuciyar Jiddah. Kina nufin akwai sauran wata tsoka a cikin zuciyarki wacce ƙauna ta ba ta gama mamaye ta ba?"
"Babu."
Ta faɗa a hankali.
"I know, Jiddah. I've trust on you. Sosai na yarda da ƙaunar da kike min. Haƙiƙa ni ɗin na zama mai sa'ar rayuwa, da ya kasance cikin kwanaki ƙalilan na gama siye zuciyar matata Jiddah. Ina fatar ɗorewar wannan soyayya tamu, har jikokinmu."
"Ni ma ina fatar hakan Yayana. Abu ɗaya ne kacal ya rage mana a yanzu kam."
"Mene shi?"
Ya gaggauta tambayarta.
"Wannan zazzafin kishin naka nake so ka rage shi D me. Na sani cewa ba abu ba ne mai sauƙi, domin kuwa shi kishi halitta ne daga Allah. Sannan kuma sai kana son abu ne har kake yin kishinsa. Amma a hakan nake so ka daure, ka rinƙa yaƙar zuciyarka, ka tausashe ta a duk sadda ta ƙoƙarta riya maka wani abu. Wani abun har da shaiɗan, zai yi yunƙurin ganin ya yaƙi zuciyarka, har ya haddasa fitina a tsakanin masoya. Don haka sai ka ba shi kunya. Duk lokacin da ya so riya maka wani abu, ka gaggauta korarsa, insha Allahu komai zai daidaita."
Ajiyar zuciya ya sauke Deedah, ya ce,
"Maganarki gaskiya ce Jiddah. Insha Allahu zan yi ƙoƙarin ganin komai ya tafi yadda ya kamata. Duk da cewa a yanzun ma na rage, kuma ina ma kan ragewa. Da yardar Allah komai zai zamto kamar ba a yi ba. Za ki same ni mutum mai kishi amma saisa-saisa."
"Yauwa sweetheart. Am so glad hearing that. I really really love you my angel."
"I love you too habibty. Ki samu ki kwanta ko?"
"Yanzu kuwa D me."
"Oya tell me something nice."
"You are my husband, by Allah's grace."
"Thanks and stay cool dear."
Ya kashe wayar.
Bayan ta janye wayar daga kunnenta ta manna mata kiss. A ranta tana jinjina yadda Deedah ya iya saye zuciyar mace. Sosai ya san hanyoyi da salo-salo na soyayya. Tana ji a ranta yanzu ta fara soyayya. Domin kuwa tarayyarta da Tahir ba wani abun arziƙi ne ta tsinta a ciki ba. Duk da cewa tana son Tahir sosai, amma ita kanta ta san akwai matsala tsakaninta da shi. Saboda sam Tahir bai da caring, bai damu da ya kula da ita ba. A rana so ɗaya tal suke waya, shi ma kuma sai idan zai kwanta ne zai kira ta, cewa zai kwanta gobe akwai aiki. Idan kuwa cikin weekend ne, tana samu har da rana su yi waya, amma da zarar sun fara za ta ji muryar ƙannenshi cewa ya zo ana kiranshi. Shi ne babba a gidansu hakan ya sa duk wasu responsibilies suka haye masa, tunda mahaifinsa ba wani mazauni ba ne.
Dafe zuciyarta ta yi tunowar da ta yi da Tahir. Sai kuma ta ji tamkar ta famo tabon raunin da ya mata na ƙaunarsa ne a cikin zuciyarta. Tana cikin haka ta ji ƙarar shigowar text message. Ta ɗauka ta duba. Deedah ne ya turo mata text mai matuƙar daɗi da sanyaya zukatan ma'abota soyayya. Murmushi ta saki a sadda take karantawar, take ta manta da wani tunanin Tahir da take yi.
*
Idanuwansa na bisa fuskar likitan, tun daga sadda ya dawo Office ɗinsa ya nemi ganawa da shi. Ɗago kansa ya yi likitan, cikin sanyin murya haɗe da girmamawa, ya fara yi wa Dady bayani.
"Akwai matsalar da yaron yake a cikin ta ne?"
Shiru Dady ya yi yana nazari, kafin ya ce,
"A iya sani na dai babu."
"Ɗan ƙara tunawa dai."
Shiru ya yi na tsayin lokaci, kusan minti biyar da ɗoriyar seconds, sannan ya ce,
"To. Ya dai yi rashin babban abokinsa, ko in ce amininsa a kwanaki kaɗan da suka gabata. To wannan mutuwar sosai ta firgiza shi, ya kuma rasa sukuninsa. Tabbas, sai ma yanzu na tuna."
Ɗan taunar leɓonsa ya yi likitan. Ya ce,
"Kuma kana ganin wannan dalilin har zai iya zama silar da zai yi yunƙurin kashe kanshi?"
Cikin kiɗima Dady ya miƙe tsaye. Idanuwansa a buɗe yake faɗin,
"Dr. What are you saying? Kana nufin Annur ya yi attempting kashe kansa ne?"
Kai kawai likitan ya ɗaga masa.
"Calm down Alhaji. Koma ka zauna please."
Komawar kuwa ya yi ya zauna, har yanzu bai daina mamaki ba. Bai ga dalilin da zai sa Annur ɗinsa ya yi yunƙurin kashe kansa ba. Bai rasa gata ba, haka kuma ba iyayensa ba ne suka mutu. Shin mutuwar Farouk Sardauna kawai za ta iya saka Annur yunƙurin barin duniyarsa?
"A yadda result na hoton cikinsa ya nunar, wani abu mai kaifi ko kuma tsini ya shiga a cikin ne, wanda har ya tsinka wasu daga cikin kayan cikinsa. Tunda nake a rayuurata ban taɓa ganin wanda hakan ta faru da shi kuma ya ci gaba da rayuwarsa ba. Da zarar wasu daga cikin kayan ciki an ƙilla su, to a take mutum zai bar duniyarsa. Amma sai ga shi shi Allah ya iyakantar da abun, ba tare da ya mutu ba.
A gaskiya ba zan ɓoye maka komai ba, duk wani taimako da zan iya yi na yi shi, na ba shi taimakon gaggawa. Abin da ya dace in dai kuna da hali, to kawai ku fitar da shi ƙasar waje, hakan zai fiye muku sauƙi.
Sannan kuma, a duk sadda yaron ya farfaɗo, don Allah ku lallaɓa shi, ku binciki damuwar da yake a cikinta, cikin ruwan sanyi. Kar ku masa da zafi, a halin da yake ciki na tabbata zai buƙaci a taushi zuciyarsa. Saboda duk wanda za ku ga ya yi attempting kisan kansa, lallai ba ƙaramar damuwa ba ce yake a cikinta."
Ya dakata daga nan yana kallon Dady. Ƙwalla ya ga Dadyn na matsowa daga idanuwansa. Cikin murya mai nuna damuwa ya ce,
"Annur why? Why did you choose to kill yourself? Me ya yi zafi haka? Wannan wace irin damuwa ce kake cikinta, wacce ta gagara ka fito fili ka faɗa ma iyayenka ita?"
Ya sake share guntuwar ƙwallarsa.
"Ka kwantar da hankalinka Alhaji. Ai komai ma ya zo da sauƙi, tunda dai an samu ya farfaɗo. Abin da ya sa na faɗa maka ya kamata a fitar da shi waje, saboda su ɗin akwai na'urorin da suke amfani da su ga irin wannan matsalolin da mu ba mu da su gaskiya. Idan ma kuma akwai, to za a ɓata lokaci ne sosai, har ciwon nashi ya tsananta."
"Babu komai Dr. Thank you very much. Insha Allahu za a fitar da shi, gobe idan Allah ya kai mu."
"To Alhaji. Zan ba ka wani kati, in da hali ku kai shi India, ina da wani aboki a can, ya san aikin sosai, tunda ɓangaren neurology ya yi karatunsa. Insha Allahu zai ba ku duk wani taimako da ya kamata."
Dady ya miƙa ma Dr. Hannu, ya ce,
"Thank you once again Dr. I really appreciated. Gobe idan na kammala