Showing 63001 words to 66000 words out of 201092 words

Chapter 22 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

tabbatar da cikin tashin hankalin da take.


"Ahm...uhm dama...uhm, I just, I just need her by my side. I love Maryama with all my heart. I want her to be my partner, abokiyar rayuwata ta har abada."


Duk da faɗin hakan da ya yi bai sa gaban Jiddah ya daina faɗuwa ba. Ta san Annur, ta san waye shi. Ta san cewa zai iya aikata komai domin farin cikinsa, haka Bobby ma. Tana gudun su cutar da Maryama. Sai yanzu take tunani lallai sun tafka babban kuskuren fara wannan plan ɗin. A ganinta shi ke nan komai ya lalace.


"Uhm, Jiddah kina ji na? Please ko lambar Maman Maryama zaki taimaka ki turo min? I mean her mother's phone number. I really want to talk to Maryama."


"Are you out of your sense? A kan mene zan baka lambar mahaifiyarta? Idan ma ka sha wata banzar ƙwayarka ne da take faɗa maka wannan banza banzar to ka gaggauta neman gishiri ka sha ko zata fice. Dan wannan gurgun tunani ne kake, wanda ba zai taɓa yiuwa ba."


Sosai muryar Annur ke rawa, ya ce,


"Please help me Jiddah! Ba zan iya bacci ba tare da na ji muryan Maryama ba. And..."


Ya dakata daga nan, yana ƙoƙain haɗiye damuwarsa, tunanin yanda suka yi da bokansa ne ya faɗo masa a rai.


*
"Kana min wasa da hankali sosai Annur. Abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Shin ya muka yi da ku ɗazu?"


Cike da rauni ya kalli bokan, yana son yin magana amma tsoron furta komai yake.


"Kamar yanda na faɗa maku ɗazu, ku tabbatar kun shagaltar da ita matuƙar kuna so aiki ya yi tasiri a kanta."


Sai a sannan ya iya ɗaga laɓɓansa, cike da rauni ya ce,


"Boka Gagarabadau, abin da nake son aikatawa ke nan. Sai dai kuma ina buƙatar taimakonka. Dole sai ka saka hannu a wannan lamarin ko zai iya kasantuwa."


"Babu wannan maganar Annur. Ka tashi ka tafi kawai, bani da abin da zan iya yi maka."


Har ya miƙe kuma ya dawo ya zauna. Ya fuskanci bokan da jajayen idanuwansa da suke neman kawo ruwa, ya ce


"Zan yi Ya bokana! Na maka alƙawarin duk yanda zan yi yau sai na yi domin gyaruwar wannan aikin. Yau nake son aikata komai, kai ma ka shirya yin aiki a kanta a cikin daren yau. Ina baka tabbacin komai zai koma daidai, zan fitar da ƙaunarta daga zuciyata, a ƙarshe a samu gyara min wancan aikin na farko."


Murmusawa baƙin tsohon ya yi sosai, har sai da haƙoransa da suke cike da baƙin gashi suka bayyana. Ya ce,


"Bana jin ka Annur. Na tabbata zaka yi. Zan kashe duk wani aiki nawa na dare, zan tare ga aikin wannan yarinyar, a cikin daren nan za a gama komai."


Cike da yaƙini Annur ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya dire a gaban boka. Jinjina masa kai bokan ya yi, kuɗin suka ɓace daga gabanshi, sannan ya ma Annur umurni da ya tashi ya tafi.


*
"Na roƙe ki Jiddah, ki taimaka min. Na miki alƙawari ba zan cutar da ita ba."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke jiddah, tunani take shin ta bashi lambar Mama ko kuwa dai kar ta bashi? Babbar matsalar ita ce kar Mama ta gano halin da suke ciki, ta san komai zai iya faruwa, tun da ba gaskiya Maryama ta faɗa mata ba.


"Ka yi haƙuri Ya Noor. Na tabbata gobe idan Maryama ta ga missed calls ɗinka zata kira ka."


Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake furta komai ba, yana jin yanda zuciyarsa ke tafarfasa, take hararo masa bokansa da yake can sake da baki zai masa aiki yau.


Latsa kiran Bobby ya yi, cikin rauni ya ce,


"Guy akwai damuwa..."


Ya kwashe komai ya sanar masa, ya ƙara da faɗin,


"What are we going to do now?"


Shi kanshi Bobby ɗin damuwa ce fal a zuciyarsa. Ya ma rasa ta inda zasu ɓullowa lamarin, ya sani, ya san sarai boka Gagarabadau baya son wasa, ko kaɗan baya so ana kawo wargi a harkarsa.


"Ka yi shiru Farouk. Please ka faɗa min, ya zan yi?"


"Calm down abokina. Be a man, ban sanka da rauni irin wannan ba. Yanzu abin da zai faru, kawai ka haƙura da wannan batun na yau. Gobe da sassafe sai ka zo mu tafi wurinsa, na tabbatar zai saurare mu, zai kuma yi maka uzuri."


Sai a sannan Annur ya sauke ajiyar zuciya, yana jin sassauci a cikin zuciyarsa.


"Kana ganin boka zai saurare mu gobe kuwa?"


Ya ɗaga laɓɓansa ya furta a tsanake, yana shanye damuwarsa.


"Na tabbatar ransa zai ɓaci, saboda yanda kuka yi cewa zai kashe ko wane aiki yau ya maka wannan aikin. Amma ba komai, zai saurare mu. Kawai dai ka zo da wuri mu tafi."


"To zan zo, zan zo da sassafe Farouk. Good night."


Sallama suka yi da juna sannan suka tsinke wayoyin nasu, ko wane da tunanin da yake saƙawa a zuciyarsa.


Sai ma yanzu Bobby ya tuna cewa ɗazu sun yi da Maryama zai kira ta, sam! Ya shafa'a sai yanzu. Latsa kiran Maryama ya yi amma shiru bata ɗauka ba. Ya sake kira nan ma shiru, hakan ya sa ya mata text cewa ta yi haƙuri bai samu kiranta ba, uzururruka ne suka sha kansa.


Ƙaramar ƙwalwa irin ta mashaya, sam! Ya kasa gane cewa Maryama ita ce suke neman ɗana wa tarko. Bai yi tunanin ga suna ya zo ɗaya ba, sannan kuma Annur ya shaida masa yana ta kiranta bata ɗauka ba, shi ma kuma ya kira bata ɗauka ba.


Ajiye wayar ya yi kusa da shi, yana tsananin tausayawa abokinsa. Matuƙar wannan ƙullin ya warware, shi kanshi Bobby ɗin yana cikin matsala.


Maryama kuwa ƙarfe sha biyu daidai alarm ɗinta ya buga. Tashi ta yi da miƙa ta miƙe zaune. Tana tunanin irin baccin da ta yi, kamar matatta, tun da ta kwanta bata farka ba sai yanzu.


Tsaye ta miƙe kai tsaye ta nufi inda wayarta ke jikin chaji. Da ƙyar take buɗe idanuwan nata, har ta tarar da tarin missed calls ɗin da ke jere a allon wayar.


"Ya Rabb!"


Ta faɗa haɗe da dafe kai.


"Ashe a silent na bar wayar nan, gashi na manta da Annur zai kira ni. Subhanallahi!"


Ta matuƙar jin haushin hakan, damuwarta ma ɗaya plan ɗinsu da yake neman lalacewa.


Kamar ta latsa kiransa, saboda kiran da ya mata ya fi ƙarfin talatin. Ga kuma na Jiddah, wanda aƙalla zasu kai uku ko huɗu. Sai na Bobby guda biyu, na wata lamba guda biyu.


Rasa wanda zata fara kira ta yi, hakan ya sa kawai ta fasa, ta cire daga silent, sannan ta nufi ban ɗaki domin ɗauro alwala.


Tun tana ciki ta fara jiyo kira a wayar, bata fito ba har sai da ta kammala alwalar duka, a lokacin wayar har ta tsinke an sake kira.


Lambar Annur da ta yi saving da sunansa ta gani, hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya, haɗe da ɗaukar wayar.


"Assalamu alaikum."


Ta faɗa cikin sassanyar muryarta, wacce ke nunar da ta tashi daga barci.


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, bai san sanda ya saki murmushi ba, yana mai matuƙar jin daɗin muryar tata. Tun bayan wayarsa da Bobby ya kasa barci, maimaita kiran Maryama kawai yake amma bai dace ba, sai yanzu da ya riga ya cire tsammani.


"Maryama kina lafiya? I've been calling your number baki ɗauka, I hope all is well."


"Zan iya sanin da wanda nake magana?"


Ta furta cikin salon jan hankalinsa, dan ta tabbatar ba zai ɓoye mata ba, dole zai mata bayanin kansa.


"Ye..yes, why not? Am Annur Iqra Al-Hussein. Na kira ki ne, akwai maganar da nake so mu yi."


Gyara zamanta ta yi bayan ta zare wayar daga chaji, ba tare da tunanin komai ba ta ci gaba da saurarensa.


"Ina fatan zaki bani aron lokacinki, ki saurari kalamaina, ki ji abin da nake tafe da shi. Amma fa sai kin daure, saboda abin da yawa, zai iya ɗaukarmu tsawon lokaci."


"Ina saurarenka."


Ta faɗa a hankali, ta ma cire tunanin karatun da zata yi, saboda a ganinta, wannan wata dama ce ta zo mata, wacce ta jima tana tsumayenta.


"Maryama! Kin tashi kuwa?"


Ta jiyo muryar Mamanta, tana tinkarowa ɗakinta.


***


A inda take zaune ta haɗa kai da guiwa ta fara jiyo takun mutane. Daga kanta ta yi ta kalle su, Mahmouda ne da ƙannen nan nasa, suna mata kallon tuhuma, suna son sanin dalilin kukan da take yi.


"Giɗe ba kuka zaki yi ba. Allah ne Ya ɗora mai wanga laluri, kuma shi zai yaye mai."


Ɗaya daga cikinsu ta faɗa, tana jin tausayin Fiddou.


Ta buɗe bakinta zata mata magana ke nan likita da nurse suka shigo, hannun nurse ɗin riƙe da takarda.


"Giɗe ga reffer letter ɗinai nan. Ku ɗaukai ku kai asibitin gwamnati. Na kira abokina na sanar mai yanzu, ku tahi dai, Allah Ya bashi lahiya."


Mahmouda ne ya karɓi takardar, yana son sanin dalilin yi ma Modu reffer ɗin.


"Gata nan zata yi ma bayanin komai. Kai ina ganin hwa mun gama da kai, ina ƴan sandan nan suke? Su taho ka yi signing, dan ya warke da duk abin da ka damunshi wanda ya danganci banka tai da ka yi, sai ƴan raunukan da ba za a rasa ba.."


Sauke ajiyar zuciya ya yi Mahmouda. Yana jin zuciyarsa ta samu sassauci, yanzu kam zai zauna zaman ta'aziyyyar mahaifiyarsa ba tare da tunanin komai ba. Sai dai kuma me? Yana tsananin tausayin Modu, gashi kuma bai san abin da yake damunsa ba.


"Mun gode ƙwarai Dr. Ka taimaka muna ƙwarai da gaske, Allah Shi saka ma da alheri."


Fiddou ta faɗa tana ƙoƙarin shanye hawayenta.


"Babu komai ai. Allah Ya bashi lahiya, Allah Ya taƙaita abin."


Amin suka amsa da shi su duka da ke wurin, kafin likitan ya juya, Mahmouda ya bi bayansa.


Kun ga ɗan ƙaramin haukan da Annur ya yi ko? wai duk gudun kar ƙullinsa ya warware. Ya manta cewa dare dubu na ɓarawo, rana guda tal ta mai kaya. Duk irin mugun abun da mutum yake aikatawa, dole akwai ranar tonuwar asirinsa, akwai ranar dana sani, akwai lokacin da zai fallasa, kowa ma ya san da halinsa


gaisuwa ta musamman gare ki Queen miemie.


Jinjina da fatan alkhairi ga ƴan group ɗin Nagarta writers fans. Ina yinku irin totally ɗin nan, fi sabilillah.


Kamar yanda na faɗa maku, ba kullum ne zaku ringa ji na ba, sai dai zan yi iya ƙoƙarina, dan ganin kuna samu akai akai.


Thanks all.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:49 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣5⃣




Cikin tsarguwa ta gaggauta janye wayar daga kunnuwanta, ba tare da ta kashe ba. Ƙoƙarin amsa kiran Maman tata take, sai dai tana gudun bincike irin na Mama, babu wuya za ta gano cikin halin da take.


"Maryama kin tashi kuwa?"


Ta sake jin muryar Mama, saboda bata riga ta kunna hasken ɗakin ba dama.


"Ehh, ehh na tashi. Har alwala ma na yi Mama."


"Ok masha Allah! A yi sallah kafin a fara karatun ko? Za ki fi jin daɗinsa sosai."


"To." kawai ta faɗa haɗe da latsa switch na wayar, ta kashe ta baki ɗaya.


Miƙewa ta yi tana jin kamar ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukar gangar jikinta ba. Ko kaɗan ba ta yi tsammanin zuwan Mamanta a daidai wannan lokacin ba.


Dafe kansa ya yi a daidai sanda yake jin kalaman Mama. Gabansa ne ya tsananta duka, yana tunanin yanda zai yi kuma.


Sake kiranta ya yi amma ya ji a kashe, bai san sanda zazzafan hawaye ya fito masa ba, duk iya jarumtar dannesan da yake yi.


"Shi kenan na san by now boka ya yi zuciya. Ya zan yi ne ni Annur? Am totally confused, I've no idea on what to do, help me out ya Allah!"


Sallarta ta fara bisa kafet, tana mai ƙoƙarin cire rauni daga zuciyarta. Bayan ta gama ta hau karatu sosai, tana jin yanda natsuwa ke daɗa sauka ga duk ilahirin jiki da jininta. Lallai karatun Al'Qur'ani wani abu ne, wanda babu tamkarshi, wanda ke dakar da zuciyar mutum, yake saka natsuwa sosai a cikin zuciya.


Ta jima tana karatun kafin ta sadaƙe, ta miƙe ta kawo raka'a biyu, a lokacin ƙarfe uku na dare kenan. Bayan ta gama ta yi addu'a sosai, ta ma iyayenta, sannan kuma ta kai kukanta wurin Allah, a kan wannan aiki da take son yi. Tana son Allah Ya taimaka mata, ya kawo mata mafita, kar wani abu ya faru da su har su gama.


Kwanciya ta yi da addu'a a bakinta, ta tofa wa kaf ilahirin jikinta, da hijabi a jikinta bata cire ba, barci ya yi awon gaba da ita.


Kwalbar codein ya fiddo daga cikin deep freezer ɗinsa, ya jijjiga ta sosai, sannan ya ɗaga kansa ya kwankwaɗe, yana son damuwar da ke cikin zuciyarsa ta kau.


Sigari a fiddo daga lakar bed side nashi, ya bata wuta, sannan ya hau zuƙarta, yana yi hawaye na fita daga idanuwansa, hawayen neman mafita kawai, dan ya tabbatar matsala ta auku, babba ma ba ƙarama ba.


Washe gari.


Da ruwan sama aka tashi kamar da bakin ƙwarya. Tun bayan da aka kammala sallar asuba ruwan ya sauko, da ƙarfi sosai, irin mai haɗe da iska ɗin nan.


Baccin safe take mai cike da jin daɗi. Tana jin daɗin baccin matuƙa, ko farkawa ba ta yi ba tun da ta yi sallah ta kwanta.


A hankali ta fara buɗe idanuwanta, tana jin yanda zuciyarta ke mata rauni, wanda ta rasa dalilin hakan. Ta sani, duk sanda ake ruwan sama daɗi take ji a zuciyarta, tana son yanayin sosai, ba wai lallai sai tana barci ba, ko idonta biyu ma. Amma a wannan gaɓar, saɓanin haka take ji. Ga tsananin duka da zuciyar tata take yi, tana tuna abin da ya faru bayan ta gama sallar asuba.


*
Da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta, saboda barcin da yake cikinsu, na tashin da ta yi.


Miƙewa ta yi bisa kafafuwanta, tana hamma haɗe da miƙa, ta nufi hanyar banɗaki.


Alwala ta ɗauro sannan ta hau bisa kafet, ta fara da raka'atainil fajr sannan ta yi sallar asuba, a lokacin ruwa ya fara saukowa a hankali, ana yayyafi, ga iska sosai ana yi.


Bayan ta gama ta yi adhkar, sannan ta cire hijabin nata, ta haye bisa gado ta kwanta.


Ta jawo bargo zata lulluɓa kenan ta ji fitsari take ji, hakan ya sa ta miƙe ta yo sannan ta dawo. Abin da ba ta saba yi ba kenan, ko kaɗan ba ta yarda ta kwanta ba tare da alawala ba, ko da kuwa bayan sallar asuba ne irin na yau.


Gabanta ne ya faɗi, ta dafe zuciyarta, tana tunanin dalilin faruwar hakan, sai dai kuma ta gagara ganowa, take ta kawar da komai, ta haye gado ta kwanta abinta.


Bakinta ta buɗe zata fara addu'a, sai hamma ta zo mata, ta ƙarisa salatin da take yi haɗe da hammar, sannan kawai ta juya ta ci gaba da baccinta.


*
Ƙoƙarin motsa hannunta ta yi amma sam! Ta kasa. Ta gwada ɗaga gangar jikinta nan ma ta kasa komai. Gabanta ne ya tsananta faɗuwa, ta fara tunanin abin da ya same ta, sai dai ta rasa gane komai, tunanin mummunan mafarkin da ta yi kawai take.


Ƙyafcin ido kawai take iya aikata wa, daga ba shi ba kuwa, komai ta kasa yi, bakinta take so ta buɗe ta ƙwala wa mamanta kira ma ta kasa.


A hankali ta fara jin wani nannauyar abu na fita daga cikin zuciyarta, yana saukowa har bisa gangar jikinta, tun daga bisa kanta ya ringa tafiya, har sai da ya iso bisa tafin ƙafarta. A daidai nan ne ya fice da ƙarfin gaske, ta ji wata irin azaba wacce tun da take a rayuwarta ba ta taɓa jin irin ta ba. Kamar an ɗauki garwashi an watsa mata a tafin ƙafar haka ta ji.


Tun bayan fitar abun kuma ta ji ta koma daidai, hannun na ta ma ya ɗagu, sannan a hankali ta tashi zaune, tana tunanin abin da ya same ta.


Ba ta san sanda hawaye mai zafi ya fara mata kwaranya ba. Hankalinta a tashe ta dafe ƙirjinta, ta runtse duka idanuwanta, tana karanto addu'a a bakinta.


Sai a yanzu ma take tunanin abin da ya faru da asuba. Ashe fa ta manta babu alwala ta kwanta, saɓanin ko yaushe, yanda ta saba a rayuwarta ko bata sallah to ba dai ta kwanta ba ta da alwala ba.


Addu'a sosai take yi, tana kuma samun natsuwa sosai, tana jin sassauci a cikin zuciyarta.


"Assalamu alaikum."


Muryar Muhammad ce ta saka ta buɗe idanuwanta, tana kallonsa cikin shiga mai kyau, ya saka farar shadda da baƙar hula.


"Yaya Maryama lafiya na gan ki haka?"


Ya faɗa yana bin ta da kallo, saboda yanayin da take ciki dole ne a fahimci ta yi rashin natsuwarta ne.


"Uhmm...babu komai Hammad. Ba dai har ka shirya ba."


"Na shirya Yaya Maryama. Ke kawai nake jira."


"Ok ka koma a falo ka jira ni ina zuwa."


"To."


Kawai ya faɗa sannan ya fita, har ya ɓule daga ɗakin bai daina waiwayenta ba.


Wanka ta shiga daga nan, a ranta tana tunanin halin da ta shiga yau. Lallai mai rai ba wata tsiya ba ne. Cikin lokaci kaɗan komai na ta ya juye, ta gagara ko da motsi. Yanzu fa idan mutuwa ce ma a haka za a ce ai an kwana da ita lafiya, aka wayi gari babu ita.


A kasalance ta gama shirin. Ta saka baƙar abaya mai adon pink. Sannan ta ɗaura ɗankwalin a kanta, ta fiddo ƙaramin mayafi pink ta ɗora a bisa gado.


Falo ta fito jikinta sukuku, sai ƙoƙari take dan ganin ta koma daidai amma hakan ya gagara. Fargaba ce haɗe da tsoron Allah mamaye a cikin zuciyarta.


"Ina kwana Mama?"


Ta faɗa da sassanyar muryarta, tana saita dubanta zuwa ga mahaifiyarta.


"Lafiya ƙalau Maryama. Kin sha barci. Ai tun ɗazu Muhammad ke son zuwa ya tashe ki nake hana sa. Wai ya ƙagara ku tafi haka nan."


"Ai fa dai na ga alama Mama. Tun da ga shi nan har ya shirya tun ɗazu. Allah dai Ya sa zakwaɗi ma ya bar shi ya karya."


"Ya ci ƴar guntuwar doya. Kin ga sauran nan ya ƙulle a leda wai zai tafi ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login