Showing 99001 words to 102000 words out of 201092 words
Chapter 34 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
ba ya haye bisa gadon ɗakin, ya runtse idanuwansa yana son barci ya ɗauke sa.
Murmushi kawai mai gadi ya yi, ya kashe masa wutar ɗakin sannan ya jawo ƙofar, yana mai matuƙar jin tausayin Modu, tunda Mama ta masa bayani kafin ya shigo yi masa wanka.
Tun bayan ta yi sallah ta yi wanka ta fito falon, ta tarar Mama ta zubo mata abinci, ta haɗa mata komai tana jiran ta je ta ci.
Zama ta yi a ƙasa ta jawo abincin kusa da ita, ta jiyo muryar Muhamnad na faɗin,
"Yaya Maryama ya bani taisayi sosai. Ina jinsa yana faɗin Amrah, hala dai wacece Amrah?"
Murmushi ta yi Maryama, ta ce,
"Masoyiyarsa ce."
Kawai ta yi shiru haɗe da fara kai lomar abinci a bakinta.
Sai da ta yi nisa ma ta tuno da wani abu, ta ce,
"Mama na tuna, Annur fa an hana ba shi duk wani abinci mai cholesterol a cikinsa."
Da fara'a Mama ta ce,
"Na sani, duk wani mai larurin zuciya akan hana ba shi choleterol, shi ya sa na yi wannan tunanin, na tura aka siyo min non cholestetol oil, da shi na yi girkin."
Ajiyar zuciya ta sauke Maryama ta ce,
"Yauwa. Sai kuma abu ɗaya, bai sha maganinsa na dare ba."
"Subhanallahi! Kuma da ƙyar idan ba ya kwanta ba. Tashi mu je mu ga, Allah sai bai yi barci ba."
Tashin kuwa suka yi a tare har da Hammad, suka isa ɗakin da ke ɗan nesa da na Abbah.
Kunna wutar ɗakin suka yi, yanayinsa kawai ya saka su murmusawa su duka ukun. Kwance yake idonsa a rufe, sai ƙyaƙƙyaftu yake, wanda kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar cewa ba barci yake ba.
Cikin murya mu ƙunshe dariya ta ce,
"Angon Amrah tashi ka sha maganinka, sannan ko koma barcin."
Firgigit ya buɗe idonsa, yana sakin murmushin yaƙe ya miƙe zaune.
Deep freezer ta buɗe ta ɗauko ruwan Sona guda ɗaya, sannan ta buɗe, ta ɓallo masa magungunansa da ke can bisa side drawer ta ba shi.
Sai da suka tabbatar ya sha sannan suka bar ɗakin, bayan sun kashe masa wuta.
***
How are y'll? Fatan muna lafiya. Ya iyali ya shirye shiryen sallah? Allah sa komai lafiya.
Ya kuka ji wannan shafin? A yanzu dai na tabbata na warware nuku kawuna, dangane da Annur da kuma Sans. Na tabbata akwai da dama masu cewa kawunansu na a duhu, wai ba su gane komai a kan salon namu na yanzu, na kwan gaba kwan baya. Kafin mu fara dama na shaida muku cewa za mu canza salon labarin, mu taɓo farko sannan kuma mu taɓo ci gaba, tun daga yanzu har a gama warware mana silar zuwan real Annur Maraɗi, da kuma silar dawowar fake Annur (Sans) gidan su real Annur. Fatan za ku ci gaba da bibiyata, har izuwa wannan lokacin.
Masu faɗin wai marubuciya Amrah ba ta kyauta ba, me ya sa za ta ce Annur Iqra Al-hussein wai ba ainahin ɗan Pharm IA ba ne? Ku ajje hankulanku ku fahimci labarin nan, za ku ga kamar ya sha bamban da dama labarukan da kuke karantawa. Salo ne a cikinsa da ba koyaushe ake amfani da irinsa ba. Ku duba tun daga jigon labarin; aure da ake yi ba tare da awon genotype ba, shin ana yawaita taɓo ire iren jigon nan kuwa? Da wuya kam. Saboda haka a yi haƙiri dai, a kuma ƙara yin haƙuri, sannu a hankali duk za mu kai ga inda za ku buɗe baki, ku yi dariya sosai tsabar farin ciki.
Ina ma kaf al'umnar musulmai happy sallah in advance. Allah Ya sa mu yi sallah lafiya. Sannan ƙarin tunatarwa, a bi a hankali wurin cin nama, dan kar a ci aita zawo😂 ahto, kar ku ce Amrah ba ta faɗa muku ba. And a ajje min nawa naman, duk wacce ba ta ajje min ba za mu ɓata, kuma sai after one week zan ringa muku posting...lol😜
Sai kuma bayan sallah idan Rabbussamawati wal-ard ya nuna mana sannan za mu sake haɗuwa. Mu dage da ibada a cikin ƴan kwanakin nan da suka rage kafin arfah, Allah Ya karɓa mana ibadunmu ameen.
4k words na muku kawai don farin cikin zuwan sallah. Fatan kun yi enjoying reading na shi.
Thanks all
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:55 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
4⃣7⃣
Taƙabbalallahu minna wa minkum. Fatan mun sallata lafiya. Allah ya maimaita mana amin. Wanda suka yi aikin Hajj Allah sa sun yi karɓaɓɓe. Wanda suka azumci ranar arfah, Allah ya karɓa, ya gafarta mana kurakuranmu ameen.
***
Haka Annur ya ci gaba da rayuwa a gidan su Maryama, ba tare da wata matsala ko kaɗan ba. Sosai suke ba shi kula, tamkar jininsu ne shi. Yadda suke tarairayarsa ko a gidansu yake iyakacin abin da za a masa kenan. Sai dai a kowace rana ƙaranci ya kira sunan Amrah sau bakwai. Amrah yake so, a kai shi wurin Amrah, ya san ita ɗin ma tana can tana jiransa. Kalaman da yake yawaita furtawa kenan, yayin da ruwan hawaye kan kwaranya daga ƙwayar idonsa zuwa bisa fuskarsa, a duk sadda zai neme ta. Maganinsa kam babu tangarɗa haka yake shansa, da zarar lokacin sha ya yi Mama za ta ce da Maryama ta je ta ba shi. Haka abincin da yake ci duk an bi ƙa'idarsa, baki ɗaya suka daina amfani da normal oil a gidan, sai dai non cholesterol, kurum don inganta lafiyar Modu.
Yanzu haka kwanakin Modu biyu kenan a gidan su Maryama, amma yadda suka shaƙu sai mutum ya ce sun shekara guda a tare ne. Sosai ta iya tafi da mahaukaci, kasantuwarta psychologist ce, psychology take karanta. Kusan duk irin wannan abubuwan ba baƙinta ba ne, ta san hanyar sarrafa shi sosai. Hatta makarantarta ta sahale da zuwa, babban burinta kawai ta shawo kan matsalar Modu, saboda ta fuskanci yana buƙatar wadataccen lokaci, yana buƙatar mai tausar zuciyarsa, haka kuma yana da buƙatuwar mutum mai muhimmanci a tattare da shi. Wannan dalilin ne ya sa ta sadaukar da lokacinta gare shi, take son zama mai muhimmanci a rayuwarsa, ta yadda burinta zai yi saurin cika.
A islamiyya ma da yake sun gama rehearzal, yanzu jiran ranar yi kawai ake, nan da kwanaki huɗu za a yi ta.
Babban burin Maryama shi ne ta kammala da abin da ke gabanta; wannan walimar saukar, sannan ta hau bincikar inda za ta samu babban likitan ƙwaƙwalwa, wanda zai duba Modu, ya kuma sama masa lafiya da ƙarfin mulkin Allah.
Zaune take da waya a hannunta, browsing take, sosai take bincikar matsalar Modu. Tun daga farkon damuwarsa, har izuwa haukansa, da kuma ciwon zuciyar da ya samu ta rubuta, tana mai neman shawara, tana son sanin haƙiƙanin abin da ya kamata ta fara bi, wurin tabbatar da lafiyarsa.
Shawarwari ta samu kala daban daban, wanda duk wadda ta ɗauka, sosai za ta iya zame mata mafita. Sai dai kuma inda matsalar take, ita ɗin ba ta kasance wacce ya san ta tun asalinsa kafin ya haukace ba. A mafi rinjayen shawarwarin kuma, sun ginu ne a kan ta nemi wanda ya sani kafin haukansa, wata ƙila zai iya tuna wani abu, har memory ɗinsa ya dawo daidai.
Mafi ƙaranci daga cikin shawarwarin, sun nunar mata da cewa wai ba hauka ba ne Modu yake, kawai dai ya yi losing memory ɗinsa ne. Don haka kawai ta ci gaba da zama a haka, ta yi haƙuri, a kowanne lokacin memory ɗinsa zai iya dawowa daidai, zai iya tuna komai da ya faru a baya.
"How could this happen? Ban gasgata wannan ba. Idan har losing memory ɗinsa ya yi, ai ba zai riƙe suna guda a rayuwarsa ba. Ba zai riƙe sunan Amrah, wacce ta kasance mai muhimmanci a gare shi ba. Da sai ya manta har ita ɗin, babu wanda zai zauna a ƙwalwarsa."
Ta faɗa a bayyane, tana mai rubuta comment a ƙasan wannan maganar, cike da al'ajabi.
Bayan ta rubuta wata mace mai suna Sandra ta sake rubuto mata; hakan ba abun mamaki ba ne. Ai don an ce mutum ya yi losing memory nashi, ba lallai komai ne zai fice masa a ka ba. Akwai abubuwan da ka iya zaunawa zaman daram a kwanyarsa, musamman ma Amrah da ta faɗi kalar darajarta a gare shi. Sosai tashin hankali kan kawo matsalar losing memory; ta yiu wata mummunar kalma ce mutum ya ji, wani tashin hankali ne ya gani, duk sukan iya ruɗa mutum, ya fita hayyacinsa, har ya manta komai na shi, sai dai kuma za ta iya yiuwa ya riƙe wancan abun wanda ya ji, ko kuma ya gani, har ya yi silar mantau ɗin. Shawarar da take ba ta, ta ci gaba da kula da shi, ta ci gaba da kyautata masa, tana bin duk wata maganarsa. A duk sadda zai furta Amrah yake so, ta ringa ƙarfafa masa guiwa, ta tabbatar ba ya yawaita shiga ƙunci. Kukan nan da yake, ta san duk yadda za ta yi wurin faranta masa, har ya mance da ɓacin ran da yake ciki. Ta kasance mai yi masa labaran soyayya, tunda dai ta silar soyayya ya shiga ƙuncin, da har ya miyar da shi haka. Ta nuna mishi ƙauna sosai, ta ba shi kulawa, har lokacin da za ta zama mai muhimmanci a gare shi, tamkar Amrar da ta yi silar komai na shi.
Murmushi Maryama ta yi a daidai wannan lokacin. Ta jinjina kanta alamun gamsuwa, ta ɗan lumshe idanuwanta sosai tana jinjina lamarin. Sosai ta yarda da hakan. Sai dai fa mafi rinjaye na zuciyarta, ya fi yarda ne da cewa lallai hauka ne yake yi, tana da wata tambayar.
A ƙasan comment ɗin Sandra ta sake rubuta; na gamsu sosai da bayananki, amma kuma idan har losing memory ne ya yi, ai kamar ba zai ci gaba da yin abubuwa irin na taɓaɓɓi ba. Da hankalinsa, kawai dai ya manta komai na shi ne, sai Amrah kawai.
Alamun murmushi Sandra ta turo mata, ta ce babu abin da losing memory ba ya haifarwa. Zai iya zautar da mutum ma, koda ba mahaukacin ba ne, a ga ya zam tamkar mahaukacin. Kar ta taɓa tunanin hauka ke damunshi, domin yana da wuya irin haka ya haukatar da mutum, sai idan wani mummunan hatsari ya samu kansa ya bugu har ya taɓo sashen ƙwalwarsa, wanda zai gaggauta harbar wani sashe na daga cikinta da zai tsayar da duk wata hanyar da za ta yi ordering mutum abu. Kenan komai mutum zai yi zai koma disorderly. Abu na biyu kuma idan ya kasance kafin mutuwar Amrah, shi ɗin drug abuser ne, a hankali kwanyarsa ta fara taɓuwa, sai kuma aka yi katari da case na mutuwar ya iso, a take komai zai iya jagulewa, ya haukace kenan.
Mafi zargi dai losing memory ɗinsa ne kawai ya yi, amma mai tsananin gaske, mai haɗe da juyewar hankali kaɗan.
Ɗan taunar leɓonta ta yi Maryama. Sosai take mamakin kalaman Sandra. To amma, alzheimer's disease (Ciwon mantau) ta kama shi kenan?
Sake rubuta ma Sandra ta yi; tun daga mutuwar Amrah kenan alzheimer's disease ta kama shi?
Sandra ta ce ko kaɗan ba zai yiu a ce alzhermer's disease ba ce ta kama shi. Saboda ita alzhermers fa komai mutum mantawa yake, including his language. Ya koma tamkar ɗan koyo, komai sai an koya masa. Kuma abun haushi da zarar an koya masa zai manta. Akwai wanda na shi ke iya ɗaukar tsawon awoyi kafin ya manta ɗin, akwai kuma wanda a take za a koya masa, kuma a take zai manta. Shi kuma wannan har sunan Amrah yake faɗi, ya iya yarensa sosai. Ba za a taɓa alaƙanta shi da mai alzheimer's disease ba.
Godiya sosai Maryama ta ma Sandra, sannan a ƙarshe ta tambaye ta ko ta san wani likita wanda yake da wannan ilimin sosai ta haɗa ta da shi? Sandra ta ce ita kanta ɓangarenta kenan, sai dai kuma ba a Nigeria take ba yanzu, UK take. Idan har za su iya kawo shi nan ɗin, babu damuwa, she can help them.
Maryama ta ce ko a cikin abokan aikinta ba ta san wani da ke Nigeria ba? Ta ce mutum biyu ta sani sosai da wannan ilimin; Dr. Aqaaq Saifullah, sai kuma Dr. Hamdan M Ramat, wanda ya kasance mentor ɗinta. Za ta nemi amincewarsu idan sun yi waya, ko me kenan, tai dropping digits ɗinta, she will contact her.
***
Tun daga sadda rayuwar su Suhaila ta dawo Katsina Pharm IA ya koma karatunsa, a Sudan. Da haka rayuwarsa yaran nasa ta fara ginuwa a bisa turbar kirki, Nadrah da Saddiqa sun shiga wata makaranta mai kyau, domin samun ingantaccen ilimi kamar yadda mahaifinsu yake so.
A tsawon wannan lokacin sosai Annur ya fara yin wayo, dariya yake sosai duk da cewa watansa biyar kenan da ƴan kwanaki duniya. Kyakkyawan yaro ne jajur da shi. Idanuwansa farare ne sol, masu matsakaicin girma. Jikinsa ɓul-ɓul irin wanda kowa ke da muradin ɗaukar irinsu. Sumar kansa kwance take luf-luf, wacce idan yau aka aske ta, gobe za a fara ganin alamun tsirowarta. Bakinsa ɗan ƙarami ne, da siririn hanci, wanda kumatu ya cinye fiye da rabinsa. Komai na yaron abun birgewa ne. Ga uwa uba kuma fara'ar da gare sa, wadda kan jawo hankalin mutane a kodayaushe.
Kwanaki na tafiya, awanni na tserayya, mintuttuka na gudanya, sakan na kwararar gudu, har Pharm IA ya cika shekara huɗu a Sudan, inda ya kammalo karatunsa, ya zama babban pharmacist, wanda irinsu ke wuyar samu a ƙasarmu ta Najeriya.
Bayan ya dawo ƙasarsa ne kuma aka saka Annur makaranta ta boko da ta islamiyya. Watansa huɗu da dawowa kuma Suhaila ta samu wani cikin, wanda ta haifi kyakkyawar yarinyarta, sai dai ita ɗin baƙa ce, kamar sauran danginta mata. Jameela sunanta; sunan kakarta aka saka mata, mahaifiyarta ta mata laƙabi da Islam, saboda tsananin son sunan da take.
A cikin lokutan da Annur ya fara mallakar hankalin kansa ne Allah ya jeho Amrah a rayuwarsa, sanadiyyar wani dalili da ya sa mahaifiyarta ta zo ƙofar gidan su Annur ɗin, har ya ga Amrah, a lokaci ɗaya ya kamu da begenta, duk da kasantuwarsa ƙaramin yaro. Ya ɗauke ta ya ajje a cikin zuciyarsa. Ya sadaukar da komai nasa saboda Amrah. Duk inda zai je sai ya biya ta gidan su Amrah ya ganta sannan yake samun kwnaciyar hankali. Haka ita ma Amrah, tun tana ƴar ƙaramarta ta shaƙu da shi, ta saka shi a cikin zuciyarta, izuwa lokacin da aka raba su, aka miyar da shi Cyprus wurin yayarsa Nadrah.
A ɓangaren Salman ma dai haka ya ringa yin wayo, kyakkyawa da shi wanda ko kaɗan ba shi da bambanci ko kaɗan da Annur, kamarsu ɗaya, komai nasu ɗaya. Sai dai matsalar babu wanda ya sani, babu kuma wanda zai iya fayyace musu gaskiya sai Dr. Rita, saboda ita kaɗai ta san kamannin Annur, ta kuma san cewa shi ne a hannun Suhaila. Matuƙar za ta ga hoton Salman na jarintaka, to tabbas za ta tabbatar da cewa kamanninsu iri ɗaya ne da Annur.
***
Tunda suka zauna a gaban teburin likitan gabansu ke tsananta faɗuwa, barinma Farouk Sardauna da hankalinshi ya gama tashi, jikinshi ya gama ba shi cewa lokacin mutuwarsa ya kusa.
Suna cikin haka sai ga likita ya shigo sanye da lab court, idonsa sanye da medical glasses yana faɗin,
"Afwan na barku da jira. Abokin nawa sai da na kai shi har gaban mota ne."
"Babu komai."
Annur ya furta haɗe da ƙirƙiro murnushi yana bin Dr. ɗin da kallo.
Bayan ya zauna a mazauninsa ya zare glasses ɗinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya hau duba results ɗin Bobby.
Sosai Bobby ke jin raɗaɗi a zuciyarsa, yake jin duniyarsa na sauya masa, tashin hankali wanda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa yin irinsa ba yake ji. Firgigit ya zabura haɗe da dawowa hayyacinsa, a lokacin da ya ji tattausan kalaman likitan, ya ƙura masa idanuwa,
"Ya kake da wannan bawan Allah'n? Ina nufin can I say anything infront of him?"
Da kai Bobby ya ba likita amsa, cewa ya faɗa ɗin kawai. A wannan lokacin kam ya gama sadaƙewa, ya kuma tabbatar da cewa ba ƙaramin ciwo ba ne a tattare da shi, tunda har likitan ba ya son faɗi a gaban Annur.
"A bisa hotuna da aka maka ga su, sun bada tabbacin cewa hunhunka ne ke da matsala. Shi ne ya yi damaged, gurɓatarsa har ta fi lafiyarsa yawa. Ko ka san abin da ya jawo haka kuwa?"
Ya sake gyara zamansa, har yanzu bai ɗauke idonsa daga fuskar Bobby ba.
Bai jira amsar da Bobby ɗin zai ba shi ba, ya ɗora da faɗin,
"Smoking ne, shi ne sila Farouk!"
Ido buɗe Bobby ke sake dubar Dr. Ba tare da ya furta komai ba yake zubar da ruwan hawaye, yana ɗan gyaɗa kansa.
Annur ɗin ma bai iya faɗar komai ba, sai dai fa cike yake da tausayin amininsa, sosai yake jinshi har cikin zuciyarsa. Me ya sa ciwo zai musu haka?
"A duk sadda mutum yake shaƙar hayaƙi, ko kun san cewa wannan da kuke tutiyar ai kuna fiddo shi ta baki da hanci, ba dukansa yake fitowa ba? Sannan kuma dole sai ya isa cikin hunhunku, sannan ma duk abin da zai yi ya yi? Wannan smoking ɗin da kuke ji da gani, ba shi da wani amfani a gare ku face matsala, wadda za ta iya kai mutum ƙabari. Yanzu dai ga shi, baki ɗaya hunhunka ya yi damaged, sauran amfaninsa kaɗan ne, matuƙar ba a tashi maka tsaye ba, akwai babbar damuwa.
Abun haushi, har da wata sabuwar sigari aka kawo yanzu, wai ita shisa. Kun san cewa duk illar da sigari za ta yi ita ɗin ma za ta yi shi? Yes! Za ta yi shi. Saboda hayaƙi ce ita ma, an shaƙe ta ne kuma aka isar da ita cikin ciki, kuma kai tsaye hunhu za ta kai mawa.
Shi hunhu wani irin abu ne, wanda