Showing 105001 words to 108000 words out of 201092 words
Chapter 36 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
Abbu? Na kasa fahimtar komai da yake faruwa. Dan Allah ka sanar da ni."
Su kansu yaran sun tsorata a wannan gaɓar. Gabansu sai tsananta duka yake, suna jin yadda duniyarsu ke juye musu.
Sakin wayar ta yi tana kuka sosai, hakan ya sa Sans ya ɗauka haɗe da kara ta a kunnensa, sai dai ba ya jin komai sai wani sauti da yake ji, wanda ya kasa gasgata cewa sauti harsashin bindiga ne ke tashi.
"Ku gaggauta guduwa Shereefa. Babu kwanciyar hankali a garin nan, ga su nan sun ƙariso inda nake. Idan sun kashe ni ki yafe min. Don Allah ku gudu kar ku zauna. Bomb suke tayarwa."
Ƙit! Ya kashe wayar. Sans na ambatar sunan Abbunsu amma ina, shiru ya ji alamar ya kashe.
Kuka suke sosai su duka ukun. Ita mamar tasu ma baje take a ƙasa tana kukan, ta kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi.
Cikin ƙarfin hali da muryar kuka Sans ya ce,
"Aunty ku tashi mu san na yi. Abbu ya ce babu kwanciyar hankali a garin nan. Mu tafi tun abun bai iso nan ba."
Da kanshi ya samu ya cicciɓi mahaifiyar tasu, sannan ya kama hannun ƙanwarsa Yamairah, ya ce lallai sai sun bar gidan yanzu. Hijabi ma shi ya saka ma Mamarsu, sannan ya kawo ma Yamaira tata ta saka, ko kuɗi ba su tsaya nema ba kawai suka bar gidan, hankulansu a tashe, tunanin Abbunsu kawai suke, da kuma makomarsu a wanann fitar da suka yi.
***
To to to to! Yanzu dai na san na warware muku kawuna dangane da Salman da kuma Sans ba? Haha! Salman shi ne Sans, wato twin brother ɗin Annur kenan😀
An fara zuwa inda kuke so ko? Maryama ta fara koyawa Modu kalaman soyayya, wanda ba mu sani ba ko so take tsuntsun soyayyar Amrah ya dawo kanta?🤐 Yo anya ma dai Modu zai taɓa iya son wata bayan Amrah, da yake ganin kamar har yanzu tana nan da ranta? Ya maganar Sandra da ta ce za ta haɗa Maryama da likita? Shin wace magana ce Maryama za ta yi da Umman Amrah?
Na san fa wasu sun manta da Ahmad Deedah, cousin ɗin Maryama ko?🤔 Ya kamata mu tuno shi haka nan. Wata ƙila akwai wata ƙarmaya ƙarmayar game da shi😷
Wayyo ni Fiddou ko a wanne hali take ciki yanzu?🤧 tana ba ni tausayi fa. Ga talauci, ga ƙiyayyar matar Yayanta, ga kuma uwa uba son maso wani da ta ɗorawa rayuwarta😰 ita ɗin ma fa ya kamata mu leƙo ta haka nan.
Sannunku ghosts🤓 kawai sai a gama shan karatu amma a kasa kankaro mutunci ta hanyar dangwala alamar tauraron nan😎 kun kyauta ai.
Na ga wasu na faɗin wai ba su ji daɗi ba ANS ya kusa ƙarewa, wa ya faɗa muku?🤔 anya ma dai ko rabi mun yi😅 kar dai kuma na shirgo ta fa😂 amma dai gaskiya akwai sauran labari. Kawai ku ci gaba da kasancewa tare da ni. Har da sugar zan daɗa ƙara ma labarin, yanda za ku ji shi da zaƙi zaƙwai kamar zuma😅.
Thanks all.
Pinky durling❤
RAZ 2
[8/30, 3:56 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
4⃣9⃣
Wattpad: PrincessAmrah
Wannan shafin sadaukarwa ne a gare ki Faɗimatu Dawaki. Haƙiƙa ke masoyiya ce ta gaske, wacce nake alfahari da ita a kodayaushe. Ƙaunar da kike ma ANS har ta wuce gaban misali. Jinjina a gare ki, na gode ƙwarai da jajircewarki.😍😘
***
Sai daf da magrib sannan Maryama ta koma gida. A gajiye take lis, hakan ya sa kai tsaye ta nufi ɗakinta, a lokacin gidan nasu duk an watse, sai ɗai-ɗaikun mutanen da ba za a rasa ba.
Tana fitowa daga wanka ta saka doguwar rigar barci, sannan ta ɗaura zani a kai, ta feshe jikinta da turare. Hijabinta ta saka har ƙasa sannan ta fito, ta tarar da Mama da ƙawayenta mutum biyu suna fira.
Har ƙasa Maryama ta duƙa ta gaishe su, sannan ta nufi ɗakin da Modu yake.
Zaune yake a ƙasa ya yi zaman dirshan, yana wasa da haruffan da Maryama ta ajje musamman tana koya masa karatu.
Murmushi ya saki a sadda ya ganta, ya gaggauta miƙewa tsaye yana sake bin ta da kallo, ita ɗin ma kallonsa take. Jallabiya ce a jikinsa kalar coffee brown, sosai ta ma kyakkyawar ƙirarsa kyau, ya fito babban mutum mai tarin ƙwarjini, wanda idan har ba ka san shi ba, ko kuma an faɗa maka ba, ba za ka taɓa cewa mara hankali ba ne.
"Ya Noor wannan irin shan kyau haka."
Ta ƙarisa matsowa kusa da shi, tana masa fara'a.
"Au shiru ma za ka min ba za ka min magana ba? Ko ka manta na faɗa maka yau an mana walima?"
Sai a sannan cikin dariyarsa ta yaƙe ya ce,
"Ban manta ba ai."
Ya kama rawa da kansa, ya ɗan duƙar da kansa ƙasa.
"To na ji, dawo nan ka zauna."
Ta gwada masa bakin gadonsa da hannu.
Babu musu ya zauna yana mata dariya, ya kai yatsunsa biyu a cikin baki yana tsotsa.
Da sauri Maryama ta ce,
"Amma Ya Noor don Allah ban hana ka cin hannun nan ba? Ba ka ga yadda kake komawa ba fa, kamar wani dolo."
Ɗaure fuskarsa ya yi a wannan karon, tare da faɗin,
"Ni ba dolo ba ne."
Ya fiddo yatsun daga cikin bakinsa.
"Yauwa ɗan albarka. Ko kai fa. Yanzu dai darasi za mu yi. Ka san wane iri?"
Ya gyaɗa kansa da murmushi, yana matuƙar son darasin da suke yi ko ma wanne iri ne; na soyayya, ko kuma boko da arabi da take koya masa.
"Yau wasu baituka ne na musamman na tsaro su domin masoyiyarka Amrah. Ina fatan za ka ajje hankalinka sosai ka saurara, kuma ka iya su don ba zan maka ƙari ba har sai ka maimaita su gobe na ji."
Ɗaga mata kai ya yi yana dariya, ya ce,
"Na yarda, zan iya sosai."
"Yauwa fa, haka nake son ji. Ka shirya?"
Kamar yadda ta saba ta masa wannan tambayar.
"Ehh! Na shirya."
Ya faɗa cikin waƙa, kamar yadda ta koya masa.
"Ka tabbata ka shirya?"
Ta sake tambayarsa.
"Ehh, na shirya."
Ya sake maimaitawa. Sai da ta faɗi haka har sau uku yana faɗin ya shirya, kafin ta yi gyaran murya tana faɗin,
"Amrah nake so!
Baiwarta nake so!
Iliminta nake so!
Halinta nake so!
Fara'arta nake so!
Kalamanta nake so!"
Ya yi shiru ya miyar da kaf hankalinsa gare ta, bakinsa a buɗe yake har yanzu, fuskarsa ƙunshe take da fara'a. Sosai yake jin daɗin waƙar, yana jin wani irin yanayi a tattare da shi, wanda ba zai misaltu ba.
Maryama ta ci gaba da,
"Ni dai na ce sai Amra,
Amrah kaɗai ce tai zarra,
Kusancinmu ya wata da zara,
Ita na bai wa dukka lamurra,
Rayuwata tata ce ta ƙara,
Ki dawo gare ni ya Amra,
Kewarki nake ni Nura,
Ke ɗai ce a gare ni Amra,
A zuciya tawa nai shara,
Na kakkaɓe ko'ina sai Amra!"
A wannan lokacin kam sosai Modu ke lila ƙafafuwansa, yana lumshe idanuwansa cike da shauƙin ƙauna. Jinsa yake a wata sabuwar duniya, yana ƙara tuno wasu abubuwa da dama da suka shuɗe na rayuwarsa. Ita kanta Maryama jin ta yake sosai a zuciyarsa. Yana girmama darajarta, martabarta, da kuma ƙimarta. Saboda kyautata masan da take. Duk da ya kasance ba ya cikin hankalinsa, amma an halicci zuciya da son mai kyautata mata, da kuma ƙin mai munana mata. Kyautatawar da Maryama ke masa, take saka shi a nishaɗi dare da rana, ko Fiddou ba ta masa haka. Saboda ita ɗin ma tana neman mai saka ta farin ciki ne. A gida ma ba daɗi take ji ba, rayuwar tsanani take ciki sosai. To ta ya ta ga farin cikin da har za ta iya saka wani?
A ɓangaren Maryama ma sosai ta ji daɗin ganin ta saka Modu farin ciki. Baki buɗe take kallonsa, tana sake maimaita baitukan tana tafawa, tana lila kanta ita ma alamar rawa.
Da haka ta fara jiyo kiran sallar magrib, hakan ya sa ta masa bankwana haɗe da barin ɗakin, ta bar Modu cike da shauƙi da begen Amrarsa.
***
Tunda suka samu nasarar fita daga gidan suke gudu gudu sauri sauri. Ko'ina suka gitta ya kaure da hayaniya. Mutane sai gudu ake domin neman tsira. Ƙarar tashin bomb kuwa ba a bakin komai yake ba. Haka ƙarar harbin bindiga ma, har sai su rasa ta inda yake tasowa.
Sosai suka siƙe, hakan ya sa Yamairah ta duƙe dafe da ƙirjinta, sai famar shessheƙa take, tana hawaye.
Kama hannunta ya yi Sans, cikin murya mai nunar da tsantsar tashin hankalin da yake ciki, ya ce,
"Daure ki tashi mu tafi Yamaira, kin ga jama'a sai guduwa suke ana neman tsira. Kar mugayen nan su riske mu a nan."
"Ba zan iya ta shi ba, zuciyata nake ji kamar za ta tsage, ku tafi kawai ku bar ni a nan, ko ku kawai ku tsira."
Cikin tashin hankali mahaifiyarsu na kuka sosai ta ce,
"Ki daina faɗar haka Yamaira, babu inda za mu tafi mu bar ki. Ki huta sosai sannan mu tafi."
Ita ɗin ma ta duƙe a gajiye, tana mai bubbuga bayan Yamaira alamar rarrashi.
Sosai ƙara ke sake kusantarsu, hankalinsu ya sake tashi. Sans da sauri ya ce,
"Aunty ku daure mu tafi, ga hanyar da mutane ke bi can, wata ƙila mu samu wurin fakewa, tun ba su ƙariso inda muke ba."
Da ƙyar ta miƙe mamar tasu, shi kuma Sans ya ƙoƙarta kama hannun Yamaira ta miƙe, sai dai kuma tana miƙewa ta sake komawa ƙasa ta duƙe.
Hankalinsu in ya yi dubu ya tashi, musamman yadda abun ke ta sake kusantarsu. Ƙarar tashin bomb ke yawaita fiye da ɗazu.
Duƙawa ya yi a daidai saitin Yamairah, cikin kuka ya ce,
"Hawo bayana Yamairah, mu gaggauta barin wurin nan."
Hawa bayan ma kasawa ta yi tsabar jigata da ta yi. Sai da Aunty ta taimaka mata sannan ta hau, cikin sauri suka ringa nufar inda suka ga al'umma na bi.
Sun yi tafiya mai nisa kafin suka ci karo da wani kango, wanda da alama babu kowa a cikinsa, tsohon gini ne.
Kallon wurin ya yi Sans, ya ce,
"Aunty ko za mu je can, ga wasu a can ma da alama duk irinmu ne, sai kuka suke."
Ba ta iya magana ba Aunty, sai dai kanta da ta ɗaga masa kawai, hakan ya sa suka ƙarisa shiga cikin kangon.
Samu ya yi ya kwantar da Yamaira a ƙasa, yana mata sannu, sannan kuma yana ma Aunty ma sannu.
Hankalinsu ya ɗan kwanta da zaman wurin, saboda ko hayaniyar ma ba a ji sosai, ƙarar tashin bomb ma sai dai su ɗan ji sautinsa kaɗan.
Sun ɗauki kusan awanni biyar a wurin kuma sai tashin hankalin yunwa da ƙishirwa, ga shi kuma babu mai guzuri a cikinsu, ba su kaɗai ba, har sauran jama'ar da suke wurin ma. Yara ƙanana sai koke-koke suke, dattijawa kuma an haɗa kai da guiwa, ana ta ambaton sunan Allah.
Dafe ƙirjinta ta yi Aunty, tana jin yadda yake mata ciwo sosai, yana barazanar tsagewa. Tun tana daurewa har abun ya ci tura, ta ringa ambaton inna lillahi a bayyane.
Cike da damuwa Sans ya ce,
"Aunty me ya faru da ke?"
Ƙirƙiro murmushi ta yi da faɗin babu komai, don ta san ko ta faɗa masa bai da maganin matsalarta.
"Aunty kina da damuwa tabbas. Don Allah ki sanar da ni."
Cikin dauriya ta ce,
"Ina jin alamun tashin ulcer'ta ne Sans. Yunwa nake ji, ga ƙishi."
Ta dafe kanta tana zubda ruwan hawaye, duk iya ƙoƙarinta na ganin ta daure amma ta kasa.
Kamar Yamairah na jira ita ma ta ce,
"Aunty ni ma yunwa nake ji. Babu komai a cikina. Ga shi kuma a bakina ko yawu ba ni da shi, tsabar ƙishi da nake ji."
Cikin dakiya Sans ya miƙe tsaye, ya zaro wayarsa da ya saka a aljihunsa tun kafin ya fita daga gida ɗazu, shi ya ma manta da ita kwata kwata.
"Zan je in dawo Aunty."
Takunsa ɗaya ya ji ta kamo ƙafarsa. da hannunta na dama. Cike da tsoro da firgici ta ce,
"Ina za ka je Sans? Cikin wannan tashin hankalin za ka fita? Ka duba ka gani, kowa ya nutsu a nan, babu mai fita. Don Allah ka dawo."
"Aunty ko na zauna dole zan fita. Rayuwa za ta ci gaba da tafiya a haka ne ba ci ba sha? Dole za a buƙaci wani abu. Don Allah ki bar ni na tafi "
Gyaɗa masa kai ta yi cikin kuka sosai ta ce,
"Idan ma ka tafi ɗin, da wanne kuɗi ne za ka samo mana abincin da za mu ci ɗin?"
Aljihunsa ya gwada mata da faɗin,
"Ga wayata nan a ciki, zan nemi mai saye Aunty, insha Alahu zan samo muku abinci da abin sha."
"Hankalina ya kasa kwanciya da fitar nan taka Sans. Don Allah ba don ni ba, ka dawo ka zauna, wallahi na yafe."
Durƙusawa ya yi har ƙasa, cikin kuka ya ce,
"Aunty addu'a kawai za ki min, insha Allahu zan dawo lafiya. Zan kuma same ku lafiya."
Gyaɗa kanta ta yi, ta ce,
"Shi ke nan Sans, Allah ya bada sa'a ya dawo min da kai lafiya. Allah Ya maka albarka."
Murmushi ya ƙirƙiro haɗe da barin wurin, yana yi yana waigen mahaifiyarsa da kuma ƙanwarsa.
***
Hannunta ya kama na dama, yana jin yadda take shessheƙar kuka ƙasa-ƙasa, da takun da take yi a hankali. Cikin tausayi ya dube ta, ya ga yadda fuskarta ta kumbure tsabar kukan da ta sha, idanuwanta sun mata luhu luhu, sun kaɗa sun yi jajur.
Cikin sassanyar muryarsa ya ce,
"Halan sai yaushe ne za ki cire ma kanki wannan damuwa Fiddou? Modu dai ya tahi wurin danginsa, babu tabbacin zai dawo gare ki. A ganina sam, bai kamata ki kasa cire shi daga rayuwarki ba. Ki sani, ko warkewa Modu yai yi yanzu bai san ki ba, bai san da zaman ki ba. Cire shi daga ranki shi zai hiye miki zama alheri a kan wannan damuwa da kike ciki. Ki duba ki gani hwa Fiddou, yau kwananki shida a asibitin nan, kwance ba ki da lahiya. A kan mi Fiddou? Mi da ba za ki kai zuciyarki nesa ba?"
Shiru ta masa kuma har a lokacin ba ta daina kuka ba. Ta sani sarai, gaskiya Mahmouda ya faɗa mata. Amma kuma ta yaya? Ta wacce hanya ce za ta bi don ganin ta cire Modu daga zuciyarta? Abu ne da ba ta da maganinsa, ya zauna a ranta matuƙa, wanda cire shi ba abu ne mai sauƙi ba.
Da haka har suka ƙarisa gaban motar Mahmouda, ya buɗe mata gaban motar ta shiga, sanann ya zagaya shi ɗin ma ya shiga, ya tayarta.
A gaban gidan su Fiddou ya faka motar, shi ya taimaka mata ta fito, sannan ya buɗe booth ya fiddo ƴan tarkacenta da ya saka a ciki.
Tare suka shiga cikin gidan, tana gaba yana bin ta a baya, har suka ƙarisa daga ciki. Kasantuwar yammaci ne, a tsakar gida suka samu Yayanta da kuma Aunty Sahiya zaune, suna fira.
A susuce take sosai, hakan ya tashi hankalin yayanta, cikin kiɗima ya miƙe tsaye, ya saki baki yana bin ta da kallo.
Mahmouda ne ya gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa, sannan ya ba shi izinin zama.
"Halan dai duk jikin Modu ɗin ne ya mai she ki hakan ga giɗe?"
Ta ji muryar yayan nata ya faɗa, cike da mamaki.
Ba ta iya furta masa komai ba, sai sake fashewa da ta yi da wani kukan mai ƙarfi, ta duƙe bisa guiwowinta.
Cike da masifa Aunty Sahiya ta ce,
"Ke do Allah de idan mutuwa yai yi ki hwaɗi ma mutane kuma ki muna shiru, ke tasa mu gaba sai wani kuka kike."
Kamar zai ce wani abu yayan nata kuma dai ya kasa. Duƙawa ya yi a gabanta, cikin ƙanƙanuwar murya ya ce,
"Ki shiru ke jiya, ki min bayanin abin da ya hwaru."
Sai a sannan ta ɗago kanta da rinannun idanuwanta, ta ce,
"Yaya ko kaɗan ba ka damu da ni ba. Ka kasa cika alƙawarin da iyayenmu suka bar ma kahin su rasu. Yanzu yaya ashe kana cikin garin nan, na yi kwana da kwanaki ban dawo gida ba, amma ka kasa neman inda nake, kuma kana nan hankalinka kwance?"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce,
"Ba haka ne ba Fiddou. Ai na san kina lahiya, tunda jinyar Modu ce kike yi."
Gyaɗa kanta ta yi Fiddou, ba tare da ta furta komai ba ta ci gaba da kukanta.
Mahmouda ne ya ce,
"Yau kwananta shida ba ta da lahiya. Modu ma dangi nai sun taho gobe sati guda kenan sun tahi da shi. Tun bayan nan kuma ita ma babu lahiya, aka ba ta gado."
Sosai ya ruɗe Yayanta, ya ma rasa me zai faɗa. Sai ya kalli Fiddou kuma ya juya ya kalli Sahiya. Jin sa yake kamar zai yi kuka, da gaske Fiddou take, tun bayan aurensa da Sahiya ko kaɗan bai taɓa kyautata ma Fiddou a matsayinta na amanarsa ba. Kullum cikin wahala take; gare shi da kuma matarshi.
Dafe kansa ya yi, ya rasa uwar ubansa, can ya jiyo muryar Mahmouda ya ce,
"Idan babu damuwa Yaya akwai maganar da nake so mu yi da kai."
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, yana jin yadda zuciyarsa ke masa zafi. Baƙin ciki ya taru ya ƙunshe a cikin ransa.
"Ina sauraren ka."
Yayan ya faɗa tare da ƙura masa idanuwa. Yana mai jin duniyarsa ta masa tsanani, tsanani mai wuyar a fasalta shi.
Readers, sannunmu sannunmu da jimurin karatu😀. Wannan shafin bai yi tsawo sosai ba, na sani. Sai ana haƙuri da ni, kun san jiki da jini, ba kullum mutum ke da cikakkiyar lafiya ba. Idan ma akwai ta cikakkiya, to akan samun canjin mood, yau rubutun da daɗi, gobe kuma babu.
Me kuke tsammanin zai faru? Menene Mahmouda zai faɗa ma Yayan Fiddou? Alheri ne ko sharri😱? Allah sa dai abun kirki ne.
Da gaske fa ina tausayin Fiddou har cikin zuciyata. Har ma na rasa gane shin ita da Annur waye soyayya ta fi zautarwa? Annur ne, na sani. Amma fa ita ɗin ma ta zauce, mahaukaci take ma wannan muguwar soyayyar da har ta kwanta kwanaki shida a asibiti kawai saboda tafiyarsa. Soyayya is real, I know. Wadda duk da faɗa tarkonta sai dai addu'a kawai, don kuwa ba