Showing 81001 words to 84000 words out of 201092 words

Chapter 28 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

kuma Ya ba shi lafiya. Ke kuma, Allah Ya fahimtar da ke gaskiya, ki daina irin wannan rayuwar da kike ciki."


Ba ta ce amin ba, saboda ba ta da muradin hakan. Idan har ta bar zaman kanta a yanzu, ta tabbata Annur zai guje ta, saboda dama jikinta kawai yake so. Ita kuwa ba ta jin za ta iya jurar rashinsa a cikin rayuwarta. Ta jima tana ƙaunarsa, tun kusan shekaru biyar da suka gabata. Sai dai a wancan lokacin, wulaƙanta ta yake, yana cin mutuncinta. A ganinsa, shi ɗin ba ajinta ba ne. Amrah ce ta shi, ita kaɗai yake so. Duk wata mace ba ta gabansa, ba ya ganin ko wace mace sai Amrah. Rayuwarsa, tunaninsa da komai na shi ya ta'allaƙa ne ga Amrah. Wannan dalilin ya sa ya guji Hadiza, ya wulaƙanta ta sanda ta taɓa kai masa tallar kanta. Tun daga lokacin ta ƙoƙarta hana kanta shiga rayuwarsa, sai dai kuma duk wasu movements ɗinshi tana kula da su. A haka har ta ji labarin mumuwar rayuwar da ya faɗa bayan rasuwar Amrah, daga nan ne ita kuma ta sake kai masa kanta, take kuwa ya amince da ita, suka ci gaba da aikata alfahshar su.


Tana cikin wannan dogon tunanin ne ta tsinkayo muryar Maryama na faɗin,


"Idan na koma gida, zan yi tunani sosai, sai in tsayar da ranar da ya kamata mu tafi."


Hadiza ta ce,


"Bai kamata mu ɗauki dogon lokaci ba mu je ba. Yana cikin matsanancin tashin hankali, wanda ke buƙatar taimakon gaggawa. Na tabbata Fiddou tana kula da shi yanda ya kamata, sai dai matsalar ita ɗin ma ta kanta take. Rayuwarta abar tausayi ce, tana buƙatar taimakon ita ma kafin ta taimaki wani.


"Haka ne. Insha Allahu ba zai ɗauki dogon lokaci ba. Daga yau zuwa jibi litinin, za mu tafi da izin Allah. Yanzu dai bara na tashi, Islamiyya zan tafi kar na makara. Tun ƙarfe tara ya kamata ina can, ga shi yanzu har kusan sha ɗaya da rabi na safe."


"Ayyah! Allah sa dai kar a samu matsala a makarantar."


Bayan ta miƙe Maryama, ta ce,


"Babu matsala insha Allah. Da yake muna ta shirye shiryen walima ne."


Ita ma Hadiza miƙewar ta yi, ta ce,


"Haka ake so to. Mu tafi?"


Kai Maryama ta ɗaga mata. Suka kama hanyar barin lambun.


A bakin titi kowacce ta tsayar da tata napep ɗin, Hadiza ta wuce gidanta, Maryama kuma ta wuce Islamiyya.


***


Tun bayan da ya farfaɗo aka dawo da shi ɗakinsa, ta ƙura masa idanuwa tana kallonsa da hawaye shimfiɗe a saman fuskarta. Shi kuwa in banda murmushi babu abin da yake yi. Sai butsu butsu idan ya kalle ta tana kukan shi ma ya ɓata fuskarshi, a dole ya ji haushin kukan da take yi.


"Modu mi da kake haɗe ranka halan?"


Ta ƙoƙarta shanye hawayenta ta masa wannan tambayar.


"Ba ke ce ba..."


Ya saki murmushi kuma, ya ce,


"Kike dariya da ƙarfi."


Kallon dolanci irin nasa kawai take. Sau da dama yakan ba ta dariya idan ya yi wani abun. Amma kuma tausayinsa da take ya fi yawa, shi yake hana ta darawar.


"Modu kana da abin dariya wani lokacin. Yaushe kag ga na yi dariya a nan? Kana ciwon ne kuma zan yi dariya dan rashin imani? Kai ma hwa ka san ba zan iya ba."


Yaƙe ya yi, ya ce,


"Ai na san kina so na, kamar yanda nake son Amrah."


Da mamaki ta kalle shi, farin ciki lulluɓe da zuciyarta. Yana son ta? Ta ma kanta wannan tambayar.


Murmushi ta yi, ta ce,


"Modu ashe dai ka san ina son ka. Na ji daɗi da kas san haka."


Ɗaure fuskarsa ya yi kuma, ya harare ta kamar ba shi ne ya gama murmushi ba, ya ce,


"Ni ba na son ki, Amrah nake so!"


Ɓata fuskar ta yi ita ma. Har ga Allah tana jin haushin wannan Amrar da yake yawan ambata. Ba ta sani ba, shin tana raye ko ba ta raye? Duk da haka dai tana kishinta. Sau da dama zuciyarta kan raya mata cewa babu wanzuwar Amrah a doron ƙasa, kawai dai surkulle ne irin na taɓaɓɓi. Sai dai kuma a wasu lokutan, wani sashe na zuciyarta yakan ba ta tabbacin akwai Amrah, sai dai inda take ɗin ne ba ta sani ba, kuma ita ɗin mai muhimmanci ce a rayuwar Annur. Sai kuma ranar da likita ya ba ta tabbacin Amrah ba ta rasa nasaba da larurar Annur, saboda yawan ambaton sunanta da yake, da kuma yanda ake tanƙwara shi ta hanyar ambatar sunanta.


Share sabon hawayen da ya fito mata ta yi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tana mai matuƙar tausayinsa, da kuma makomarsa idan har ba a samu kuɗin siyan maganin nan ba.


"Kin ji haushi na ce Amrah nake so ko? Ita ɗin ma na san tana so na. Mu yi auremmu mu haifi ƴaƴammu..."


Ya rufe fuskarsa alamun ya ji kunya.


Murmushin ƙarfin hali ta ƙirƙiro, ta miƙe haɗe da faɗin,


"Kana jin yunwa, na sani. Bari in tai in samo ma abinci."


Kafin ta fara ajje takunta ta ji sallamar Dr. Huzaif. Kallo ta bi shi da shi fuskarta ba yabo ba fallasa. Sallama ya yi ta amsa, sannan ta daidaita masa kujerar da zai zauna, ita kuma ta fasa fitar da za ta yi, dan ta san akwai abin da yake tafe da likitan.


"Ashe ya farka."


Ta Jiyo muryarsa, bayan ya zare glasses ɗinsa yana bin Modu da kallo yana murmushi.


"Ehh, bai jima da tashi ba."


Ta faɗa a hankali, cikin sanyin murya.


"Ni za ki kira dama da kika miƙe?"


Ya tambaye ta yana ƙoƙarin ciro takarda daga aljihun lab court ɗinsa.


Ba ta ba shi amsa ba, kanta sunkuye yake a ƙasa, haka kawai ba ta ƙaunar haɗa ido da shi. Ita dai ta tsane shi, tun daga sanda ta fahimci rashin iya maganarsa. Ga shi dai likita, amma ko kaɗan bai san yanda zai yi magana ya kwanatarwa mutane hankali ba. Har da son ganinshi ba ta yi, dan dai kawai ya zame mata dole ne. Sassauci ɗaya take samu a wannan tsanar da ta masa, da yake ƙoƙarta kula da Modunta.


Gyran murya ya yi a karo na uku, saboda sai faman miƙa mata takardar yake amma sam! Hankalinta ba ya gare shi, tana can tana faman tunani.


Da saurinta ta miƙa hannu ta karɓi takardar, ta buɗe cikin sanyin jiki. Magungunan ne a rubuce guda biyu, da kuma gargaɗin kar ya ringa amfani da duk wani abu mai cholesterol, saboda har da shi ne ya masa yawa a zuciyarsa.


"Ki tabbatar an siyo magungunan nan, daga yau zuwa gobe nake so ya fara amfani da su."


Kanta kawai ta ɗaga masa, hawaye na ƙoƙarin fara fita daga idanuwanta.


"I repeat, ki tabbatar an siyi magungunan nan, rayuwar giɗe na cikin matsala matuƙar ba a siya wanga magunguna ba. Ciwon zai iya kai wa har inda bai kai a yanzu ba."


Hawayen da take ɓoyo ne suka gangaro a daidai wannan lokacin. Ita ba ma ta san yanda za ta yi ba. Shin sata za ta yi ta samo wannan kuɗin? Ko kuwa kanta za ta miƙa da maza domin ta samu kuɗin siyan magungunan nan? Kanta ta gyaɗa alamar a'a, ko kaɗan ba ta yarda da wannan shawarar ba. Sam! wannan ba mafita ba ce. To miye abun yi? Miye mafita?


Share hawayenta ta yi. Abincin da za ta nemo masa ya ci ma take tunani, tun ma kafin a kai ga kuɗin siyan maganin.


"Akwai inda na masa order'n abinci, sau biyu kullum a wuni. Na biya kuɗin duka, na tsawon sati biyu. Na hwaɗi musu irin abincin da za a ringa kawo masa ɗin, saboda na san indai dan ta ke ne, za a iya samun matsala, dan da ganinki ke ma ba ki kula da kanki ba, bare kuma a yi maganar kula da wani, wanin ma kuma mai larurin zuciya."


A fusace ta ɗago kanta ta kalle shi. Hawayen da take ɗin ma tayawa suka yi cak! Takaicinsa take. A kan me zai ringa jifar ta da duk kalaman da suka fito daga bakinsa? Dan yana likita kawai sai ya raina mata hankali? Talauci hauka? Ai ba kanta farau ba, kuma ba kanta ƙarau ba.


Da sauri da sauri zuciyarta ke bugawa. So take ta maida raddi amma wani sashi na zuciyarta yana hana ta. Ba ta gama tunanin yanda za ta yi da shi ba ta ji ya yi murmushi, ya ce,


"Kar ki bar giɗe bai sha maganin nan ba. Idan kin san ba ki da kuɗin saye nai tun wuri ki hwaɗi min, a san yanda za a yi da shi. Da ganin ki hwa..."


"Wai kai wane irin mutum ne, wanda ke hwaɗin magana duk yanda rai nai yas so? Halan dai kaina hwarau talauci? To bari ka ji in hwaɗi ma, kai ba ka isa ka wulaƙanta ni ba. Kuma magani ka riƙe ba a so, da yardar Allah zan sai mai magani daga yau zuwa gobe. Abincinka ma ka riƙe ba a buƙata."


Ta ƙoƙarta shanye hawayenta daga nan. Tana tunanin duk maraici ne ya ja mata hakan. Inda iyayenta suna raye shi har ya isa ya wulaƙanta ta haka? Ya ma isa ya kalli idanuwanta ya faɗa mata wannan maganganun?


Gyaɗa kanta ta yi, cikin fushi ta ce,


"Kana cin arziƙin Modu ga shi nan. Wallahi dan dai kana kula da shi ne, da tuni na hwaɗi ma maganar da har ka mutu ba za ka taɓa mantawa da ni ba."


Cikin halin ko in kula ya murmusa, shi kam da alama dai ranshi ba ya ɓaci. Sai ya gama guma wa mutum, sai kuma ya dawo yana dariya. Sam! Bai da damuwa. Wanda ma ya biye shi shi ke cikin matsala, dan shi kam zai ɓata maka rai amma bai san ya yi ba.


"Abinci kam na riga da na yi magana, na tabbata ba da daɗewar nan ba kina ganin an kawo mai na dare. Magani kuma tunda kin ce ke ba matsiyaciya ce ba do Allah dai a ƙoƙarta saye nai yau."


Ya ƙarisa maganar yana dariya ya bar ɗakin.


Wurin zama ta nema ta zauna tana kuka sosai. Duk da ta san ba ta da hanyar siyan maganin, ta gwammaci hakan a kan ta zauna Dr. Huzaif yana cin mutuncinta.


Bayan kamar minti talatin sai ga wani matashi tafe ɗakin, hannunshi riƙe da robar take away.


Gaishe da Fiddou ya yi ta amsa. Ya miƙa mata ledar abincin cikin girmamawa ya bar ɗakin.


***


Tun bayan dawowarta daga islamiyya take tunanin mafita. Ta ma rasa ta hanyar da za ta ɓullowa lamarin. Ya za ta yi Mama ta amince da buƙatarta? Shin ta wace hanya ma za ta bi wurin faɗa mata taimakon da take son yi? Allah Ya sani, tana son taimakon bawan Allah. Tana son tabbatar da zarginta; na kasantuwar wani bawan Allah mai kama ɗaya da Annur. Tabbas ba za ta iya tabbatar da zarginta ba, har sai ta haɗu da wancan ɗin, sannan.


Rashin samun mafita ya sa ta kiran Jiddah a waya. Babu ɓata lokaci Jiddah ta ɗauka, a nan Maryama ke sanar da ita duk yanda suka yi da Hadiza. Ta ƙare da faɗin,


"Na samu na shawo kanta har za ta taimaka da kuɗi, amma ni ban san ta inda zan ɓullowa Mama da maganar ba. Na sani, kuɗi ba matsala ba ne, saboda Abba yana so ma ya ji wani mabuƙaci, don ya taimaka masa. Samun damar tafiyar dai ita ce matsala."


Shiru suka yi su duka biyun, Jiddah na tunanin shawarar da za ta ba ƙawarta, Maryama kuma zullumi kawai take, kar lokaci ya ƙure mata har iyayen nata su kwanta, kuma ga shi gobe take son tabbatar ma Hadiza da tafiyarsu jibi litinin.


Bayan shiru na wani lokaci da suka yi, Jiddah ta ce,


"Ga shawara..."


Ta ci gaba da tsara mata zance ƙasa ƙasa, wanda duk ƙwaƙwaf ɗin mutum ba lallai ya ji me suke faɗi ba.


Bayan Jiddah ta gama maganar Maryama ta saki lallausan murmushi wanda sai da haƙoranta suka bayyana. Shi ya sa take son Jiddah, take kuma alfahari da ita. Yana da wuya a wannan zamanin ka samu ƙawa irin Jiddah; wacce za ta so ki saboda Allah, ta mayar da damuwar ki tamkar tata, ta ƙaunace ki tamkar ke ɗin jininta ce.


"Na tabbata idan na faɗi haka su Mama za su amince. Allah Ya ga zuciyata, taimako nake son yi. Zan kuma roƙe sa gafara, insha Allahu Zai gafarta min."


Jiddah ta ce,


"Da yardar Allah kuwa. Ki tafi yanzu, kar ki ɓata lokaci dan Allah. Ki yi duk yanda na ce miki, kar ki nuna wata alama ta rashin gaskiya, wadda za ta sa a gano ki. Allah na tare da mu, kuma Shi Zai taimaka mana da ƙarfin mulkinSa."


Da wanann ƙwarin guiwar da Jiddah ta ba ta suka yi sallama. Ta miƙe bisa takunta, cikin tafiyarta ta rashin kuzari ta doshi hanyar falo.


A yi haƙuri da wannan.


Da gaske fa dramar Dr. Huzaif da Fiddou na ba ni dariya yasin. Wato dai Dr. Huzaif tsokanar faɗa, Fiddou kuma saurin ɗaukar zafi.😁😂


Maman labyb ina yin ki, ina son ki, ina kuma ƙaunarki fisabilillah👐


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:53 PM] Princess Amrah✍🏻💞: 🅰MRAH NAKE SO!♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)


4⃣2⃣


Follow me on wattpad: PrincessAmrah


***


Zazzaune ta tarar da Mama da Abba, sai Muhammad zaune daga gefe yana game da ipad ɗinsa.


Ƙarisowa ta yi ta zauna a ƙasa, murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce,


"Sannunku da hutawa Abba."


Da fara'a shi ma mahaifin nata ya ce,


"Yauwa Maryama sarauniyar mata. Yanzu ko muke maganar saukar ku."


Mama ta karɓe da,


"Invitation cards ɗin duka an bugo, kin gan su can ajiye a tv stand. Idan akwai wanda za ki kai ma, sai ki ɗiba ki kai gobe. Akwai wani abu kuma da kike so?"


Hannunta ta ɗora a gefen goshinta alamar tunani, ta ce,


"Mama an canza kalar hijab ɗin anko, wai ya yi shige da uniform ɗin wata islamiyya. To da dai wasu sun ce kar a canza, saboda ƙurewar lokaci, mafi rinjaye dai sun tsaya a kan a canza ɗin. A taƙaice dai an canza shi yanzu haka."


Mama ta ce,


"Babu damuwa. Sai kuma me?"


"Uhm...ban san ko ya ake ciki ba wurin masu buga takardun nan."


"Yanzun nan Abbanku ya kira Shamsu, an gama jotters da tissues, biro ce kawai ba a gama ba, amma wai aikinta kaɗan ne, cikin daren nan za su ƙarƙare komai, gobe da safe a je a karɓa."


Maryama ta yi murmushi mai nuna zallar farin ciki, ta ce,


"Lallai sun cika alƙawari ko."


Mama ta ce,


"Gaskiya kam. Dama gobe muka yi da su."


Dariya Abba ya yi, ya gyaɗa kansa ya ce,


"Kuna da aiki. Ku da ba a je an tabbatar sun yi ko ba su yi ɗin ba ne har kun fara faɗin suna da cika alƙawari. To ba girin girin ba dai..."


Mama ma murmushin ta yi, ta ce,


"Kuma fa haka ne. Amma dai na tabbata za su cika alƙawari, da yardar Allah. Shi kenan abin da kike so?"


Ƙoƙarin danne rashin gaskiyarta ta yi, da ƙyar ta haɗiyi yawu, ta zaƙulo magana daga ƙasan maƙoshinta,


"Mama dama ina son sanar da ke wani abu, taimakon da nake son na yi."


Ta dakata daga nan, tana son jin martanin Maman tata, kafin ta shiga cikin zancen kai tsaye.


"Wane irin taimako kike son yi, Maryama? Allah sa dai lafiya."


Shiru ta ɗan yi na wani lokaci, kafin ta zaro magana daga can cikin maƙoshinta, muryarta can ƙasa, tana son yin maganar yadda za ta tabbatarwa Abba da Mama iyakar gaskiyarta.


"Uhm...dama akwai wata ƙungiya da nake, ƙungiya ce ta taimakon al'ummar musulmai, maza da mata. Ana bin duk asibitoci domin duba wanda ba su da lafiya, a ba su tallafi, a taimaki duk wani mai buƙatar taimako."


Ta ɗan jinjina maganar da za ta yi a gaba, kafin ta ɗora da,


"Tunda ake yi ban taɓa zuwa ba, sai dai ina bayar da gudummowa daga nan inda nake. Sau tari idan na karɓi kuɗi daga wurin Abba, transfer ɗinsu nake kai tsaye zuwa ga account ɗin shugaban foundation ɗin. To kuma yanzu wata tafiya ta taso, Maraɗi za a je, mun ji labari cewa wai asibitocinsu na gwamnati suna da buƙatar taimako, shi ya sa aka yanke shawarar kai musu ziyara, mu taimaka musu."


Tana rutsewa ta guntse bakinta, tana sauraren martanin Mama, dan ta san halinta sarai, ita ɗin ba ta son wargi.


Daga can ta tsinkayo muryar Abba, ya ce,


"Banda abinki Marayama, ina ke ina shiga irin wannan foundations ɗin? Ba wai na ce shigarsu tana da aibu ba, sai dai sam! Bai kamace ki shiga a yanzu ba, yanzu da kike kan yin karatunki. Ina laifin dai ki bari ki gama, gudun rabuwar hankalinki?"


Shiru ta yi tana saurarensa, ya ci gaba da,


"Kuma ai ba mutuncinki ba ne tafiya har Nijar, ba tare da iyayenki ko wani na ki ba. Ki dai sake duba wannan lamarin."


A fusace Mama ta ce,


"Har ma sai ka tsaya kana mata lallaɓi? Ita ai ta sani, ta san daidai, ta kuma san bana son wannan shirmen. Ni ai Maryama ban ma san sanda kika fara yin wani abu, ba tare da kin faɗa min, ko kin nemi shawarata ba. Kuma ki gaggauta fita daga ƙungiyar, tun ban ɓata miki rai ba."


Hawaye ta ji suna bin kumatunta. Ta ma kasa furta komai, kanta sunkuye a ƙasa. Ji ta yi Abba ya ce,


"Zan miki transfer na 10k yanzu, sai ki tura musu, ki ba su haƙuri kan cewa ba za ki samu damar zuwa ba."


"To Abba, na gode."


Tana gama faɗin haka kawai ta tashi da saurinta ta bar falon, ta nufi nata ɗakin.


Gadonta ta haye tana kuka sosai, dama jikinta ya ba ta, sai da ta yi wannan tunanin. Amma yanzu ita ya za ta yi? Me za ta faɗawa Hadiza? Har ga Allah tana son taimakon bawan Allah'n, ta na matuƙar son ta gan shi.


Tunani ta fara a ranta; sun yi plan ɗin farko ya lalace, babu nasara. To ga shi wannan ma tun ba a je ko'ina ba ya lalace. Ko dai ƙaryar da take ma iyayenta ne? Akwai fa alamar tambaya a wannan lamarin. Tunda take a rayuwarta, ba ta taɓa ɓoyewa mahaifiyarta wani abu ba, sai daga fara case ɗin nan. Ko dai hakan ne ke bibiyarta, ya sa suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login