Showing 135001 words to 138000 words out of 201092 words

Chapter 46 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

yin irin wannan maganar ba, sai dai mai cikakken hankali.


"Na tsince shi ne ya galabaita sosai, yana matuƙar jin ƙishi. Sai na fiddo da gorar ruwa daga motata na ba shi. A nan nake tambayarshi waye shi? Kuma ina zai je? Shi ne yake ce min shi ma bai san inda zai je ba. Bai ma san ta yadda akai ya baro gidansu ba. Na tambaye shi ko zai iya gane gidan nasu? Ya amsa min da ehh. Na samu da ƙyar motata ta tashi, ashe kan batir ne ya goce. A hankali muka taho yake gwada min, har muka iso nan."


Kukan farin ciki Momy ta fasa da ƙarfi.


"Annur ɗina hakan na nufin ka warke kenan?"


Kanshi ya ɗaga alamar ehh. Sannan ya ƙara da faɗin,


"Da gaske ne Amrah ta rasu?"


"Amrarka ta rasu Annur. Ta rasu a daidai lokacin da ya rage satika kaɗan a ɗaura muku aure."


Sai yanzu ya fahimci ko ita ɗin wacece a rayuwar Annur. Sai ya ce,


"Ina matuƙar ƙaunar Amrah. Na so a ce ta ci gaba da rayuwa, mu gina rayuwarmu tare. Amma Allah bai nufa ba. Ashe dai mutuwa za ta mana yankan ƙauna, za ta raba jini da hanta."


Cikin tausayawa Dady ya ce,


"Ka yi tawakkali Annur. Ka ga irin haka ne fa ya sa ka samu matsalar ƙwalwa. Amma ga shi fitar da ka yi ɗin ma ta zame mana alkhairi baki ɗaya, tunda ga shi da alama ƙwalwarka ta zama normal. Ko ka faɗi ka bige kanka ne?"


"Ni ma ban sani ba."


Sans ya faɗa a hankali.


*


Washe gari da sassafe Bobby ya tafi ƙauyen Jani wurin boka, kamar yadda ya ma Sans alƙawari. Boka ya yi murmushi, ya ce,


"Aikin kurciya na ɗaya daga cikin sauƙaƙƙun ayyukan da muke yi a nan. Saboda haka wannan ba wani babban aiki ba ne."


Ya yi wani irin tsafi, sai ga kurciya mai kalar baƙi da fari ta ɓullo a gabanshi, idanuwanta jajaye, ta tsura su a fuskar boka Gagarabada, tana kallonshi ƙyam.


***


Tunda ta kwanta take juyi. Sam! Barci ya gagara ɗaukarta. Tunanin rayuwa kawai take. Tunanin yadda komai ke faruwa tamkar a mafarki take yi. Wai aure za a mata a cikin ƴan kwanakin nan? Ita exam ɗin da za ta fara ma take ji, tana buƙatar samun nutsuwa sosai ta yi karatu, tunda second semester exams ce, wacce daga ita za ta shiga level 3.


Wani tunani ne ya faɗo mata, hakan ya sa ta lalubo wayarta daga jikin chaji, ta latso kiran Jiddah. Ba ta yi tsammanin za ta ɗauka ba, lura da yadda dare ya tsala, ana neman ƙarfe ɗaya na dare ne fa yanzu.


Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan Jiddah ta ɗauka, cikin magagin barci ta ce,


"Maryam lafiya?"


"Ba lafiya ba Jiddah."


Maryama ta faɗa, a daidai sadda kuka ke zo mata.


Tashi zaune ta yi Jiddah. Ta murje idanuwanta, haɗe da daidaita muryarta, ta ce


"Me ya faru kike kuka Maryama? Ko jikin Yaa Noor ɗin ne ya tashi?"


Maryama ta share hawayenta, wani na shirin sauko mata ta ce,


"Ko kaɗan ba jikinsa ba ne ba, Jiddah."


"To mene ne?"


"Akwai abubuwan da suka faru ne..."


Maryama ta kwashe komai ta sanar wa Jiddah. A ƙarshe ta ce,


"Yanzu dai an tsaya a kan cewa za ki haɗa ni da kawun Annur, zan fayyace mishi komai, sannan a ƙarshe in haɗa shi da kawu Imrana, su yi magana. Wai ba za a saka Abba yin kaffara ba. Yadda ya rantse cewa aure zai min a cikin ɗan taƙin nan, to dole auren zai min, idan ba haka ba kuma zai haɗa ni da duk wanda yake so."


Cike da tausayi Jiddah ta ce,


"To ke Maryama me ya ja miki zaɓar mahaukaci a matsayin wanda za ki aura? Yanzu idan aka ɗaura muku auren, sai ya warke, ba kya tunanin zai guje ki? Ba kya ga kamar zai ce ba ya son ki? Maryama wallahi tsaf zai iya rabuwa da ke, tunda dai ba saninki ya yi ba. Bai kamata ki yanke wannan ɗanyen hukuncin ba. Ai da ki auri mahaukacin ma gwara ki auri Yah Deedah ɗin ma. Yanzu ina alƙawarin da kika ma Fiddou, kan cewa Annur zai koma gare ta ya aure ta?"


Dafe kanta ta yi Maryama. Sosai take jin haushin kalaman Jiddah, daurewa kawai take.


"Ba ma wannan ba, ni yanzu ina na wani san Kawun Annur? Ina ma na san yana da kawun ko bai da shi? Ni dai kawai na faɗa miki cewa Mamina ƙawar Momyn su Annur ɗin ce."


"To ai a hakan za ki iya binciko mana komai Jiddah. Ke kaɗai ce za ki iya yi min wannan taimakon Jiddah, da ke kaɗai na dogara, you are my only hope, Jiddah. Ki rufa min asiri don Allah gobe mu haɗu, duk ma yadda za a yi a yi."


Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke. Sosai take jin tausayin ƙawar tata. Sai dai kuma gani take kamar zaɓin da ta yi bai kamata ba. Amma babu komai, za ta taimaka mata iya ƙarfinta, domin fitar da ita daga wannan ƙangin da ta faɗa.


"Shi kenan Maryam. Allah ya kai mu goben. Insha Allahu da safe zan ma Mami maganar, cikin dabara zan binciki dangin mahafin nashi. Komai kenan zan kira ki na sanar miki."


Da sauri Maryama ta ce,


"A'a Jiddah. Kar ki ma Mami ƙarya. Ni yanzu na san illar yi ma iyaye ƙarya Jiddah. Ki faɗa mata gaskiya, wata ƙila ita ɗin ma akwai wani taimako da za ta iya yi mana."


Jiddah ta ce,


"To shi kenan. Insha Allahu zan faɗa mata gaskiya. Amma don Allah Maryam ki kwantar da hankalinki. Wannan kukan da kike yi ki daina shi. Dukkanin abin da ya yi tsanani to yana tare da sauƙi. Da yardar Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe. Wannan damuwar da kike ciki dukkaninta za ta koma farin ciki."


"To Allah Ya tabbatar mana da hakan Jiddah. Na gode ƙwarai, Allah saka miki da alkhairi. Sai da safe."


"Ameen Maryam. Sai kin ji ni."


Suka kashe wayoyin, kowacce da tunanin da take yi a cikin zuciyarta.


Samun kanta ta yi da samun nutsuwa sosai a cikin zuciyarta. Bayan ta miyar da wayarta a jikin chaji ta miƙe, ta nufi ban-ɗaki domin gabatar da alwalla, ta yi ƙiyamul-laili, ta sanar wa Allah damuwarta, da neman agaji a wurinSa.




*


Washe gari da sassafe Maryama ta tashi. Sosai take jin dukkanin nutsuwarta da ta rasa tana dawo mata. Sassauci take ji sosai a cikin zuciyarta.


Sauka ta yi daga bisa gadonta. Ta cire hijabin da ke jikinta, sannan ta nufi hanyar barin ɗakin, ta doshi kitchen.


Dankalin turawa ta hau ferewa. Bayan ta gama ta kama aikin suyarshi, ta jajjaga tarugu da albasa da maggi, sannan ta fasa ƙwai ta ma Abbanta sauce ɗin ƙwai.


Sai da ta gama duka sannan Mama ta shigo Kitchen ɗin. A tsammanin Maryama Mama ba za ta kula ta ba. Sai dai kuma ta ga akasin hakan. Da murmushi Mama ta ce da ita,


"Sannu da ƙoƙari. Yau barci ya so ya ƙwace min wallahi. Allah dai ya sa kin tashi Hammad daga barci."


Dafe kanta ta yi Maryama.


"Shaf na manta Mama. Bara na hanzarta to. Har bakwai ta wuce."


Da saurinta ta nufi ɗakin Mama, inda Muhammad ke kwana shi kaɗai.


A zaune ta same shi. Ya ɗora tafin hannunsa na dama a bisa haɓarshi, ya yi zurfi a tunani.





Tsaye ta yi tana ƙare masa kallo. Ta rasa abin da yake tunani. Ba ta farga ba ta ga ya kuma juyawa, ya koma ya yi kwanciyar rigingine a bisa gadon ya ƙura ma wuri ɗaya kallo, hannayensa ya tallabe ƙeyarshi da su.





Take Maryama ta ji hankalinta ya tashi. Jiki saɓule ta iso gare shi. Ta saka hannunta na dama tana bubbuga shi.


"Tunanin me kake haka Hammad?"


Ta nemi wuri ta zauna.


Sai a sannan ya ji ƙwalla ya zubo masa. Cikin muryar kuka ya ce,


"Yaya Maryama ina tunanin rabuwa da ke ne. Wai yanzu shi kenan aure za ki yi ki bar ni? Tafiya za ki yi ki bar ni Yaya? Zan yi kewar ki sosai."


Hawaye ya gama wanke mishi fuska.


Hannunshi na dama ta kama ta riƙe. Cikin kwantar masa da hankali ta ce,


"Ba na son ganin hawayenka ƙanina. Ka share su please. Don an ce za a min aure ai hakan ba wai yana nufin na bar ka ba kenan. Sannan kuma yanzu ko an yi auren ma ai a nan gidan za mu ci gaba da zama, har sai sadda Annur ya samu lafiya. So, ka kwantar da hankalinka. Okay?"


Kai ya ɗaga mata kawai, ba tare da ya furta komai ba.


"Then, stand up and act like a man, not a boy. Its already time for school. Hurry up and get ready for going to school."


Cike da jarumta ya miƙe, ya nufi ban-ɗaki domin shirin makaranta.


Gyaɗa kanta ta yi Maryama, tana jin tausayi haɗe da soyayyar ƙaninta na daɗa shiga duk wata kusurwa da take cikin zuciyarta.


Bayan fitar ta ta samu babu kowa a falon, ta leƙa kitchen babu Mama, hakan ya sa ta nufar ɗakin Abba, tana jin zuciyarta na bugawa sosai, tunanin abin da za ta tarar daga wurin Abbanta. Zai kula ta ko ba zai kula ta ba?.


"Mama na duba ban gan ki ba."


Ta faɗa bayan ta duƙa har ƙasa, ta ce,


"Barka da tashi Abba."


"Yauwa."


Ya faɗa ƙasa-ƙasa.


"Ina kwana?"


"Lafiya."


Duk da yanayin yadda ya amsa mata gaisuwar, hakan bai hana ta samun sassauci a zuciyarta ba. Sosai ta ji daɗi, ta kuma tabbatar cewa ya rage jin haushinta, da alama Kawu Imrana ya roƙa mata gafara a wurin shi.


"Kin tashi Hammad ɗin dai ko?"


"Ehh Mama. Na tashe shi. Ya shiga wanka ma na baro ɗakin"


Ta ƙarisa da fita ta bar ɗakin.


Kai tsaye daga nan ɗakin Annur ta nufa. Fuskarta cike da fara'a. Zuciyarta na tsananta ƙaunarshi. Duk wata gaɓa ta jikinta tana jin yadda jijiyoyi da jininsu ke yawo da soyayyar Annur.


***


*How y'all? I hope you're all fine. Ban ma san me zan faɗa ba. Bakina ya gagara furta komai. Zuciyata na cike da ƙaunarku. Hannuwana na cike da son rubuta sunan nan. RAZ NOVELLA 1. Ina yin ku, ina ƙaunarku, ina muku soyayya ta fisabilillah. Haƙiƙa na matuƙar jin daɗin comments ɗinku na jiya. Na yi farin ciki fiye da tunaninku. Ina fatar ɗorewar hakan, ba wai a kaina kaɗai ba, ga kowa ma.*


*Masu mutunci ba sai na ce komai ba. Kun san me ya dace, I know.*


Team Marnoor
Team ANS
Team Princess Amrah
Team NWA


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/10, 7:30 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣0⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Runtse idanuwansa ya yi boka Gagarabadau. A hankali ya buɗe su, ya sauke a saman kurciyar. Take nashi idanuwan ma suka rikiɗe, sukai jajur, tamkar jan gaushi.


Kallonshi take yi sosai kurciyar, a hankali idanuwanta na komawa normal, kamar na kowacce irin kurciya.





Haɗe dukkanin tafukan hannayenshi ya yi, ya kanga su a saman fuskarshi, ya rinƙa ambaton wasu irin kalamai, wanda shi kaɗai ya bar ma kanshi saninsu. Sai dai kawai yana ambatar Salman Sans, a cikin yaren nashi, sannan kuma sunan Annur ya biyo baya.


A hankali kurciyar ta rinƙa tasowa sama, har ta iso a daidai saitin fuskar bokan, sannan ta dakata a saman iska.


Ciro hannuwan nashi daga jikin fuskarsa ya yi. Sai ga wata irin ƙatuwar laya ta fito, ya saƙalo zarenta a jikin wuyan kurciyar, sanann ya sake yi mata wani tsafi. Jinin da ke cikin ƙwaryarsa ya ringa ɗiba yana watsa mata, a hankali ta rinƙa yin sama, har ta ɓula rufin ɗakin ta fice, sanann ya daina watsa mata ruwan.


Murmushi ya saki mai ƙarfin gaske. Ya ce,


"Ta tafi kenan, har abada. Ka ga yadda ta tashi sama, haka za ta ci gaba da tafiya, ba za ta tsaya ba har sai ta fice daga ƙasar nan, koma dai ina ne. To a duk inda ta dakata, a nan wanann mahaukacin zai dakata shi ma. Kamar yadda za ta ci gaba da rayuwa a wurin, shi ma a haka zai ci gaba da rayuwa a wurin. Duk ranar da ta tafi, shi ɗin ma zai tafi. Abu guda ɗaya ne tal zai iya dawo da shi garin nan. Shi ne a samu wani wanda zai cire layar nan daga wuyan waccan kurciyar, to lallai daga sannan zai iya dawowa garin nan, koma ta wacce hanya ce."


Ajiyar zuciya ya sauke Bobby. Yana mai fahimtar dukkanin bayanan bokan.


Akwai dokoki sosai na wannan aikin. Sai dai kuma ba wasu masu tsauri ba ne. Doka ta farko, babu soyayyar gaskiya (True love). Daga sadda ya aikata haka, lallai za a iya samun matsala da wannan aikin, komai zai iya lalacewa. Abu na biyu, zai samu karuwa, ina nufin mace mai zaman kanta, wacce zai rinƙa aikata zina da ita, na tsawon lokuta. Ina mai tabbatar maka da cewa, matuƙar ya tsaida dokokin nan, ya aikata komai yadda ya kamata, to zai dauwama a gidan. Rayuwarsa da komai za su koma ƙarƙashin mutanen, ba tare da kowa ya fahimta ba. Fatar kana fahimta."


Kanshi ya ɗaga da sauri Bobby, ya ce,


"Na fahimci komai Boka Gagarabadau."


"Da kyau. Sai ka ɗauki ƙwaryar nan ka sha jini a madadin abokin naka. Ka ajje abin da za ka aje."


Bayan ya ɗauki ƙwaryar ya kwankwaɗi jini, ya zaro kuɗi daga aljihunshi, ya ajje a gaban bokan. Sai da ya masa kirari sosai, sannan ya tashi ya tafi.


Annur da ke zaune ya takure jikinshi, ya ɗora tafukan hannayenshi a bisa fuskar, yana sanye da wata baƙar T-shirt wadda Sans ya umurci Yax ya saka mishi.





Ji ya yi kamar wani abu ya daki zuciyarsa da ƙarfi. Bai san sadda ya miƙe tsaye ba. Ya fara waige-waigen gaba da bayanshi. Bai ga kowa ba, hakan ya sa ya gaggauta barin ɗakin da sauri, ya isa falo.


Yax da Esien a zaune suna fira, suna ganinshi suka mimmiƙe da mamaki, Yax na faɗin,


"Me ka fito yi?"


Bai ko damu da su ba bare su sa ran zai amsa musu tambayarsu. Da iya ƙarfinsa ya bangaje Esien da ya matso daf da shi. Ya gaggauta isa bakin ƙofar, ya buɗe ta.


Haka ya rinƙa tafiya da sauri da sauri, babu waiwaye haka kuma bai damu da kallon gabanshi ba, har ya fita titi. Tafiya ya yi sosai, sai dai idan ya gaji ya nemi wuri ya zauna ya huta, har duhu ya fara yi. A lokacin ya isa wani ƙauye ne, a bakin wata bishiya ya zauna hutun, bai ankara ba barci ya ɗauke shi. Shi ne bai farka ba sai da safe, kamar wanda ake tsikara ya miƙe, bai damu da yaran da suka zuba mishi ido suna kallo ba, ya ci gaba da zura sauri, har ya fice daga ƙauyen.


Da haka da haka har Annur ya isa Maraɗi, inda ya ɗauki kusan kwanaki huɗu yana tafiya a hanya, kafin ya isa Maraɗin. Saboda dama daga Katsina zuwa Maraɗi ba wata tafiya mai tsayi ba ce. Sadda ya isa boarder, ƴan sandansu na can sun so su dakatar da shi, amma wani daga cikinsu ya ce su bar shi, tunda dai ba shi da hankali.


Wannan dalilin ne ya sa rayuwar Annur ta koma Maraɗi. A ranar da ya isa ya haɗu da Fiddou, wacce ta taimake shi, ta ba shi dukkanin gata, tamkar dama can ta san shi.


*


Tun bayan da boka ya gama aiki, iyayen Annur suka samu kansu da samun nutsuwa sosai, dangane da Sans. Ko kaɗan babu wanda ya taɓa tunanin cewa ba Annur ɗinsu ba ne, duk kuwa da cewa ba duka abu ba ne za a ce iri ɗaya da Annur ɗin, dole za a samu bambanci komai ƙanƙantarsa. Sai dai kuma asiri ne ya ci su, ya ci dukkanin wani makusancinsu. Abokanan Annur baki ɗaya wanda suka zo yi mishi jaje, Sans ya wulaƙanta su, ya ci mutuncinsu, sannan kuma ya musu korar kare.


Muguwar rayuwarshi ta shaye-shaye da bin mata ta ta'azzara. Baki ɗaya zuciyarsa ta gama ƙeƙashewa, ta bushe, babu tsoron Allah ko kaɗan a cikinta.


A lokacin ne kuma Bobby ya gabatar da Annur a gidansu, cewa ga babban abokinshi, sun haɗu ne ta dalilin wani biki da suka yi. A take iyayenshi suka aminta da Sans, saboda asali sun san Pharm. IA. Sun san cewa mutumin kirki ne. Haka kuma yaransa na da tarbiyya sosai.


Akai-akai ya rinƙa ziyartar likita, domin tabbatuwar lafiyar ƙafarsa, kuma ya yi nasara, ƙafar ta gyaru sosai, sai dai ƴan lokuta da ciwon yake ɗan taso mishi.


Maganar aikinsa kuwa dole ya bar shi, saboda shi kam bai iya zane ba. Ko sadda suka koma wurin boka, sai dai bokan ya ce ya haƙura da zanen kawai, ya rungumi kowanne irin matsayi aka ba shi a kamfanin. Wannan dalilin ne ya sa ya bar zane. Ya zama CEO na kamfanin ƙere-ƙeren ƙarafan Pharm IA, aka nemi wani mai zanen daban.


*


Bayan wasu lokuta.


Wasu mutane ne zaune a majalissa, sai fira suke a tsakaninsu, suna maida yadda akai.


Kamar wasa suka ga wata kurciya ta faɗo ƙasa a inda suke, da laya maƙale a wuyanta.


Wani daga cikinsu ya ce,


"Ilu ji ikon Allah. Kurciya ce ga ta nan maƙale da laya a wuyanta."


Wanda aka kira da Ilu ya ce,


"Hala ma wani ne akai ma tsahi, aka korai daga garinsu. Wayyo Allah! Ke duniya, ina za ki tahi da mu?"


Wani dattijo da ke zaune gefe ya ce,


"Aikam cire ta nikai yanzu, babu ko ɓata lokaci."


"Mallam Rabe mi ruwanka halan? Kai dai ka ƙyale ta, bari ma in tada ta ta tashi, koma ina za ta tai ta tahi."


Mallam Rabe ya ce,


"Kar ka kore ta Ilu. Cire layar nan daga wuyar kurciya ga ta, tamkar jihadi ne, mai matuƙar girma. Allah kaɗai ya san ladar da za mu samu, idan har wanda akai ma ita ya koma ga dangi nai."


Kai suka jinjina su duka, alamun sun gamsu da zancen Mallam Rabe.


Da sanɗo da dabara ya lallaɓa ya cafke kurciyar, tana ta ƙoƙarin zille mishi, amma ya riƙe ta tam! Bai sake ta ba, har sai da ya cire

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login