Showing 66001 words to 69000 words out of 201092 words
Chapter 23 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
Abdul-Ahad da ita."
Dariya sosai Maryama ta kece da ita. Da gaske Muhammad ya bata dariya. Wato shi ya rasa ma abin da zai kai wa Abdul tsaraba sai soyayyar doya, wadda ta riga da ta gama hucewa.
"Nawawo for this boy. Kai yanzu fi sabilillahi wannan doyar ce zaka kai ma ƙaninka tsaraba?"
Matsowa ya yi kusa da ita yana murmushi.
"To Yaya Maryama ai ya fi na je masa haka nan ko? Amma idan na kai masa doyar nan na tabbata zai ji daɗinta."
Su dukansu dariya suke a wannan gaɓar, har shi kanshi Muhammad ɗin dariyar yake.
Miƙewa ta yi za ta ɗauko kalacinta ta ji wayarta na ringing. Aunty Islam ta gani a rubuce, hakan ya sa ta koma ta ɗauki kiran da sallama a bakinta.
Kusan mintinsu biyu suna waya, kafin ta juyo ga Mama ta ce,
"Wai a gidansu zamu same su. An fara yi masu aikin gida ne yau, tun jiya da dare mijin ya ce kawai ta je can gida. Har kira na ma ta yi da wata lamba a cikin daren ban ɗauka ba. Ga shi nan za ta turo min address yanzu."
Mama ta ce,
"To ba damuwa ai. Sai ki hanzarta, na tabbata yanzu za ku ga Mallam Ado ya zo ɗaukar ku."
Kitchen ta nufa ta zubo doya a plate, sannan ta ɗauko lemon 5 alive haɗe da cup a hannunta.
Zama ta yi tana ci a hankali, fiye da rabin tunaninta yana ga abin da ya faru yanzu. Ta na son kiran Jiddah ta sanar da ita komai, sai dai kuma yanzu babu lokaci, dole sai idan sun dawo.
Ba ta gama ci ba Mallam Ado ya yi sallama. Yana Shaida masu cewa ya iso, su same sa a waje.
Tashi ta yi ta mayar da kayan kitchen, sannan ta shiga ɗaki ta yafa mayafinta ta fesa body spray ta fito.
Bankwana su ka yi wa Mama, sannan su ka fice daga gidan, zuciyar Muhammad sayau take, yana tsananin jin daɗin ziyarar da za su kai ma Abdul.
***
Annur kuwa tun da sassafe ya shirya cikin ƙananan kaya ya fita, ko sallama bai tsaya ya yi ma Momy ba kawai ya kama hanyar gidan su Farouk Sardauna.
Kiran Bobby ɗin ya yi a waya, bai ko tsaya ya ɗauka ba ya fito, dan ya san dalilin kiran nasa.
Buɗe motar ya yi ya zauna a gaba sannan ya rufe. Ya kalli yanayin abokin nasa, yanda duk ya bi ya susuce a cikin ƙanƙanin lokaci.
"Annur wannan fa damuwar da ka saka kanka a ciki sam! Ba ita ce mafita ba. Dolenka ka zama jarumi, ka ƙoƙarta mayar da komai ba komai ba, sannan walwalarka za ta dawo. Amma idan kana cikin wannan halin, ba ka tsammanin su Momy za su iya fahimtar wani abu? Lallai dole za su fahimta."
Duk da tuƙi yake amma hakan bai hana shi kallon Bobby ba. Ɗan lumshe idanuwansa ya yi, sannan ya mayar da kallon na shi ga tuƙinsa, ya ce,
"Duk yanda zan yi dan ganin na kawar da wannan damuwar na kasa. Haka kawai nake jin gabana na faɗuwa, kamar komai ya kusa dagule wa. Ina fargabar haɗuwarmu da boka, dan ba ni da hujjar da zan kare kaina a wurinsa."
Ajiyar zuciya ya sauke Bobby, a tsanake ya ce,
"Haka ne. Amma kuma ai dole ya maka uzuri. Shi kansa da yake aiki da tsafi tun farko ya ce yarinyar ta gagae shi, bare kuma kai da ba ka taki komai ba?"
"Haka ne Farouk. Maryama kam ta yi nisa ba ta jin kira. Ta riƙa sosai a ibada, ban kuma ga abin da zai iya dakatar da ita ba."
"Ina ga kawai abin da ya kamata, idan da yanda zai yi ya canza salon aikin baki ɗaya sai ya taimaka mana. Wannan dokar ta true love gaskiya dole a karya ta, saboda fa zuciya ba ta da ƙashi. Ba ka isa ka tanƙwara ta a kan abin da ta gani tana so ba."
Da wannan firarrakin suka isa wurin bokan. Kai tsaye suka zarce tare da aikata duk yanda su ka saba idan sun je wurinsa.
Zama suka yi a ƙasa, Bobby ya masa kirari sai ga shi ya ɓullo, yana kallonsu su duka biyun.
Murmushi ya saki da ƙarfin gaske. Ya dunƙule hannuwansa duka biyun sannan ya buɗe su.
"Ka yi aiki mai kyau, ban taɓa tsammanin yiuwar aikin nan ba. Daga farko na ji haushinka sosai, saboda wahalar da ka ba ni, kuma a banza. Sai dai na daure a ƙarshe, sai ga shi kuma mun yi nasara."
Ido buɗe suka kalli junansu, suna matuƙar mamakin kalamansa. Su da su ka yi zaton zai balbale su da masifa, amma sai su ka ji akasin hakan, hasali ma yabo ne ya fito daga bakinsa.
Page din nan ya ba ni wahala. Sai da na rubuta fiye da rabi ya goge😭 da ƙyar na samu maimaita shi. Amma duk da hakan dai ya sha banban da na farkon.
Thanks my fans, ina jin daɗin yanda kuke bibiyata.
Saƙon ta'aziyya ga masoya Irfan. Ina mai taya mu jaje na rashin jarumin labarin MH da mu ka yi😧 na sha kuka kamar ba gobe, har nake jin mutuwar kamar da gaske ne ta faru. Sai dai kuma ba abun mamaki ba ne, saboda mutuwa ko kalmarta kawai ka ji wani tashin hankalin ne. Fatanmu dai Allah Ya sa mu yi kyakkyawan ƴarshe, ya kyautata makwancinmu.
Ina jajen ƙawata XARAH BB. Ban san ina kika shige ba, ta yiu kuma ɗan Baba ne ya ɓoye mana ke.😂 Allah Ya bada lafiya amin.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:50 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
3⃣6⃣
Assalamu alaikum.
Na samu ƙorafi daga wasu cewa; wai duk karatun da Maryama ta yi kuma sai asiri ya kama ta?
Abin da nake so ku gane shi ne; a duk duniya babu mutum sama da manzon Allah, (SAW). Shi ne mafi daraja, ma fi soyuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki!
Shi ne wanda ya fi kowa ilimi, kuma ya fi kowa aiki da shi.
Shi ne wanda ya fi kowa ibada, kuma yake kiyayewa.
To kuma asiri ya kama shi. Shin mu waye da asiri zai gagara kama mu? Shin Maryama wace iriyar mutum ce, wacce asiri zai gagara kama ta? Kar ku manta, an jima ana ƙoƙarta asirin ya kama ta, amma ya gagara shigarta, saboda kariya.
To lokaci ɗaya kuma Allah Ya jarrabe ta, Ya shagaltar da ita, sam! Ta gagara yin abin da ta saba yi. Kenan dai ba abun mamaki ba ne dan asiri ya kama ta.
Masu wannan tunanin, ku yi haƙuri ku zuba min ido. Ni na san kan labarina, na kuma san yanda ya kamata.
Please and please, ku zuba min ido kawai, ku dai aikinku karatu ne. Ku bari har sanda na kammala, duk mai ƙorafi ƙofa a buɗe take. A daidai lokacin an ga yanda ƙarshensa zai yi kenan.
Fatan za a fahimce ni.
Wanda na ɓata wa ya yi haƙuri.
***
Cikin ɗaga sauti bokan ya ce,
"A yanzu kam an gama komai. Duk wata damuwa ta ka ta ƙare Annur, saboda an samu nasara a kan yarinyar, duka soyayyar da kake mata an fitar, aiki kuwa zai gyaru sosai yanzu."
Murmushi suka saki su duka biyun a tare, duk da ba su san dalilin faruwar hakan ba, sai dai su na ji a jikinsu akwai dalili.
"Ku ajje abin da za ku ajje, ku tafi, an kammala da aikinku. Ina mai tabbatar ma ku da cewa asirinku ba zai taɓa tonuwa ba. Wannan ɓoyayyen al'amarin ba zai taɓa fallasuwa ba."
Kuɗi ya ciro daga aljihunsa Annur, ya dire su a gaban boka, sannan suka miƙe su duka biyun, suka nufi barin gidan.
A mota har rige rigen magana suke, Annur ya ce,
"Ko ta ya wannan aikin ya faru?"
"Tambayar da ke cikin zuciyata kenan. Amma dai wannan ba shi yake gabanmu ba. Fatanmu dai aiki ya yi, kuma ya yi ɗin. Faƙat."
Hannu suka haɗa suka tafa da ƙarfi, duk wanda zai kalle su zai tabbatar da tsantsar farin cikin da suke cikinsa.
***
Tun daga sanda aka ba Fiddou reffer letter take rusar kuka. Tana son zuwa gidansu ko dan a ji daga gare ta, amma kuma ba ta son tafiya ko yaya ta bar Modu. Tun washe garin da suke asibiti ta je gida ta ɗauko kaya, ba ta sake komawa ba. Yayanta dama ya yi tafiya, matsarsa ce kawai, kuma ba ta damu da ita ba bare har ta nemi jin halin da take ciki.
Tagumi ta buga a bisa teburin da take zaune, sai Modu kwance suna jiran likita. Kimanin awarsu biyu kenan a asibitin, sai dai da yake asibitin gwmanati ce, akwai layi sosai, dole sai sun bi har a zo kansu. Ita babban tsoronta ma kar Modu ya farka, dan ba ta san yanda za ta yi da shi ba.
Da haka har aka zo kansu. Irin kujerar ɗaukar marar lafiyar nan ce ta yi magana aka zo da ita, mutum biyu su ka cicciɓa Modu suka zaunar a ciki, sannan su ka tura shi har cikin Ofishin likitan.
Zama ta yi bisa kujera tana fuskantar likitan, damuwa ce danƙare a cikin zuciyarta, tana ƙoƙarta danne hawayen da ke fita daga idanuwanta.
"What's his problem?"
Muryar likitan ta dawo da ita hayyacinta.
Takarda ta miƙa masa, ta ce,
"Mu ne Dr. Huzaif yat turo daga Amana clinic. Ga takarda tai nan."
Karɓa ya yi likitan yana dubanta, ya ce,
"Mi da ba ki shigo ba tun ɗazu? Ai ban san kun iso ba giɗe."
Shiru ta yi bayan ta sadda kanta ƙasa, dan ba ta ji ko kaɗan tana da ra'ayin yin doguwar magana. Damuwar halin da Modu yake ciki kawai ta ishe ta. Ga kuma zullumin abin da zai faru.
"Gado za a ba shi."
Ya faɗa bayan ya ajje takardar bisa teburinsa. Ya ɗauko abin awon zuciya ya ɗora a saitin zuciyar Modu, yana jin yanda ba ta tafiya yanda ya kamata.
"Giɗe na cikin matsala mai girma. Ina gudun kar zuciya tai ta mutu, wato ta tsaya cak!..."
Yana neman ci gaba da magana Fiddou ta dakatar da shi da hannu.
"Halan wane irin likita kake? Mi da ba ka san irin maganar da za ka hwaɗi ma mutane ba? Yanzu idan aka yi gawa biyu hwa? Ba ka gudun maganar da kai yi tana iya tsaida bugun zuciyata? Halan ka san irin darajar da Modu gare shi a cikin zuciyata?"
Kuka sosai ya ci ƙarfinta. Kalaman likitan take ji suna ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Tsoro take kar maganarsa ta tabbata.
"Haba i haƙuri giɗe!"
Ya faɗa yana murmushi, kamar ma bai damu da munanan kalaman da Fiddou ta jefa masa ba.
"Kwantar da hankalinki ke jiya. I'll try my best dan ganin giɗen ga ya samu lahiya. Likitan zuciya nike, na miki alƙawarin ba shi kulawa iya ƙarhina."
Sai a sannan ta ɗan samu sassauci, amma duk da hakan ba ta daina yin kuka ba.
Nurses ya kira cewa su ba Modu ɗaki, kuma Amenity za a ba shi, saboda mutum mai matsalar zuciya ba ya son wurin da za a yawaita hayaniya, ko kuma mai cinkoso da yawa.
Bin bayansu ta yi Fiddou, a daidai wannan lokacin ta daina kukan, sai dai kukan zuci kawai take, wanda da shi ta gwammaci tai ta yin mai ƙarfi.
Gyare yake ɗakin tsaf, su na shiga wani lebourer ya shigo da bed sheet da pillow case, ya shimfiɗa a gadon, sannan aka kwantar da Modu a kai.
Bayan sun bar ɗakin ne aka bar ta daga ita sai Modu. Hakan ya sa ta tashi ta ɗan rufe shi da blanket, sannan ta fara haramar tafiya gida.
Ta Offlishin likita ta fara biyawa, ta shaida masa cewa za ta je gida, idan akwai wani abu da ake buƙata sai a rubuta mata yanzu kafin ta tafi.
Babu komai ya shaida mata. Yanzu jiran farkawarsa kawai yake, saboda akwai abin da yake son ji daga gare shi.
"Dr. Ya na da taɓin hankali hwa. Halan mi za ka ji daga garai?"
Ta faɗa cikin muryar tausayi.
"Duk da haka akwai dabarar da zan ringa yi mai, sannu a hankali za mu yi shaƙuwar da da kai nai zai hwaɗa min damuwa tai."
Shanye kukanta ta yi, ta ce,
"To shi kenan likita. Ina hwatar hakan. Bari in tai."
Har ta juya za ta bar ofishin ta jiyo muryarsa ya ce,
"Ba ki ji ba."
Ta juyo da kallonta gare shi, tana jiran abin da zai faɗa.
"To idan kin tahi kin bar shi shi ɗai, halan wa zai hwaɗi min idan ya tashi?"
Shiru ta ɗan yi jim! Kafin ta ce,
"Ba daɗewa zan yi ba likita. Na jima ban tai gida ba. Ina da buƙatar in koma su gan ni in gan su. Minti arba'in ya ishe ni."
Kai kawai ya jinjina ba tare da ya ce komai ba, ta kama hanya ta bar ɗakin.
Kai tsaye gida ta nufa, ko kuɗin abun hawa babu a tare da ita, ta hau ne dai kawai komai ta fanjama, fanjam! Idan kuma zai haƙura ta shiga gida ta ɗauko masa to.
A ƙofar gida mai mashin ɗin ya dakata. Bayan ta sauka ta ce da shi ya mata haƙuri ta shiga gida ta fito, za ta sallame shi. Babu ko musu ta tafi ta bar shi, bayan ya faka mashin ɗinsa.
Sumi sumi ta shiga gidan, hankalinta a tashe, dan ba ta san kalar masifar da za ta tarar ba. Sallama ta yi ƙasa ƙasa, tana bin mutanen da suke cikin gidan da kallo.
Babu wacce ta amsa sai mutum ɗaya, wadda har da fara'a a fuskarta ta iso ta rungumi Fiddou. Ita ma Fiddou rungumar tata ta yi, tana faɗin,
"Hadiza halan yaushe kika zo?"
Kafin Hadizar ta yi magana ta jiyo muryar matar yayanta ta ce,
"Tun sanda kika tahi wurin yawon iskancinki. Ke Fiddou bari ki ji in hwaɗi miki, na gaji da wanga iskanci naki, wanda kullum babu sauyi sai ma ci gaba da yake. Dan dai kin ga Yayanki ba shi nan ne hwa. Waton idan ya zo ya ce na bar ki kina hita yawon karuwanci ko? To walle ba ki isa ba!"
Wata budurwa da ke gefenta ta ce,
"Salon jan sharri ne kawai. Waton idan ya tashi ya ce ke kina harkar bikin gidanku, kin bar ta ita kuma tana biɗiɗinta. Makira ana magana tana bin mutane da idanuwa kamar warinta."
Wata mata ta buɗe baki ita ma za ta tofa na ta albarkacin bakin kenan Hadiza ta ce,
"Wai me ke damunku ne dan Allah? Wannan wane irin hali ne? Daga dawowarta babu ko maganar arziƙi kawai sai mugayen kalamai? Ku za ku so a muku haka ne? Ni fa ba na son haka gaskiya."
"Inye! Lallai ma Hadiza. Ni hwa ba na son wanga hali kuma ke sani. Ke a dole wayayya wadda ta je Katsina. To walle ba za mu ƙyale giɗe ba. Dole ne mu hwaɗi ta yi iskanci."
Kuka sosai Fiddou ta fasa. Tana matuƙar jin haushin kalmar da matar yayanta ke yawan jifanta da ita. Wai ita ce ƴar iska. Ga ƙanwarta nan Hadiza, wadda tsabar yawon bariki ya sa ma ta bar garinsu, ta koma Katsina da zama. Amma ba su ga nata ba, sai ita da ke ƙoƙarta kare mutuncin kanta a ko da yaushe.
A cikin kukan ne ta tuna da mai mashin da ba ta sallama ba. Da sauri ta bar wurinsu, ta nufi ɗakinta.
A cikin lakarta ta fiddo ƴan kuɗaɗen da take ajiya, ta zari daidai wanda za ta sallami mai mashin ɗin, sannan ta fito domin ta kai masa.
Fizgo ta ta yi matar yayanta, ta matse mata kafaɗa da ƙarfi, tana binta da wani wawan kallo.
"Dan Allah dai Aunty Sahiya ki rabu da ni. Ki ƙyale ni."
"Na ƙi in ƙyale ki Fiddou. Waton in sake ki ki koma wurin iskancin na ki ko?"
Cikin jarumta ta fizge jikinta, a hanzarce ta fita daga gidan, ta bar su sake da baki.
Bayan ta sallame shi ta dawo. Tana jin yanda tsoron Aunty ke fice mata daga zuciya. Ita fa in dai kan Modu ne, to za ta iya jure komai, wulaƙanci da kyara, matuƙar dai ba zai cutu ba.
Tana shiga Aunty ta jawo hannunta da masifa. Ba ta ankara ba Hadiza ta janye Fiddou da fushi sosai, ta ce,
"Wallahi ba ki isa ba! Wai me ya sa ba ku da imani ne? Yarinya marainiya amma babu imani sai a ringa cutar da ita? Wuce mu tafi Fiddausi."
Ɗakin Fiddou ɗin suka nufa, Fiddou sai kuka take, Hadiza na rarrasarta.
"Fiddou in dai ba za ki fitar da tsoronsu ba wallahi a haka za ki ci gaba da rayuwa. Yo wannan rayuwar ko naka na jikinka wa ya ce miki ana gwada tsoronsa a fili? Ai sai ya raina ki. To bare kuma matar yaya. Me ake ci da matar yaya ko ta ƙwarai ce bare kuma muguwa kamar Aunty Safiya?"
"Ban san yanda zan yi ba Hadiza. Ina cikin matsala. Aunty Sahiya ta kasa ganewa. Ta ƙi ta bar ni da damuwad da ac cikin zuciyata. Ga Modu can kwance ba lahiya. Ni ban ma san inda zan dosa ba. Rana zahi inuwa ƙuna!"
Kuka sosai take a wannan gaɓar. Tana ƙara tuna halin da ta baro Modu a ciki.
"Yi haƙuri ya isa haka to. Yanzu ki samu ki yi wanka mu je na siya miki abinci, dan nan gidan dai babu komai, idan ma akwai na tabbata masifaffun can ba za su bar ki ki ci ba."
Nufar yin wankan kuwa ta yi Fiddou. Kafin ta fito har kaya Hadiza ta fiddo ta ajiye mata. Tana jiran fitowarta.
Bayan ta shirya suka kama hanyar fita. Ko kallon inda su Aunty suke ba su yi ba. Saboda Hadiza na ƙoƙarin fitar da shakku da fargabar Aunty Sahiya da Fiddou ke yi.
Kai tsaye wurin sayar da abinci suka nufa. Siya suka yi suka ci, sannan Hadiza ta sa a ma Modu take away su tafin masa da shi.
Bayan Hadiza ta biya kuɗin suka fito. Mashin suka tara ko wace ta hau ɗaya, kai tsaye suka nufi asibitin da Modu yake.
Fiddou ce a gaba sai Hadiza bayanta, har suka shiga cikin ɗakin Modu.
Modu suka samu a zaune, hannunsa ɗaya dafe da ƙirjinsa, ɗayan kuma a cikin bakinsa, yana tsotsar duka yatsun hannun.
Dariya ya saki da ƙarfi a lokacin da ya haɗa ido da Fiddou. Ya yi yunƙurin miƙewa amma kansa ya sara masa, dolensa ya runtse ido, ya dafe kan nasa.
Ledar hannunta ta saki Hadiza a