Showing 186001 words to 189000 words out of 201092 words
Chapter 63 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
tashi daga barcin da take yi.
Dr. Hamdan suka ji ya ce,
"Kamar yadda na faɗa muku a farko, daurewa za ku yi ku shirya ku tafi Maiduguri. FMC ɗin tasu an dawo da ita nan cikin Maiduguri, da ma'aikatan nasu da duk wasu records da ke akwai, duk da dai ba na tunanin har yanzu za a iya samun nurse ɗin da ta karɓi haihuwar tasu tana aiki ba ta yi retire ba. Amma dai sanin nata yana da amfani, nemanta kuma ba zai yi wahala ba."
Alhaji Marwan ya ce,
"Wannan gaskiya ne. Kuma abin da ya kamata a yi kenan, wata ƙila ba za a rasa wani labari daga gare ta ba."
Dady ya ce,
"To gobe idan Allah ya kai mu sai mu tafi. Hausawa suka ce da zafi-zafi kan daki ƙarfe. Mu yi komai kan lokaci, ta yadda za mu gama a kan lokaci."
"Haka ne. Pharm IA ni bari in kama hanya, yanzu insha Allahu."
Hanan da ke daidai isowa wurin ta ce,
"Uncle an fa gama abinci ta ya za ka tafi ba tare da ka ci ba? Ga shi can a dining na jera."
Da fara'a ya ce,
"Ɗebo ki kawo min a nan kawai in ci."
Ta koma dining ɗin. Faten dankalin turawa da kaza ne ta zubo masa a plate, ta sako fork da spoon sannan ta kawo masa. Drink ta kawo masa ta dire a gabansa sannan ta juya ta tafi.
"Wai ni kam Maryama, ban ma tambaye ki lafiyar ango ba. Wannan tashin hankali bai bar ni ba."
Kallon juna Maryama da Annur suka yi suka sakar ma junansu murmushi. Sannan ta ja hannunta suka wuce ɗaki. A can ta labarta mata duk abubuwan da suka faru tun daga farko har ƙarshe. Islam ta fasa kuka.
"Haƙiƙa Amrah haske ce, haka mahaifiyarta ma. Tun ina yarinya ni da Aunty Saddiqa muka ɗora wa Amrah da iyayenta karan tsana. Muka tsane su kasantuwarsu talakawa. Sai ga su ta dalilin Mahaifiyar Amrah komai ya bayyana. Yes, ita ce sila. Saboda inda ba ta ba ki labari ba da komai bai faru ba. Da a haka za a yita zama cikin duhu ba tare da su Momy sun gano cewa Yah Noor ba ɗansu ba ne. Sannan ke Maryama."
Ta rungomo Maryama, ta ce,
"Tabbas ke jaruma ce. Mace ce ta kirki wacce ta san me take yi. Allah ne kaɗai zai iya biyanki abin da kika aikata. Har kika iya daurewa kika auri mahaukaci, wanda ko ni nan ba zan iya ba. Insha Allahu zan je har gidan su Amrah in roƙi mahaifiyarta gafara, a kan abubuwan da na aikata mata ita da Amrah."
Maryama ta yi murmushi cike da jin daɗi, ta ce,
"Za kuma ta yafe miki. Na san halin Umma sosai, a wurinta Amrah ta gado kyawawan halaye."
Sai bayan sallar la'asar sannan Dr. Hamdan ya tafi. Sun masa godiya sosai, har Maryama ma sai da ta masa. Ta yi mamakin mutumin, yadda Dr. Sandra ta mata bayanin matsayinsa da kuma iliminsa, amma a haka yake da irin wannan sakin fuskar.
Annur da Sans kam sai suka kasa rabuwa. Daidai da sallah tare suka je masallaci. Labari kawai suke yi. Sans na daɗa neman gafararsa bisa ga abin da ya aikata masa. Sai a yanzu ma yake jin duk yadda abun ya faru. Murmushi kawai ya saki yana jin daɗi, saboda a ganinsa hakan ma alkhairi ne, tunda har ya gano ƴan uwansa na jini wanda bai san da su ba. Sannan kuma ya gane cewa iyayensa basa raye, ko ba komai zai musu addua.
A falo suka samu Momy da Dady zaune. Fuskar Momy duk ta kumbure tsabar kuka. Duk ba ta da walwala sosai. A gabanta suka zauna a tare. Ta tsura musu idanuwa tana kallo. Sai yanzu take daɗa tabbatar da tsantsar kamannin da ke tsakaninsu. Bambancinsu ba wani mai yawa ba ne. Sai wanda ya ajje hankalinsa sosai sannan zai fahimta.
"Momy murmushi fa ya kamata a ce mun same ki kina yi a daidai wannan lokacin. Ga yaranki sun ƙaru, sun zama ƴan biyu. Sannan kuma ga ƙanwarsu Yamaira. Ai idan ni ne ke dariya zan ta yi inta famar wagar baki."
Dady ya yi dariya sosai.
"Yo Annur idan taita wagar baki kuma ai sai a kai ta psychiatry a ce ba ta da lafiya."
Sans ya ce,
"A'a fa Dady. Murna ce kawai."
Ba su bar wurin ba har sai da suka ga sun saka ta dariya sosai. Dady ya ce da Annur ya je ya ce ma Maryama ta fito su tafi har an fara kiran magrib. Annur ya ce a dai bari har su yi sallah sannan su tafi.
A ɗaki kuwa Hanan da Janan sai famar zaulayar Maryama suke. Wai yau za ta amarce, saboda sun mata, wacce tun ga bikin ta so yi mata ita amma sai ba ta samu damar komawa washe garin bikin ba, saboda zuwan su Hanan.
"Tunda dai komai ya bayyana, na tabbata a yau komai zai kammama."
Harararta ta yi cikin wasa,
"Ke don Allah Aunty Islam."
"Yo ai gaskiya ce Maryam. Da gaske sai kin dage, don yayan can nawa da alama gwarzon namiji ne."
Ta yi saurin doɗe kunnuwanta.
"Ai ba na ma jin ki ni kam."
"Ke dai kika sani. Na tabbata a zuciyarki kina nan kina ta shi min albarka. Amma don iyayi sai wani rufar kunnuwa kike..."
Ba ta rufe baki ba wayarya ta yi ringing. Baban Abdul ne ke kira hakan ya sa ta gaggauta ɗauka. Ce mata ya yi ga shi nan a falo ta fito su tafi da sauri, saboda sai sun biya ta gidan iyayensa sun ɗauko Abdul da aka kai tun safe yini, kasantuwar har yanzu hutunsu bai ƙare ba.
Tashi ta yi Maryama ma ta bi bayanta. Daga rakiyar su Islam sai Annur ya ce ita ma ta fito su wuce.
Bayan ta ɗauko hijabinta sai da Dady ya musu nasiha sosai sannan ya ba shi makullin Corolla LE ɗinsa cewa ya mallaka masa ita. Tunda asalin tashin ita ce a hannun Sans, ba kuma za a iya karɓarta daga gare shi ba.
Ta yi mamakin yadda ya iya gane gidan nasu babu ko ɓata lokaci, amma sai da suka fara biyawa ya musu siyayya. Suna isa gida mai gadi ya buɗe musu gate bayan ya tabbatar cewa su ne. Suka shiga ya faka a madaidaicin parking space ɗin gidan.
Maƙale da juna suka iso bakin ƙofar. Faɗi take ya sake ta ta fiddo key daga jikarta amma ya ƙi sakinta. Da dabara ta samu ta fiddo ta miƙa masa. Kasa buɗewa ya yi dole sai da ta karɓa ta buɗe ɗin, suka ƙarisa ciki.
Sallar isha'i ya fara jan su suka yi. Sannan ya ce da ita ta tashi su yi nafila, irin wacce amarya da ango ke yi. Tun a nan jikinta ya yi sanyi, sai ta ƙara tabbatar da zancen Dr. Islam, cewa ba zai ɗaga mata ƙafa ba yau. Tana so, tabbas. Saboda babu macen da za ta zauna tare da namiji a matsayin mijinta na tsawon wannan lokacin, kuma a ce ko yaya ne ba ta ji sha'awarsa ba.
"Ɗauko plate a juye kazar nan. Ina jin yunwa."
Ta harare shi.
"Sai fa da Hanan ta ce maka ta kawo abinci ta yi tuwon semo da ɗanyar kuɓewa ka ce a'a. Shi ne kuma za ka ce wai kana jin yunwa?"
Ya kama hannuwanta duka biyun ya saka a nashi.
"Da gaske ina jin yunwa Maryam..."
Ji ta yi wata irin kasala ta wanzu a jikinta. Yadda ya kira sunan nata dole jikinta ya yi sanyi, ga kuma yadda yake wasa da ƴan yatsunta, duk sai ta fara rasa nutsuwarta. Da ƙyar ta iya saita kanta. Ta ce,
"Ina zuwa."
Ta yi saurin zare hannuwanta daga cikin nashi. Ba ta jima ba sai ga ta ta dawo da plate sai cups guda biyu. Naman kazar ta juye a ciki, sannan ta zuzzuba musu lemukan a cups ɗin. Tana gamawa kuma sai ta yi shiru, ta saita idanuwanta a wuri guda tana kallo. Ganin haka ya sa Annur kamo ta ta dawo a jikinsa.
"Tunanin me Mi_amor ke yi?"
Samun kanta yi da jin kunyarsa. Ta rufe fuskarta tana murmushi.
"Kawai na tuno wasu lokuta ne, da nake mana irin wannan zuba abincin, nake baka a baki da nufin ba ka da lafiya. Wai ashe dai ɗan bawan Allah'n nan kallo na yake ƙyar, lafiyarsa ƙalau."
Ya haɗa fuskarsu tana gogar juna.
"Ba kodayaushe ne nake da lafiya ba, kamar yadda na faɗa. Abun yakan kaɗo min ne. Tun daga ranar da Umma ta zo ne dai ban ƙara jin ciwon ba."
"To na ji. Ka ce kana jin yunwa kuma ka tsaya zuba surutu."
Ya janye fuskar tasa sannan ya taɓe baki.
"Yunwar fa ba wata ta a zo a gani ba ce. Ko kalamanki kawai na ci gaba da saurara zan iya jin cikina ya cika."
Dukan wasa ta kai masa.
"Lallai ma mutumin nan. Dama ba yunwar kake ji ba."
Ta ɗauko plate ɗin. A hankali suka rinƙa feeding junansu, suna yi suna kora lemu mai sanyi har suka ƙoshi. Kwashe kayan duka ta yi ta kai kitchen, sannan ta dawo ta fesa freshner, a take ɗakin ya gauraye da ƙamshi.
"Yah Noor na bar ka lafiya. Ni zan kwanta."
Ta doshi hanyar barin ɗakin. Ai ko bakin ƙofa ba ta isa ba ta ji shi ya damƙo ta. Bai ce mata komai ba sai ji ta yi ya ɗauke ta ɗaf kamar wata jinjira. Ta rinƙa mutsu-mutsu tana faɗin ya sauke ta amma ya yi kamar bai ji ta ba. Sai a tsakiyar gado ya dire ta.
"Yarinya kin ma isa? Kin san irin dauriyar da na rinƙa yi a baya ina kwanciya da ke a gadon nan ba tare da wani abu ya haɗa mu ba? To yau duk sai na fanshe dauriyar da na yi a baya"
Sai ta samu kanta da faɗuwar gaba.
"Yah Noor please..."
Bai ko jira ta ƙarisa zancen ba ya haɗa bakinsa da nata. A take lamurran suka fara sauyawa. Soyayya yake gwada mata wacce ya jima yana wa Amrarsa tanadinta. Shi kanshi ya yi mamakin kansa, bai taɓa tsammanin akwai macen da zai damƙa wa dukkanin soyayyarsa ba, sai ga shi a yau ya samu wannan tabbacin.
Tun tana noƙewa har ta miƙa masa ragama tare da ba shi haɗin kai.
Da asubah ya kunna side lamp. Kyakkyawar fuskarta ya ƙura wa idanuwa. Lallausan gashin kanta duk ya barbazu bisa fuskarta. Barci take yi sosai ga hawaye da ya bushe a fuskarta. Sai ya saki murmushi haɗe da dafa goshinta.
"Allah ya yi miki albarka Maryam. Allah ya biya miki dukkanin buƙatunki. Na ba ki amanar rayuwata Maryama. Duk da cewa Amrah na nan a cikin zuciyata, kamar rubutun da aka zana a jikin dutse, wanda babu gogewa a gare shi. Hakan ba zai taɓa saka ni daina ƙaunarki ba. Kalmar Amrah nake so ba za ki sake jin ta a bakina ba, har abada! Daga yanzu sai dai kin rinƙa ji na ce MARYAMA NAKE SO!"
Ya sauke hannunshi daga dafewar goshin da ya mata. Sannan ya nufi toilet ya yi wanka ya ɗauro alwalla.
***
*Masu kuka ina fatar kuka ya ƙare😀. Yanzu kam na tabbata babu sauran ɓacin rai. Sai dai zuwa Maiduguri da su Dady za su yi, ko za su dace? Amsar na a shafin gaba, wanda daga shi sai na ƙarshe insha Allah.*
*Finally, the long awaited day has come. Annur da kansa ya furta Maryama yake so. Ya haƙura da faɗin Amrah yake so, har ƙarshen rayuwarsa. Wa da wa suka ji daɗi? In ga hannuwanku sama...lol.*
*Masu kirana, masu turo min saƙon waya duk ina godiya. Allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci.*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/28, 8:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
7⃣4⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
A bisa stool ta zauna tana shafa mai. Ji ta yi ya ɗora fuskarsa bisa kafaɗarta, ya tsura mata idanuwa ta cikin mudubi. Kallon sa ta yi ita ma ta cikin mudubin haɗe da ɓata fuska cike da shagwaɓa. Ya janye fuskar tasa.
"Daure min fuska ma za ki yi ko?"
"Ehh mana."
Ta saki kakkausan murmushi.
Bai sake faɗin komai ba ya ji wayarsa na ƙara. Ya koma ya ɗauko ta daga bakin gado sannan ya yi recieving.
"I'll be on my way now, Dady. Na tsaya karyawa ne."
Ya juyo ya kalli Maryama.
"Dady ne. Wai in hanzarta. Ashe ma a jirgi za mu tafi, kuma ƙarfe goma jirgin zai tashi. Ki ga ikon Allah, jiya-jiyan nan ashe Uncle Marwan ya je ya binciko kuma aka yi sa'a akwai jirgin da zai tashi zuwa Maiduguri ɗin yau."
Maryama ta miƙe tsaye.
"To kuma ko karyawa fa ba ka yi ba a hakan za ka tafi?"
"To ya zan yi Baby? Pass 9 fa. Ni kaɗai ake jira har Uncle Marwan ma ya kai Yamairah, dayake tare za mu tafi da ita."
"Ina zuwa to."
Ta nufi ɗakinta.
Cakes irin na leda ɗin nan ta ɗebo masa guda huɗu. Sai ta ɗauki lemo ta saka a ledar ta miƙa masa.
"Ban yarda ka zauna da yunwa ba. Ga shi ka samu ka ci please. Sai yaushe za ku dawo?"
Ya ce,
"Ina tsammanin in dai mun samu yadda muke so to gobe ma mu juyo. Sai idan abun ya yi tsayi ne sai jibi, wanda ma ba mu fatar hakan."
"To yanzu Yaya ya za a yi? Mugunta ma ba ta bari ka faɗa min yadda zan yi ba?"
Ya mata hararar wasa.
"Ashe ma dai mugunta."
"Ehh mana."
Ya taɓe baki.
"Yadda zan yi da ke a me wai?"
"Ka san fa ba zan iya kwana a gidan nan ni kaɗai ba. Ko in tafi gidanmu kawai?"
Cikin shagwaɓa ta yi maganar.
Ya jawo ta ya haɗa fuskokinsu wuri guda, har hancinansu na gogar na juna.
"A hakan ne za ki tafi gida? Ji fa ko tsayuwar kirki ta gagare ki yi. Idan na je yanzu zan turo miki Hanan da Janan, tunda har da Momy za a tafi, dama bai kamata a bar su gidan su kaɗai ba. Kawai sai a rufe."
Ta jinjina kanta.
"Allah ya kawo su lafiya to."
Turaren oud ta fesa masa sannan ta taka masa har parking space. Da kanta ta buɗe masa motar ya shiga sannan ta rufe. Har ya fice tana ɗaga masa hannu sannan ta juya zuwa cikin gidan.
Zama ta yi bisa 3 seater ta runtse idanuwanta. Wani irin farin-ciki take ji yana sauka a duniyarta. Ashe haka aure yake da daɗi? Sai yanzu ta gasgata. Musamman ma dai mutum ya auri wanda yake so yake son sa. Sai ka ji tamkar babu yakai a duk duniyar ma. Ta sakar ma kanta murmushi bayan ta buɗe idanuwanta. Abubuwan da suka wanzu tsakaninta da Annur a daren jiya ne suka hau dawo mata a ka. Kunyar kanta ta ji, ta saka tafukan hannayenta ta kare fuskar, sannan ta miƙe domin gyaran gidan.
Yana isa ya samu duk sun hallara shi kaɗai ake jira. Sai suka masa uzuri saboda sun san ango ne. Yadda ake bin sa da kallo bayan ya gaishe su kuma duk sai ya ji kunya.
Sans ya dafa masa kafaɗa.
"Ango ka sha ƙamshi."
Ya faɗa ƙasa-ƙasa, yana sakin murmushi. A take kuma sai ya tuno da alƙawarin da Farouk Sardauna ya nemi ya cika masa, na cewa ya auri Maryama. Ga shi bai samu damar cika alƙawarin ba, amma ɗan uwansa ya cika masa. Ya kuma sakin murmushi da ya tuno wasu abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Maryama. Ƙaunar da ya yi mata daga kallo ɗaya , yadda ya gagara fitar da ita daga zuciyarsa har sai da boka ya masa aiki a kanta. Sai kuma ya tuno ranar da ya je har ƙofar gidansu ɗin nan.
"Yaya ina kwana?"
Yamairah ta gaishe da Annur cikin ladabi. Dama tun isowarta suka gaisa da Sans cike da ƙaunar juna, tana jin yadda ƙaunarsa ta shiga zuciyarta a lokaci guda, duk sai ta ji kewar iyayenta ta ragu daga cikin zuciyarta.
"Lafiya lau ƙanwata. Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah."
"To madalla. Ina su Hanan ne?"
Momy da ke daidai fitowa ta ce,
"Suna ɗaki Annur. Ka iso kenan."
Ya sosa ƙeyarsa.
"Na samu isowa Momy. Dama cewa na yi ko za a tura su Hanan ne wurin Maryama? Na ga su ɗin ma bai kamata su zauna su kaɗai ba. Ga ta ita ma can ita kaɗai."
"Ehh gaskiya bai kamata ba. Amma kana ga kamar babu takura a tura wa Maryama su?"
Ya ɗaga mata kai.
"To ai shi kenan. Kawai sai ka shiga ka sanar da su su shirya ɗin."
Ƙarfe goma saura kwata suka rankaya zuwa Airport. Goma da minti biyar jirginsu ya tashi. Mintuna arba'in suka saukar da su a babban Airport ɗin garin Maiduguri.
Taxi biyu suka tsayar drop. Dady ya ce da su FMC yake so a kai su. Kai tsaye aka nufi can ɗin da su. Bayan sun sauka suka sallame su, sannan suka rankaya zuwa cikin asibitin.
Maternity suka nufa, a baki-baki su Dady suka zazzauna bisa benci. Sai Momy da Yamaira suka ƙarisa cikin labour room ɗin, ta baro Yesmeen wurin Babanta. Daga farko ba a bar su shiga ba, saboda labour room ba wurin shige-da-fice ba ne. Sai suka musu bayanin abin da yake tafe da su sannan suka shiga ciki.
Inda ke da tarin takardu aka nufa da su. Momy ta faɗi exact date ɗin haihuwar su Annur, sannan aka hau bincikar takardun. Ba a wani sha wahala ba aka gano, tunda komai jere yake an saka tambarin shekarar a jiki. Files guda goma sha ɗaya ne ta ɗauko, alamun a ranar yara sha-ɗaya aka haifa kenan.
A hankali aka ringa dudduba kowanne. Sai a na uku da buɗewa ta ga sunan shereefah a jiki. Dukkaninsu sai da gabansu ya faɗi a daidai lokacin. Aka duba sunan wacce ta karɓi haihiwar, sunanta Sister Feenah, amma an rubuta cewa har da taimakon Dr. Rita, kasantuwar ba nace guda ke karbar haihuwar ba. Kuma twince ne ta haifa amma a lokacin na farkon ya rasu. Aka ajje file ɗin daga gefe sannan aka ci gaba da neman na Momy. A na biyun