Showing 180001 words to 183000 words out of 201092 words

Chapter 61 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

an kashe min yaro. Wallahi matuƙar an kashe shi kuwa, tabbas da wannan hannuwan nawa zan kashe Salman. Da wannan hannuwan zan luma masa wuƙar da ya luma wa kansa, sai dai a wannan karon zai mutu ne kai tsaye. Sai ya baƙunci lahira, in ya so ni ma ɗin a kashe ni."


Ya yi saurin doɗe mata baki.


"Haba Suhailah! Me kike faɗa ne haka? Idan rai ya ɓaci, hankali ba ya gushewa. Ban tsammaci jin kalmar kisa ta fito daga bakinki ba. Ko ma dai miye, idan ma mutuwar ya yi ai sai mu sada shi da hukuma, ita ta san matakin da za ta ɗaukar masa. Amma ɗaukar mataki da hannunmu ai wani babban laifin ne."


"Ban damu ba don na yi wani laifi a yanzu. Annur kaɗai na mallaka a matsayin ɗa namiji. Ta ya wani mugu zai zo kwatsam ya raba mu? Karya ne! Wallahi bai isa ba!"


Sosai ta dake a daidai wannan lokacin. Hawayen ma ta daina yinsa, sai saƙe-saƙe da mugayen ƙudirirrika a zuciyarta. Da haka har asubah ta yi, Dady ya nufi masallaci, ita kuma Momy ta tashi jiki babu ƙwari ta yi tata. Sosai take jin kanta na sara mata, tsabar kukan da ta sha, ga kuma uwa uba rashin barci. A kan darduma ta zauna har gari ya ƙarisa wayewa, zuciyarta ƙagare da yin arba da Sans.


***


*My pipu how was this chapter? So so so...ba zan ƙarisa ba, idan ta muku daɗi to ku da kanku ku ƙarisa in ji.👂*


*Hehehe! Mun dai ji ƙudirin na Momy, ko ya abun zai kaya? Ga dai gari ya waye, duk mai faruwa a yau za ta faru, sai mu yi tsumayen shafi na gaba, insha Allahu za mu warware komai.*


*Na yi tsammanin daga wannan shafin sai na ƙarshe, to kuma dai abun bai kasance ba, ashe ya fi haka. Ko ma dai nawa ya rage, ku juri bibiyata, na tabbata dai ba za mu ƙara shafi huɗu nan gaba ba ba tare da ya ƙare ba. Da yardar Allah.*


*Don't forget to vote,*
*Comment,*
*And share with your family and friends.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/27, 12:36 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




7⃣2⃣




Wattpad: PrincessAmrah


***


Momy ta yi zaune falo da kumburarrar fuskarta. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, jiran fitowarsa kawai take yi. A haka Hanan ta fito ta same ta. Ita ɗin ma kanta jikinta babu ƙwari, sai tarin fargaba da tararrabin abin da zai faru a yau take yi. Ta gaishe da Momy cikin girmamawa, sannan ta nufi kitchen domin haɗa kalaci. Rashin kuzarin kirki ya sa ba ta tsiri yin abu mai wahala ba. Kawai sai ta dafa ruwan zafi sannan ta soya ƙwai, tunda dama akwai breadi. Da ta gama ta kwaso komai ta kawo dining. Ɗaki ta koma ta samu Janan ta tashi har ma ta shiga wanka. Kayan sawa ta fito da su sannan ta zauna a bakin gadon har Janan ta fito ɗaure da towel.


"Ranki shi daɗe ashe kin samu tashi."


Ta ɗaga mata kai.


"To ya yi. Ga kaya nan na fitar saura in fito in samu ƙyuya ta hana ki fitar da naki kin saka nawa."


Ta yi murmushi.


"Ni ba ki ga duk a saɓule nake ba? Damuwa ce linkime a cikin zuciyata. Sosai nake tsoron abin da ka iya faruwa yau."


"Insha Allahu babu abin da zai faru sai alkhairi."


"To Allah ya tabbatar."


Janan ta furta bayan ta zauna bisa stool za ta fara shafar mai. Hanan kuma ta shigewarta wanka.


Yana can yana barci shi kuma, sai buɗe idonsa ya yi ya fara hangen haske alamar gari ya waye. Sauƙinsa ɗaya dama ya yi sallar asubah. Sai ya gaggauta tashi haɗe da ɗora idanuwansa ga agogo. Ƙarfe takwas da rabi ya gani, ya tashi tsaye. Toilet ya nufa ya yi brush da wanka sannan ya fito. Baƙin jeans ya saka da farar T-shirt irin ta police wacce ta bi jikinsa, kasantuwarta body hug. Ya feshe jikinsa da turare, ya ɗan ɗaga rigar ya duba cikinsa. An yi ceiling ɗin wurin tamkar wani abu bai faru ba. Sai ka ƙura ido sosai za ka iya ganewa. Nan ya ƙara jinjina wa Indiyawa da wannan baiwar tasu. Shi ya sa da zarar ciwo ya tsananta ga mutum ake tura shi India. Ya ɗauko wayarsa daga jikin chaji sannan ya fito.


Haka kawai sai ya samu kansa da faɗuwar gaba. Ya dafe ƙirjinsa haɗe da tsayawa cak! A daidai ƙofar falon. Ta biji-bijin labule ta hango shi, hakan ya sa da azama ta miƙe, sai dai ta ji Dady ya riƙe ta, ya ja ta zuwa bisa doguwar kujera.


"Take heart, Suhailah. Wallahi dukkan abin da kika ga ya faru da bawa to dama can haka Allah ya tsara ga rayuwarsa. Jarabawar ubangiji babu ta inda ba ya hukunta ta. Sai dai a ga shin za ka haye wannan jarabawar ko kuwa za ka yaƙe ta? Calm down, don girman Allah. Ki dube ki Suhaila, ko wanka ba ki yi ba tun ɗazu kika fito. A runtse kika kasa runtsawa sai ka ce hakan zai kawo miki mafita. Tunda nake da ke ba ki taɓa jayayya da ni ba. Ban taɓa hana ki abu kika kartake sai kin yi shi ba sai jiya zuwa yau. Why Suhailah?"


Sai ta ji zuciyarta ta sanyaya. Amma ji take fa har yanzu ba za ta taɓa iya yafe wa Salman ba. Dole ta ɗauki mataki a kansa, in ya so komai ma zai faru a ƙarshe sai dai ya faru.


Ɗaga kansu suka yi su duka biyun a daidai sadda suka ga Sans zaune a gabansu. Ya ji duk abin da suke faɗi, sai dai bai san inda maganar tasu ta dosa ba. Bai ma san cewa da shi suke yi ba.


"Momy barkanku da tashi."


Ya faɗa cikin sassanyan murmushi.


Ƙarfin hali ne kawai ya hana Dady sako masa wani zancen. Ganin irin kallon da suke bin sa da shi kuma duk sai ya tsargu. Ya sake maimaita,


"Dady ya gajiyar tafiya?"


"Annur..."


Tun daga kan sunan da Dady ya faɗa sai Momy ta dakatar da shi da hannu. Cikin masifa take kallon Sans cike da tsana da wulaƙanci. Ta ce,


"Point of correction, Alhaji. Annur kodai Salman?"


Durum! Sans ya ji gabansa ya yi mummunan faɗuwa. Sai ya saki idanuwansa yana bin Momy da kallo.


"Ka kalle ni da kyau, baƙin munafuki. Mugu, macuci, mayaudari, azzalumi, maha'inci malalaci..."


Ta shanye kukan da ya zo mata.


"To Allah ya toni asirinka mugu! Allah ya fi ka, kuma wallahi sai ka faɗa min inda ɗana Annur yake, ko kuma in yi ƙararka, shari'a ce kawai za ta raba ni da kai."


Gabansa ya ji yana bugawa da sauri da sauri. Tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka ya ji. Baki ɗaya kunnuwansa biji-biji yake ji tsabar tashin hankali.


"Mu za ka yaudara? To Allah ya toni asirinka baƙin makiri."


"Don Allah Momy ki saurare ni..."


Ya ji saukar mari a kumcinsa. Dafe kumcin nasa ya yi, hawaye na sauka a kansu sosai, zafin marin ya shige sa.


"Ka tashi ka bar ɗakin nan, na ba ka daga nan zuwa ƙarfe sha biyu na ranar yau, wallahi idan har ba ka gano min inda ɗana yake ba sai na yi ajalinka, da wannan hannuwan nawa."


Ta gwada masa tafukan hannayenta, cike da ba shi tabbacin za ta iya kashe shi ɗin.


Jiki babu ƙwari ya miƙe tsaye. Sai yake ƙara yin da na sanin abubuwan da ya aikata a rayuwarsa. Yake jin haushi da bai kasance na-gari ba. Takaicin sauyuwar halayensa na ƙara kururuwa a cikin kunnuwansa. Yana miƙewa jiri ya diɓe shi ya sulale, don dole ya dawo ya zauna.


Sosai Dady ya ji ya ba shi tausayi. Ko ba komai labarin da ya bayar a cikin diary ɗin dole za a ji tausayinsa. Jarrabtar da ya gani a rayuwarsa. Halin da ya shiga tun bayan da ƴan ta'adda suka shiga garinsu. Ya runtse idonsa, sai kuma ya rinƙa tunowa da kalaman Sans ɗin a asibiti ranar da yake masa nasiha. To ko ma dai dalilin da ya sa ya roƙi kar ya guje shi duk rintsi duk wuya kenan har abada?


Ya share hawayensa. A hankali ya sauko ƙasa kusa da Sans ɗin, ya ɗago masa kansa suka kalli juna, sai dai kunya ba ta bar Sans ya ci gaba da haɗa idon da Dady ba. Da hanzarinsa ya ɗago idonshi, yana kuka mai cike da ban-tausayi.


"Salman..."


Dady ya kira sunansa.


"Haƙiƙa ka tafka babban kuskure, kuskure mai wuyar a yafe maka. Wane irin mawuyancin hali ne za ka shiga wanda zai saka ka yin shirka, ka manta da ubangijinka? Me zai sa ka raba jini da hanta? Haba Salman! Ka cuci kanka, ka kuma ci amanar tarbiyyar da iyayenka suka gina maka. Yanzu abin nan da ka yi, a wace rayuwa kake tunanin Annur ɗinmu ya faɗa? Za ka so a ce kai ne abun nan ya faru da kai? Ka manta ma'aiki SAW ya ce ka so wa ɗan uwanka abin da ka so wa kanka? Me ya sa ba ka so ma Annur abin da kai za ka so wa kanka ba?"


Ya yi shiru daga nan, sanadiyyar kukan da ya ji ya zo masa.


"Alhaji ji nake kana masa magana tamkar kana tsoronsa. Shin kana nufin ka masa nasiha kenan kawai mu ci gaba da rayuwa da shi? Impossible! Rayuwarsa a gidan pharm. IA ta zo ƙarshe. In fact, rayuwarsa aduniyar ma ta zo ƙarshe, matuƙar bai gano min ɗana ba."


"Ku yafe min Dady..."


Abin da ya iya faɗa kenan, duk da cewa akwai tarin maganganu a bakinsa. Sai dai kuka ba zai iya barinsa faɗarsu ba. Tashin hankalin da yake a yanzu fatar mutuwa ta zo ta ɗauke sa kawai yake yi.


"Laifin da ka aikata Salman, laifi ne mai wahalar a yafe maka. Laifi ne da ba kai tsaye za a iya yafe wa mutum shi ba. Ka aikata babban zunubi Salman. Wallahi ban san me zan yi da kai ba. In yafe maka ka tafi ka bar gidan nan, ko kuwa in tirsasa ka sai ka gano inda Annur ɗinmu yake?"


Hanan da Janan ne suka iso a daidai lokacin. Cikin kuka Hanan ta ce,


"Ko ɗaya Dady."


Ta ƙarisa isowa daf da su, ta rusuna tare da riƙe hannun Dadyn.


"Dady idan har kuka kore shi, shi kansa bai san inda zai nufa ba. Mu duka ba mu san a rayuwar da zai faɗa ba. A baya ya yi yaudara ya zo gidan nan da zama ne saboda rashin madosar rayuwa, a sadda ma yake da Farouk Sardauna kenan. To Dady yanzu babu Farouk Sardauna, kuma an kore shi daga nan, wane hali kuke tunanin zai faɗa? Ba ku ganin kamar zai iya aikata abin da ya fi wanda ya yi a nan ma muni...?"


Momy ta katse ta.


"Ko ma gidan uban wa zai je sai dai ya je. Amma tabbas yau ne ƙarshen zamansa a gidan nan. Dole ya gano min ɗana, sannan kuma ya tafi uwa duniya ma ban damu ba."


Janan ta doɗe ma Momy baki.


"Haba Momy. Da bakinki kike faɗar wani ya tafi uwa duniya? Ashe ɗa ya fi ɗa kenan. Kina jin haushi saboda an ma Uncle Noor kurciya ya tafi ba a san inda yake ba, sannan kuma ke ma ga shi kina son wani ya tafi uwa duniyar."


"Janan ramuwar gayya ce zan yi. Shi ma ya ɗanɗani yadda Annur ɗina ya ji. Ya ɗanɗani daɗi ko rashin daɗin yawon duniya."


Janan ta gyaɗa kai.


"Momy kar tashin hankali ya sa ki aikata abin da bai kamata ki aikata shi ba. Ban san haka zuciyarki take ba. Ni zuciyar Momy da na sani sassanya ce mai sauƙin hali. Tana da tausayi da jin-ƙan mutane."


"Surutanku duk ba za su yi tasiri a gare ni ba. Kai!"


Ta gwada wa Salman ƙofa.


"Maza tashi ka tafi ɗakin Annur ka harhaɗa duk tsummokaranka. Na ba ka nan da sha-biyu na rana ka kammala komai, yanzun nan zan kira ƴan sanda su bi ka ka nemo min yarona. Idan suka ga za ka ba su matsala su tafi Office da kai, su maka tsinannen duka, in ma mutuwa za ka yi ka mutu ni ba ni da damuwa."


Ya yi kneel down, hannuwansa tallabe da ƙeyarsa, yana kuka sosai mai sauti, ya ce,


"Har ga Allah ban ga laifinki ba Momy, ba kuma zan taɓa gani ba. Sai dai zan miki rantsuwar ɗan musulmi, wallahi thumma tallahi na tuba, Allah kuma shi ne shaidana. Sannan kuma ban san inda Annur yake ba, wallahi."


"Wa za ka marairaice mawa? Ba zan taɓa tausaya maka ba, tunda dai kai mugu ne, ka kasa tausaya wa bawan Allah. Mahaukaci amma kai har ka ga abun ka ci amanarsa, ka ha'ince shi."


"Babu komai Momy zan tafi. Sai dai don Allah ina mai neman gafararku ke da Dady a bisa yaudararku da na yi. Ku yafe min ko zan samu rabauta a wurin Allah. Na sadaƙas, ko yanzu ki kira ƴan sanda su tafi da ni, don ban san inda zan gano Annur ba."


"Ko ba ka faɗa ba zan kira su. Ka tashi ka ɓace min daga gani. Idan ka ga dama ka gudu kafin ƴan sandan su zo."


Jiki ba ƙwari haka Sans ya tashi, Hanan ta riƙo ƙafar wandonsa tana kuka sosai. Tausayinsa take ji. Me ya sa Momy za ta kasa tausaya masa? Wannan wace irin zuciya ce wacce ba ta yafiya?


A hankali ya sa hannu ya cire hannunta daga riƙon ƙafar wandonsa da ta yi, ya tafi yana waigen Dady, sai dai kan Dadyn sunkuye yake a ƙasa, yana zubar da ƙwalla.


Kai tsaye ɗakinsa ya nufa. Rijif ya faɗi ƙasa, ya yi kneel down a bakin gado, kansa a bisa gadon sai hannuwansa ya miƙar da su ma a jikin gadon.


"Ya Allah ka gaggauta ɗaukar rayuwata. Allah ka sani, na fi son mutuwa ta ɗauke ni a daidai wannan lokacin, ya Allah ka kawo min mutuwa ta zo ta tafi da ni..."


Ya ci gaba da kuka sosai.


A ɗaki kuwa sosai Hanan da Janan ke rarrasar Momy amma ta kartake lallai sai ta kira ƴan sanda. Dady ma duk da yana jin tausayin sans ɗin, yana kuma tunowa da alƙawarin da ya masa a asibitin India, amma takaicinsa da yake ji a yanzu sai ya ji sam! Ba zai iya cika masa alƙawarin ba. Ko ba komai yana ƙaunar ɗansa Annur, kuma ga shi Sans ne silar da suka rasa shi, rashin da suka gwammaci a kawo musu gawarshi ma afiye da zama inda ba su san ya yake ciki ba. Har wani irin zazzaɓi yake ji yana sauko masa.


Cikin ƙarfin hali Hanan ta ce,


"Dady ka taso ku karya, ka ga har kusan goma da rabi."


"Ba na jin zan iya cin komai Hanan."


Ta dawo kusa da shi.


"Dole za ka ji yunwa Dady. Ba na so wannan tashin hankalin ya hana ka cin abinci. Ka ga kana da ulcer."


Ta juya ga Momy.


"Please momy go and have your break fast."


"Hanan ba zan iya cin komai ba. Ku je kawai ku ku karya."


Duk yadda Hanan ta yi da su a kan su zo su karya ɗin ƙi suka yi. Hakan ya sa su ɗin ma suka kasa cin komai. Sai kawai ta je dining ɗin, ta ɗauko ƴar launch box daga cikin dining carbinate. Ta zuba soyayyen ƙwai a ciki sannan ta ɗauki bredi guda ta ɗora a kai. Ta ɗauki flask da cup da spoon ta haɗa wuri guda, sannan ta shiga kitchen ta ɗauko ƙaramin basket. Jera kayan ta yi a ciki, ta ɗora container ɗin madara da sugar da milo, sannan ta nufi barin falon. Ji ta yi Momy ta ƙwala mata kira.


"Ina za ki je da kaya?"


Babu ko shakka bare tsoro ta ce,


"Zan kai ma Uncle Salman ne."


Ta taɓe baki.


"Ba zan hana ki ba shi abincin ƙarshe na gidan nan ba. Ki kai masa, sannan ki ƙara ba shi tabbacin ƴan sanda na daf da zuwa su tafi da shi."


Ba ta ko jira ta ƙarisa maganar ba ta ficewarta zuwa ɗakin Sans.


Ta same shi a yadda ya shiga tun ɗazu sai famar kuka yake. Fuskarsa ta gama kumburewa, ta tako kusa da shi bayan ta ajje kwandon.


"Uncle Salman..."


Ya ɗago kansa cikin mamaki ya kalle ta.


Ta zauna kusa da shi cike da tausayinsa.


"Ka ɗauka cewa wannan ƙaddararka ce. Rubutaccen al'amari ba ya taɓa kauce wa mutum. Ba na so damuwa ta saka ka komawa ƴar gidan jiya. Ka yi attempting kashe kanka ko kuma ka koma harkar shaye-shaye. Don Allah ka cire komai a ranka. Insha Allahu Allah zai bayyana Uncle Noor, zai dawo ku ci gaba da rayuwa tare, tunda ka riga da ka saba da zama a nan."


"Kayya! Hanan me ya yi saura a rayuwata? Farin-ciki ya daɗe da ƙaurace min. Tashin hankali kawai nake fuskanta. Mutuwa kawai nake..."


Ta dafe masa baki.


"Don Allah ka daina mana Uncle Salman. Ko da ƴan sandan sun zo sun tafi da kai na tabbatar da Dady zai fitar da kai. Ba zai juri ganinka a wurin ƴan sandan ba. Banda ma abun Momy, in nice ita ai ci gaba zan yi da zama da kai ko don sabon da muka yi. Ga kuma tsabar kama da kuka yi da Uncle Noor ɗin. Da kawai sai mu ci gaba da addua Allah ya bayyana mana shi. Tunda dai ƙaddara ta riga fata, mai faruwa ta riga da ta faru."


Ya gyaɗa kansa cikin kuka.


"Ka tashi ka karya please, ga kalaci nan na haɗa maka. Ta ce wai ƴan sandan za su zo. Amma da yardar Allah komai zai zo da sauƙi."


Ta tashi ta tafi.


Momy kuwa sake kiran ɗan sandan da mijin Islam ya turo mata lambarsa ta yi. Ya ba ta haƙuri cewa wani case ne suka tsaya handling, amma sun gama yanzu za su taso. Ta kashe wayar tana faɗin sai sun zo, tunda already ta musu text na address ɗin gidan.


Janan da ke zaune ta rafka uban tagumi ta ce,


"Momy ashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login