Showing 123001 words to 126000 words out of 201092 words
Chapter 42 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
yi fitsarin, sannan suka dawo, suka ci gaba da shan hanyar Katsina.
Shigarsu ƙofar Katsina ne hankalin Sans ya ƙara tashi, tuna cewa bai da wurin zuwa fa. A wannan lokacin kam hawaye ne ya kufce masa, mai cike da zallar damuwa da tashin hankali.
Yana jin yadda wasu ke faɗin a sauke su nan a sauke su can, shi dai ya yi shiru, har sadda aka isa tasha da shi. A lokacin har wancan mutumin mai taimakonsa ya sauka, wanda inda a ce Sans ya faɗa masa ba shi da wurin zuwa, mai yiuwa ne ya taimaka mishi.
Cikin hikima ya samu ya fito daga motar, bayan kowa ya watse, sai shi kaɗai.
Kimanin ƙarfe uku da rabi na rana kenan, daf da la'asar. Tashar a cike take kamar koyaushe, kowa na harkar gabansa.
Ajiyar zuciya kawai Sans ke saukewa, yana tunanin mafita. Lalubar aljihunsa ya yi, ya zaro kuɗaɗen da suka masa saura, kimanin dubu takwas da ɗari biyar. Gama ƙirgar kuɗin kenan yana ƙoƙarin miyarwa aljihu, fit! Ya ji an warce su, ya ɗaga kanshi ya ga mutum sai tiƙar gudu yake.
Ihu ya kurma haɗe da faɗin,
"Ku riƙe shi, kuɗina ya fige min."
Amma ina, tuni ya yi nisa, har ma ya fita daga cikin tashar.
Mutane ƴan tasha sai masifa suke ma Sans, wai don me ya san halin tasha zai yarda ya fiddo kuɗi, yana ƙirgawa a gaban mutane?
Kansa kawai ya dafe, yana jin zuciyarsa na masa zafi, tamkar za ta tsage ta fito waje.
Wannan wace irin rayuwa ce? Wane irin zamani ne muke ciki, wanda ake miyar da abububuwan banza ba a bakin komai ba? A ce wai mutum yana ji, yana gani a fige masa kuɗi daga hannu?
Ji ya yi baki ɗaya tashar ta fita ransa. Mutanen da ke cikinta ɗai-ɗaiku ne na kirki. Daga masu shaye-shaye sai masu faɗace-faɗace, ana zage-zagen banza. Gurgura kekensa ya yi, ya bar harabar tashar ma baki ɗaya.
Babu nisa daga nan zuwa wani masallaci. A bakin masallacin ya tsaya, cikin hikima ya gabatar da alwalla, sannan ya ajje keken bakin ƙofar masallacin, da rarrafe ya shiga ciki, ya gabatar da duk sallolin da suke kanshi.
Bayan ya gama ya ɗan kishingiɗa, da niyyar hutawa, nan barci mai nauyi ya ɗauke shi, saboda already an yi sallar la'asar an gama a masallacin.
Bai ankara ba ya ji wani mutumi na bubbuga shi, cewa ya tashi za a yi kiran sallar magrib. Cikin mamaki ya tashi zaune, yana murtsika idanuwanshi, yana mai leƙen ƙofa, idanuwansa suka yi tozali da duhun da garin ya fara.
Bayan sallar ishai ya fara ƙoƙarin gyara kwanciya, ya ji wani mutumi na bubbuga shi, cewa ya tashi, an hana kwana a masallaci yanzu, rufe shi ake saboda ɓarayi.
Kamar ya kurma ihu haka ya ji. To shi yanzu ya zai yi? Ina zai tafi ya kwana?
Bai da yadda zai yi haka ya miƙe, ya rarrafa har zuwa bakin ƙofa, ya jawo kekenshi ya hau, yana mai tura shi a hankali, yana kuma tunanin mafita.
Kuka yake sosai, damuwa na daɗa addabarsa, ba ya ko kallon gabanshi, har ya isa bakin titi. Ƙarar mota ya ji tiiii! Da ƙarfi ana neman kaɗe shi. Hakan ya kiɗimar da shi, ya rasa dukkanin nutsuwarshi. A masife matashin ya fito, hannunshi riƙe da karan sigari, yana faɗin,
"Mallam ba ka da idanuwa ne kai? Yanzu da a ce ka ja na kaɗe ka fa? Azumi sittin kake so ya hau kaina?"
"Yi haƙuri."
Sans ya faɗa, yana mai sadda kanshi ƙasa. Rayuwarsa ta baya ta faɗo masa a rai. Irin dukiyar mahaifinsa, mota sai dai ya hau wacce ya ga dama. Amma wai yau shi ne a bisa keken guragu, har wani matashi da bai wuce sa'anshi ba yake kawo masa wargi, kuma ya biye shi da ban-haƙuri.
Zuciyar matashin mai taushi ce. Haka kawai haƙurin da Sans ya ba shi ya sa shi jin tausayinshi. Fuskarsa ya kalla da hasken mota ya dalle shi. Kyakkyawan saurayi ne, fari sol da shi, mai cikar zati. Sai dai fuskar tasa da raunukan da ba su gama warkewa ba, amma duk da haka ba su hana kyawunsa bayyana ba.
Duƙawa ya yi a gaban Sans, cikin kulawa ya ce,
"Me yake damunka bawan Allah? Da alama kana cikin matsananciyar damuwa."
Hawayen fuskarshi ya share Sans. Ya ce,
"Babu komai bawan Allah. Je ka kawai."
Miƙewa ya yi matashin, ya juya zai nufi motarsa. Har ya isa bakin motar kuma ya fasa, ya juyo cikin takunshi, ya iso gaban Sans, yana faɗin,
"Ba zan tafi in barka a haka ba, a cikin daren nan. Idan ni an ci sa'a ban kaɗe ka ba, ban san wanda za ka haɗu da su a gaba ba."
Shiru kawai Sans ya yi, ba tare da ya furta komai ba.
"Ka amince ka bi ni mu tafi."
Matashin saurayin ya faɗa, yana kallon Sans.
Kai kawai ya ɗaga mishi, hakan ya ba shi damar tura keken na Sans, ya isar da shi gaban motar tashi, ya saka shi a ciki, sannan ya ninke keken ya saka a bayan motarshi.
***
Washe gari tunda asuba ta fara tariyar abubuwan da suka faru jiya. Da gaske ba ta koma wurin Modu ba tun bayan da Mama ta fara mata maganar Deedah. Kenan hakan na nufin ta saɓa alƙawari, ba ta ba shi maganin dare ba? Gyaɗa kanta take, tana mai tsananin jin haushin kanta. Haushin da take ji a yanzu, ji take ya ninka na aura mata Deedah ma da ake son yi.
Kuka ta fasa mai ƙarfi, tana ambatar,
"Na saɓa alƙawari. Allah ka gafarta min ya Allah. Yanzu me zan faɗa ma Yaa Noor? A wanne hali ya shiga bayan babu ni? Allah Allah!"
Ta dafe kanta, a saman sallayar da take zaune.
Wayarta ta zaro daga jikin caji, ta duba ta, a silent take tun jiya da ta saka, hakan ya sa ba ta ga duk kiran da ake mata ba. Abun mamaki, har da Dr. Hamdan M. Ramat ya kira ta, da kuma sunan Bobby, wanda ya mata kira kusan guda goma sha biyar, shi ne ma ƙarshen ɗaga wayarsa da ya yi, kafin ya galabaita.
Mamaki take, ta yadda likitan da kanshi ya kira ta, duk kuwa da ayyukan da suke gabanshi. Kuma ba haka suka yi ba, sun yi ne cewa ita za ta kira shi ƙarfe takwas, amma abun mamaki, shi da kanshi ya kira ta.
Kawar da mamakinta ta yi ta hanyar miƙewa tsaye, ta ninke sallayar ta ɗora a bakin gado, sannan ta doshi barin ɗakin, zuwa na Modu.
A takure ta same shi, ya haɗa kai da guiwa, yana ta wani irin kuka mara sauti, sai dai shessheƙarsa kawai ake ji.
Cikin kiɗima ta iso gare shi. Hannunta a ka take faɗin,
"Ya Noor me ya faru da kai?"
Tunani yake, mafarki ne wannan yake yi. Irin zuwan da Amrah ta saba yi masa a mafarki ne ita ma Maryama ta masa. Hakan ya sa ya ƙi ɗago kanshi, yana mai tsananta kukan da yake yi.
"Ya Noor me kake ne wai haka? Ko wani abu yana maka ciwo ne?"
A nan ɗin ma bai ɗago kanshi ba. Haka kuma bai rage sautin kukan ba, sai ma ƙarfafa shi da ya yi.
Hankalinta ne ya daɗa tashi. Ta sa hannunta tana mai dafa kafaɗarshi, a hankali take ɗan bubbugawa.
"Zan yi fushi ma in tafiyata, tu da dai ba za ka min magana ba."
Taba shin da ta yi ne ya ba shi tabbacin ba mafarki yake ba. Ya dago kansa, da idanuwansa da suka gama rinewa.
A kidime ta zaro idanuwanta tana kallon bakinshi. Ta ce,
"Yaa Boor me ya samu bakinka? Na shiga uku? Ko wani abu ya faru ne?"
Daina kukan nashi ya yi, ya dora dukkanin idanuwansa gare ta, yana bin ta da wani irin kallo, mai cike da zallar jewarta da ya yi.
"Yaa Noor talk to me. Me ya faru da labbanka duk suka farfashe?"
"Yo ni na ciccije su."
Ya fada cikin halin ko'inkula. Farin cikinshi dai da ta dawo garr shi. Ita kam ba ta masa nisa kamar yadda Amrah ta masa ba.
"Me ya sa za ka ciccije labbanka?"
Ta tambaue shi, cike da al'ajabi.
"Ba ke ce kika ki zuwa ba? Ni kuma na ji haushi, na keta riga ta, na kuma ciccike labbana."
Ya fashe da dariya, yana mai sadda kanshi, wai ya ji kunya.
Samun kanta ta yu da murmusawa. Har cikin ranta ta tausayawa masa. Wani irin dadi ta ji ya ziyarci zuciyarta. Ashe har Annur ya damu da ita haka? Kodai ya fara ba ta matsayi ne kamar Amrah?
Ba ta samo wannan amsar ba ta juyo muryarsa yana fadin,
"Ke kika ce ba za ki taba yi min nisa ba, za ki zame min madadin Amrah."
Habarta ta dafe da hannun dama, tana tuna ranar da suka yi wannan maganar da shi, tamkar hankalinshi ba ya gare ta. Amma ga shi har bai manta ba, har ma ya fara yarda cewa babu Amrah. Lallai ta yarda sosai da Dr. Sandra. Ta amince cewa Lost of Memory shi ne bbsvbar damuwar Annur. Bayanan da ta mata cewa makusanci yake nema, wanda zai nuna masa dukkanin soyayya, ya ba shi dukkanin kulawar da wani masoyi zai samu daga wurin masoyiyarsa. Yau ga tabbaci ta gani. Har Annur na ambatar za ta zame masa madadin Amrah.
"Ko jiya ma ta zo min a cikin barci, ta ce da ni wai in dauka cewa ke ce ita, in moyar da duk wata soyayyarta gare ki, wai in dai ina so ta yi farin ciki. Farin cikin Amrah nake so! Duk abin da zai faranta mata rai ina biye da shi, hakan ya sa na mata alkawari cewa zan miki kauna, sai dai ba kamar wacce nake mata ba. Ta yarda da hakan, kuma ta bace da ganina, hade da raubtsuwar ba za ta taba dawowa a gare ni ba har abada."
Kuka ya fasa a daidai nan, yana mai kallon wuri daya, tamkar wanda yake tunkwa da wani abu.
Tun sadda ya fara maganar take kallon shi, kallon mamaki. Wai kodai Annur ya warke daga hauka ne? Wannan kalaman da yake mata, mahaukaci ba zai taba iya yin su ba.
A hankali take jin duk wata damuwarta tana rarewa izuwa farin ciki. Kaunar Annur na shiga duk wata kusurwa da ke cikin jikinta. Soyayyarsa na ambaliya a jini da dukkanin jijiyoyinta.
Ji take ta manta ma da wata damuwa da take cikinta. Maganar auren da ake so a hada ta da Deedah nna disashewa daga cikin zuciyarta. Tana canzuwa da farin cikin da Annur ya jefa ta a ciki.
"Kawai a zo a mana aure..."
Ta tsinkayo muryarsa ya fada, yana mai sadda kanshi kasa, alamun jin kunya.
***
*My pipu how was this chapter? Was it nice? In ga hannuwan wanda ta ma dadi...lol.*
*To kar dai a manta da kankaro mutunci.*
*Masu mutunci ku karkata ku kankaro shi.*
*Ni ma sai in karkata in kankaro muku dogon shafi irin na yau.🤗😘😃*
*Ku kuma ghosts masu hancin yalo, ku ci gaba da labe, Allah yana ganinku. Kuma insha Allahu gobe sai kun tashi karanta next oage dina chajin wayoyinku ya kare. Ehen. Masu hakoran bera kawai.😏🤒*
*Jinjina ga yan RAZ NOVELLA 1&2. Ina kaunarku all fisabilillah. Iya wuya ana tare.*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/6, 11:23 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
5⃣6⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
A bakin wani gidan gona suka faka motarsu. Tun sadda suke shigowa cikin dajin Sans ke son yin magana. Yana son sanin ina za su je da suke keta daji irin haka. Sai dai ya yi shiru ne saboda ya san wasu ba su son yawa magana. Zai haƙuri har su isa ɗin, don ya ga iya gudun ruwansu.
Taimaka masa ya yi matashin ya fiddo keken daga bayan motarsa, ya ajje a daidai ƙofar gaba da ya buɗe ma Sans, sannan ya tallabo shi ya ɗora a bisa keken.
Bayan ya zauna daram ya rufe murfin motar, sannan ya ringa tura shi har suka isa daga bakin ƙofar, ya hau ƙwanƙwasawa. Babu jimawa sai ga wasu matasa sun fito, ɗaya na magagin barci, ɗayan kuma yana ma wancan saurayin sannu da zuwa.
"Yax. A kama shi a shigar ciki, zan gyara parking ɗina."
"To Oga."
Wanda aka kira da suna Yax ya faɗa, yana mai kama keken Sans, haɗe da shigar da shi cikin gidan.
Bayan sun ƙarisa tangamemen falon, Yax ya ce da ɗayan abokinsa,
"Esien, taimaka kawo mishi ruwa ya sha. Da alama yana jin ƙishi, ga bakinsa nan duk a bushe."
Bai musa ba Esien, ya nufi inda fridge yake, ya ɗauko masa ruwan roba, mai tsananin sanyi, har da raɓa.
Miƙa ma Sans ɗin ya yi bayan ya buɗe, bai karɓa ba, sai cewa ya yi,
"Ina jin zazzaɓi sosai a jikina, ba zan iya shan ruwa mai sanyi ba. Kuma ga magungunana nan a cikin aljihu ina son sha, ba a sha da ruwan sanyi."
Wancan matashin da daidai shigowarsa kenan ya ce,
"Esien kawo masa mara sanyi don Allah. Wanda ba a saka a fridge ba."
Ya ƙariso gaban Sans, da faɗin,
"Sannu ko?"
Kai kawai Sans ya jinjina masa.
Esien na kawo masa ruwan ya ɓalli magungunanshi ya sha. Sanann ya ce,
"A ina zan yi wanka? Ku taimaka min, duk jikina babu daɗi."
"Yax, ka dafa masa ruwan zafi yanzu. Da alama akwai zazzaɓi sosai a jikinsa, bai kamata ya yi wanka da ruwan sanyi ba."
Cikin bin umurnin wancan matashin ya miƙe, ya ƙarisa cikin kitchen domin ɗora ruwan zafin.
"Ka kwantar da hankalinka. Ni sunana Farouk Sardauna, you can call me Bobby. Za ka iya ci gaba da zama a nan tare da wa'yannan bayin Allahn, duk yarana ne, har sadda ka samu wurin zuwa."
Kansa kawai ya jinjina ma Bobby. Yana mai samun dukkanin nutsuwarsa da ya rasa a baya.
Sai da Yax ya haɗa mishi komai sannan ya sanar da shi ya haɗa masa, ya tura shi har toilet ɗin, sannan ya bar shi ya yi.
Bayan Yax ya dawo, Bobby ya ce da su,
"Ina son ku nutsu mu yi magana da ku."
"To Oga."
Suka haɗa baki wurin faɗi.
"Wannan da kuke gani, ina son duk wani girma da za ku ba ni, shi ma ku ba shi. Ku girmama shi, ku ɗaga darajarshi, matuƙar kuna son ganin farin cikina. Duk wani abu da yake da buƙata, ku tallafa masa, tunda kun gan shi gurgu."
Cikin gamsuwa Esien ya ce,
"Mun maka wannan alƙawarin Oga."
Yax ma ya ce,
"Deal!"
Tafa hannunsa ya yi Bobby, ya ce,
"Shi ya sa nake alfahari da ku a kodayaushe. Kuna faranta min rai sosai. Duk abin da zan nunar muku da ina so kuna aikata shi."
Yax ya ce,
"Ai Oga dole ne mu faranta maka, saboda kai ma kana faranta mana. Ka duba ka ga, ba wani aiki sosai muke yi a gidan gonar nan ba, amma duk sadda Dadynka zai zo ka ringa koɗa mu kenan, yana mana kyautukan ban mamami. Tsakaninmu da kai sai dai godiya kawai."
Murmushin jin daɗi ya yi, sannan ya shiga ɗakin da kayanshi suke, wanda idan ya zo gidan yake sakawa.
Wasu kayan sanyi ya fiddo ya ɗora a bisa gado, ya feshe su da turare, sannan ya dawo falon.
Ya tarar har ya fito daga wankan Sans, hakan ya sa ya tura shi izuwa ɗakin da ya fito daga shi ɗin.
Mai ya gwada mishi ya shafa, sannan ya ba shi kayan, yana mai fita daga ɗakin.
Abincin da ya tsaya ya siyo ne ya koma ya ɗauko daga cikin mota, ya mimmiƙa ma su Yax nasu sannan ya ajje ma Sans nashi gefen kujera, shi ma ya hau cin nashi.
Ƙarar keken Sans da suka ji ne ya tabbatar musu cewa ya fito, duk suka ɗaga kawunansu suka kalle shi. Sosai kayan jikinshi suka amshe shi, tamkar dama can nashi ɗin ne.
Bayan ya iso gaban Bobby ya fasa kuka, yana mai runtse idanuwansa.
Da sauri Bobby ya ajje robar take away ɗin, yana tambayar Sans dalilin yin kukan nashi.
"Kawai ina jin daɗin halaccin da ka min ne. Har ma ban san ta hanyar da zan bi don na gode maka ba."
Gyaɗa kansa ya yi Bobby, cike da tausayi ya ce,
"Ka daina kuka in don wannan ne. Har ga Allah ka shiga raina, a lokaci guda na ji tausayinka ya shiga duk wata gaɓa da ke cikin jikina. Karɓi wannan."
Ya miƙa masa wani hankici babba, mai ɗauke da tambarin tutar USA.
"Share hawayenka, kar kuma na kuma ganin koda ɗison hawaye ne ya fito daga idanuwanka."
Karɓar kuwa ya yi Sans, yana mai share hawayensa, da hankicin.

"Yauwa ko kai fa. Yanzu sai ka ci abincinka. Daga nan sai ka samu ka kwanta, ko za ka samu ƙarfi-ƙarfi a jikinka. Gobe da safe zan dawo insha Allahu, zan kai ka asibiti."
Godiya Sans ya sake jaddada masa, sannan ya fara cin abincin, zuciyarsa na cike da ƙaunar bawan Allahn da ya ba shi taimako ba tare da ya san cikakken asalinsa ba.
***
Bubbuga shi ya ji an yi, a lokacin da kanshi yake bisa guiwowinsa, yana saƙe-saƙe haɗe da zancen zuci.
Ɗago kan nashi ya yi, yana kallon mai taɓa shi ɗin. Dadynshi ya gani sanye da farin glasses, yana sakar masa murmushi.
"Ya ƙarin haƙuri?"
Dadyn nashi ya faɗa, yana mai ƙoƙarin gyara zamansa a kusa da Sans.
Share guntuwar ƙwallarsa ya yi, ya ce,
"Haƙuri an gode Allah, Dady."
Yana mai jin nauyin Dadyn nashi, wanda shi kanshi ya kasa gane dalilin hakan.
"Allah Ya ji ƙan Farouk, Ya sa ya huta. Ka yita haƙuri ka ji? Na sani, akwai zafi da raɗaɗi. Akwai ciwo mai tsanani, mutuwar babban aboki. Amma ka daure, ka kai zuciyarka nesa. Ba wai gaggawar tafiya ya yi ba, lokacinsa ne ya yi."
Dady ya ɗan yi shiru daga nan, yana karantar yanayin ɗan nashi, wanda hakan ya ƙara sagar masa da jiki.
Cikin kwantar da hankali ya ci gaba da faɗin,
"Dukkan mai rai mamaci ne, Annur. Yanzu ina Amrah take? Ka manta irin soyayyar da kuka yi da ita? Ka ga kuma, a hakan Allah ya ɗauki rayuwarta. A haka ka ci gaba da rayuwa kamar kowa. Ka jure, ka yi haƙuri, duk da dai kalar ƙalubalen da ka fuskanta a lokacin da ta rasu. Ba na so a kuma ƴar gidan jiya Annur. So nake ka miyar da komai ba komai ba. Ka ci gaba da yi ma Farouk addua, har sadda kai ma taka mutuwar za ta zo ta ɗauke ka."
Tun daga sadda Dady ya fara yi mishi maganar Amrah yake jin gabanshi na faɗuwa. Shi da bai santa