Showing 33001 words to 36000 words out of 201092 words
Chapter 12 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
video ba. Muna kallon komai da yake faruwa a kan idanuwanmu. Sai dai mun gagara furta komai a tsakanin mu duka ukun.
Tashin hankali, wanda ba a saka masa rana. Matar na d'an jijjiga Amrah kad'an, sai ta rikito daga bisa kujerar ta fad'o k'asa.
Take Annur ya sake wayar tasa k'asa a rikice, har sai da ta yi rugu rugu. Ya dafe gefen da zuciyarsa take, idanuwansa suka kawo ruwa, jikinshi ya hau rawa baki d'aya.
A yanda muka ji labarin faruwar abun, wai daga sanda suka ga ta fad'o d'in, hankalin mutane da dama dake wurin ya tashi, take aka yi waya aka kawo ambulance, domin a kai ta asibiti.
Babu jimawa kuwa sai ga motar ta iso, tun wanda suka d'auke ta d'in, suka tabbatar cewa gawa ce, bata raye. Amma gudun akasin haka, yasa suka yi shiru, tare da malaminta, da sauran jakadan Najeriya suka tafi asibiti.
Sai dai suna zuwa, likita ya tabbatar masu cewa bata raye, ta rasu.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Mun shiga tsananin tashin hankali Maryama. Ba zan ta'ba iya kwatanta miki adadin tashin hankalin da muka shiga ba.
Amrah ta rasu, Amrah bata raye, Amrah ta mutu ta bar mu. Shi ke nan mun rasa ta, shi ke nan mun rasa Amrah, ba zata tab'a dawowa gare mu ba.
Malaminta aka sa ya kira ya sanar mana, shi d'in kanshi cikin kuka muke waya da shi, cikin kuka yake sanar da mu abin da ya faru.
A can aka binne gawarta, gudun kar a d'auki dogon lokaci kafin a iso da ita Najeriya. Har da hoton gawar aka d'auka aka gwada a gidajen talabijin da dama, ana sanar da rasuwar baiwar Allah'r da sai da ta gama musaba'karta, a bisa teburin Allah Ya kar'bi rayuwarta.
Duk wani mai imani sai da ya girgiza da wannan al'amari mai matuk'ar d'aure kai. Wadda dubban al'umma sun kalli komai da ya faru. Sun saurari daddad'an karatunta. Sun ga yanda ta rikito 'kasa, har lokacin da aka d'auke ta.
A yadda sanarwar ta zo, Amrah ce ta zo d'aya a wannan musabak'ar, ita ce wacce ta fi kowa maki, ba wai a mata kad'ai ba, har ma da mazan baki d'aya.
Duk wata kyauta tata zasu damk'a ta ga malaminta, da kuma jakadan Najeriya, su isar da ita ga magadanta.
Ko da Malamin nata ya sanar mana a waya, cike da tashin hankali Mallam ya ce masa kar ma ya karb'o, a mata sada'katul jariya kawai da su. Mu kam mun yafe. Kujerar Makkar da aka bata ma, mun sadaukar da ita ga malaminta, ya je ya yi aiki, ya mata addu'a. Saboda a halin tashin hankalin da muke ciki, bana jin zan iya amfani da duk wani abu wanda ya shafe ta.
Annur kuwa dama tun daga lokacin da labarin rasuwarta ya riskemu ya sume, bai sake farfad'owa ba, har sai da ya yi kwana biyar a haka.
Ko da ya farfad'o da sunan Amrah ya tashi, yana fad'in,
"Dan Allah ku ce min mafarki nake, ku tasar da ni daga wannan mummunan mafarkin da nake yi. Wallahi ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. Amrah ce wani 'bare na zuciyata, ita ce tunanina baki d'aya."
Kuka yake sosai, wanda dole duk na kusa da shi sai ya tausaya masa.
Rasuwar Amrah na d'aya daga cikin rasuwar da ta girgiza al'ummar Najeriya. Ta shiga record na Najeriya.
Wai ashe bankwana muka yi da Amrah a lokacin da zata tafi. Ashe ganin 'karshe na mata. Ashe ba zan sake ganin y'ata ba. Ashe mutuwa zata mana yankan k'auna.
Ranar da Annur ya farfa'do ne ya tilasta ma Hajiya Suhaila cewa zai zo inda muke, akwai maganar da yake son yi da mu.
Duk da halin da yake ciki, a haka suka zo, su duka jikinsu sanyaye.
Kallo d'aya na ma Annur hankalina ya tashi, na sake tuno da y'ata, nake ganin kamar tafiya ce ta yi, zata dawo gare ni.
Shi kanshi Annur d'in abun tausayi ne. Cikin lokaci 'kank'ani ya gama zubewa, ya koma kamar zautacce.
Cikin kuka na masu iso, Hajiya Suhaila ce ta zauna bisa tabarmar, Annur kuwa k'asa ya rashe, yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Yana gyad'a kanshi, da alama magana yake son yi amma ta gagara fitowa.
"Sannunku da zuwa Hajiya."
Na furta cike da k'arfin hali, muryata da ta gama disashewa da k'yar ta fito, har ake jin abun da na fad'a.
"Ya kamata ku daina kukan nan haka nan. Bai kamata ku ma Amrah kuka ba, sai dai kukan sabo kawai.
Amma irin mutuwar da Amrah ta yi, mutuwa ce wadda kowa zai yi fatan ya yi irinta.
Amrah ta yi kyakkyawan k'arshe, kuma dama an ce mutum zai tashi a kan abin da ya mutu yana aikatawa, ke nan Amrah zata tashi tana karatun littafi mai tsarki.
Ga Annur nan, shi ya takura lallai sai ya zo, akwai maganar da yake son ya yi da ku."
Ta k'arisa maganar tana mai gya'da kanta.
"Umma..." ya fad'a cikin rawar murya, yana mai k'ok'arin had'iyar k'wallarsa.
"Umma shi ke nan...shi ke nan na rasa ta. Na rasa Amrah har abada, ta tafi ta barni, bayan kuma alk'awarin da muka ma junanmu na rayuwa tare. Amrah ta tafi ta barni..."
Ya sake fashewa da wani kukan.
Ni ma kukan nake sosai, na du'kar da kaina ka'sa, ina k'ara tuna rayuwar Amrah, rayuwa mai cike da abubuwan koyi, rayuwa mai tsananin ban mamaki.
"Umma...bana jin zan ci gaba da rayuwa a doron k'asar nan. Bana jin rayuwata zata yi kyau matuk'ar babu Amrah a cikinta."
Kuka riris yake, kamar jinjirin da ya jima bai ci abinci ba. Shesshek'a yake sosai, idanuwanshi na nunar da tsantsar damuwar da yake cikinta.
_Dan mutum yana fama da wata cuta, ba lallai ba ne a ce ita zata zama silar mutuwarsa. Kar dan kana ciwo, ka ringa tunanin lallai lokacin tafiyarka ya kusa. Ita cuta ba mutuwa ba ce. So da yawa mai lafiyar ma yana mutuwa ya bar wanda yake ciwo. Kamar yanda muka gani a rayuwar Amrah. Mun ga yanda ta kasance mai ciwo, tun tana 'yar shekara d'aya a duniya, har ta gama mallakar hankalinta kullum cikin ciwo take. Mun ga yanda cutar sickler bata zama ajalin Amrah ba. Mun ga yanda ta mutu babu ciwo, sai dai gawarta kawai. Ikon Allah ke nan._
_Ya Allah! Ka sa mu yi kyakkyawan 'karshe. Allah ka sa mu cika da imani. Allah Ya ji k'an magabantanmu. Wanda suka rasa iyaye, Alllah Ya ji k'ansu da rahama. Wanda suka rasa makusanta, ko kuma wasu malamansu, Allah Ya had'a mu a darussalam.
_*I was crying when I was typing this chapter. Ba wai kukan littafin ba, a'a, kukan rayuwa kawai, kukan mutuwa, wacce dole zata zo mana komin daren dad'ewa. Ni, ke, kai, ku dole wata rana zata d'auke mu. Me muka tanadar mata? Idan yanzu Allah Ya zare ranmu, me muka shirya na had'uwa da Mahaliccinmu?*_
wattpadians, comment on each line. Ko da ban samu damar baku amsa ba, kuna raina.
Thanks.
Pinky durling💗
RAZ 2
[8/30, 3:37 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
2⃣1⃣
_*AMRAH NAKE SO* the book, everywhere you go. I don't even know what to say but Thank You very much. Am very very sorry for the last chapter, cuz, every soul shall taste death kaman yanda Allah mad'aukakin sarki Ya fad'a. We're all waiting for it, now, tomorrow, next tomorrow or even next year. Allah kad'ai Ya bar ma kansa sani. Fatanmu dai, Allah Ya sa mu cika da imani._
***
Shiru kake ji a kaf ilahirin gidan, in banda shesshek'ar kukan Annur babu abin da ke fita. Kwana biyar ke nan da rasuwar Amrah, amma kamar yau aka yi ta, kullum d'anya shar take dawo mana.
Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya Suhaila ta sauke, cikin muryar da ke nunar da tausayi ta ce,
"Ka fad'i abin da kake son fad'i, Annur. Ka ga baka da lafiya, mu samu mu koma ka kwanta, Islam ta duba lafiyar zuciyarka. Dan wannan halin da kake ciki, babu wuya zuciyarka ta samu matsala. Though bama fatan haka."
"Gaskiya fa." Na furta had'e da share k'wallar da ta sake fito min. "Amrah ta riga da ta tafi, duk wata damuwa ko kuka namu, ba zasu tab'a dawo da ita ba. Ta tafiya inda ni, da ku duka sai mun je, komin daren dad'ewa.
Addu'armu kawai take da buk'ata, ita ce kawai zata nunar da zallar soyayyar da muke mata. Ta nan kawai zamu saka mata da kyawawan halayen da ta kasance tana da su sanda tana raye."
Kyarma yake sosai, zuciyarsa na tafarfasa da kalamaina. Na yi da nufin ya yi shiru, amma sai k'arfafa kukan nasa ma da ya yi.
Da k'yar cikin wata murya ya ce,
"Ya zan yi rayuwa ba tare da Amrah ba? Ya zan ci gaba da numfashi a doron k'asa ba tare da baiwar Allah'r da aka gina rayuwarmu domin mu so junanmu ba? Ta yaya? Ta ya zan iya Umma? Momy ku fad'a min, ya zan yi da rayuwata? Wallahi *Amrah nake so,* ita kad'ai. Amrah nake k'auna, bata da kishiya..."
Ya sake dafe zuciyarsa, yana wani irin kuka, wanda ban tab'a jin irinsa ba. Ba wani sauti ne da shi ba, sai dai ya bayyanar da yanda yake fitowa kai tsaye daga zuciyarsa.
"...Baki d'aya rayuwata na sadaukar da ita ne gare ta. Hankalina, tunanina duka tare suke da nata. Jini da jijiyoyin jikina duka tare suke gudanya da na Amrah."
Yana kaiwa nan ya runtse idanuwansa, yana mai k'ok'arin danne sabbin hawayen da ke fitowa,
"Mutuwa dan Allah ki zo ki d'auke ni, ki zo ki tafi da Annur, ki kaishi inda Amrah take..."
Saurin dakatar da shi na yi, cikin kuka na ce,
"Kar ka yi sab'o, Annur. Dukkanmu nan ko ba dad'e ko ba jima zamu tafi, zamu je inda Amrah ta je. Dukkan mai rai mamaci ne, haka Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin littafinsa. Baki d'ayanmu jiran lokacinmu muke yi. Ita d'in kanta Amrah ba wai gaggawar tafiya ta yi ba, a'a, iyakacin lokacin da ta d'ibo wa kanta ke nan. Dan haka mu sakawa zuciyoyinmu salama, mu mik'a lamurranmu ga Allah, mu ma Amrah addu'a. Ka ci gaba da addu'a ma kanka kai ma, insha Allahu, Allah zai had'a ka da kamar Amrah, wacce zata soka, kaima kuma zaka so ta kamar Amrah..."
"Ba dai a duniyar nan ba, Ummah. Bana jin akwai mai irin halaye da d'abi'u irin na Amrah. Ko da ma akwai, bata dame ni ba. Ba ma sai idan zan iya ci gaba da rayuwar ba, bare har na had'u da wacce kike fad'i? Mutanen da komai nasu yake a had'e, Umma, kina tunanin lokaci guda zasu iya rabuwa? Bana tunanin haka."
Ya dakata daga nan, yana taunar lab'bansa.
Da k'yar ya iya ci gaba,
"Maganar da nake so na miki, dama alfarma nake nema a gare ki, Umma."
"Ina saurarenka." Na furta cike da tausayinsa.
"Baki d'aya kayan aurenta, da wanda kuka siya, da wanda aka kawo daga gidanmu, nake so ku had'a a gina mata Masallaci babba, ko kuma wata Islamiyya, a matsayin sadak'atul-jariyah. Ina son lada ta ci gaba da kai ma Amrah, ta samu rabo mai k'wari a wurin mahaliccinta."
Wani sabon hawayen ya sake fito min, da k'yar na k'irk'iro murmushi na ce,
"Insha Allahu haka za a yi, Annur. Ko jiya da dare mun fara magana da Mallam, cewa nan da kamar sati d'aya zamu had'a komai da kuka kawo a mayar maku, saboda mu dai nan babu abin da zamu yi da su wallahi. Ganinsu da nake ma sake shiga tashin hankali kawai nake. Ina tuna mai su, wacce babu wanda ya tab'a tunanin ba zata amfane su ba."
A wannan ga'bar kam, Hajiya Suhaila kanta kuka ya kufce mata, wanda da alama tun zuwansu yake son fitowa, take yak'i da shi domin ya koma.
"Haba Maman Amrah. Ke ma kanki kin san ba zamu tab'a kar'bar kayan nan ba. Yanda suka fito daga gidanmu, suka zo nan gidan da nufin na Amrah ne, to natan ne. Duk ma yanda zaku yi da su dai sun zama na magadanta. Maganar da Annur ya yi mai kyau ce. A mata sadak'atul-jariyah kawai."
Mallam da ya shigo daidai nan ya jinjina kansa, samun wuri ya yi ya zauna a kusa da Annur, ya dafa kafad'arsa cike da bashi k'warin guiwa, murmushi lullub'e a saman fuskarsa.
"Annur, d'ana." Ya furta idonsa cikin nashi.
"Kai fa namiji ne ba mace ba. Ya zaka ringa yin abubuwa kamar dai mace? Ko ka manta dama rayuwar tamu dukanta aro ce, watan wata rana sai wanda Ya bamu aron Ya karb'e abarSa? Ba zan hana ka yin kuka ba, sai dai kuma a ganina sam! Amrah bata cancanci a mata kuka ba. Yarinyar da duk wanda ya bud'e bakinsa shaidar kirki zai bata. Duk wanda ya san Amrah ya santa da halayen kirki. Natsuwa, girmama mutane, karamci, kamun kai, duka halayenta ne. Ka ga kuwa ai ba abar a mata kuka ba ce. Tun daga sanda aka yi sanarwar rasuwarta, yau kwana biyar ke nan, babu ranar da ba a fad'in rasuwarta a gidajen radio, babu ranar da ba a d'ora karatunta a gidajen talabijin. Kullum da mutanen da suke kirana a waya, da wanda suke zuwa har gida, ba wai dan sun sanmu ko ita Amrah'n ba, sai dan labarin rasuwarta da ya kewaye al'umma. Dan Allah Annur ka cire damuwa daga zuciyarka. Kar ka bari damuwa ta illata maka zuciya, kai d'in ma mu rasaka kamar yanda muka rasa Amrah, ba zamu so hakan ba."
Sai a nan Mallam ya dakata, ya saki kafad'ar Annur d'in, yana masa murmushi mai tabbatar da maganganun da ya fad'a masa.
Hajiya Suhaila ta ce,
"Ni kaina abin da na nunar masa ke nan. Allah fa baYa barin wani dan wani ya ji dad'i. Amrah kuma lokacin tafiyarta ne ya yi, kuma dole zata tafi ko ba dad'e ko ba jima, ko da ba yanzu ba."
"Haka ne, Hajiya. Akwai damuwa kam, amma dole sai an daure."
"Yanzu Annur ka tashi ku je, a duba mana lafiyarka. Dan Allah." Na fad'a bayan na sauke ajiyar zuciya.
Tashi kuwa ya yi jiki babu k'wari, tangal tangal ya yi kamar zai fad'i, sai da Mallam ya hanzarta ri'ke shi da iya k'arfinsa.
Har mota ya kai shi ya zaunar, sannan ya ma Hajiya Suhaila bankwana ya dawo gida.
A lokacin da ya dawo, ya same ni ni d'in ma na dasa wani sabon kukan, tausayin Annur da kuma rayuwar da zai fad'a kawai nake.
Ranar da Amrah ta cika sati da rasuwa Mallam da kanshi ya fidda komai nata, aka sadakar da wasu, wasu kuma aka had'a shi da wata mata wacce ke siyan komai na aure, tun daga kayan d'aki, zuwa kayan lefe da komai ma.
Siyan wulak'anci ta ma kayan, amma a haka sai da aka had'a kud'i kusan miliyan d'aya da dubu d'ari biyu, dan inda siyayyar mutunci ta masu ma, sai sun kai miliyan uku. Ko lefenta kad'ai ya fi miliyan da rabi.
Da wannan kud'in ne aka gina wannan Islamiyyar, da su ne aka saka duk wasu kujerun da suke ciki. Aka saka ma islamiyyar suna *MADRASATUL AMRAH BNT ABDALLAH.* Kud'in da yara ke biya duk wata da su ne ake biyan Malaman albashi daga farko, amma daga sanda Islamiyyar ta bunk'asa sosai, gwamnati ta d'auki nauyin albashin malaman, kuma aka yi sa'a hakan ya d'ore. Kud'in makarantar yara kuma duk wata ake kaiwa gidan marayu, da nufin Allah Ya kai ladar ma Amrah.
Annur kuma tun daga ranar da suka yi wannan zuwan shi da Hajiya Suhaila, ban kuma jin labarinsa ba. Ranar da abun ya dame ni, na yanke hukuncin zuwa har gidansu don jin halin da yake ciki.
Tare da Mallam muka kama hanyar gidan nasu, ko da muka isa, kai tsaye aka mana iso har d'akin Hajiya Suhaila.
Ko da ganinmu kuka ta fasa da 'karfi, wanda har sai da ya razanar da ni. Kukan nata ba na wasa ba ne, duk wani mai zuciyar imani dole zai tausaya ma Hajiya Suhaila, ganin Babbar mace na kuka wiwi, kamar k'aramar yarinya.
Da hanzari na isa inda take, na dage idanuwana da ruwan hawaye suka fara fitowa, na zauna k'asan kujerar da take.
"Hajiya Lafiya?"
Na furta cikin k'arfin hali.
"Babu lafiya, Maman Amrah."
Sanda ta fad'i maganar ras! Na ji gabana ya fad'i, jikina ya d'auki rawa, lab'bana sai k'yarma suke, ina son yin magana amma na kasa.
"Annur ya haukace, Maman Amrah. Ya haukace tuk'uru hauka yake."
Mik'ewa na yi tsaye ina zare idanuwa, da mamaki na ce,
"Hauka, Hajiya Suhaila?"
"Hauka kuwa. Tun ranar da muka baro gidanku na rasa gane ma kansa. Sai sabbatu yake yana fad'in *"AMRAH NAKE SO"* ya yi dariya, sai kuma ya fashe da kuka a k'arshe. Gudu yake tik'awa iya k'arfinsa wai zai je inda Amrah take, sai an kamo. Abun kamar wasa, yanzu haka yana wancan d'akin an d'aure shi. Saboda idan aka sake shi, ko an rufe d'akin ya ringa bubbuga shi iya k'arfinsa ke nan. Ya nemi b'ab'balla komai dake cikin d'akin. 'Yar uwarsa ce ke masa allura, kafin mu ga gudun ruwan abun."
Ta k'arisa maganar da sadda kanta, tana kuka sosai.
Ni d'in kaina kukan nake, jin shi nake tamkar d'an da na haifa da cikina, saboda duk wata damuwa ta Annur tamkar tawa ce. Yadda Annur ya kula da Amrah sanda tana raye, ya so mu, ya kula da rayuwarmu baki d'aya. Dole in damu da shi, in damu da halin da yake ciki.
Mun nemi mu ganshi ta raka mu har bakin d'akin, sai dai ta taga muka hango shi kwance yana bacci, wai Islam ce ta masa allurar bacci.
A haka muka dawo gida jiki sab'ule, babu mai furta komai a tsakaninmu ni da Mallam.
_Ba a gama halittar mutum har sai sanda ya kwanta damarsa. Ka san farkonka, haihuwarka aka yi. Ka san k'arshenka, mutuwa zaka yi. Amma baka san tsakiyarka ba, baka san me zai same ka ba, baka san wace gwagwarmaya zaka fad'a ba. Wasu su zama nak'asassu, bayan lafiya lau aka haife su.