Showing 78001 words to 81000 words out of 201092 words
Chapter 27 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
san inda zan samu kuɗin siyan su ba."
Gyaɗa kansa ya yi, da tausayi ya ce,
"Halan har nawa ne kuɗin?"
Bayani ta masa na kuɗin maganin, da kuma adadin wanda ake so ya shanye. Ta ƙarashe da faɗin,
"Ya ce duk da abun ba mai girma sosai ne ba, zai iya zama mai girma in dai ba a daure an sai mai maganin nan ba."
Da sabon kuka ta dire maganar, ta sake duƙar da kanta a guiwowinta.
Dafe kansa ya yi, zuciyarsa na masa raɗaɗi, tausayin Modu yake, ji yake tamkar ciwon a jikinsa yake. Ina ma dai a ce yana da kuɗin siyan maganin nan? Bai da su. Shi kan shi rufin asiri ne da shi. Lokacin da ya kaɗe Modu ma daga wurin neman aiki ya dawo, kuma bai samu ba. Tashin hankalin da yake ciki a lokacin, ba wai na lururar mahaifiyarsa ne kawai ba, har da takaicin wahalar da ya sha wurin neman aikin, kuma a ƙarshe ya ƙi samu.
Ajiyar zuciya ya sauke, cikin kwantar da hankali ya ce ma Fiddou,
"To do Allah dai ki cire damuwag ga daga cikin zuciyarki. Kar wani abu ya same ta, kin ga dai yanda ta Modu tai yi."
"Ba zan iya ba, ba zan iya ba Mahmouda! Modu na cikin haɗari, haɗari mai wuyar shawo kai. Ban san yanda zan yi ba, ba ni da halin taimakonsa."
"Allah zai rufa asiri, ki kai kokenki kawai wurinSa, ba Ya gyangyaɗi Allah, Yana jin ƙan bayinSa, Yana kuma karɓar adduar bayinSa a duk sanda suka kai maSa kokensu."
Shiru kawai ta yi tana kallonsa. Mamakinsa take, mamakin kalamansa take. Ta ya za ta iya kwantar da hankalinta bayan kuma ba ta da wata mafita?
***
Mai napep ɗin take ɗaga ma murya ta yanda zai iya jin ta sosai, saboda sautin da ya kunna a ciki.
"Mallam!"
Ta faɗa a karo na biyar, da ƙarfi fiye da yanda ta kira shi a baya.
Rage sautin ya yi sannan ya ce,
"Lafiya? Ai kaman ba a zo inda zan kai kin ba."
"Ehh ga shi tana kira na cewa mu dakata ta hange ni. Dama ita ce ba ta yi kwatancen da kyau ba."
Reverse ya yi, saboda sun wuce ta da yawa. Bayan sun kai inda take ta sauka, ta miƙa masa kuɗinsa sannan ta ta yi taku uku, wanda ya kai ta gaban Hadiza.
Hannu ta ba ta suka gaisa. Da fara'a Maryama ta ce,
"Ai da mun zarce kuwa."
Ita ma Hadiza ta yi murmushin, ta ce,
"Ban wani san kan area'n sosai ba, shi ya sa ma na zaɓi nan ɗin. Kuma ga shi babu hayaniya sosai, babu ƴan sa ido."
"Haka ne."
Hadiza ta faɗa.
"Mu je. Akwai wani babban lambu ta can baya. Sai mu biya kuɗin shiga mu shiga, kamar za mu fi samun natsuwa a ciki."
Bin bayanta ta yi suka nufi hanyar lambun, ba su wani yi tafiya mai nisa ba suka isa.
Maryama ta fiddo kuɗin za ta bayar amma Hadiza ta hana, ita da kanta ta ciro kuɗin ta bayar.
A bisa wasu ƙayatattun kujeru suka zauna, babu jimawa aka kawo musu lemuka aka jera a gabansu.
Ajiyar zuciya Maryama ta sauke, ta ce,
"Mun fara magana a waya."
Buɗe robar fanta ta yi Hadiza, ta ɗan kurɓi kaɗan, sannan ta rufe, ta ajje a gabanta. Fuskantar Maryama ta yi da dukkan nutsuwarta, ta saita idanuwanta a cikin nata, ta ce,
"Yanda duk na faɗa miki a waya to hakan ne. Annur ko kaɗan bai zama mutumin kirki ba, face fasiƙi! Mazinaci! Mayaudari!"
Ta yi shiru daga nan, sannan cikin rauni ta ci gaba,
"Ina ƙaunar Annur, da dukkan zuciyata. Ina burin ya kasance nawa, na har abada. A da, ban taɓa tsammanin akwai namijin da zan ma soyayyar tsakani da Allah ba. Ban taɓa tunanin zan so yin aure a wannan ɗan taƙin ba. Sai ga shi na dulmiya, ban farga ba, zuciyata ta tsunduma da ƙaunar Annur Iqra Al-hussein. Ƙaunar da nake masa ta gaskiya ce, wacce hankalina zai tugunzuma a duk sanda zan ganshi cikin wata larura, ko kuma damuwa. Wannan dalilin ne ya sa zuciyata ta ba ni tabbacin Annur ne na gani a Maraɗi. Zuciyata da ta shi kamar akwai wani connection a tsakaninsu; wanda ke ba ni tabbacin cikin halin da rayuwarsa take.
Abin da na kasa in gane shi ne, shin a cikin awanni shidda ne Annur ya tafi Maraɗi? Me ya kai shi? Me zai shigar da shi cikin wannan halin, ba tare da iyayensa sun sani ba?
Akwai alamar tambaya a zancen nan. Da alama dai akwai ɓoyayyen al'amari, wanda daga Annur ɗin sai mahaliccinsa kawai suka sani..."
"Sai kuma abokinsa Farouk Sardauna!"
Ta tsinkayo muryar Maryama ta faɗa, tana jinjina kai.
"Na tabbata Bobby bai rasa masaniya dangane da wannan al'amarin, tunda kansu a haɗe yake, gudansu ba ya yin abu ba tare da shawarar guda ba. Duk wani mugun halinsu tare suke aikata shi."
Ta dakata daga nan, jin wayarta na ringing. Dubawa ta yi sai ga sunan Bobby ɓaro ɓaro ya fito, hakan ya sa ta sakin murmushi, ta ce,
"Kin ga ɗan halak!"
Ta amsa kiran, tana ƙoƙarin gyara muryarta daga ta murmushin da take, zuwa ta asalin Maryama ɗinta.
"Hello-salamu alaikum."
Ta furta a tsanake, da muryarta dallah-dallah.
"Maryama ya kike? I have been calling you amma bakya ɗauka. Fatan dai kina lafiya. Ya gida? Ya school? Wai, ashe hutun easter ake. Ya su Mama? Ya..."
Ta gaggauta dakatar da shi, dan wannan surutun na shi ba mai tsayawa ba ne.
"Everything is okay."
Ta faɗa a takaice, tana kuma jiran abin da zai faɗa.
"Uhm...dama Maryama please ina so ki ba ni lokaci mu haɗu. Ina da buƙatar ganinki, idanuwana na matuƙar son su yi tozali da kyakkyawar fuskarki, mai cike da walwala."
'Ya Allah!'
Ta faɗa cikin zuciyarta. Surutun Farouk yawa ne da shi. Duk haƙurin mutum sai ya ƙule sa.
"Farouk na sha faɗa maka cewa iyayena ba za su taɓa bari na tsayuwa da kai ba. Na rasa me ya sa ba ka fahimta. Ba wai ba na sonka ba ne, wallahi halayenka ne ba na ƙauna. Kai ma ka san ba ka da wani abu da zai sa a ƙi ka, fa ce gurɓatattun halayenka, wanda babu na ɗauka a cikinsu."
"Da sauƙi Maryama. Tunda dai kina so na shi kenan, kin gama min komai wallahi. Na tabbata iyayenki abin da kike so shi za su so. Wallahi zan zama na kirki saboda ke..."
"Saboda ni?"
Ta tari zancen nasa.
"Kenan ba saboda Allah za ka nadama ba? Ashe dai tubar ba ta zama ta kirki ba kenan. Duk abin da aka yi saboda wanin Allah, to wannan abun ya zama riya, Farouk."
"Please ki fahimce ni, ba wai ina nufin haka ba ne."
"Ya kake nufi Farouk? Hausa fa ka yi, wacce kai tsaye za a iya fahimtarta."
"Yanzu dai ba wannan ba. Ki min alƙawari in dai na daina komai za ki aure ni."
Ya marairaice murya haɗe da yin wannan maganar.
"Ni kam ba wannan ba, akwai maganar da nake so mu yi da kai."
Ajiyar zuciya ya sauke haɗe da faɗin,
"Allah sa alkhairi ne."
Bayyanannen murmushi ta yi, irin mai narkar da zuciya ɗin nan, wanda ke faranta ran Farouk Sardauna.
"Alkhairi ne ma."
Ta ɗan dakata haɗe da murmusawa, sannan ta ce,
"Wai dan Allah waye Annur?"
Shiru ya ɗan yi na tsawon sakan goma, kafin ya ce,
"Wani abu ne?"
Ya gaggauta tambayarta.
"No, kar ka zata wani babban abu ne. Kawai dai tambayarka na yi."
"He's my best friend. A best friend of mine."
"Good. Can you tell me little about him?"
"Yes, why not?"
"Great."
Ta faɗa haɗe da gyara zamanta, ta ɗan kalli fuskar Hadiza da murmushi. Ita ma Hadiza murmushin ta sakar mata, duk da yake ba ta san inda zancen ya dosa ba.
"He's Annur, a son of Pharm Iqra Al-hussein. He's a nice person. Mutumin kirki ne mai riƙon addini..."
"Kamar kai kenan?"
Ta tari zancensa tana murmushi.
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce,
"What do you mean?"
"Just a question."
Ta ambata har yanzu ba ta daina murmushi ba.
Ko kaɗan ba ya jin zai iya kasa faɗawa Maryama tambayar da ta masa. Amma wallahi in da a ce wata ce ba ita ba, har marinta yana iya yi idan ta masa wannan tambayar banzar. Idan kuwa a waya ne to tsaf zai iya zagin iyayenta, sannan a ƙarshe ya kashe kiran.
"Lemmi tell you the fact; Annur is a nice person, as I told you. But...ehm...duk halayemmu iri ɗaya ne. Amma dan Allah me ya sa kika min wannan tambayar?"
"Babu komai fa. Kawai dai ƙawata yake so ne, shi ne take faɗa min sunanka wai kai ɗin abokinsa ne. To ina jin sunan kuma na gane kai ne. Ta ce na bincika mata halayensa ne."
Ta canza akalar zancen, ba haka suka yi da Jiddah ba, kawai dai shawara ta sake ne da zuciyarta. Ba yanzu ya kamata ta bayyana ma Farouk manufar Annur ɗin a kanta ba, gwara komai a bi shi a hankali, da sannu za a zo wurin.
"Ok...ok thats nice."
Ya faɗa da sauri don kar ta sake yo masa wata tambayar.
"Har ɗazu ma mun tafi Maraɗi tare da su ai. Ƙawar tawa ce ta je gidan danginta a can, to sai muka tafi tare ya kai mu."
Cikin mamaki ya ce,
"Amnur ɗin?"
"Ehh fa. Sai dare ma muka dawo, suka sauke ni har gida."
"Gaskiya ba dai Annur nawa ba ne. Saboda tun safe muke tare da shi, har dare sannan ya tafi gida. Da alama dai wani ne ba shi ba."
"Ina tababa fa."
"Wallahi gaskiya nake faɗa miki. Tun safe muke tare ba mu rabu ba. Babu inda ya je, wata ƙila dai mai irin sunan ne."
Gudun kar ta yi insisting ya gano ta ya sa ta ce,
"To ina ji dai kam sunan ne ya zo ɗaya. Ƙila kuma wani Farouk ɗin ne daban abokinsa ba kai ba ne."
Ƙwalwar banza irin ta ƴan shaye shaye kawai Bobby ya ce,
"I think so. Lets back to business bae. Ina muka tsaya?"
"Call me later, please. Am busy right now."
"Please ki ɗauka idan na kira ki. Bana jin daɗin rashin ɗaukar nan da kike sometimes idan na kira ki."
"Insha Allahu zan ɗauka. I promised!"
Ta faɗa haɗe da gaggauta tsinke kiran, ta fuskanci Hadiza da fara'a.
"Done."
Ta furta bayan ta ajje wayar bisa cinyarta. Ta be lemon sprite, ta kurɓa a bakinta.
"Me hakan ke nufi? Ya shafi aikin da muke ne?"
Hadiza ta faɗa, saboda ita ɗin ba wai tana gane turanci ba ne.
Bayan ta ajje lemon ta ce,
"Sosai ma kuwa. Ina hankalinki ya tafi sanda muna wayar?"
"Yana tare da ni."
Ta faɗa a taƙaice.
Cikin halin ko in kula Maryama ta ce,
"Na gano abin da nake son sani. Ya bayyana min muhimmin abin da ya kamata na sani."
Shiru ta yi Hadiza tana sauraron Maryama. Lemonta take sha a tsanake.
"Ya shaida min duk yinin jiya yana tare da AIA. Ko kaɗan ba su rabu ba."
"Waye AIA kuma?"
Dafe kanta ta yi Maryama. Duk iya haƙurinta na jure tambayoyi Hadiza na neman ƙular da ita. Tambaya mara ma'ana, wacce ya kamata a ce ta san amsar. Guntun tsaki ta yi a bayyane, ta ce,
"Ban san dalili ba, kamar dai ƙwalwar taki ba ta ja yanda ya kamata. Ko kaɗan ba na son hulɗa da mutum irin haka."
Kallonta Hadiza ke yi cike da jin haushinta. Kawai dan ita ɗin kanta tana son sanin haƙiƙanin abin da yake faruwa ne, amma da tuni ta gwadawa Maryama halinta na tashanci, wanda take ma duk wani wanda ya nemi ya kawo mata wargi a lamurranta.
"Ko kaɗan ba su rabu da Annur ba jiya. Suna a cikin garin nan. Kin ga kenan dai ba Annur ba ne kika gani a Maraɗi..."
Miƙewa ta yi tsaye a fusace, cike da masifa ta ce,
"Ke kar ki nemi miyar da ni shashasha mana! Ta ya da idona in ga mutum kuma ki nemi ƙaryata ni? Dan Bobby ya faɗa miki son ransa dole ne sai ya zama gaskiya? To ni dai ko ki yarda ko kar ki yarda na ga Annur a Maraɗi jiya. Ko tantama babu shi ne na gani."
Miƙewa ta yi ita ma Maryama, ta dafa kafaɗar Hadiza, da murmushi ƙunshe a fuskarta ta ce,
"Calm down Hadiza. I din't mean to hurt you. Dawo ki zauna mu ci gaba da maganarmu."
Ba dan ta so ba ta koma ɗin ta zauna, tana mai tsananin jin haushin Maryama.
"Ko kaɗan kar ki zaci wai na ƙaryata ki ne Hadiza. Wallahi na yarda da ke ɗari bisa ɗari. Na tabbata idan har ba ki ga fuskarsa ba, ba za ki ƙirƙira ba."
Sai a sannan Hadiza ta ɗan ji sassauci a ranta. Amma fa har yanzu ba ta daina jin takaicin Maryama ba.
"Am very confused. Baki ɗaya kaina a ƙulle yake. To ko dai Annur ɗin biyu ne wai? Ina nufin ko akwai mai irin kamanninsa ne? Idan ba haka ba, ya za a yi wanda ke Nigeria ya tafi Maraɗi cikin awanni shida, kuma a cikin awannin nan shida ya haukace, sannan zuciyarsa ta samu matsala? Kamar dai akwai alamar tambaya."
Shiru Hadiza ta yi tana nazarin kalaman Maryama. To ko dai haka ɗin ne? Amma kuwa kamannin na su ta yi yawa. Ba su da bambanci ko kaɗan.
"Ina so ki nutsu, ki kuma yi tunani mai kyau. Ya za a yi Annur ya haukace kuma ya warke cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da wani makusancinsa ya sani ba? Idan ma hakan ta kasance, kina tunanin zaluciyarsa za ta samu matsala a iya wannan lokacin, har likita ya kula da shi, a ƙanƙainin lokacin nan? Kamar dai ciwon ya daɗe a jikinsa."
Sai a sannan Hadiza ta faɗa kogon tunani. Tana ƙara tuna yanayin da ta ganshi. Haƙoransa baki ɗaya rinannu ne. Kayan jikinsa lalatattu, matattu. Sumar nan ta shi ƙazan ƙazan, duk ta cukurkuɗe. Fuskarsa duk ƙasumba, wadda ke ƙunshe da ƙazanta sosai.
"Na yarda da batunki Maryama. Tabbas na amince, ba Annur ba ne na gani. Sai dai kuma kamar tasu har ta yi yawa. Ko kaɗan ba su da bambanci."
Sosai Maryama ta ji daɗi da Hadiza ta fahimce ta. Ta ce,
"Ina neman alfarmarki guda ɗaya tal, Hadiza."
Laɓɓanta ta tsotsa duka biyun, bayan ta fiddo ta ce,
"Ina jin ki."
Gyara zamanta ta yi Maryama, ta ce,
"Za ki iya raka ni mu je Maradi?"
To fa! Tafiya Maraɗi ta taso. To ita Maryama ya za ta yi da gidansu? Ko iyayenta za su amince mata ta tafi Maraɗin? Ta wacce hanya za ta bayyana musu tafiyar ma? Ya za ta kaya idan ta haɗu da Modu? Ya za su yi ita da Fiddou idan sun haɗu? Akwai fa cakwakiya mai girma, wacce duk iya hasashemmu ba za mu iya cankowa daidai ba, dole sai dai alƙalamin marubuciyar ne kawai zai iya warware mana. Fatana dai a juri bibiyar marubuciyar, sannu a hankali za ta warware mana komai.
Gaisuwa haɗe da jinjina ga ƴan Zauren Sadiya novels. Ina yinku, ina ƙaunarku, ina son ku all fi sabilillah!
Thanks all for the love and care. Ina ƙaunar duk mai karanta littafin nan, har ma da wanda ba sa karantawa amma suna sharing ɗinsa.
To wattpadians, gaskiya na raina yawan votes ɗin ku. Da alama dai kun fi son ƙananan pages. To hakan zan muku, idan kun shirya ma dogayen pages, sai in ga votes da yawa.🤓
RAZ Aminnan juna, jinjina ta musamman. Allah ya ƙara ɗaukaka amin.
My Xarah BB, congratulations for the successeful completion of your novel named AMINAN JUNA. A very educated novel. Allah Ya ƙara miki ɗaukaka da nisan kwana. Fatan ana ba ma ɗammu kyakkyawar kula, yanda ya dace.😘
To my Sis, Rabiatu sk msh. We are still waiting for you fa. Kin san komai ba sai na bayyana ba.😸
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:52 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
4⃣1⃣
Follow me on wattpad:
PrincessAmrah
Aunty Sady Jegal
Khadeeja Candy
Ashnur pyaar
Miemie Queen
Qurratul-ayn
Easha md
Fauziyya Ammany
Lainat
Meelah Adeel
Wannan shafin na ku ne kyauta. Na gaishe ku, ina son ku, ina ƙaunarku all fi sabilillah.
***
Cike da mamaki ta kalli Maryama, kamar dai ba haka ta so faɗi ba. A kan wane dalili za ta ce wai su tafi Maraɗi? Miye damuwarta ne ma wai? Tunda dai sun tabbatar da ba shi ɗin ba ne, a ganinta ai gwara kawai a bar maganar.
Saurin barin tunanin ta yi ta miyar da hankalinta ga Maryama, ta ce,
"Mu je Maraɗi?"
"Kin ji me na faɗa ai. Ba kya buƙatar maimaici."
Jinjina kanta ta yi Hadiza, ta sauke ajiyar zuciya haɗe da faɗin
"Amma, me ya sa kike son mu je Maraɗi? A gani na ai babu wani abu da ya shafe ki da shi, tunda dai mun tabbatar ba Annur ɗin ba ne."
Guntun murmushi ta saki Maryama, ta gyaɗa kanta, ta sake surɓar lemo tana faɗin,
"Uhm...na san abin da nake..."
Ta ƙarisa haɗe lemon daga bakinta, ta rufe gorar lemon ta ajje a bisa teburi.
"...ke da kanki kika faɗi cikin halin da wancan ɗin yake ciki. A gani na tunda dai muna da halin taimakonsa, daga ni har ke ɗin, bai kamata mu zauna ba. Allah Yana jinƙan duk wanda yake jinƙan mutane. Ko bakya son samun lada ne?"
Murmushin yaƙe ta yi Hadiza. Ba ta iya furta komai ba saboda yanda Maryama ta yi maganar, ba za ta iya cewa a'a ba.
"Na san kina da halin taimakonsa. Ki fiddo kuɗi ni ma zan ƙoƙarta fiddowa, mu je Maraɗi mu taimaki bawan Allah'n, mu masa gata, dan Allah!"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba. Ta san tana da kuɗi kam tabbas, wanda ita kanta kai tsaye ba za ta iya faɗin adadin kuɗin da suke cikin account ɗinta ba, sai idan ta yi checking balance ne.
"Ki taimaka, na yi alƙawari ni ma zan taimaka da dukkan abin da Allah Ya hore min. Baya ga haka, ina son ganinsa, ina son sanin ainahin waye shi? Ta yiu akwai abin da zai iya taimakona da shi."
Babu abin da Hadiza ta fahimta a maganar Maryama ta ƙarshe. Kawai dai ta ce,
"Ni ma na yi alƙawarin taimaka masa iya ƙarfi na."
Kama hannunta ta yi Maryama, da murmushi ƙunshe a fuskarta ta ce,
"Alhamdulillah! Na ji daɗi sosai da wannan. Allah Ya ba mu ikon taimaka masa. Allah