Showing 120001 words to 123000 words out of 201092 words
Chapter 41 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
Dadyn Farouk ɗin kuka yake. Zuciyarsa na masa tuƙuƙi, ya dafe kanshi da ɗayan hannunsa.
Bayyanannen kuka Sans ke yi, mai cike da nadama da da na sani. Me ya hana su zama mutanen kirki? Me ya sa a lokacin da Bobby ya fara ƙoƙarin ɗora shi a turbar banza, bai fahimtar da shi gaskiya ba? Bai faɗa masa babu kyau maye ba?
Cikin wannan halin ne suke amsar gaisuwar. A duk sadda wani zai tambaye shi ya haƙuri? Lokacin ne kuka ke ƙara zo masa. Zuciyarsa ke ƙara azabtuwa da rashin babban amininsa, mai share masa hawaye a duk sadda zai shiga cikin damuwa. Ya sani, ya san cewa ba zai taɓa samun madadin Farouk ba. Ba zai taɓa samun mutumin da zai zame masa tamkar Farouk Sardauna ba.
***
A bisa sofa yake zaune Abba. Mug ne a hannunsa wanda yake maƙale da hoton Maryama na sauka. Dama kuma tadarsa ce, duk dare sai ya sha ruwan lipton kafin ya kwanta.
Zaman dirshan ta yi a gabansa, tana ƙoƙarin haɗiye sabon kukan da ke niyyar kufce mata.
"Barka da dawowa Abba."
Ta yaƙi zazzafar zuciyarta wurin tsamo wannan maganar a dunƙule, ta furzo ta waje.
"Yauwa Sarauniyar Mata. Tun ɗazu ƴar Baba ba ta zo ta ma Baba barka da zuwa ba. Ko karatu ake ne?"
Kanta ta sadda ƙasa, ta ce,
"Ehh Abba. Ban ma ji shigowarka ba."
"To babu komai ai haka ake so. Ya kamata ma dai ki koma makaranta haka nan, kusan satinki biyu rabon da ki je fa. Ko har yanzu ba a darasin sosai ne?"
"Abba mun yi covering ne, exam za mu fara next week."
Ta faɗa, har yanzu ba ta ɗago kanta ba. Wanda duk ta sanadin ta tsaya ta kula da Modu ne ta daina zuwa, da gaske sun yi covering ɗin, amma da babu Modu, da za ta ringa zuwa, saboda shiga Libry yin karatu.
Bayan ya ajje mug ɗin bisa side drawer, ya ɗora idanuwansa ga Maryama, haɗe da maida dukkan hankalinshi gare ta.
"Wata shawara ce Yaya Imrana ya yanke..."
Ras! Ta ji gabanta ya faɗi. Ji take tamkar ta ɗora hannuwanta a ka ta kurma ihu.
"Cewa za a haɗa ku aure da Babana Ahmad, tunda dai har yanzu bai tsaida mata ba, ke ma kuma ba ki tsaida miji ba. Na tabbata za ku ji daɗin wannan haɗin, koda a gaba ne za ku gode mana."
Kukan nata bai iya ɓoyuwa ba, dole ya bayyana. Shessheƙa take ƙasa-ƙasa, ta dafe goshinta da hannun hagunta. Hakan ya tabbatar ma Abbanta cewa zaɓin bai mata ba.
Cikin kiɗima mahaifinta ya ce,
"Maryama me kike ma kuka? Kar dai ki ce min haɗin ne bai miki ba."
Kanta ta ɗaga bayan ta ɗago da fuskarta ta dube shi. Ta kuma sunkuyar da kanta a karo na biyu, kukan nata na daɗa yin ƙarfi.
"Don girman Allah Maryama kar ki baɗa min ƙasa a idanuwana. Yaya Imrana mutum ne mai halacci, wanda ya min abin da har in kwanta damata ba zan taɓa mantawa da shi ba. Ya kyautata min, ya riƙe ni da amana a matsayina na ƙaninshi, da iyayemu suka mutu suka bar mu mu biyu kacal, bayan duk danginsu sun guje mu. A lokacin da nake karatu Yaya Imrana ya hana kansa ci da sha, don ganin kawai ya biya min kuɗin makaranta. Akwai lokacin da shekara ta zagayo, shi kuma ya gama UDUS, yana fama da babu, saboda wahala da ɗawainiyar project. Har aka kusa rufe portal ban biya kuɗin makaranta ba. Hakan ya saka shi shiga tsananin damuwa. Ya fara buga can buga nan, don ganin na tsira, na ci gaba da karatuna. Wallahi Maryama har dako Yaya Imrana ya yi, don kawai ya biya min kuɗin karatuna. Tuƙin baro ya yi shi, in taƙaice miki zancen, a wahalce, ni da zai biyama ɗin ma ban wahalar da ya sha ba, ya samu da ƙyar ya biya min wannan kuɗin.
Ci da sha da suturata duk a kansa take, saboda shi ya fi ni zafin nema, ya iya aikin ƙarfi sosai, ni kuma ina da laziness.
Daidai da auren mahaifiyarki ga ta nan zaune da ranta, Yaya Imrana ya min. Ban san duk wata wahalar neman aure ba, saboda a lokacin har ya fara aikinsa, kuma yana ɗan kasuwanci bakin gwargwado.
Maryama da me zan iya saka ma Yaya Imrana? Shin kina tunanin zan iya tinkararsa da zancen wai ba kya son ɗan da ya haifa da cikinsa? Impossible! Wallahi ba ki isa ba! Ba zan iya wannan butulcin ba."
Ya ƙarisa wannan maganar da miƙewa tsaye, ya fara jeka-ka-dawo a farfajiyar ɗakin.
Sosai kukan da take yi ya tsananta. Wai yanzu da gaske Deedah ake son aura mata? Kar fa abin da take ga kamar ba zai yiwu ba ya yiwu. Ya za ta yi da Annur?
"Alhaji a yi haƙuri. Insha Allahu Maryama ba za ta taɓa ba mu kunya ba. Za ta amince da auren Ahmad."
"Ko ta amince ko kar ta amince dole a ɗaura wallahi. Yarinya ƙarama kamar Maryam ba ta isa ta saka ni jin kunya ba. Wato a haka kike son ki yita zama babu aure ko? To ba ki isa ba! Aure babu fashi, kuma cikin kwanakin nan. Tashi ki fice min da gani!"
A guje ta bar ɗakin ta nufi nata. Muhammad ma bin bayanta ya yi, yana kallon yadda ta faɗa bisa gadon da ƙarfi, tana yin kuka mai sauti.
"Am sorry Yaya Maryama. Abba is so angry. Ki bari har ya huce, am very sure zai saurare ki."
Ɗago rinannun idanuwanta ta yi ta kalli Muhammad.
"Har yaushe kuma Hammad? Rantsuwa fa Abba ya yi. Tunda nake da shi ban taɓa ganinshi a cikin yanayin damuwa ko kuma ɓacin rai irin haka ba, sai yau. Ka sani, Mama ita ce ma mai zafin rai, amma Abba ba ya ɓacin rai, ko ɓata masa rai aka yi yana da wuya ya nunar. Tunda har ka ga haka kuwa, na tabbata ba zai taɓa juyuwa ba.
Mama ta taɓa bani wani labari, cewa duk yadda muke ganin Abba da sauƙin kai da sauƙin hali, akwai lokutan da idan ya yi fushi ba ya da sauƙi. Babu kuma wanda ya isa ya sauko da shi sai Kawu Imrana..."
"To kawai ki haɗa shi da kawu Imranan."
Muhammad ya dakatar da ita da faɗin haka.
Murmushin takaici ta yi, ta ce,
"You don't know anything Hammad. Ka manta cewa Kawu Imrana shi ne mahaifin Yaya Deedah?"
"Ban manta ba Yaya Maryama."
"To kuma sai in kai ƙarar Abba wurinsa cewa zai haɗa ni aure da ɗan da ya haifa? Ka ga ai ba zai yiwu ba ko?"
"Haka ne."
Ya faɗa bayan ya zauna a gefenta. Yana tunanin abun yi.
"To yanzu what's the solution Yaya?"
"I don't really know Hammad, that's why am crying. Wallahi ba na son Yaya Deedah da aure, kamar son da nake maka shi ma irinsa nake masa. Ta ya zan iya yin zaman aure da shi?"
Muhammad ya ce,
"Ke ma dai Yaya Maryama, tun tuni na taɓa faɗa miki Malamin Islamiyyarmu ya ce yana sonki amma kika gwasale ni. Da yanzu an miki aurenki kin huta da wancan Yaya Deedah ɗin."
Matsalar yaro kenan. Yanzu zai maka abun kirki, yanzu kuma zai ɓata maka rai. Da hannu ta dakatar da shi, haɗe da faɗin,
"I need to rest Hammad. Je ka ɗakinka."
Babu musu kuwa ya miƙe jiki babu ƙwari, har ya kai bakin ƙofa ya juyo, ya ce,
"You've to stop crying Yaya, move on. Ƙila ma shi Yaya Deedah yana can yana jin daɗinsa, ke kuma kina nan kina ta famar kuka. Idan fa wani ciwo ya kama ki? Na tafi, good night."
Ya ja mata ƙofar bayan ya fita.
Zaune ta tashi Maryama, ta cire hijabinta ta ajje a bisa gadon, kwantaccen gashinta da Mama ta tsefe mata kalaba ya bazu a bisa bayanta, ya sha mai sosai. Ta haɗa tafukan hannayenta a bisa kyakkyawar fuskarta, ruwan hawaye na zuba a samansu.

Mafita take nema daga wurin Allah, Ya yaye mata dukkan damuwarta. Tsantsar ƙiyayyar Deedah na daɗa shiga cikin zuciyarta.
"Ya Allah!"
Ta faɗa haɗe da komawa bisa gadon ta faɗa tim! Tana mai rasa dukkanin nutsuwarta.
*
Tun ɗazu yake zaman jiran zuwanta, amma shiru ba ta zo ba. Sosai ya shiga cikin damuwa, har ya fara ƙoƙarin zubar da ƙwallansa. Me ya hana ta zuwa ta ba shi magani? Ya tambayi kanshi.
Gyaɗa kan nasa yake, yana mai jin tsananin kewarta na shiga duk cikin wata gaɓa ta jikinshi.
"Ta ce ba za ta taɓa tafiya ta bar ni ba. Wai za ta zame min tamkar Amrata, za ta zama madadin Amrah a duk sadda na buƙaci kasancewa kusa da ita."
Tamkar mai hankali haka ya yi wannan maganar. Ya daure miƙewa bisa ƙafafuwansa, yana mai tsananin jin yunwa.
Kodayake ba mai hankali ba, amma fa ya tabbatar ba lafiya ba. Ba a taɓa fashin kawo masa abinci ba. Amma ga shi yau tun na rana ba a kuma kawo mishi wani ba. Kuma wacce ke kawo mishin ma babu ita.
Bakin drowar da magungunansa suke ya nufa, kamar yadda ya ga Maryama na masa shi ma haka ya yi. Ya ɓalli magungunan iya wanda take ba shi, sannan ya buɗe deep freezer ya ɗauko robar ruwan Sona, ya kafa a bakinshi haɗe da maganin ya shanye.
Bayan ya gama ya koma bisa gadon nashi, ya kwanta a takure, yana jin yadda damuwa ta turnuƙe zuciyarsa.
Ya saba da ita. Ya saba da kyautatawarta, amma ga shi yau babu ita, ita ma ta masa nisa kamar yadda Amrah ta masa. Ko ranar da za su yi walima sai da ta sanar da shi cewa ba za ta dawo da wuri ba. Kuma tana dawowa sai da ta zo inda yake. Amma yau ba ta zo ba, ba ta shigo inda yake ba tun sadda ta kawo masa abincin rana.
Tashi ya yi zaune kuma, ya ƙurawa ƙofa ido, a tunaninshi ko zai ga ta shigo. Amma ina, ko motsin mutum babu, alamun dai ba za ta zo ɗin ba kenan.
Takaici ya dame shi, ya kama wuyar rigarshi da ƙarfin gaske, ya ɓarka ta, har sai da ta dire ƙasa. Laɓɓansa yake tauna da iya ƙarfinsa, take jini ya fara fita daga cikinsu, duk suka farfashe.
Da wannan damuwar barci ya ɗauke shi zaune, sai dai kawai ya ɓingire bayan barcin nasa ya yi nisa.
***
Kwanan Sans goma a asibiti aka ba shi sallama. Sai dai kuma, ba ya iya tafiya da ƙafafuwanshi, sanadiyyar bullets ɗin da suka shige shi ba su fice ba, ciki suka zauna, har sai da suka illata shi. Da ƙyar ma likitocin suka samu nasarar fitar da su.
Tsananin tashin hankali Sans ya shige shi. Yau wai shi ne ya zama gurgu, ko kaɗan ba zai iya tafiya da ƙafarsa ba.
Wa'yannan bayin Allah'n da suka taaimaka masa, su suka haɗa kuɗi suka siyo masa keken giragu, wanda ba ma sabo ba ne, tunda su ɗin kansu rufin asiri ne gare su.
"Tunda an sallame ka, ina za ka nufa yanzu? Ko za ka amince ka zauna a gidanmu?"
Babban yayan wancan ɗin ya faɗa, yana mai kallon Sans da dukkan hankalinshi.
Runtse idanuwansa ya yi Sans. Ko kaɗan ba ya marmarin ci gaba da zama a Borno State. Jiharsu, inda kaf ƴan uwa da danginsa suke. Ba don komai ba sai abin da ya faru, kowansa da ya rasa, saboda wannan tashin hankalin da ake ciki.
"Ba zan iya ba. Ba zan taɓa iya ci gaba da zama a garin nan ba."
"To sai ina? Ko kana da dangi a wani garin ne?"
"Ku kai ni ko ma ina ne. Amma dai in fita daga cikin jihar Borno."
"Kar ka yi haka Salman. Ya kamata ka ɗauki ƙaddararka, ka sani cewa kowanne ɗan-Adam yana da tashi ƙaddarar. Allah bai manta da kai ba, zai kawo maka ɗauki a kodayaushe ne"
"Ku kai ni tashar mota don Allah."
Babu musu suka taimaka mishi suka saka shi a mota, kai tsaye suka nufi babbar tashar garin da shi.
"Wane gari za ka je to?"
"Katsina."
Ita ta faɗo masa a rai, ita kuma ya faɗa. Ba wai don ya san wani a can ba. Kurum zuciyarsa ta ƙisima masa can ɗin, ya kuma aminta da hakan..
***
*A yi maneji da wannan.*
*Masu mutunci kar a manta da kankaro mutunci.*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/4, 4:31 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
5⃣5⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Kallonta ya yi cikin idanuwa, yana nazartar yanayin nata. Cikin sanyin murya ya furta,
"Ki yi haƙuri Fiddou, ko kaɗan ban yi hakan da nuhin ɓata ranki ba. Soyayya ce ta ja, ita ce sila Fiddou. Don Allah ki duba lamarin nan, ki min kwatankwacin koda rabin ƙaunar da nake miki ce."
Shessheƙar kuka take, tana mai ƙoƙarta ɗauko rinannun idanuwanta ta kalle shi.
Dusasshigar muryarta da kuka ya gama disasharwa ta buɗe, ta ce,
"Na amince zan aure ka Mahmouda. Na yarda, na kuma tabbatar cewa kai masoyina ne na gaske. Amma ina so ka san wani abu, cewa soyayyar Modu na nan ta yi zaman daram a cikin zuciyata. Ba zan taɓa iya hidda ƙauna tai daga raina ba. Ya riga ya bi jini da jikina. Idan ka amince za ka iya a hakan to, idan kuma ba za ka iya ba ka tahi, zan iya ci gaba da rayuwata a haka ba tare da na auri kowa ba."
Cike da mamaki ya ɗago fuskarsa ya kalli Fiddou. Shin da gaske ne kalaman da yake ji daga bakinta? Da gaske ta amince za ta aure shi? Kamar a mafarki yake jin lamarin. Abin da bai tsammani ji ba kenan, saboda tun sadda ya zo wurinta take ta faman kuka, ta gagara furta komai.
"Na gode ƙwarai da damar da kika ba ni ta aurenki Fiddou. Na miki alƙawarin zan kyautata miki, zan kula da ke, zan ba ki dukkanin gata da ya kamata ɗiya mace ta samu."
Ba ta furta komai ba, sai dai kuma har yanzu ba ta daina kukan ba. Kanta sunkuye a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta.
"In dai har kin shirya, to ina ga ba ma za a ɓata lokaci ba a yi auren ba. So nake na cika burin da mahaifiyata ta tafi da shi a ranta, ba tare da ta ga tabbatuwarsa ba. Abin da nake so da ke yanzu, don Allah de ki daina kukan nan, kar a je wata cutar ta kama ki. Bari in tashi in wuce, gobe da yamma zan dawo, ki faɗa wa Yaya Labib ɗin."
Miƙewa ta yi bayan shi ɗin ma ya miƙe. Ta masa sallama sannan ya fita daga gidan, tana mai bin sa da kallo har ya fice.
Ba wai son shi take ba, har ga Allah ba ta da wanda take so sama da Modu. Amma ya za ta yi? Ba ta da zaɓin da ya wuce ta amince da soyayyar Mahmouda, saboda aikin banza take, Dakon Son mahaukaci, da yanzu haka ya gama mantawa da ita ma.
***
Su suka biya mishi kuɗin motar da kansu, sai da suka tabbatar motar ta tashi, sannan suka bar tashar, cike da tausayinsa.
Tafiya daga Maiduguri zuwa Katsina ba wasa ba ce. Sosai suka sha zaman mota, wanda har sai da suka yi branching a Abuja suka kwana, saboda ta can suka bi. Dukkanin hanyoyin da za su bi a sauƙaƙen babu kwanciyar hankali, dole sai mai tsayi.
Washe gari da asubar fari suka kama hanyar Katsina, ta Dikko ɗakin kara, daga babban birnin Abuja.
Kamar yadda yake tun barowarsu Maiduguri yanzu ma haka yake. Ya haɗa kansa da guiwa, tunanin duniya kawai yake.
Rayuwarsu ta yarinta yake tunowa. Soyayya da gatan da iyayensa suka gwada masa, da kuma ƙaunatayyar da ke tsakaninshi da ƙanwarsa Yamaira.
Wa ya sani a Katsina? Shin idan ya sauka ina zai dosa? Ya makomar rayuwarsa za ta kaya a garin da bai taɓa zuwansa ba?
Duka wannan jerin tambayoyi ne da yake ta yi ma kansa su, sai dai kuma bai da amsoshinsu, wannan dalilin ne ya sa shi haɗa kai da guiwa, tun jiya da suka baro Maiduguri.
A Kaduna suka tsaya, da nufin duk wani mai uzuri ya yi, mai cin abinci ya siya, saboda a wani babban gidan mai ne suka tsaya.
Zaune yake bai fita ba, sai kallon jefi jefin mutanen da ke shige da fice a farfajiyar gidan man kawai yake.
Ji ya yi an dafa shi, da sauri ya karkato da dukkanin hankalinsa zuwa ga mutumin da ya taɓa shi ɗin, yana son sanin dalilin haka.
"Yaro na kula da kai, tun jiya da muka taho a yadda kake haka kake. Shin me ya yi zafi shi ba wuta ba? Ko ruwa sau ɗaya tal na ga ka sha, bare kuma ai maganar abinci. Ban san damuwarka ba, kuma ba na so na sani. Amma ka fauwalawa Allah dukkanin lamurranka. Ka nemi abinci ka saka ma cikinka, maganin shiga wata damuwar ko kuma ciwo."
Ya ji daɗin kalaman mutumin sosai. Hakan ya sa shi ƙirƙiro murmushi, haɗe da furta,
"Na gode."
"Ba sai ka min godiya ba. Ka faɗa min abin da kake son ci. Ga lemu can, ga nama, ga doya da ƙwai, me kake so?"
"Lemun dai ya wadatar."
Sans ya faɗa yana kallon mutumin.
"Bai kamata ka sha zallar lemo ba, duk yunwar da ka kwaso tun jiya. Bari dai in siyo maka doyar, sai in haɗo maka da lemun."
"To shi kenan, na gode ƙwarai."
Ya karkace aljihunsa, da nufin fiddo kuɗin abincin ya ba mutumin, cikin wanda bayin Allahn nan da suka taimake shi suka ba shi.
"Ba sai ka ba ni kuɗinka ba. Bari in siyo maka."
Godiya ya sake yi wa mutumin, yana kallonshi ya sauka daga luxirious ɗin, ya nufi wurin mai doya da ƙwai.
Mintinsu kusan arba'in a wurin suka tafi, ba kuma su tsaya ba har sai da suka je Malumfashi, aka tsaya saboda masu uzuri.
Roƙar wancan bawan Allahn ya yi Sans, cewa ya taimaka masa zai yi fitsari.
Tallabar keken nasa ya yi ya fitar, ya buɗe shi sannan ya kama Sans ya fitar, ya zaunar da shi a bisa keken, haɗe da tura shi.
Da taimakonsa ya