Showing 57001 words to 60000 words out of 201092 words
Chapter 20 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
ya yi nisa kuma ya juyo ga nurse ya ce,
"A kuka da shi sosai hwa. Kar ki bar wuringa dan kar ya hwarka babu kowa a tattare da shi. Tun da na hidda kowa daga ɗakin, na kuma hana su shigowa. Matsalar da ta shafi zuciya hwa dole sai ana taka-tsantsan."
Fita suka yi tare da Fiddou suka nufi Office ɗinsa. A zuciyarta tunanin yanda zata yi da likitan kawai take. Bata san ta yanda zata fara faɗa masa a haka ta ganshi har suka shaƙu ba.
***
Da gudunshi ya shigo yana faɗin,
"Yaya Maryama! Yaya Maryama!!"
Ɗago kanta ta yi daga latsar wayar da take da sauri tana binsa da kallon tuhuma, tuhumar dalilin shigowarsa ɗakin babu ko sallama kuma sai ihu yake mata.
Raina kansa ya yi ganin kallon da take binsa da shi.
"Uhmm...dama, dama Maman Abdul ce ta zo. Tana falo Mama ta ce na kira ki."
Fasa yi masa faɗan da ta yi niyyar yi ta yi, gyaɗa kanta kawai ta yi ta ajje wayar bisa gado, sannan ta zira hijabinta iya guiwa, ta nufi hanyar falon.
Ko da ta isa ta samu Mama suna fira da Maman Abdul, firar abun da ya faru ɗazu, na rashin zuwa ɗauko sa.
Da fara'a Maryama ta zauna, gaishe da Maman Abdul ta yi sannan ta miƙe ta nufi kitchen. Fruits ta yayyanka cikin lokaci ƙanƙani ta haɗa ftuit salad ta fasa ƙanƙara ta ɗora a kai. A bowl ta juye ta haɗa da cokali sannan ta koma falon ta ajje a gaban Maman Abdul da faɗin,
"Ɗazun nan kuwa Muhammad ke ce min wai ya ji ku shiru har yanzu, gashi kuma babu lambarki bare na kira ko kun fasa zuwa ne."
Cokali guda ta kai bakinta sannan ta ajje ƙasa, ta dubi Muhammad da fara'a ta ce,
"Abdul ne zai ƙyale ni bamu zo ba? Ai yanda ya saka ka a ranshi abun ba a magana. Kullum damun Abbansa yake da maganarka. Abban nasa ma ya tilasta lallai kar mu wuce yau bamu zo gidanku ba."
Mama ta ce,
"Yara kuwa sun haɗa zumunci."
Ta faɗaɗa murmushinta.
Sun jima suna hira har magrib ta kusa. Muhammad da Abdul kuma suna harabar gida suna buga ƙwallo. Miƙewa ta yi ta ce,
"Bari dai mu kama hanyar gida Mama. Maryam mu yi musayar number mana."
Miƙewa ta yi ita ma Maryama ta ce,
"Aikam mu ma insha Allahu muna nan zuwa gobe ko jibi. Zamu zo mu ga gidan su Abdul daga nan sai zumunci."
"Da kuwa na ji daɗi ƙwarai."
Suka yi musayar lambobin wayar sannan Maryama ta taka mata har tsakar gida. Ta ce,
"Maman abdul baki faɗa mana sunanki ba."
"Dr. Islam sunana."
Daga nan suka isa tsakar gidan.
"To malami sai a zo mu tafi ko?"
"Oh Mami! Muna kan yin ball ne zaki ce mu tafi?"
Ya faɗa cikin shagwaɓa da yarinta. Duka a shekaru ba zai wuce shekara uku ba, ba ma lallai idan zai yi ukun ba. Amma sai wayo da son mutane yaron.
"Abdul-Ahad dare ya yi fa. Ko gobe zaku haɗu a School, ko ka manta? Kuma sun ce zasu zo mana yawo mu ma."
Murmushi ya saki haɗe da faɗin,
"Yauwa Mami. Na ji daɗi da zasu zo gidanmu."
Ya bi bayanta yana dariya.
Har mota suka raka su sannan suka dawo gida. Fuskokinsu ɗauke da dariya.
***
Tsaki ya yi a bayyane haɗe da ɗaukar wayarsa da ke ringing, ya kara a kunnensa da faɗin,
"Hello guy."
"Abokina ya dai?"
Bobby ya faɗa da fara'a.
"Ba lafiya fa guy. Akwai damuwa sosai. Ina tunanin ɓalli na neman kwancewa fa. Tun ɗazu nake kiranka baka ɗauka ba."
Dafe kansa ya yi Bobby, ya tausasa muryarsa ya ce,
"Tell me something, what is going on? (Ka faɗa min wani abu, me yake faruwa ne?"
"Guy kiran da Dady yake min sanda nake gidanku ɗin nan, ashe laifin da na yi a company aka faɗa masa. Guy baka ga faɗan da ya min ba, ban taɓa tsammani ba. Kuma abun haushi hasarar da ta fi wannan ma na jawo amma bai min faɗa ba sai wannan. Kamar dai sai mun koma wurin boka, dan da alama maganarsa ke neman tabbata. Gwara tun wuri ai wa tufƙar hanci."
Bobby ya ce,
"Lallai kuwa. Daddyn ne ya maka faɗa? Akwai damuwa tabbas. Dole zamu koma masa. Gashi kuma yanzu dare ya yi. Sai dai gobe da sassafe na zo na ɗauke ka sai mu tafi."
"To zan jira ka guy. Dan Allah kar ka bari na yita jiranka. Ka san a matse nake, kar a samu matsala mai girma."
"Babu wannan a tsakaninmu, ka sani. Kawai ka jira ni da sassafe. Kar kuma ka sha komai, kar bacci ya ɗauke ka. Sai ka yi shigar zuwa wurin aiki, daga can kawai ka wuce aiki."
Daga haka suka yi sallama zukatansu a raunane.
Ummu Ayeesher where are you? Ban manta da ke ba. Gaisuwar taki ta musamman ce. Ina yinki irin sosai da sosai din nan.
Duk members na NAGARTA WRITERS FANS na gaishe ku. Ina yinku irin totally din nan. Fatan kun san da hakan.
Alhamdulillah! Jiki kam ya yi sauki sosai. Na gode kwarai da adduoinku. Allahu ya bar zumunci da zaman tare.
What do you expect here? Shin wacece Dr. Islam din nan Maman Abdul? Menene dalilin kulla wannan alakar da marubuciyar ta yi?
Modu mai matsalar zuciya, yaya abun zai kaya? Me Fiddou zata fada wa likita bayan kuma ita kanta bata san asalinsa ba?
A dai juri zuwa rafi, wata rana tulu zai fashe.
Marubuciyar zata yi amfani da alkalaminta wurin fayyace mana komai, kawai mu ci gaba da bibiyar labarin. Zamu yi mamakin komai a karshe.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
32
Tun da sassafe ya hau shiri. Manyan kaya ya saka, farar shadda mai matuƙar kyau, an mata surfani da kalar baƙi. Hakan ya sa ya saka baƙar hula, baƙar agogo da kuma baƙin takalmi. Kallo ɗaya ka ma Annur zaka ji ya shiga ranka, kamar ba shi ne wannan mugun mashayin ba.
Turaren cinema ya shafa a jikinsa sannan ya fesa explore.
Lakar madobinsa ya jawo ya fiddo kuɗi ya saka a aljihunsa, sannan ya kama hanyar fitowa daga ɗakin nasa.
Sai da ya fara biyawa part ɗin su Momy. Ya same ta a falo tana zirga zirgar haɗa kalaci ita da mai aikinta.
Har ƙasa ya duƙa ya gaishe ta. Akwai fa ladabi ko ba komai. Ko da yake, dama an ce wai masu irin mugayen halayen nan sun fi kowa ladabi da girmama na gaba da su. Ladabin kunama ke nan.
"Ya da fitowa haka tun da wuri?"
Ta faɗa bayan ta iso daidai inda yake zaune.
"Yau da wuri nake son zuwa aikin ne Momy. Akwai ayyuka da dama da nake son na warware su."
Ajiyar zuciya ta sauke tana binsa da kallo. Kallon yanayin nasa na yau. Babban mutum mai ƙwarjini a fuska, sai dai kuma babu halaye na gari. Ya yi rashin halayen kirki tun shekaru uku da suka gabata. Ko ma fin hakan.
"Annur dan Allah ka kula. Ka ga ka ɓata wa mahaifinka rai ba kaɗan ba. A kiyaye gaba, bana fatan hakan ta sake faruwa nan gaba. Ka ji?"
Miƙewa ya yi ya zauna bisa kujera, yana sosa ƙeyarsa ya ce,
"Insha Allahu Momy na miki alƙawari hakan ba zata sake faruwa ba."
"Ina fatan hakan, Annur. Allah Ya maka albarka ya ƙara shirya ka, ko ka samu ka ajje hankalinka wuri ɗaya ka tsayar da matar aure."
Bai furta komai ba wayarsa ta ɗauki ƙara. Dubawar da ya yi ya ga Bobby ne ke kiransa ya sa shi saurin miƙewa a kan kafafuwansa. Ya ce,
"Momy har an fara kirana. Usman ne secretary na san jirana yake. Zan tafi, sai na dawo."
"Au! Kalacin ma ba zaka tsaya a kammala ba?"
Taku ya yi haɗe da furta,
"Ina sauri ne Momy. Ina son gyara kuskuren da na tafka a baya. In gyara tsakanina da Dady."
Da fara'a ta ce,
"Allah Ya tabbatar da hakan. Ina ji a jikina dai hakan ya zama alkhairi. Dan ga zahirin canji nan na gani a tattare da kai. Kai ɗin nan da baka tashi tafiya aiki sai ƙarfe goma, amma gashi yau ko bakwai bata cika ba zaka tafi. Na ji daɗi ƙwarai."
"Na wuce, Momy."
A ransa mummanan ƙuduri ne kawai, a daidai ƙofar ya gyaɗa kansa haɗe da sakin murmushin ƙeta, wanda ya bayyana zallar muguwar manufarsa a daidai lokacin.
Daidai zai shiga mota ya latsa kiran Bobby. Kamar yana jiransa kuwa ya ɗauka yana faɗin,
"Am on my way."
Kawai ya latse kiran ya shiga motarsa ya kunna.
Kai tsaye gidan su Bobby ya nufa. Ya same sa a tsaye bakin gate yana jiransa. Shiga gaban motar kawai ya yi suka kama hanyar Jani sai wurin boka Gagarabadau.
Yanda suka saba yi idan sun je wurin bokan suka yi. Bayan sun sha jini boka ya shanye sauran, sannan ya fuskanci Annur da faɗin,
"Akwai matsala ne a aikin. An samu an fitar da ƙaunar da kake ma ɗaya daga cikinsu. Amma ɗayar na kasa ganin komai game da ita. Aikin da na yi a kanta a gabanku ya yi, amma washe gari na kasa fahimtar abin da ke faruwa. Wani irin haske ya ringa mamaye ƙwaryata a duk sanda na tura masu aljannu. Har na gaji na haƙura. Dan haka wannan aikin naka ne. Ni ba zan iya ba, kar wani abu ya faru kamar yanda ban taɓa tsammani ba. Yau ni Gagarabadau an samu abin da ya gagare ni. Ban san dalili ba. Ka ƙoƙarta fitar da ita daga zuciyarka, idan ba haka ba kuwa asiri na daf da tonuwa."
Cike da tsoro da fargaba Annur ya ce,
"Boka a dai ƙara ƙoƙartawa. Ban san ya zan yi ba idan wannan mugun ƙullin ya kwance. Ban kuma san yanda zan yi na fitar da yarinyar daga zuciyata ba. Ni kaina jinta nake a raina, duk yanda zan yi na fidda ƙaunarta na kasa. Har ƙudira na yi zan hukunta su amma na kasa. Na rasa me zan yi boka Gagarabadau!"
"Aljannu basa magana biyu. Ka tashi ka tafi ka bani wuri! Kar kuma ka sake dawo min har sai ka fidda wannan soyayyar daga ranka. Idan ka jinkirta kuma, ka shirya zama abun tausayi, dan komai sai ya lalace."
Kansa ya dafe Bobby, yana tsananin jin tausayin abokinsa. Ya rasa ta inda ma zai fara. Da ƙyar ya samu ya ce,
"Boka a dai taimaka mana. Ka san gare ka kaɗai muka dogara. Kai ne kake rufa mana asiri, a yanzu ma muna neman rufin asirin nan. A duba wannan zancen boka, a bamu mafita."
Manyan zane ya ringa yi a hannunsa na hagu, cikin wata irin murya ya ce,
"Duba ku gani!"
Ya juyo masu da hannunsa da ke fitar da haske.
"Babu nasara ko kaɗan. Akwai abin da wannan yarinyar ta taka wanda tsafi ya gagara yi mata wani abu. Idan da hali dole sai ta shagala da aikin ta ajje sa, ko zamu samu nasara a kanta."
Shiru suka yi su duka suna tunanin mafita. Ko kaɗan basu da idea a kan abin da zasu yi, kawai dai basu so bokan ya gajiya da su ne.
"Zamu ƙoƙarta boka. Zamu san yanda zamu yi dan ganin yarinyar ta shagala da aikin nata. Muna godiya da ƙoƙarinka."
kuɗi Annur ya ajje masa sannan suka miƙe a ƙafafunsu. Tunani fal a zukatan ko wannensu suka bar gidan.
***
Zama ta yi a bisa kujerar da ke fuskantar tasa. Idanuwanta a raunane take kallonsa. Zuciyarta fal da tunanin abin da zata faɗa ma likitan.
Muryarsa ce ta dakatar da ita daga tunanin da take, ta dawo da hankalinta gare shi, tana sauraren abin da yake faɗi.
"Giɗe ki kwantar da hankalinki hwa. Abin da na hwaɗi ba lallai bane ya tabbata, hasashe ne dai kawai nai yi. Yanzu dai ki hwaɗi min. Halan mi as silar haukan can nashi? Ta haka kawai zan tabbatar da hasashen da nake yi a kan giɗe."
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Cikin wata murya rinanna ta fara bashi labari.
*
Tafiya yake da ƙafafuwansa, kayan jikinsa sun yayyage, tsiraicinsa duk ya bayyana, yana kuka kamar ransa zai fita.
Gajiya ya yi sosai da tafiyar, jiri na ɗibarsa sosai, hakan ya sa ya fara dafe kansa, da ƙyar ya samu ya duƙe ƙasa, yana wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wanda zai ji sa.
Tun sanda yake tafiya take kula da shi, take bibiyar lamurransa, har sanda ya gaji da tafiyar ya tsaya a ƙafafuwansa. Ya kuma gaji da tsayuwar ya tsuguna a guiwowinsa.
Cike da tausayi ta ƙarisa inda yake, tana jin tsanan fargabar tinkararsa. Sai dai kuma duk da hakan, bata jin ko kaɗan zata iya tafiya ta bar shi a wannan halin ba. Ko kaɗan ba zata iya fitar da tunaninsa daga cikin zuciyarta ba.
"Giɗe."
Ta faɗa cikin sanyin murya. Zuciyarta na dukan uku-uku, ba ma ta san ta inda zata fara ba.
Ɗagowa ya yi da rinannun idanuwansa ya dube ta. Duba ta tsanaki kafin ya sake duƙar da kan nasa, yana mai ci gaba da kukansa.
Dakewa ta yi ta sake furta,
"Giɗe ba zan cutar da kai ba, Allah kuwa da gaske nake."
Bai ɗago kanshi ba a wannan lokacin, sai ƙara ɗaga sautin kukan nasa da ya yi.
Duƙawa ta yi a gabansa, tana jin duk wata fargaba na fita daga zuciyarta. Zallar son taimaka masa ne a cikin farar zuciyarta.
"Giɗe ka hwaɗi min do Allah de. Mi ka damunka?"
Sai sannan ya ɗago fuskarsa yana gwada mata cikinsa da hannuwansa. Alamun yunwa yake ji sosai, da alama ita ce ta galabaitar da shi.
Bata fahimci manufarsa ba, sai faɗin ta yi,
"Cikinka yake maka ciwo? Bara na kawo maka magani yanzu. Dan Allah kar ka tafi, ka ji?"
Kansa ya gyaɗa mata, yana sake nuna mata cikin nasa da duka hannuwansa a wannan karon, ruwan hawaye na sake wanke masa fuska.
"Mina ne halan giɗe? Ko yunwa kake ji?"
Saurin ɗaga mata kai ya yi, kukan da yake lokaci ɗaya yana sauyawa zuwa murmushi, murmushin da duk ƙazantar fuskarsa bata hana kyawunsa bayyana ba.
Murmushin ta yi ita ma, duk da tausayinsa da take ji, da damuwar da ke cikin zuciyarta.
"Zauna a nan kar ka tafi. Yanzun nan zan kawo maka abinci."
Bai ce da ita komai ba sai murmushinsa da ya faɗaɗa, ya gyara zamansa yana bin bayanta da kallo.
Ta ɗan jima bata dawo ba sai gata ta taho da plate ɗin abinci a hannunta an rufe, sai kuma wani yaro biye da ita, wanda zai tafi da plate ɗin idan an gama.
Yana ganinta ya hau murmushi, da haƙoransa a yaƙe, yana miƙo mata hannu tun bata ƙarisa isowa inda yake ba.
Zama ta yi a kusa da shi, ta motsa shinkafa da miyar da cokali, sannan ta miƙa masa tana murmushi ta ce,
"Ka ci gashi. Ga kuma ruwa nan idan zaka sha."
Bai bi ta kan karɓar ruwan ba. Cokalin ma yar da shi ya yi ya ringa cin abincin hannu baka hannu ƙwarya. Kyakkyawar loma biyar ya cinye baki ɗaya abincin, ya miƙo mata hannu ta bashi ruwa.
Tsabar sauri ya sa ya gagara fasa ledar ruwan ma, ya ringa kai shi bisa leɓonsa ya kasa buɗewa.
Karɓa ta yi ta fasa masa, sannan ta miƙa masa a daidai bakinsa. Zuƙa ɗaya ya shanye duka ruwan ledar, ya saki kyakkyawar gyatsa, alamun ya ci ya ƙoshi ke nan.
Miƙa wa yaron plate ɗin ta yi, ta ce,
"Giɗe tahi ka kai mata, na gode ma ka jiya."
Ya karɓa ya tafi, yana yi yana ɗan waigen mahaukacin, wanda al'aurarsa take bayyane.
Ganin irin kallon da yaron yake binsa da shi ya sa ta yi saurin cire ɗan ƙaramin mayafinta, ta lulluɓe masa jikin nasa, tana mai tsananin tausaya masa.
Rasa yanda zata yi da shi ta yi, miƙewa ta yi bisa ƙafafuwanta, tana faɗin,
"Giɗe tashi mu tai gidanmu. Ina baka ƙarin wani abinci ka ci."
"Zaki kai ni wurin Amrah?"
A ba zata ta ji maganar tasa, dan bata yi tsammanin ko magana ya iya ba. Ta dai tabbatar ba kurma ba ne, saboda yana jinta, kuma yana yin duk abin da ta ce masa ya yi.
Da murmushin yaƙe ta ce,
"Zan kai ka mana. Amrah ko?"
Dariya sosai a fuskarsa ya ce,
"Ehh, Amrah fa. Wallahi ita nake so, AMRAH NAKE SO!"
"To can zan kai ka. Mu tahi."
Ta tasa shi gaba tana binsa a baya.
Duk ta inda suka gitta binsu ake da kallo, kallon tuhumar inda ta samo wannan ƙazamin matashin, sauƙinta ma yanda ta ɗaure masa ƙugunsa da mayafinta, ya rufe tsiraicinsa da ya bayyana.
Kallon da ake mata ko kaɗan bai sa ta ji ko ɗar a jikinta ba. Sai ma ƙoƙarin jansa fira da take, amma ko kaɗan baya amsa ta. Shiru ya yi, kuma bata yi shirun ba ita.
A daidai ƙofar gidansu suka isa. Gabanta ya tsananta faɗuwa a lokacin, tana tsoron yanda zata shiga gidansu da shi, haka kuma bata jin zata iya barinsa haka ya tafi, ba tare da ta samar masa suturar kirki ya suturce jikinsa ba. Kuma ta tabbatar cewa bai ƙoshi da abincin da ya ci ba, saboda halam halam ɗin da ta ganshi yana yi.
Runtse idonta ta yi tana tunanin mafita. Tana buɗe su ta dire bisa fuskar Yayanta, yayanta da take shakku, take matuƙar jin tsoronsa.
"Yaya...uhm..."
Ta samu ta matso da ƙyar, tana jin wani sauyi a duniyarta, ƙirjinta sai tsananta duka yake.
"Foddousi mi halan? Ina kika samo giɗe gashi nan tsaye?"
Kyarmar laɓɓa ta fara yi. Da ƙyar ta samu tattara laɓɓanta wuri guda, ta tsaida tunaninta wuri ɗaya, hankalinta duka ya koma ga yayan nata. Ta sanshi, ta san halinshi. Ko kaɗan baya son wasa, baya son yana magana ana ƙyale shi. Hakan ya sa ta fara magana da rawar murya,
"Yaya a saman godabe na haɗu da shi, cikin halin tashin hankali, ga tuhwahi nai a yage, jiki nai ya bayyana, dan shi ne nat taho da shi. Ina tausai nai ne."
Wani irin wawan kallo yayan nata ya bi ta da shi. Take Fiddou ta raina kanta, jikinta ya fara rawa tana tunanin mafita.
Bata samo mafitar ba ta ji muryarshi yana faɗin,
"Kina ɓace min ko sai na ɓaɓɓalla ki? In banda hauka da