Showing 90001 words to 93000 words out of 201092 words
Chapter 31 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
Suhaila take sha, banda salati babu abin da take yi. Ta sani, ta san cewa tana shan wahala sosai a wurin haihuwa, amma fa tunda take ba ta taɓa shan wahala irin wannan ba. Sabbatu take tana furta a kira mata Dady ta roƙi gafararsa, ta san cewa tata ta zo ƙarshe, mutuwa za ta yi.
Sosai mid-wives ɗin ke bata baki, arniyar ciki na furta "push." Musulmar kuma na faɗin "yi ta addua, haihuwar na kusa."
Haka dai sukaita fama har suka ɗauki kusan awa biyu da rabi babu haihuwa.
A daidai wannan lokacin ne kuma aka kawo wata shuwa da ciki ƙerere, da ƙyar take tafiya, naƙuda ta ci ƙarfinta ita ma.
Nan da nan masu karɓar haihuwar suka raba kawunansu, wasu na wurin Suhaila da suka fara tunanin ko ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai an yanka ta, wasu kuma na kan wannan shuwar kyakkyawa, wadda a shekaru ba za ta wuce sa'ar Suhailar ba.
A daidai lokacin da arniyar nurse ɗin ke furta,
"Lemmi go and call the doctor, it seems like there's a problem..."
Kukan jaririn da ta jiyo ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi, ta ɗaga kanta ta hango ashe wannan shuwa ɗin ce ta haihu, hakan ya sa ta sake juyowa ga Suhaila, a daidai sadda kan jinjirin ya gama fitowa.
Da taimakon abokiyar aikinta suka ƙarisa fiddo jinjirin, ɗan ƙarami da shi, kamar wani pre-tamp (Yaron da bai isa haihuwa ba, amma kuma ya wuce bakwaini. Ɗan kimanin watanni takwas kenan). Juya kanta ta yi ta sake ganin waccan shuwa ɗin tana sake yin wata naƙudar, alamun da sauran wani yaron a cikin cikinta kenan.
***
A hankali cike da mamaki suke takunsu, ba su san sanda suka ƙariso gaban gadon ba su duka biyun.
Kallonsu Fiddou ke yi ita ɗin ma mamaki bai gushe daga fuskarta ba, tana son sanin su ɗin su waye, kuma me suka zo yi a ɗakin? Tunawar da ta yi cewa tare suka shigo da Hadiza ya sa ta dakatar da wannan tunanin, da alama dai ƙawayen Hadizar ne, tunda suka zo tare.
"Sannunku da zuwa."
Ta furta cikin sanyin murya, tana ƙoƙarta ƙirƙiro murmushi a fuskarta.
"Yauwa dai, sannu."
Jiddah ta faɗa, Maryama kam ko samun damar amsa gaisuwar Fiddou ba ta yi ba. Tabbas ikon Allah ba ya taɓa ƙarewa. Al'amarin Allah mai girman gaske ne. Tunda take a rayuwarta, ba ta taɓa ganin kama irin wannan ba. Da ba don ta tabbatar cewa Annur na Katsina ba, da ita kanta ta yi irin na Hadiza, ta ce lallai shi ne wannan a gabanta. Sai dai kuma ta tabbatar cewa ba shi ɗin ba ne, tsantsar kama ce kawai da suka yi.
"Modu ga baƙi nan sun zo duba ka hwa. Ka yi musu magana."
Fiddou ta furta tana kallon Modu da murmushi.
Dariyar yaƙe ya yi ya ce,
"Ai na gan su, su ne wanda za su kai ni wurin Amrah?"
Sai a sannan Maryama ta ɗan murmusa, ta kalle shi da fara'a ta ce,
"Ka dai shirya ma tarar ta ko?"
Kai ya ɗaga mata da sauri, alamar ehh, yana ƙoƙarin saukowa daga bisa gadon.
"A'a Modu..."
Ta gyaɗa masa kai tare da ambatar sunan da ta ji Fiddou ta kira sa da shi.
"Kai zamanka, ai ba ka da lafiya, idan ka ji sauƙi ba sai mu je ba?"
Kuka ya fasa a wannan lokacin, duk wanda zai zo ya masa maganar Amrah sai dai ya masa ƙarya cewa zai kaisa wurinta amma ba a kaisa ɗin, ga Maryama ma yanzu tana neman yi masa haka.
"Ba za ki kai ni ba, haka kowa yake yi min. Amrah nake so, Amrah nake son gani, na san ita ma a duk inda take tana can tana tunanina, tana son ta ganni a kusa da ita..."
Kuka wiwi kamar ba shi ne ya gama dariya ba.
Jinjina kai ta yi Maryama, lallai hakan ya sake tabbatar mata da zarginta. Ko tantama babu wannan shi ne real Annur, wancan ɗan iskan fake Annur ne, wallahi ba shi ba ne, ta faɗa a ranta.
Cikin dabara Jidda ta fara rarrasar Modu, tana faɗin,
"Wannan karon kam ba ƙarya za mu maka ba, ba za mu taɓa tafiya mu barka a nan ba, ƙafarmu ƙafarka. Amma fa sai idan ka yi shiru, ka daina kukan nan."
Shanye kukan nasa ya yi Modu, ya ɗan dafe ƙirjinsa, saitin da zuciyarsa take. Ji yake ciwo mai tsanani, a duk sanda zai tuna da wani abu da ya shafi Amrah haka zuciyarsa ke masa zafi da raɗaɗi, ya ringa jin ƙwalwarsa tana juya masa, na tsawon lokaci kafin ya dawo daidai.
Haka suka ringa rarrasar Modu, cikin hikima da dabara har suka shawo kan Modu, ya cigaba da fara'arsa kuma.
"Halan ƙawayen Hadiza kuke?"
Suka tsinkayo muryar Fiddou ta yi wannan maganar daga inda take zaune.
Jiddah za ta yi magana kenan Maryama ta yi saurin yi mata signal alamun ta yi shiru, shirun kuwa ta yi ta zurawa Maryama idanuwa tana son sanin ainahin abin da take nufi, da hana ta maganan da ta yi.
"Uhmm...mu ƴan uwan Annur ne..."
Tun Maryama ba ta rufe baki ba Fiddou ta zaro idanuwanta cike da mamaki tana kallonta. Me suke nufi?
"Shekara da shekaru kenan ana nemansa ya ɓata, ba kuma a san inda yake ba. Duk iya inda za a duba an duba amma ba a ga Annur ba. Da haka har ya ɗauki tsawon wannan lokacin da aka riga aka cire rai da ganinsa. Kwatsam! Sai ga Hadiza ta zo nan, to ita kuma ta sanshi, shi ne fa da sauri ta kai rahoto gidanmu, iyayenmu basa nan ne shi ya sa sai mu muka zo." (Dole dai sai an yo ƙaryar nan🙊)
Kuka ta fasa Fiddou da ƙarfi, wanda ita kanta ta rasa gane ko na menene. Shin na farin cikin samun dangin Modu da aka yi ne, ko kuwa na baƙin cikin lokacin rabuwarsu ya yi? Ta sani, dama akwai irin wannan ranar, wacce ita kanta tsumayenta take, cike take da ɗokin zuwanta. Amma kuma me, ba ta san ya rayuwarta za ta kasance a lokacin da Modu ya tafi ya barta ba. Ba ta san ya rayuwarta za ta kasance ba matuƙar babu Modu a cikinta. Ƙaunarsa take, ta yi nisa a begensa. Ashe haka so yake? Ta tambayi kanta. Ita da soyayya ta tashi kama ta sai ta faɗa ga mahaukaci, wanda ba ta san asalinsa ba, wanda ko kaɗan bai kasance yana ƙaunarta ba, wata yake so daban, wadda da alama sun shaƙu iya shaƙuwa. Rayuwarsa da komai sun ta'allaƙa ne ga waccan ɗin, wacce take yawaita jin yana ambatar sunanta. Wacce a kullum yake begen kasancewa a tare da ita dare da rana. Duk yanda yake aikata wani abu idan ta so ya daina sai ta ambaci wannan suna yake dainawa. Haka zalika ko wani abu take so ya yi to dole sai ta ambaci wannan sunan zai aikata shi. Ita kam soyayya ba ta mata adalci ba, ko kaɗan ba ta kyauta mata ba.
Da ƙyar ta samu dawowa cikin hayyacinta. Hawayenta ta samu da wahala ta share, sai dai kuma wasu ne ke ƙara gangarowa a bisa fuskarta. So take ta tsaida kukan, amma abu ya gagara. Shikenan yanzu za a raba ta da Modu. Ba ta san sanda ta ɗora hannuwanta duka biyun a bisa kanta ba. Kuka take sosai, tana gyaɗa kanta, tana jin yanda zuciyarta ke mata zafi, take tafarfasa ta kowanne lungu da saƙo da ke cikinta.
Kallonta suke da mamaki. Ita fa wannan baiwar Allah'r wacece ita? Me ya sa take kuka sosai haka kawai dan sun ambaci su dangin Modu ne?
Cikin ƙarfin hali Maryama ta ce,
"Baiwar Allah please ki daina kuka. Bakya so danginsa su zo ne?"
Cikin shessheƙar kuka Fiddou ta ce,
"Babban muradina shi ne in ga ƴan uwan Modu sun zo. Abin da na jima ina jira kenan. Giɗe na tabbata zan yi kewar Modu, zan jima ina tunani nai, walle ba zai taɓa hita daga raina ba. Soyayya nike mai ta tsakani da Allah, mai cike da tsantsar tausayi da jinƙai. Ban san me ya sa ba dama, tunda kuka shigo ɗakin gabana ke hwaɗuwa, na rasa dalili. Sai yanzu nag gane dalilin, ashe dai tahiya za ku yi da Moduna..."
Kuka sosai ya ci ƙarfinta. Ita kanta mamakin kanta take. Babanta da mamanta duka sun rasu, sun bar duniyar baki ɗaya. Amma tafiyar da za a yi da Modu ji take tamkar da rayuwarta za a tafi.
Tausayinta sosai suke a wannan lokaci. Lallai so cuta ce, cuta mai matuƙar girma kuwa.
"Ke ni bana sonki, Amrah nake so! Na sha faɗa mata cewa ita kaɗai zan so, ba zan taɓa son wata mace ba bayan ita. Hehe!"
Ya kama dariyarsa, yana wasa da haɓar gyalen Jiddah da ke zaune gefensa.
Gyaɗa kanta ta yu Fiddou. A duk lokacin da Modu zai faɗi makamancin haka, tafarfasa zuciyarta ke yi. Tana ƙara kunna wutar tsanar Amrah, tsanar sunan Amrah, da duk wata magana da za ta fito daga bakin Modu a daidai wannan lokacin.
Sosai take jin kanta na mata ciwo, zazzaɓi ke saukowa a jikinta. Gangar jikinta na tsananta karkarwa, zuciyarta na tsananta tafasa, idanuwanta na daɗa kawo ruwa, tsayuwar da take kuwa ƙafafuwanta sun gagara ɗaukar gangar jikinta.
Duƙawa ta yi a gabansa, ta riƙe ƙafarsa ta dama, cikin muryar kuka ta ce,
"Na san ba ka so na Modu, ba ka taɓa ƙaunata ba ko kaɗan. Amma do Allah dai ina biɗar alhwarmarka, kar ka mance da ni idan ka tahi, kar ka mance da Fiddousi a rayuwarka. Ka ajje a zuciyarka cewa Fiddou mai ƙaunarka ce, mai matuƙar ƙaunar Modu duk da bai kasance mai hankali ba. Ka ajje a birnin zuciyarka cewa babu mai ƙaunarka sama da ni, babu wanda nake ƙauna sama da kai, ba kuma za a samu ba har abada!"
Ta haɗa kanta da guiwa, sosai take zubar da ƙwallanta, kamar wacce aka sanarwa mutuwar wani mai muhimmanci a rayuwarta.
Da sauri Maryama ta tallabo Fiddou, a hankali ta zauna kusa da ita, ta ɗora kanta a bisa cinyarta, tana ɗan bubbuga bayanta kaɗan kaɗan, tana ƙara jin tausayinta a cikin zuciyarta.
Muryar Modu suka jiyo ya ce,
"Ke ki daina dariya, wai don na ce bana sonki ne kike ta faman yin dariya? To ki daina, ki yi kuka, na ji ina sonki, amma na fi son Amrata"
Ya girgiɗa kanshi, irin dai yanda mahaukata ke yi.
Sosai Maryama ke ƙara tunawa da labarin da Maman Amrah ta bata. Irin soyayyar da suka yi, yanda suka yi yarintarsu, soyayyarsu da komai, shaƙuwarsu da matuƙar tausayin junansu. Sadaukarwar da Annur ya yi na rayuwarsa, lokacinsa, farin cikinsa da komai ma saboda Amrah. Wannan wace irin ƙauna ce? Soyayya ta tsakani da Allah kenan, wacce kuɗi ba sa gusar da ita. Soyayya da zuciya ɗaya, wacce babu kwaɗayi ko son abun dubiya a cikinta. Ga Annur dai ya jima da haukacewa, amma ya kasa mantawa da soyayyarsa da Amrah, wacce duka silar haukan nasa ma mutuwar Amrah ne.
Ita kanta Maryama hawayen take, sosai take ƙara tunowa da labarin Amrah. Tausayin Annur take, sosai tausayinsa ke shiga cikin ɓargo da jininta. Sosai yake ratsa duk wata gaɓa ta cikin jikinta. Ina ma dai tana da damar da za ta iya zame masa Amrah, da ta yi, ko dan ya dawo a cikin hankalinsa.
A cikin ranta ta ɗauki alwashi, cewa za ta yi duk yanda za ta yi don ganin Modu ya warke, ya dawo a cikin hankalinsa. Da ikon Allah zai warke, zai koma gaban iyayensa, ƙarshen wancan mugun zai zo.
How are y'all? I hope you're all fine. Sannu a hankali an fara warware ƙullallu ko in ce sarƙaƙƙun abubuwa ba? Yes! Da haka da haka za mu zo wurin. How was this chapter? Was it nice? Oh yes! Very touching😰 tausayin Modu nake. Ina matuƙar tausayawa rayuwar da soyayya ta jefa shi. Wai wasu sai su ce rashin tawakkali ne ya saka shi haukacewa? No! Ko kaɗan ba haka ba ne. Kar ku manta, soyayyar Modu (real Annur) da Amrah soyayya ce da aka gina da tubalin kirki, mai cike da tsafta. Soyayyar tsakani da Allah, wadda babu ƙarya, yaudara ko kuma ha'intar juna a cikinta. Soyayya ce wacce ta yi ƙaranci ga mutanenmu na yanzu. Ko kun manta cewa soyayya wata halitta ce, wacce Allah Yake dasawa bawa ba tare da saninsa ba? Yes! Akwai malamai da dama da ke bayyana cewa wai ma mutum ya mutu saboda soyayyar tsakani da Allah, to ya yi mutuwar shahada. Ashe dai bai kamata mu ga laifin Annur ba. Bai kamata mu alaƙanta hakan da rashin tawakkali ba.😫
Turawa suka ce; no condition is permanent. Duk yadda muke ganin halin da Modu yake ciki, akwai ranar da Allah zai kawo masa sassauci, zai kawo masa sauƙi a rayuwarsa.
To ita kuma fa fiddou? Me za mu ce da ita da take mutuwar ƙaunar mahaukaci, wanda ba ta san asalinsa ba? Shin ita me ta yi kenan? Ƙauna ce kawai, kuma ta tsakani da Allah, irin wacce nake ma masu bibiyar wannan labarin, har suke kula da motsin marubuciyar, suke kiranta, da kuma tura mata saƙo a duk sanda suka ji ta shiru.
Thanks all.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:54 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
4⃣5⃣
Follow me on wattpad:
PrincessAmrah
Sister ɗin mai suna Sister Rita ita ta ƙudundune jinjirin da Suhaila ta haifa, kasantuwar yanayi ne na sanyi sosai, musamman kuma ga jarirai pre tamp, wanda ko kaɗan basa son sanyi.
Bayan ta isar da jinjirin zuwa ga ɗakin da ake auna su, domin a zahirin gaskiya sam ba ta yarda da lafiyar yaron ba, ga wani irin numfashi da yake yi sama sama, sai fitar da nishi yake sosai.
Tare suka shiga da ɗayar nurse ɗin mai suna Sister Feenah, ita kuma tana ɗauke da jinjirin da waccan shuwa ɗin ta haifa.
Ɗora shi ta yi Sister Rita a bisa sikelin awo, sannan ta ce da matar wurin a yi duk abin da ya dace, za ta je ta sanar da mahaifin yaron cewa matarsa ta haihu, dan ya samu kwanciyar hankali.
Bayan ta fita Sister Feenah ta miƙa ma matar jinjirin hannunta, cewa za ta koma wurin mahaifiyarsa, saboda har yanzu naƙuda take, akwai sauran jinjiri a cikinta.
A cikin wannan halin ne mai karɓar dutyn rana ta iso, ba tare da Sister Rita da Sister Feenah sun dawo ba.
Kasantuwar yaran dukansu ƴan ƙanana ne, yaron Suhailah ɗan ficil ne kamar an fyato, haka yaron shuwa ɗin nan ma ficil ne, kasantuwarsa twin ne. Ba lallai ba ne kallo ɗaya ka iya bambance su, kuma duk a cikin showel iri ɗaya suke, farare ne.
Sister Rita ce ta dawo ɗakin, ba tare da haufin komai ba ta ɗauki yaron da ke bisa abun awon sikeli ɗin, dan ita ba ta san cewa an fitar da shi, an saka yaron shuwar ba.
Bayan ta fito ta ƙariso gaban Suhaila da murmushi ta ce,
"Your boy is okay now. Time da kika haife shi yana wani numfashi kamar ba shi da lafiya, and now, his breath is normal."
Karɓar shi ta yi Suhaila, ta ƙura masa idanuwanta tana kallo. Fari ne sol yaron, hannuwansa duka biyun a dunƙule, kyakkyawa da shi.
A cikin wannan halin suka ji zancen mutuwar wancan yaron, wanda har a lokacin wannan shuwar ba ta daina naƙudar ba.
A cikin halin da take ɗin aka nemi kwali aka saka gawar yaron, ba tare da ta ga fuskar ɗanta ba, saboda wahalar da take sha, ba za a tsaya jiran har ta haihu ba, ana kallon gawar yaron haka.
Ganin Suhaila ta haihu lafiya ne ya sa aka miyar da ita resting room, inda ake kai masu haihuwa bayan sun haihu, dan jiran wani lokaci, wanda a lokacin an tabbatar da lafiyarsu.
Su Nadrah da Dadynsu ma ɗakin suka koma, cike suke da farin ciki da jindaɗi, Saddiqa na faɗin,
"He's so cute Momy, but he's small."
Suhaila ta murmusa ta ce,
"Zai girma ai, ke ma ɗin da haka aka haife ki."
Haka dai suka cigaba da zaman asibitin har Suhaila ta yi awa shida da haihuwa, a lokacin ne kuma aka ba su sallama, suka bar asibitin.
Sister Rita ce kawai ta ga fuskar yaron da ke wurin Suhaila, ita kuma ta gama dutynta, wata ta karɓe ta. Shuwa kuma ta haifi kyakkyawan yaronta, mai kamanni ɗaya da yaron wurin Suhaila, ba su da bambanci ko kaɗan.
A lokacin da Suhaila suka fito za su bar ɗakin, ita kuma Shuwa za a mayar da ita can, har suka yi kiciɓus a bakin ƙofa, Suhaila ta ɗora yaron a kafaɗarta, nannaɗe da showel.
Da fara'a suka gaisa, suka ma junansu barka, ta mata ta'aziyyar jinjirinta da ya rasu, sannan Suhaila ta bi bayan maigidanta, da kuma yaranta.
Haka rayuwarsu ta kasance cike da annashuwa, danginsu da ke Katsina sun zo tun saura kwana biyu suna, kowa sai yaba kyan yaron ake. Uba baƙi, uwa kuma wankan tarwaɗa, amma kuma yaronsu jajur, kamar ba Bahaushe ba.
Ranar suna aka ma yaron suna da Annur, Annur Iqra Al-hussein. Ko kaɗan jikinsu bai taɓa basu cewa ba ɗansu ba ne, ba su taɓa tsammanin an musu musayar yaro ba ne.
***
A cikin wannan halin da suke ciki sai ga Hadiza ta dawo, hannunta riƙe da ledar magunguna, fuskarta ƙunshe da fara'a.
Tun daga nesa ta fara faɗin,
"Na siyo masa duka magungunan da aka rubuta masa. Likita ya ba ni tabbaci da ƙarfin Allah ƙarshen ciwon zuciyarsa ya zo kenan. Matuƙar dai ana kiyaye ba shi wannan magungunan a kan tsari, to tabbas shi da ciwon zuciya kuma sai dai wani ɓaren, ba dai inda yake yi a yanzu ba."
Miƙewa tsaye ta yi Fiddou, murmushi take mai haɗe da kuka, finally, yau dai an sayi wannan magungunan, wanda Dr. Huzaif ke goranta mata rashin siyansu.
"Sannu da ƙoƙari Hadiza. Da kin sani ai ki min magana na bayar da kuɗin a siya masa, tunda akwai a wurina."
Maryama