Showing 150001 words to 153000 words out of 201092 words
Chapter 51 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
yake mun jaddada musu cewa da wuri ne na san insha Allahu za su je da wuri ɗin."
"To Allah ya sa."
Sannan ta nufi fita zuwa ɗakin Mama.
Maryama na fitowa wayarta na fara ruri. Koda ta duba ta ga sunan Dr. Islam ne. Da hanzari ta goge jiƙar da ke a hannunta sannan ta ɗaga kiran da sallama a bakinta.
"Habawa Maryana. Ai wallahi kin ba ni mamaki."
Furucin da ta ji Dr. Islam ta yi kenan, ba tare da ko saallamar ta amsa ba.
"A yi haƙuri Aunty Islam, duk da dai ban san me na yi ba amma dai na ɗauki laifina."
"Hmm! Na ji to. Ya shirye-shirye?"
Cikin faɗuwar gaba Maryama ta dafe ƙirjinta, da rawar murya ta ce,
"Na me fa?"
Gyaɗa kanta ta yi Dr. Islam tamkar tana a gaban Maryama ɗin ne. Ta ce,
"Aure za ki yi Maryam amma ko ki sanar mana? Maryam amana ba ta ce haka ba. Tamkar ƙanwata ta jini haka na ɗauke ki. Amma da alama ke sam ba ki ɗauken tamkar yayarki ba."
Sosai bakin Maryama ya ɗinke. Ƙoƙarin tattaro magana take amma ta kasa. Sai famar muzurai take kamar wacce ta yi ƙarya aka turke ta.
"Dole za ki yi shiru ai. To duk da dai ba a gayyace mu ba muna nan zuwa anjima ni da Momy da yaronki. Za mu zo matsayin gayyar nagayyaro."
"Uhm...Aunty Islam kina ji na? Wallahi ba haka ba ne. Komai da komai a cikin ƙurewar lokaci ya kasance. To ni kuma ba na so na tayar muku da zaune tsaye. Wannan dalilin ne ya sa ban sanar muku ba. Don Allah a gafarce ni, insha Allahu ba zan kuma ba."
Dr. Islam ta ce,
"Uhmmm! Kamar da gaske, sai wani marairaicewa take. To na ji. Sai ki turo min address na inda za a yi. Kuma ki ce da angon ya tanadi kalaman da zai kare ki a wurina idan na zo. Ina jiran text na address ɗin yanzu."
Ba ta jira Maryama ta sake faɗin komai ba ta tsinke kiran.
Da ƙyar ta haɗiyi yawu Maryama. 'To a ina suka ji?' Tambayar da ta ma kanta kenan. Hammad ya faɗo mata a rai. A zahiri ta furta,
"Tabbas idan ba wurin Hammad ba babu inda za ta ji. Amma wannan yaro ya iya tsiya. Har sai da na ce da shi ya kame bakinsa fa."
Saudat ta ce,
"Maganinki kenan ai. Nikam Hammad ya min daidai. Ban ga dalilin da zai sa ki ƙi faɗa mata ba ai, duk da ban santa ba."
Ta sake gyara kwanciyarta.
A daidai nan Jiddah ta dawo. Tun daga bakin ƙofa take faɗin,
"To wallahi manya dai sun ce daga gare su babu matsala. Tunda dai already sun yi wankansu tun na waazi ɗazu. Matsalar daga gare mu take. Na ce da su insha Allahu babu damuwa. Komai a kan lokaci za a yi shi. Tunda dai har wurin can an kimtsa komai."
"Wurin wa kika ji an kimtsa komai?"
Maryama ta faɗa tana shimfiɗa dardumar sallah a ƙasa.
"Yaya Deedah ne ɗazu da yake jaddada min cewa da wuri za a zo kwasar mutane ya ce an gama decoration, kuma ya yi kyau sosai."
Cikin taɓe baki Maryama ta ce,
"Ni dama da shi kika daidaita kawai."
Harararta Jiddah ta yi.
"Yar rainin hankali. Sai aka ce miki rasa masoyi na yi da za ki min ƴan kwashe-kwashe?"
"Ba wani kwashe-kwashe ai. Tun sadda kuna waya ɗazu ai na fara fahimtar wani abu. Wannan wasa da dariya haka."
Saudat ce ta jeho wannan maganar. Ta miƙe zaune.
Bayyanannen tsaki Jiddah ta yi, ta ce,
"Duk ba ni da lokacinku."
Ta shiga toilet abun ta.
*
Bayan an gama shirya Maryama, sai da ta fara shiga ɗakin Annur, a lokacin duk an gama kwashe mutane, daga Jiddah sai Saudat ne kawai a gidan, sai mai gadi kawai. Har Mama ma danginta sun ce ba za a barta a gida ba. A gabanta za a yi komai.
Rusunawa ta yi ƙasa tana fuskantarshi, har ƙamshin turarenta na dakar hancinsa.
Cikin wani irin salo yake sakin tattausan murmushi, mai cike da soyayya da ƙauna. Ya haɗe tafukan hannayensa a wuri guda, yana fuskantarta ido cikin ido. Ji ta yi baki ɗaya ya gama tsuma ta da ƙaunarsa. A haka da ba yi da hankali yake mata irin wannan kallon na soyayya, to ina ga ya samu lafiya?
"Yah Noor za mu tafi, wurin event na bikinmu. Will you say something, please?"
Shiru ya mata, amma har yanzu bai daina sakin murmushi ba.
"Say something Yah Noor, please. Yau na ɗaya daga cikin ranaku masu muhimmanci a rayuwarmu. Na so a ce kana a cikin hankalinka, ka halarci wannan rana. Sai dai kuma kash! Allah bai nufa ba, haka Ya tsara ma rayuwarka. Ka kwantar da hankalinka, Allah ba mantawa ya yi da kai ba, sannu a hankali za ka samu lafiya, za ka warke ka dawo da cikakken hankalinka."
Hannunta na dama da tun shigowarta yake kallonshi, ya kama ya riƙe. Daidai tafkeken zoben zinarin yatsarta ya kai hannunsa, a hankali ya zaro shi, ta ci gaba da binsa da kallo. Bayan ya fiddo, ya kawo shi kusa da idonshi yana binsa da kallo. Tamkar ya san zoben, haka ya ji. Wani irin sara ya ji kansa ya masa, a lokacin da yake kallon zoben. Kamar zai tuna wani abu game da shi, sai dai kuma ya kasa tunawa. Ɗan taunar leɓonsa na ƙasa ya yi, sannan a hankali ya miyar mata da zoben daga yatsar da ya fiddo shi, ya miyar mata, ya zauna kuwa daram.
"Time is going Yah Noor. Will you let me go?"
Bai san me zai faɗa mata ba, haka kawai ya samu kansa da ɗaga mata kai, yana sakar mata tattausan murmushi, duk da cewa har yanzu bai daina jin kansa na sara masa ba.
Tashi ta yi da sauri ta tafi, tun daga nesa take faɗin,
"Am so sorry Babes. Kuna ta jirana ba? Ga ni na iso."
Fitowa suka yi Jiddah na riƙe da purse ɗin Maryama a hannunta. A harabar gida suka tarar da Deedah ya yi zaune a mota, yana jiransu. Sosai yake kallon Maryama, yana jin yadda wutar ƙaunarta ke daɗa kunnuwa a cikin zuciyarsa. Amma ya zai yi? Dole ya ƙoƙarta fitarwa ko ba ya so. Saboda ya sani, Maryama ba za ta taɓa zama ta shi ba.
Murmushi ya saki bayan ya fito daga motar.
"Amarya, you know what? Kin yi kyau sosai, lemmi snap you before we leave."
Ya hau ɗaukarta hoto, da Iphone X ɗinsa. Sai da ya mata da yawa, sannan suka shisshiga motar, Jiddah na zaune a gaba sai Maryama da Saudat a baya.
Sadda suka isa gidan su Deedah, Maryama da Saudat ba su fita ba, sai da Jiddah ta je ta sanar cewa ga amarya nan ta iso. Ƙawaye wanda suka yi ashobe su fito, za a shigo da amaryar.
Sauya kiɗa aka yi, yayin da amarya ta fito daga motar, aka yi jeri kowacce ƙawa da partner ɗinta, amarya kuma na daga tsakiya, sai Hammad da Abdul-Ahad biye da ita a tsakiyar, saboda Hammad ya ce ba za a yi babu su ba.
Isowarsu harabar gidan, sautin ya ƙara tashi, yayin da mutane suka mimmiƙe tsaye, cike da farin ciki ana tattafawa.
Yadda aka tsara wurin kanshi abun kallo ne. Decoration ɗin wurin kalar yellow aka yi, an jera kujeru masu matuƙar kyau.

Har gaban kujerar amarya suka raka ta. Sai da ta zauna sannan masu hoto suka hau yi, masu video kuwa dama tun fitowarta daga mota suka fara.
Wuri ya yi wuri fa. Domin kuwa taron mutane maabota karatun Hausa Novels ne jere, wasu ma sai ka yi mamakin ta yadda aka yi suka ji. Laakari da yadda bikin ya zo, a gaggauce aka yi komai.
Hotuna ake sosai, uwar amarya ma ta taso aka musu, dangi da ƴan uwa har da ƙawaye, sai shan hotuna ake.
Da ƙyar MC ya roƙe su suka watse, sannan aka ci gaba da gudanar da partyn.
An yi nisa sosai ne MC ya ce,
"Ga Princess Amrah nan za ta fito, za ta rera mana tata waƙar da ta yi musamman saboda ango da amarya."
Nan fa aka hau tafawa. Ana jiran isowar Princess ɗin.
Cikin taku mai nutsuwa ta iso, tana sanye da wata doguwar riga kalar pink, wacce ke ja har ƙasa. Ta sha ɗaurin ɗankwalinta mai matuƙar kyau, da make up na ji da gani.
Ita ce a gaba, sai ƴan RAZ NOVELLA bayanta sun jera layi. A hankali sauti ya rinƙa tashi, nan fa suka hau takawa cikin rawa mai kyau.
Waƙar ta fara rerowa, tana faɗin,
"Biki wan shagali,
Eh biki wan shagali, ake a yau gidajen girma, Maryama da Annur masoyan asali.
Farko da sunan Rabbi ubangiji maqagin halitta,
Shi ne ya bani damar da nake zubo dukkan hajata,
Daɗo dubun salati ga Annabin gaban duk halitta,
Da alihi sahabbansa a kullum suna yin ƙyalli.
Wannan waƙar aure ce nake a yau ba ƙyashi,
Ga wanga ango da amarya suna ta yin ƙamshi,
A duk ta inda na gitta wannan bikin ina yin son shi,
Domin ko ƙaunar junansu suke ta yi tun asali.
Ga dandazon mutanen arziƙi fa duk sun zozzo,
Farko Nagarta Writers na hanga sun zo,
Sai Raz Novella a gefe murna suke har da ƙwazo,
Nagarta Writers Fans group ƙaunarsu yau sun furzo,
Ga wannan aure rawa suke ta yi ga ƙyalli.
MH fans na gaishe ku a wannan waƙar tawa,
Queen group of Novels ku marmatso ku yi rawa,
Ga Lubbatu's Crew ma na gansu suna takawa,
House of Novels ma a gefe murna suke ba misali.
Pherty Novels gaishe ku nake a yau kun ji ni,
Asisi Fans Club ma na gaida ku fa ba bimbini,
Zauren Sadeeya Novels ku Marmatso nan ga ni,
Ƙarshe na sa ƴan Meesha group novels kun hau tubali.
Wattpadians ga taku fa gaisuwar ku yo amsawa,
Dukkan mutuncin nan da kuke yi min ina jinjinawa,
Comments da votes ɗin naku ku ƙara yo ninkawa,
Masoyiyarku fa Amrah Princess ce mai ƙyalli.
Sauran groups da dukka nake kuna cikin ruhina,
Na san kuna son auren Annur da Maryama ku nuna,
Ni ma ina ƙaunarku da gaske cikin ƙalbina,
Maryam Indabawa group Chart ƙaunarku nake yi tun asali."
Tana kaiwa nan suka rinƙa rawa sosai, har ƙasa-ƙasa suke duƙewa. Amarya Maryama da ƙawayenta suka hau yin liƙi, saboda sun ji daɗin yadda Princess ta waƙe amarya da ango.
Duk da cewa Dr. Islam ta yi mamakin sunan angon da ta ji an faɗa, sai ba ta kawo komai a ranta ba, aka ci gaba da cashewa.
***
*Ban yi tunanin shafin zai kai har tsayin haka ba. Sai ga shi kuwa ya kai.*
*Akwai muhimmin abu da na warware a cikinsa. Wa zai canka?*
*Well...😀 kun ga mun gangara ɓangaren nishaɗi ko? Kar dai ku shagala, akwai cakwakiya da dama nan gaba. Tahm.*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/15, 8:06 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
6⃣4⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Sai dare sannan aka tashi daga Partyn. Sosai duk wanda ya halarci wurin ya yi enjoying ɗinsa, barinma ƙawayen amarya da suka sha casu wanda suka jima ba su yi irinsa ba.
Daga nan kai tsaye part ɗin amaryar Kawu Imrana suka nufa. Ba wata babbar mace ba ce sosai, duka babban ɗanta shekararsa goma. Hakan ya sa suke shiri sosai da Maryama, ko gidan ta zo ma a ɗakinta take kwana.
A falo suka zauna ita da wasu ƙawayenta da za su bi mota guda. Matar ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da food flask ta ce,
"Sannun ku. Kun gaji ba? Ai dole ne gajiya. Wannan uwar rawa da kuka sha. Ita kanta amaryar rawar da ta yi ai na sha mamaki."
Ta ƙarisa da ajje food flask ɗin a bisa centre table.
"Aunty Ruky ni kaina ban san yadda aka yi na dage rawar nan ba. Ni da rawa ma ba ta dame ni ba."
Taɓe baki ta yi Aunty Ruky. Ta ce,
"Ke gwara da kika yi. Komai na duniyar nan fa lokaci gare shi. Idan ba ki yi ba yanzu akwai sadda da kuɗi ma a ce ki yi ba za ki yi ba."
Dariya suka ɗauka duka ƴan matan, suna kallonta.
"Da gaske fa. Ku dai ku jira in fito ku sha labari."
Ta koma Kitchen. Plates ta ɗauko sannan ta dawo, biye da ita ƴar yarinyar da ke mata aiki ce ta kwaso lemuka a babban tray.
Bayan ta zauna ta ce musu,
"Ku zuba abinci ku ci kafin ya dawo ɗaukarku. Na tabbata kuna jin yunwa, musamman ma ke amarya, na san amare abinci ba damun su ya yi ba."
Da murmushi Maryama ta ce,
"Za mu ci Aunty Ruky. Amma ki ba mu labarin da kika ce za ki ba mu."
"To in faɗa muku lokacin aure na, ina ji ina gani kunya ta hana ni yin rawa. Kun san dai irin abun, mace ta auri wanda ba sa'anta ba, akwai jin nauyi sosai. Wallahi sai bayan biki na rinƙa da na sani. Har gobe ban daina ba. Har ji nake ina ma dai a dawo da bikin baya, ai da na yi rawa wadda wata ƴila har sai jikina ya ƙille, ke wata ƙila ma har sai Alhajin da kansa ya janye ni."
Dariya suka sake ɗauka su duka. Dama haka take matar, akwai ta da wasa da dariya, ba dai a zauna da ita a yi ɓacin rai ba. Abincin suka ci kaɗan, sannan wayar Jiddah ta yi ƙara. Tana dubawa ta ga Deedah ne ke kiranta, ta ɗauka. Ce mata ya yi su fito ga shi nan ya zo, tana tsinke wayar ta faɗa musu. Aunty Ruky ta ce,
"To kuma ko lemun ba ku sha ba. Aikam tafiya za ku yi da shi idan kun je gida ku sha."
Suna faɗin ta bar shi ta bar shi amma ta ƙi, ta ce da mai aikinta ta kawo mata leda mai girma, ta juye musu duka lemukan, sannan ta sa ta kai musu har mota.
Godiya suka mata sannan suka fita, sai famar dariya suke mata. Maryama na faɗin,
"Ai ku ne baƙin Aunty Ruky. Haka take da ban-dariyar tsiya."
Skwatin suka yi a motar ba ta amshe su ba, saboda yawan su, duk wanda za su kwana ne suke tare. Mutum biyu ma suka zauna a gaba; Jiddah da wata ƙawarsu Afrah.
Bayan ya sauke su suka firfito, ya ce da Jiddah don Allah ta tsaya yana so su yi wata magana.
Kallon Maryama da saudat da ke ɓoye dariyarsu ta yi, sannan ta musu gatsine da baki ta dawo ta tsaya kusa da murfin motar, shi kuma ya fito, ya zagayo inda take.
Haka kawai kuma sai ya samu kanshi da rashin samun abun faɗi. Ɗan dafe kanshi ya yi, kafin ya ce,
"Ba ku da buƙatar komai dai ko?"
Da murmushi a fuskarta ta ce,
"Babu komai Yah Deedah."
"To shi kenan. Idan dai akwai abin da kuke so ko ma mene ne kina da numberna, kar ki samu damuwa kawai ki kira ni ko kuma ki min text."
"To insha Allahu. Mun gode ƙwarai Allah saka da alkhairi."
"Ameen ya Rabbi. Gobe dai na tabbata Dady da kanshi zai kai amarya gidanta. Motocin ɗaukar amarya za su zo, na yi magana da friends ɗina kamar yadda suka yi yau. Please kar ki hau motar kowa, saboda ina so mu yi magana ne bayan an kai amaryar. Ai babu takura ko?"
"Ehh."
Ta faɗa ƙasa-ƙasa cikin jin nauyinsa.
"To ni bara na wuce Jiddah. Idan na koma gida insha Aahu I'll give you a call. Ki tabbatar kin saka ma cikinki wani abu."
Kai kawai ta ɗaga mishi, sannan suka yi sallama ta shige ciki. Bai tayar da motarsa ba har sai da ya tabbatar ta shiga gidan.
Tana shiga kuwa suka hau yi mata tsiya. Ba ta ce musu komai ba sai guntun tsakin da ta saki, sannan ta zauna bakin gado, tana jiran Afrah ta fito ta yi alwalla.
Maryama kuwa suna shigowa ta ce musu za ta je ɗakin Abba, ba kuma can ɗin ta je ba, ɗakin Annur ta nufa cike da ɗokin ganinsa.
Kwance ta same shi ya kalli can jikin bango, a tunaninta ma barci yake, saboda yadda ta ga ya takure wuri ɗaya.
Gyaɗa kanta ta yi cike da tausayi, ta jawo blanket ta rufa masa, ta juya da nufin tafiya ta ji muryarsa ya ce,
"Ni na yi fushi."
Sassanyan murmushi mai haɗe da ajiyar zuciya ta saki, sannan ta juyo tana kallonshi.
"Na'am me ka ce?"
Ta faɗa a hankali.
"Ba ke ce kika ƙi dawowa ba."
"A yi min afwa. Kalla ka ga na kama kunnena, alamun na tuba kenan. Ba zan sake ba insha Allah."
Tashi ya yi zaune yana kallonta, ya ɗan lumshe idanuwan kafin ya buɗe, ya ce,
"Ai wannan mutumin ya zo nan, shi ya min wanka ma ya saka min wannan kayan masu kyau."
Ya hau gwada mata light brown yadin jikinsa, wanda ya ji aikin hannu kalar coffee brown. Ɗaya daga cikin kayan da Kawu Imrana ya ɗinka masa ne. Kuma ɗazu da safe Uncle Marwan ya aiko masa da wasu kala biyu, cewa ya saka, duk da dai ba wurin ɗaurin auren zai halarta ba.
"Inye angon nawan ba. Ka ga yadda ka yi kyau sosai kuwa? Tamkar na sace ka na gudu haka na ji."
Harararta ya yi, ya ɓata fuska, ya ce,
"Ai dai ba za ki iya sace ni ba. Yauwa, na tuno wani abu."
Ya ɗora hannunshi a goshi alamar tunani. Ba ta ce masa komai ba, kamar yadda ta karanta, cewa ba a ma mutum gajen haƙuri a irin wannan lamurran, musamman ma masu matsalar ƙwaƙwalwa, ko kuma wanda ake tunanin sun samu lost of memory. Barin sa ake don kanshi ya faɗa.
Ya yi kamar seconds arba'in a haka, kafin ya ce,
"Wasu mutane ne suka kai ni gidansu, har suka cire min kayan jikina."
Cike da mamaki ido a buɗe take kallon sa, ba kuma ta nemi jin ƙarin bayani daga gare shi ba, har sai da don kansa ya ce,
"Kuma sai suka saka min wasu a jikina. Ni dai kawai na ce musu Amrah Nake So!"
Ya saki dariya, yana mai bin ta da kallo. Ita ɗin ma dariyar ta ƙirƙiro, duk da cewa zancen nashi ya matuƙar ɗaure mata kai. Sosai take daɗa gode ma Allah. Domin kuwa ba laifi sauƙi