Showing 171001 words to 174000 words out of 201092 words
Chapter 58 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
abin da ke hannunta. Ji ta yi an ce,
"Sarkin ƙiriniya tabbas akwai abin da kika yi, wannan sanɗon da kike yi ba a banza ba."
Zabura ta yi alamar jin tsoro, ta yi saurin tattaro dukkanin nutsuwarta, fuskarta ƙunshe da dariyar yaƙe ta ce,
"Babu fa komai Momy. Wani tiƙeƙen ƙadangare ne fa na gani shi ne nake laɓe don kar ya kama ni."
Bayyanannen tsaki Momy ta yi.
"Ba ki da gaskiya da ganin fuskarki. Faɗa min gaskiya Ussaina. Miye a cikin ledar nan?"
"Uhm...Momy..."
Ta kama susar ƙeya. Muryar Hanan ta ji ta ce,
"Shara na ce mata ta yi ta ƙi yi Momy. Kuma na faɗa mata fa ba ni da lafiya cikina na ciwo. Na koma in ga ta yi sharar ko ba ta yi ba? Na tarar ta jawo lakokin Uncle Noor sai bincike take masa. Idan ƙarya nake kuma ta buɗe wannan ledar ta hannunta a gani."
Harara take buga ma Hanan amma hakan bai sa ta yi shiru ba har sai da ta dire.
"Wallahi mutum magulmaci dai bai yi ba. Yanzu sharri za ki min a wurin Momy?"
"Ba wani sharri. Idan ba tsoro ba ki buɗe ledar a ga."
"Ba zan buɗe ɗin ba. Maganin zafi ne fa na karɓo daga wurin Mallam Ya'ulle."
Dariya ta ba Momy. Ta ce,
"Allah dai ya shirye ki. In ma dai wani abu kika kwaso wa kawun naki kwa haɗe da shi ne. Kun ga ni dai, har sha ɗaya ta yi, ku hanzarta nufar kitchen, ƙarfe ɗaya jirginsu zai sauka Kano. Dreba ma ya tafi ɗauko su."
"Duk baƙin-cikin mutum dai..."
Ta ma Hanan gwaliyo haɗe da nufar ɗaki. Gyaɗa kai Hanan da Momy suka yi. Ta ce,
"Momy bari in daure in sharo masa ɗakin, don na tabbata ba ta share shi ba."
Ta nufi fita zuwa ɗakin nasa. Janan kuwa wardrobe ta buɗe can tsakiyar kaya ta saka ledar, bayan ta fiddo diary ta saka a ƙarƙashin pillow ɗinta.
Fitowa ta yi ta nufi kitchen. Tafashen nama ta ɗora ta zuba kayan ƙamshi da albasa. Ta taɓe baki ta ce,
"Na yi iya yi na. Wallahi fruits kawai zan yanka na gama. Ba zan iya ba."
Ta murguɗa bakinta, ta fiddo fruits ɗin daga cikin babbar ledar da aka siyo su, ta hau aikin yanka. Tana cikin yi Hanan ta shigo, Momy biye da ita.
"Janan what are you doing fisabilillah? Miye na fara yankan fruits bayan babu abin da aka yi?"
"Gaskiya matar nan kina da damuwa. Idan ban yi ba ki ce na cika ƙyuya. Ga shi ina yi kuma ban yi daidai ba. Gaskiya dai Momy ki shiga tsakanina da Hanan. Ta cika ƙorafi da mitar tsiya."
Murmushi kawai Momy ke yi. Sosai lamarinsu ke ba ta dariya. Kamar mage da ɓera haka suke, su yi faɗa su shirya.
"Ga tafasar nama can na ɗora. Shi kaɗai na gani ban san kuma me za a ɗora ba."
"Aikin kenan."
Hanan ta faɗa bayan ta isa ta buɗe tukunyar. Ruwan zafi ta ɗora a makimanciyar tukunya, sannan ta fiddo kaza mai ƙanƙara daga cikin freezer. Ta zuba mata kayan ƙamshi da su maggi da albasa. Nan take aiki ya tashi. Bayan ruwan ya tafasa ta zuba shinkafa da vegetables, kazar kuma pepper chicken ne dama za ta yi da ita.
"Malama tafashen namanki ya yi fa tun ɗazu har ruwa ya tsane. Ko blending cefanen ma ba ki yi ba, kin dage ma aikin fruit salad tun ɗazu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa."
"Ke ni fa ba wata miya da zan yi. Kin dai samu na rage miki aiki ne. Kina ganin har yankewa na yi wurin peeling kankana."
Ta kama yarfar hannunta. Gyaɗa kai Hanan ta yi. Duk da cikin nata bai daina ciwo ba, amma ta samu sassauci. A hakan ta ci gaba da aiki, ta gyara cefanen ta markaɗa a blender, ta soya naman sannan ta zuba cefanen a ciki. Cikin ƙanƙanin lokaci miyar ta hau turbar dahuwa. Ita kuwa Janan ta gama fruit salad ta yi ceiling da cling film ta saka a fridge.
"Yanzu tafiya za ki yi Janan ki bar ni da uban aikin nan saboda Allah?"
"Tambaya ma kike? Malama ki gama mana girki kawai mu kwasa."
Ta mata gwalo da gudu ta bar kitchen ɗin. Dariya Hanan ta yi,
"Allah ya shirya min ke Janan."
Ta ci gaba da aikinta.
*
"Bai kamata ki tasa mu gaba kina sharar kuka ba Yamaira. Yamma ke yi fa, magrib ake neman yi. Tun bayan da kika farfaɗo nake fama da ke ki faɗa min damuwarki amma kin ƙi. Sai famar zubar da ƙwalla kike yi."
Sai a sannan cikin kuka ta iya buɗar bakinta ta ce,
"Kukan da nake yi da biyu; farin-ciki da kuma baƙin-ciki."
Duk suka kalle ta cikin mamaki. Ita kanta Maryama mamakin Yamaira take, yadda take kuka haiƙan, ga kuma wani suna da ta ambaci Annur da shi.
"Ina jin ki Yamaira, please talk."
Ta share ƙwallarta. Wata sabuwar ƙwallar ce ta ƙara saukowa, ta ce,
"Ka san komai game da ni Dadyn Yesmeen, duk abin da ya faru a rayuwata ka san shi. Ka kuma san yayana Salman da na faɗa maka tun bayan rabuwarmu da shi, ya je nema mana abincin da za mu ci ni da Aunty, ba mu sake ganinsa ba har sadda aka zo aka tafi da mu. To wannan bawan Allah'n na zaune shi ne Yayana Salman! Wallahi shi ne!"
Kuka ya kuma cin ƙarfinta.
Kansa ya ɗaga Alhaji Marwan. Ya ce,
"Ehh ƙwarai na san da zancen. Amma ya aka yi ya zama Salman? Kodai kin manta fuskar tasa ne?"
"Haba Dadyn Yesmeen! Ko ina manta fuskar kowa ta ya zan iya mantawa da ta gudan jinina? Babu ko tantama yayana ne wannan. Salman."
Cikin mamaki da son jin zancen Maryama ta ce,
"Ban san komai ba. Please ko za ki faɗa min? Ta yiu akwai wani taimako da zan iya ba ki."
Ta kuma share kumatunta. Ta ce,
"Sunana Yamaira..."
Ta kwashe komai, tun daga farko har ƙarshe ta sanar da Maryama. A ƙarshe ta ce,
"Bayan wannan mutanen sun tafi da mu, suka ɗaure mana fuskoki ba tare da mun san inda suka nufa da mu ba. Sai da muka isa wani ƙasurgumin daji sannan suka buɗe mana fuskokin namu, suka shigar da mu wani babban gida. A nan muka ga jerin mata birjik, wasunsu a cikin damuwa, wasu kuwa hankalinsu kwance suke hidimar gabansu.
A wannan gidan muka ci gaba da zama, har tsawon wata ɗaya. Kwatsam cikin wani dare aka kawo ma ƴan ta'addar hari, sojoji da gwamnati ta turo, kuma suka gano daji da gidan da muke.
Wannan sojojin ne suka fitar da mu, suka dawo da mu a cikin garin Maiduguri, cewa daga nan kowa ta nemo asalin gidansu ta koma.
A nan tashin hankalina ya sake ninkuwa. Tuna ƙarar bomb ɗin da ya tashi a kangon da Aunty suke, da kuma fitar Yaya Salman bai dawo ba, ga uwa uba wayar ƙarshe da Yaya Salman ya yi da Abbu, ya ji sautin bindiga. Na ɗora hannuna a ka, na rasa uwar ubana. Damuwa ta bi ta dunƙule a cikin zuciyata.
A nan inda nake tsaye na ji an taɓa ni, na juyo don ganin mai taɓa nin, sai na ga wata budurwa wacce ba za ta wuce sa'ar haihuwata ba.
"Ki yi haƙuri kin ji. Dukkan tsanani yana tare da sauƙi."
Ta faɗa cikin sassanyar muryarta. Na ce,
"Ban san sadda nawa sauƙin zai zo ba."
Ta murmusa,
"Duk daren daɗewa zai zo gare ki."
"Ina fatar hakan."
Na faɗa cike da damuwa.
"Zama a nan bai kamace ki ba a matsayinki na ƴa mace. Ki zo mu je gidanmu."
Ban musa mata ba, saboda ko yawan magana ba na so. Na bi bayanta. Gaban wata danƙareriyar mota muka isa, aka buɗe mata baya, ta shiga haɗe da ba ni izinin shiga ni ma.
Bayan mun isa gidansu ta sa na yi wanka, ta kawo min kayanta na saka. Ko da na gama shiryawa an jera min tarkacen abinci a gabana. Na yi mamakin yadda cikin daren nan aka iya haɗa liyafar abinci kamar wannan. Kaɗan na ci na ce na ƙoshi. Na kwanta barci. Nan fa damuwa ta sake ninkuwa, na nemi barci na rasa. Sai kuka da tunanin rayuwata da nake yi.
A gidan su Ummi na ci gaba da rayuwa har tsawon watanni biyu, sannan ta ce min hutunta ya ƙare ita kam, za ta koma makaranta. A nan kuma hankalina ya kuma tashi. Na ce da ita zan koma Bama in binciki dangi da iyayena, ta ce ina, ai har yanzu akwai sauran tashin hankali a garin. Na kartake cewa sai na je, ta haɗa ni da mahaifanta. Da yake mutanen kirki ne, suka lallaɓa ni kan cewa in haƙura har a samu kwanciyar hankali a garin, duk da dai da sauƙi ba kamar da ba. Kalamansu masu daɗi suka siye min zuciya na haƙura. Kuma suka ce idan ina ga kamar zaman gidan ba zai min daɗi babu Ummi ba, sai in bi ta makaranta.
Tare aka mana siyayyar dawowa duk da ni ba ɗaliba ba ce. A nan Al-Qalam University. Tare muka ci gaba da rayuwa, a lokacin da na cika watanni uku a garin ne Allah ya haɗa ni da Alhaji Marwan, har muka fara soyayya da shi. Sadda hutun first semester ya ƙare na su Ummi, muka koma gida hutu, na gabatar da Alhaji Marwan a matsayin wanda zan aura. Abii ya ce ya zo ya same shi su yi magana, tunda dai har na amince zan aure shi.
Kin ji yadda komai ya faru. Kuma tun daga wannan lokacin muka koma Bama tare da Ummi da iyayenta da kuma Alhaji Marwan, muka tarar iyayena babu su, sai dai wasu daga cikin danginmu, wanda suka ɓuya. Amma mafi rinjaye duk an karkashe su basa raye.
Sosai Abii ya yi bincike game da Alhaji Marwan, tamkar ƴarsa da ya haifa haka ya yi ɗawainiya da ni, ya aurar da ni ga Alhaji Marwan. Ga shi har da tukuicin Yesmeen, wacce na saka ma sunan mahaifiyata, Shereefah."
Cike da mamaki Maryama ke kallon ta. Tausayinta take ji sosai, sai dai tsabar al'ajabi da labarin ya gama ba ta.
Da ƙyar ta samu ta tattaro magana ta haɗa, ta ce,
"To amma bara na miki wata tambaya Maman Yesmeen. Yaya Salman ɗin naku ƴan biyu ne asalinsa ko kuwa dai shi kaɗai ne aka haifa?"
Yamaira ta ce,
"Aunty ta faɗa mana wai twince ne, amma wancan ɗin ana haihuwarsa ya rasu..."
Tun ba ta rufe baki ba Maryama ta miƙe tsaye. Sai yanzu hasashen nata ya tabbata. Kanta ta dafe, tana jin tunani kala da kala a cikin zuciyarta. Ta ma rasa abun yi, ganin komai take tamkar a mafarki.
"Ta faru ta ƙare! An yi wa mai dame ɗaya sata."
Ta furta tana fifita da tafukan hannayenta duka biyun, saboda wani irin gumi da ta ji yana tsattsafo mata.
"Kenan dai Yah Noor ba su Momy ne suka haife shi ba?"
Shi kanshi Alhaji Marwan zancen da yake kenan a zuciyarsa. Ya cire hular kansa yana fifita da ita.
Dawowa ta yi ta zauna Maryama. Cikin kuka ta ce ma Yamaira,
"Wannan ba shi ne ainahin Salman yayanki ba..."
"Don't tell me rubbish! Ta ya za ki ce min wai ba yayana ba ne, bayan kuma ina a cikin hankalina?"
"Duba shi da kyau Yamaira. Na tabbatar da dole koma ƙaƙa ne akwai abin da za a iya samu bambanci nasu. Sannan kuma wannan ma ba shi da hankali fa."
Yunƙurin miƙewa zaune ta yi ta kasa. Maryama ta taimaka mata ta tashi zaunen, ta zuba ma Annur idanuwa.
Da ƙyar ta iya gano wata tawada da take a fuskar Salman wacce ta nema ta rasa a fuskar Annur. Ta jima tun suna yara tana masa zancen tawadar, har wata rana yake ce mata da yana da yadda zai yi ya cire ya ba ta ita da ya yi, sai dai kuma babu hali. Ba kowa ba ne zai iya kula da ita, saboda ta kusa da wuyansa take, ita ma saboda tun suna yara ne ya sa ta iya fahimta. Yanzu kuwa ta darara idonta sosai babu ita. Sannan kuma kamar fuskar wannan ɗin ta fi walwala fiye da ta Salman. Duk da ba wai dariya ya yi ba, amma daga yanayin yadda yake za a iya sanin cewa mutum ne shi mai faraa fiye da Salman.
"Na tabbata a shirun nan da kika yi kin gano bambancinsu, ko da kuwa kaɗan ne."
Kai ta ɗaga mata cike da mamaki. Kafin ta buɗi baki ta ma Maryama tambaya ita ta riga ta yin magana.
"Kenan dai ƴan biyu ne..."
"Amma kuma ai aunty ta ce mana gudan ya rasu."
"Duk ma dai yadda za a yi ƴan biyu ne Yamairah. Salman ɗin ku shi ne Sans. Ko?"
"Ehh. Aunty ta saka masa wannan sunan, saboda ɗan fari ne. Please yana ina yanzu?"
"Yana gidan su wannan..."
Ta gwada mata Annur da hannu.
"Gidan su yayan Uncle Marwan."
Ta ƙwalalo ido.
Kai Alhaji Marwan ya jinjina mata.
"Ku faɗaɗa min maganar."
Ajiyar zuciya Maryama ta sauke. Ta labarta mata kaf abin da ta sani, tun daga farko har ƙarshe.
Ta ɗora hannunta a ka,
"Yaushe Yaya Salman ya zama riƙaƙƙen mashayi? Yaushe ya zama mazinaci ban sani ba? Ba halinsa ba ne, wallahi ƙaddara ce ta miyar da shi haka. Yaya Salman ɗina mutum ne mai tsoron Allah. Mutum ne mai ilimin addini, da sanin hukunce-hukuncensa."
Ta kuma sakin wani kukan.
"Ni yanzu mamakin da nake yi, ta yaya Annur ya dawo hannun su Yaya IA? Ina nasu ɗan da suka haifa yake?"
"Ni kaina ina son sanin hakan. Amma kam alamu sun tabbatar cewa Yah Noor ba ɗan su Momy ba ne. Twin brother ɗin Salman ne, yaya ga Yamairah."
"Tirƙashi!"
Alhaji Marwan ya ambata a fili.
*
Ƙarfe biyu da rabi Hanan ta gama haɗa komai ta jera a dining. Ta nufi ɗaki ta samu Janan ta yi wankanta ta cancaɗa kwalliya, ta saka doguwar rigar roba amma ba mai bin jiki ba. Ta tasa waya a gabanta tana ta famar yin selfie.
Hanan ta gyaɗa kai.
"Sannu da aiki Hajiya Janan."
Ta kanne ido haɗe da karkace baki ta ɗauki wani hoton, sannan ta ce,
"Yauwa ke dai ƴar albarka..."
Ta sake karkace baki ta ɗauki hoton. Hanan ta yi dariya sannan ta nufi toilet ta yi wanka.
Tana fitowa ta kimtsa cikin riga da skirt na atamfa da Momy ta siya mata. Saboda ita kam tana son native dresses, duk da cewa ba a ƙasar Hausa suka tashi ba. Ta feshe jikinta da turare sannan ta fice daga ɗakin.
Fira suka yi da Mony sama-sama har aka fara kiran la'asar Momy ta je ta gabatar da tata. Tana dawowa suka jin horn alamar su Dady sun iso. Aikuwa ihu Hanan ta yi haɗe da ficewa a guje domin tararsu. Janan ma daga ɗakin ta fito tana yin video ta snap chart har ta kusa kai ma Momy karo sanann ta farga.
"Idan ba ki ajje wayar nan ba sai na faffalla miki mari."
"Tuba nake ranki ya daɗe."
Ta ɗora wayar bisa hannun kujera sannan ta bi bayan momy suka fice waje.
Sosai suka yi farin-ciki ganin yadda Sans ya warware kamar bai taɓa jin ciwo ba. Kwana ashirin ba wasa ba. Suka rankaya zuwa falo.
Ya jiki suka hau yi masa yana amsa musu da walwala. Kafin suka rankaya zuwa dining table ɗinsu mai kujeru shida, suka jera. Hanan ce ta yi serving ɗinsu, cike da farin-ciki da jin daɗi suke cin abincin, Janan na ta famar surkullenta da ta saba.
Sai da duk suka ƙoshi sannan suka watse. Momy ta buƙaci ganawa da Sans domin ta masa nasiha.
Bedroom ɗinta suka nufa. Nan ta hau yi masa faɗa cikin ruwan sanyi take tafasa shi. Ta masa nasihu masu ratsa zukata, sannan a ƙarshe ta masa addua, haɗe da ba shi izinin tashi ya tafi zuwa ɗakinsa.
Wanka ya watsa sannan ya ɗauro alwalla. Bayan ya gama sallah bai sauka daga bisa kafet ba sai da ya yi istighfari sosai, yana mai tsananin nadama. Sai dai fa damuwar nan ɗaya tana nan addabe da zuciyarsa. Tararrabin ranar da asirinsa zai tonu yake.
***
*To mutanena...an zo wurin fa. Wasu sun ce wai bakin Amrah ya gwanance da faɗin an zo wurin😀 to ba bakinta ba ne. Alƙalamin ne ya saba da faɗar an zo wurin, kuma saboda an zo ɗin ne ya sa yake rubutawa...lol🤣*
*Me za ku ce game da wannan shafin?*
*Na warware muku sirrin auren Yamaira da Alhaji Marwan? Kun ga ta yadda rayuwarta ta dawo Katsina? Kun ga yadda ta kuɓuta daga hannun ƴan ta'adda?*
*Idan har kun gani da gaske kuma kun gode, I need more comments here.*
*Ita kuma ƙawata Janan da ta ɗauki diary, ta kuma rantse sai ta karanta, ko ya abun zai kaya?*
*Da gaske ina son Janan, ina ma dai za ta yi ƙawance da ni🤣😀*
*Tafiyar tamu tana ta gangara. Sannu a hankali alƙalamin ya kusa sauka. Insha Allahu.*
*Masu mutunci sannunku da aiki, sannunku da jimirin kankaro shi. Aikinku na kyau. Keep it up durlings.*
Thanks all.
Pinky durling💞
RAZ 2
[9/24, 11:51 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*
_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_
Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)
Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
7⃣0⃣
Wattpad: PrincessAmrah
***
Sai da ta sha ruwa sannan Alhaji Marwan ya ce da ita ta tashi su tafi, cewa gobe za su sake dawowa su ɗauki Maryama da Annur ɗin, sai su gana da Dr. Hamdan a gidansa.
Har gaban motarsu Maryama ta raka su, sannan ta dawo dafe da kanta, har yanzu al'ajabi bai kau daga zuciyarta ba. Tunanin yadda rayuwar Annur ta dawo a gidan su Momy kawai take, da kuma yadda aka yi aka ce wai Annur ɗin ya mutu a lokacin da aka haife sa. Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce da Annur ya tashi su nufi sallah, saboda tuni aka kira magrib ɗin. Tashi ya yi suka tafi jiki babu ƙwari, shi kanshi kallo guda za ka masa ka tabbatar cewa ba ya cikin walwalarsa.
*
A hankali ta leƙa fuskar Hanan, ta tabbatar da ta yi barci sannan ta ɗaga pillow ɗinta ta jawo diary ɗin Sans. Buɗewa ta fara yi, anan ta ga head line na Bama da kuma exact day na ranar