Showing 48001 words to 51000 words out of 201092 words
Chapter 17 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
launinsu ja, ƙwayar idon kuwa da wani irin fari a cikinta, wanda ya ƙara ma fuskar tasa ban tsoro.
"A duk cikin sharuɗɗan da na gindaya maku, babu soyayya ta gaskiya. Me ya sa kake son ƴan matan biyu, kuma kake son su da gaskiyarka?"
Shiru Annur ya yi, yana jin jikinsa na karkarwa, laɓɓansa na rawa, ya gagara furta komai.
"Na san abin da ya kawo ku. Kana so na cusa wa ƴan matan sonka ta ƙarfi da yaji, saboda kana ƙaunarsu, kuma kana son ka aure su. Haka ne!?"
A daburce Annur ya ɗaga kansa, gabansa sai faɗuwa yake.
"Komai zai iya lalacewa ta dalilin haka. Babu alkhairi a soyayyar da kake ma duka biyunsu. Ka sani, tun farkon aikinmu da kai, na faɗa maka kar ka kuskura ka yi soyayya ta gaskiya, ita ce tonuwar asirinka. Me ya sa ka kasa tanƙwara zuciyarka?"
Cikin murya ƙasa ƙasa Bobby ya ce,
"A yi haƙuri boka gagarabadau, sharrin zuciya ne, ka san bata da ƙashi. A taimaka mana."
Shiru bokan ya yi daga nan, ya fara tsaface tsaface da tafukan hannayensa, yana zane da hannun damansa bisa tafin na hagun.
A hankali ya juyo da hannun gare su, yana faɗin,
"Kun gani? Matuƙar na yi tsafi hannuna ya yi haske, to babu sa'a a cikin tsafin nawa. Gashi kuma hannun ya yi haske. Bani da wani abu da zan iya yi maku har sai sanda ka fitar da soyayyarsu daga cikin zuciyarka. Sanda duk ka shirya, sai ku dawo, zan yi ƙoƙarin gyara ɗaurin da ka so kwancewa."
Shiru suka yi su duka biyun, suna bin bokan nasu da kallo, kafin a hankali Annur ya ce,
"Zan ƙoƙarta ya bokana! Ko dan gudun ɓallowar wata maganar. Ina neman taimakon boka da ya agaza min, ya bani taimakon da zan yakice soyaygarsu daga zuciyata."
Zane ya sake yi a tafin hannunsa, kafin ya ɗan murmusa kaɗan alamun nasara ya juyo da tafin hannunsa saitinsu.
Jajur suka ga hannun nasa, hakan ya sa su yin murmushi a tare, suka kalli junansu alamun jin daɗi.
"A nan dai ka yi sa'a, aljannu sun yarda, zasu taimaka maka."
Ya haɗa hannayensa guda biyu, ya ɗora su a ƙasa, ya ringa faɗin wasu kalamai, wanda jinsu kawai zai iya rikitar da mutum. A hankali ya ɗago hannuwan nasa, ya buɗe su. Wani irin jan gari ne ya fito daga hannun nasa, ya runtse idanuwansa, sannan ya ce,
"Rufe idonka."
Rufewar kuwa Annur ya yi, yana sauraren abin da bokan zai yi masa.
Saukar garin ya ji a fuskarsa, wanda sai da ya ji wani irin ɗau! Tun daga fuskar tasa, ya ringa tafiya cikin jikinsa, ya mamaye duk gangar jikin, kafin ya isa cikin zuciyarsa.
Wani irin abu ya ji ya masa nauyi a zuciyarsa, kafin a hankali ya ji yana sauka, komai nasa yana dawowa daidai.
"Buɗe!"
Boka ya faɗa da ƙarfi, bayan shi ɗin ma ya buɗe nashi idanuwan.
Buɗewar kuwa Annur ya yi, yana jin sauyin yanayi a tattare da shi.
"Ku ajje abin da zaku aje ku tafi. Bayan sati ɗaya ku dawo."
Kuɗi Bobby ya zaro daga aljihunsa ya dire su a gaban boka, kafin suka miƙe a tare, suka nufi ƙofar fita.
Hatta da duniyar da yake ciki sai da ya fita daga ita, ya dawo asalin tasa duniyar. Codein ɗin ya sake sa, kamar ba yanzu ya shanye kwalba ɗaya a cikin lemo ba.
A wannan karon kam shi da kansa ya ja motar, yana jin daɗi matuƙa, da wahaltacciyar soyayyar da aka cire masa.
"Abokina...abokina na gode ƙwarai."
Ya yana kallon Bobby da fara'a a fuskarsa.
"Babu godiya a tsakaninmu, na san ka sani ai."
"Haka ne kam."
Ya faɗa bayan ya mayar da hankalinshi ga tuƙin da yake yi.
Tafiyar minti sha biyar ce ta shigo da su cikin garin Katsina. Sai da suka fara biya wa suka siya flavor na shisha kafin suka kama hanyar gidan su Bobby.
"Abokina, sai na koyar da yaran can lesson, sai sun san cewa ni ba sa'ansu ba ne, ni ba irin mutanen da ake wulaƙantawa ba ne a ci riba. Wallahi! Ka ji na rantse, ba zan barsu ba."
Ya saki wani mummunan murmushi, mai cike da tarin ma'anonin da shi kaɗai ya bar ma kansa saninsu.
Bayan sun isa gidan su Bobby sai da suka biya cikin gidan, Annur ya gaishe da maman Bobby kafin suka nufi ɗakinsa.
Ƙarƙashin gadonsa ya jawo wata ƴar jaka, wacce ke cike da kayan maye iri daban daban, masu tsada sosai kuma, irin na manyan yara.
Sosai suka sha suka bugu, bayan sun gama sha kuma suka ɗora da codein. Basu jima ba bacci ya ɗauke su su duka biyun.
To fa! Masu karatu. Kun ga dai yanda abin ya kasance.
Me zaku iya cewa?
Su Maryama zasu ci riba kuwa?
Wane irin asiri ne aka masu, wanda har boka ke cewa saura ƙiris ya lalace?
Wane irin mataki ne Annur ya yanke daukawar Jiddah da Maryama?
Mu je zuwa dai...da sannu zaku samu amsar kaf wannan tambayoyin.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:46 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
2⃣8
Wayarta ta jawo daga jikin caji, ta zare daga cajar, sannan ta latsa kiran Jidda, ta kanga ta a saman kunnenta na hagu.
Cikin sassanyar muryarta ta ce,
"Har yanzu fa bai kira ni ba, Jiddah. Ina tunanin ko dai akwai damuwa? Kar a je fa Annur ya faɗa masa komai, wata ƙila ya gano ni."
Cikin kwantar da hankali Jiddah ta ce,
"Ki kwantar da hankalinki, insha Allahu babu abin da zai faru. Ni ɗin ma dai Noor bai kira ni ba, to ban yi mamaki ba, saboda kin san halin mashaya, da zarar sun shiga damuwa sai su afa kayan maye, shi ne kawai suke ga zai kai su duniyar da suke so, wacce zasu samu sassauci a zuciyarsu. Ina tunanin abin da Annur ɗin ma ya yi ke nan."
Shiru Maryama ta yi kamar tana son magana, bata kai ga faɗin komai ba ta sake jiyo muryar Jiddah na faɗin,
"Ina ji a jikina komai zai tafi yanda muke sonsa. Zamu yi nasara da ƙarfin Allah."
Sai a lokacin Maryama ta buɗe bakinta ta fara magana, cike da rauni da fargaba.
"Ina fatan hakan, Jiddah. Ni yanzu abin da ma ya dame ni yanda zan tinkari Mama da maganar, tun sanda na dawo daga Islamiyya take bin kaina na faɗa mata damuwata, wai da alama akwai abin da yake damu na. Na rasa ta inda zan fara, ban saba yi ma Mamana ƙarya ba, ko na mata ma sai ta gane."
Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke, ta ɗan runtse idonta kafin ta buɗe a hankali, tana tunanin ta inda zasu ɓullo ma wannan al'amarin.
"Idan har kika yi kuskuren faɗa mata komai, plan ɗinmu zai iya ɓaci, taimakon da kike son yi zai iya tsayawa, ladar da zaki samu ta kufce miki. Ba dan komai ba sai sanin da na yi babu uwar kirkin da zata ji ƴarta na neman jefa kanta a wannan risky ɗin kuma ta amince. Na san Mama, na san wacece ita, na san cewa bata son shirme, bata son duk wani abu mai wala wala. Na tabbatar ba zata taɓa barinki wannan gagarumin aikin ba."
Tana dakatawa nan, Maryama ta ce,
"Sanin hakan ya sa nake tambayarki mafita, Jiddah. Ban san ya zan ɓoye wannan damuwar, har Mama ta kasa ganewa ba."
Jiddah ta ce,
"Idan ta sake tambayarki, kar ki ɓoye mata komai game da rayuwar Amrah, ki faɗa mata duk abin da kika sani. Idan kin tashi sai ki ce tausayin Amrah ne yake azalzalar zuciyarki. Sai dai kar ki yi kuskuren kawo mata zancen lalacewar da Annur ya yi, kin san iyaye da hangen nesa, babu wuya zata iya ɗago ki."
Cike da gamsuwa da wannan shawarar Maryama ta ce,
"Insha Allahu hakan za a yi. Kuma na san Mama da sanyin hali, da taushin zuciya. Ita ɗin ma zata iya shiga damuwar da ta fi wacce na shiga, a lokacin da na ji labarin Amrah. Kin ga daga nan sai ta daina mamakin shiga ta damuwa."
"Exactly."
Jiddah ta furta cike da farin ciki.
"Sannu ƙawata, Jiddah. I've nothing to say, but thank you very much. You're indeed a nice person. Allah Ya bar min ke."
Ta ƙarisa maganar da lumshe idanuwa, kamar tana a gaban Jiddah ɗin ne.
"It's my pleasure to make you happy, Maryam. Dan Allah bana son godiyar nan, kin sani. Kin fi ƙarfin komai a gare ni. Zan iya sadaukar da komai nawa, dan samuwar farin cikinki. Ki sani, ina tare da ke, duk tsanani, insha Allahu babu wani abu da zai faru face alkhairi. Bobby kuma..."
Kafin ta faɗi abin da zata faɗi ta jiyo muryar Maryama na faɗin,
"Kin ga ɗan halak! Gashi nan yana kirana."
Da murna Jiddah ta ce,
"Bara na kashe da sauri, kafin ta tsinke. Duk yanda kuka yi, let me know, please."
"Insha Allahu."
Maryama ta faɗa haɗe da tsinke wayar, tana ƙoƙarin ɗaukar ta Bobby. Kafin ta ɗauka har ta tsinke, sai dai tana tsinkewa yana sake kiranta. Ta ɗan jima bata ɗauka ba, kafin ta ɗauka cikin ruwan sanyi ta ce,
"Hello."
"Maryama, sarauniyar mata."
Tana jin ya fadɗi haka ta ji gabanta ya faɗi, dan ta tabbatar abin da suke tunanin bai faru ba, dan inda a ce ya faru da bai kira ta da hakan ba.
A wani ɓangare na zuciyarta kuma tana jin kamar lokaci ne bai yi ba, sun yi gajen haƙuri na tsammanin cikar plan ɗinsu a daidai wannan lokacin.
"I can't sleep without hearing your voice, and you know."
Ya ƙarisa maganar da sakin wani murmushi, mai cike da bayyanar da soyayyar da yake ma Maryama.
"Dan Allah Bobby..."
"Na ƙyale ki? Wai sau nawa kike son na maimaita miki? Na faɗa miki for many times cewa ba zan iya rabuwa da ke ba, ba zan iya ajje soyayyarki, ta tashi a iska ba. Me ya sa ba zaki gane hakan ba? Me ya sa kike son ina maimaici a ko wane lokaci? Dole ki so ni Maryama, dole ki koya wa kanki so na, ko ma ta halin ƙaƙa ne."
Dafe kanta ta yi, tana mai jin takaicin kalamansa. Tunowa ta yi da plan ɗin nasu, hakan ya sa ta sassauta muryarta, cikin wata murya ta ce,
"Bobby...Bobby ba wai bana sonka ba ne, kawai dai bana son halayenka ne. Yanzu ka ga fa, wai so na kake, amma kake min irin wannan kalaman, kake son tilasta ni, wai dole sai na so ka. Ina amfani? Ina amfanin halinka? Kai ke nan sai abokan banza, wanda suke ƙara ɓata maka suna.
Yanzu kana tunanin ko na amince da soyayyarka, iyayena zasu yarda su aura maka ni, bayan sun san baka da abokan kirki?"
Wani irin sanyi ya ji a zuciyarsa, ashe dai zata iya sonsa ɗin, ashe akwai ranar da irin wannan maganar ta kirki zata shiga tsakaninsa da Maryama?
Murmushin gefen fuska ya yi, ya ɗan taune leɓonsa na sama kaɗan, kafin ya ce,
"Babu kamarki, Maryama. I love you with all my heart. Ki dai so ni ɗin, ki amince da soyayyata, komai zai iya zuwa da sauƙi."
Tafin hannunta ta sa ta ɗan shafi fuskarta, tana jin yanda kalamansa ke mata yawo a cikin zuciya. Haushinsa take ji, bata ko son jin muryarsa. Ta tsane shi, kalamansa kuwa, ƙara rura wutar tsanarsa kawai suke a cikin zuciyarta.
"Na gode."
Kawai ta faɗa a hankali.
"Sau ɗaya tak, ki furta kina so na, I'll be glad, zan kwana ina murna, ina jin sauyi a duniyata."
Janye wayar ta yi daga kunnenta, tana jin ko kaɗan ba zata iya daurewa ba, ba zata iya jurar jin kalaman nan nasa ba.
Guntun tsaki ta yi a hankali, tana ƙara ɓata fuskarta, ta ce,
"Ban taɓa furta wannan kalmar ga kowa ba, ba kuma zan fara a kanka ba. Ka daina tunanin ma zaka ji ta, saboda kalma ce mai matuƙar muhimmanci, wacce bata cancance ka daga gare ni ba."
"Abu mai sauƙi ke nan. Na daina tunanin zan ji ta daga bakinki? To na daina. Lokacinki kawai zaki bani, na tabbatar akwai ranar da da kanki zaki furta min ita, ba wai sai na roƙe ki ba."
Ajiyar zuciya ta sauke, ta ce,
"Bacci nake ji, zan kwanta, please."
"Zan so masoyiyata ta kwanta cikin aminci. Ki kwanta, ki yi bacci mai daɗi. Safe night."
Bata ko tsaya jin wata kalamar daga gare shi ba ta tsinke wayar haɗe da dafe kanta, tana yin bayyanannen tsaki.
Jiddah ta kira ta shaida mata yanda suka yi da Bobby, ta ƙara da,
"Ni ina gudun samuwar matsala ne. Kar na amince masa kuma ƙalli ƙalalla ta ƙale min, Jiddah. Kin san halin irin samarin nan, babu wuya sun illata mutum. Na ma rasa me zan yi wallahi."
Cikin kwantar da hankali Jiddah ta ce,
"Insha Allahu babu abin da zai faru sai alkhairi. Idan ba ta wannan hanyar ba babu hanyar da nake ga zata zame mana maslaha. Saboda Farouk Sardauna ne kaɗai abokin Ya Noor wanda ya yarda da shi. Shi ne wanda suka fi sheƙe ayarsu tare. Kinga rabuwarsu ce kawai zata iya gyara rayuwar Annur, zata sa ya ji komai na banza ya fice daga duniyarsa, har ya sake waiwayarmu."
Jinjina kai Maryama ta yi, a hankali ta ce,
"Haka ne, Jiddah. Zan bashi lokaci tukuna, kafin na furta na amince masa. Daga nan sai a mu san miye next."
"Yes, haka za a yi. Mama kuma kar ki tinkare ta da maganar can har sai idan ta sake tambayarki."
"Insha Allahu. Bara na kwanta, sai da safe."
Tsinke wayar suka yi su duka biyun, mafi rinjaye na zukatansu na ƙarfafa masu guiwa cewa zasu yi nasara, kaɗan ɗin zuciyarsu ne yaƙe tsayar da su.
***
Wayarsa ce ta ɗauki turi, a daidai sanda ya shiga gida. Dubawa ya yi ya ga mai kiran nashi, bayyanannen tsaki ya yi haɗe da silencing nata.
"Momy..."
Ya furta a daidai sanda yake shiga cikin ɗakin, ya nemi hanyar kujerar da ta fi kusanci da tata.
"Kin kira ni."
Ya faɗa yana kallonta da idanuwansa da har yanzu basu gama dawowa daidai ba, ƙwayoyi da cyrup ɗin da ya sha basu sake sa ba.
"Ehh. Dadynku ke kiranka."
Kanshi ya ɗan sosa kaɗan, cikin daburcewa ya ce,
"Momy, lafiya dai ko?"
"Ina fa lafiya, Annur? Ka san abin da ya faru kuwa? Ka san muguwar asarar da ka ja wa mahaifinka a kamfaninsa? Wai me yake damunka ne? Sai yaushe zaka san cewa ka girma? Sai yaushe ne zaka kimtsatsa halayenka, su zama na gari, asalin yanda suke a baya?"
Shiru ya yi kansa a ƙasa, yana jin haushin kalaman da suke fita daga bakin mamansa, wanda basu da wani tasiri a gare shi.
"Da kai fa nake, Annur. Sai yaushe ne zaka zama cikakken mutum mai kamala?"
Da ƙyar ya iya ɗaga laɓɓansa ya ce,
"Momy ni fa ban san abin da na yi ba."
"Ba kuma zaka taɓa sani ba, tun da baka da tunani da lissafin sanin. Ka tashi ka same shi a ɗaki, kai yake ta zaman jira."
Tashi ya yi jiki babu ƙwari, a hankali yake ajje takunsa, gabansa na faɗuwa, har ya isa bakin ƙofar ɗakin mahaifinsa.
Ba wai baya son shiga ba ne, ba kuma yana tsoronsa ba ne, a'a, kawai dai yana ganin ƙwarjinin Babansa ne, duk iya munanan halayensa yana shakkun Dady. Ba dan komai ba sai irin gatan da yake gwada masa, yake fifita sa a duk cikin yaran da ya haifa, ko da yake dai duk mata ne, shi ne kawai namiji, amma bai kasance mao halayen kirki ba.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, kafin a hankali ya fara ƙwanƙwasa ƙofar, ya shiga da sallama ƙunshe a bakinsa.
Bai ko amsa sallamar ba mahaifin nasa, ya juyo yana binsa da wani kallo, kallo mai cike da tsantsar takaicinsa da yake ji a daidai wannan lokacin.
"Barka da zuwa Dady. Ka kira ni bana nan, ina gidan su Farouk ne. Kuma lokacin magrib ya kusa, shi ya sa kawai na bari har na yi sallah sannan na shigo."
Gyaɗa kai kawai Dady ya yi, ba wai dan ya gamsu ba, sai haushinsa kawai da ya ƙara dira a zuciyarsa.
"Yanzu Annur abin da zaka min ke nan? Ɓarnar da zaka ma kamfaninmu ke nan? Ni ina ganin na bar komai a hannunka, kana kula da komai yanda ya kamata, ashe banzan tunani nake? Ashe sam! Ba hakan ba ne? Ashe ba zaka taɓa yin abin da zai zama farin ciki a gare ni ba?"
Har a lokacin kansa a sunkuye yake, ya gaza faɗin komai, ya kuma kasa haɗa ido da Dady.
"Sanadiyyar munanan halayenka, da damar mutane sun fara yunƙurin barin kamfanin, dan babu wani abu da suke ƙaruwa da shi.
Ashe kamfanin tractor da suka nemi a masu wasu parts da dama na motocin, har kuɗinsu sun bayar, amma ka saka masu shiririta, ka kasa tsayawa a yi komai yanda ya dace.
Dama dai na daɗe da haƙura da zane, tun daga sanda ka warke, ka daina mana zane zane, wanda su ɗin kansu wata asarar ce, tun da inda a ce zaka tsaya ka yi da kanka, na tabbatar za a fi samun yanda ake so, tun da kowa ya sanka, ya san sunanka ta wannan ɓangaren. Amma a karshe dole muka samo wanda yake mana ta wannan ɓangaren, tun buɗe kamfanin bayan warkewarka, kai kuma ka tsaya a naka, general manager. A hakan ma ka kasa yin komai yanda ake so.
Ko ka san cewa kuɗin parts of that tractor da suka bayar, sun dulmiye a cikin kamfani, kuma an rasa inda suka shige? Ka san cewa mun yi babbar asara, babu uwar babu ribar?
Shi ke nan ai, sai ka zuba ruwa a ƙasa ka sha, ka samu yanda kake so. Ka ga idan kaf ma'aikatan suka gama guduwarsu, sai mu rufe kamfanin, mu ci gaba da zama a haka, tun da abun da kake so ke nan."
Ya ƙarisa maganar da ɗaga murya sosai, duk irin ƙaunar da yake gwada wa Annur, amma ya ji ko kaɗan ba zai iya haƙuri ba wannan karon, duk da ya san abubuwan da yake yi a kamfani a baya, bai taɓa tinkararsa da maganar ba sai yau.
"Ɓace min daga gani."
Ya gwada masa ƙofa da hannuwansa.
Da ƙyar ya iya ɗaga tafukan