Showing 114001 words to 117000 words out of 201092 words

Chapter 39 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ƙudirin wancan na ƙaryar ba. Amma kin ga idan ya ji sauƙi, zai iya nemawa kansa kariya, zai kuma iya tabbatarwa iyayensa cewa shi ne ainahin Annur."


"Tabbas kuwa kin yi gaskiya Maryama. Allah Ya ba shi lafiya. Ki min kwatance gidanku insha Allahu zan zo gobe."


Kwatancen kuwa ta yi ma Umma, sannan ta kama hanyar barin gidan.


Da faraa ta shiga gidansu bayan ta yi sallama. A falo ta samu Mama zaune da hijabi a jikinta, da alama sallar azahar ta gama, saboda lokacin har sha biyu ta wuce.


"Sannu Maryama. Har an dawo?"


"Na dawo Mama."


Ta faɗa cikin muryar gajiya haɗe da cire hijabinta.


"Umman Amrah ta ce na gaishe ki Mama. Gobe ma za ta zo ta duba Yaa Noor."


Mama ta ce,


"To Allah Ya kai mu. Ina amsawa. Sai ki nufi sallah ko. Idan kin fito ki kai ma Annur ɗin abincinsa, ki ba shi magani. Ki zo ki ci naki ke ma."


"To Mama."


Ta furta bayan ta miƙe. Ta nufi ɗakinta.


Sai da ta ɗan watsa ruwa sannan ta saka ƙananan kaya ta fito. Abincin na Modu ta zuba masa a plate, sannan ta nufin ɗakin nasa, fuskarta ƙunshe da murmushi.


Yana ganinta ya miƙe tsaye, da alamun dama ita yake tsumaye.


"Ya Noor sannu da hutawa."


Ta faɗa cikin sassanyar muryarta, bayan ta zauna a bakin gado.


Bai ce da ita komai ba, kamar yadda dama ba ta yi tsammanin jin wani furuci daga gare shi ba.


"To ga abincinka nan. Ka ci sai ka sha magani. Ina zuwa bari in dawo."


Ta bar ɗakin, babu jimawa sai ga ta ta dawo hannunta riƙe da wayarta.


Samunsa ta yi bai ci komai ba. Hakan ya sa ta ɓata fuskarta, ta saita idanuwanta a cikin nasa.


"Me kake nufi na ga ko taɓa abincin ba ka yi ba. Ko wani abu ya faru ne? Akwai abin da kake so Yaa Noor?"


Duk ta marairaice fuska, cike da damuwa.


Gyaɗa mata kansa ya yi, take ta fara ganin ruwan hawaye a idanuwansa. Nan take jikinta ya ɗauki rawa. Ba ta san me ke damun Modu ba. Yau ga shi yana kuka, wanda tunda ta ɗauko shi yau ce rana ta farko da ya yi kuka.


"Yaa Noor na maka laifi ne? Bayan na tafi Mamana ta maka wani abu ne? Ko Abba ne? Please tell me."


Runtse idanuwansa ya yi tare da matso wasu ruwan hawayen. Ya sunkuyar da kansa ƙasa.


"My God!"


Ta dafe kanta, tana jin wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ba ta san me yake damunsa ba.


"Amrah ta ƙi dawowa gare ni, bayan kuma ta san ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. Me ya sa za ta min haka? Me ya sa za ta min nisa ta ƙi waiwaya ta?"


Cike da tausayi ta sauke ajiyar zuciya, cikin kwantar da hankali ta fara masa magana,


"Ka daina kukan to ya isa haka. Mun yi waya da Umman Amrah, ta ce min gobe za ta zo..."


Bai ko bari ta rufe bakinta ba ya yi caraf ya ce,


"Tare da Amrah za su zo? Yeee! Na ji daɗi zan ga Amrata."


Ɗan taunar leɓonta ta yi Maryama. Ta ce,


"Ai in dai har ba ka daina kukan nan ba to zan hana ta zuwa."


Hannuwansa duka biyun ya sa ya ringa shafar hawayensa, yana faɗin,


"Na daina. Allah ba zan kuma yin kukan ba."


"Yauwa Yayana. To ka ci abincinka. Ko ni kake so na ba ka a baki?"


Bai ce mata komai ba ya fara zira abincin a bakinsa, hannu baka hannu ƙwarya.


Sai da ta tabbatar ta ba shi magani sannan ta masa sallama ta fita, saboda jin Mama ta ƙwala mata kira, kuma ma akwai abin da take son yi a waya, kukan da ya yi ne ya dakatar da ita.


Kusa da Mama ta zauna bayan ta ɗora wayarta a bisa cinya. Ta ce,


"Mama ga ni."


Tun kafin Mamar tata ta ce komai suka ji sallama. Wata ƙawar Mama ce ta yi sallamar, fuskarta ƙunshe da faraa.


Amsa sallamar suka yi a tare, Maryama ta gaishe ta, sannan ta ba su wuri.


A bisa gadonta take kwance. Ta kunna datarta, sannan ta shiga website ɗin da suka fara magana da Sandra.


Tana shiga ta inbox ɗinta ta ci karo da lambar Dr. Hamdan M. Ramat, sai kuma ta Dr. Aqaaq Saifullahi daga ƙasa. Ta ba ta haƙuri cewa ta ji ta shiru ba ta neme ta ba, ayyuka ne suka sha kanta. Ganin kamar ba ta kusa Dr. Sandra ɗin, ya sa Maryama ta sauka, bayan ta ɗauki lambobin.


Ta Aqaaq Saifullahi ta fara nema Call forwaded, hakan ya sa ta latsa ta Dr. Hamdan ɗin.


Bugu uku ya ɗauka da sallama ƙunshe a bakinsa, ita ɗin ma haka. Hakan ya sa suka amsa sallamar a tare, Maryama ta gaishe shi cikin girmamawa. Cikin seconds kaɗan ta gano cewa Dr. Hamdan mutumin kirki ne, babu girman kai ko kaɗan a tattare da shi, a yanayin da ya amsa gaisuwarta kawai.


"How may I help you?"


Ta jiyo muryarsa ya ambata, cikin sassanyar muryarsa mai cike da dattako.


"Ahmm...I'm Maryam by name, calling You from Katsina."


"Go on..."


Ta ji ya ambata, da alama yana wani aiki ne, kasantuwar likitoci dama lokutan kansu ƙalilan ne.


"I heard alot about you, from Dr. Sandra. So, I just decided to contact you, am sure you'll help me out of my problems."


"Uhm."


Ya faɗa yana saurarenta.


"My brother is seriouly ill, for a long time. He has a mental problem, or may be a lost of memory, I don't exactly know."


"Oh! This is serious. The most important thing is that in gan shi zahiri. Kin ce you are from Katsina right?"


"Yes Dr."


Ta faɗa cike da girmamawa.


"Can you come to Maiduguri?"


Ras! Ta ji gabanta ya faɗi. 'Maiduguri?' ta ambata a birnin zuciyarta. A yadda take jin matsaltsalun Borno ne za ta yi fatar kai kanta can? Lallai kuwa akwai damuwa.


"Are you with me?"


Ta ji ya ambata. Hakan ya sa ta gaggauta faɗin,


"Ye...yes Dr."


"Ok. The best solution shi ne a kawo shi ɗin, saboda I can't decide anything without seeing the patient. Zan duba schedules nawa, zan ba ki appointment. Ki kira ni by 8pm today."


"Thank you very much Dr. I'll call you by Allah's will."


Ta kashe kiran. Tana jin yadda gabanta ke faɗuwa. Saboda har ga Allah ita kam tinkarar Borno a ganinta babban siyar da rai ne. Idan ma har ta amince za ta je ɗin, ta tabbata iyayenta ba za su amince mata ba. Miƙewa ta yi jiki babu ƙwari ta jona wayarta caji, sannan ta koma falo wurin Mama.


Ta samu har baƙuwar ta tafi, sai Mama kaɗai zaune tana kallon tashar Arewa 24, da suka saka film ɗin Ƴar Duniya.


Yanayinta kawai Mama ta karanta ta tabbatar akwai abin da yake damunta. Ba ta damu da sanin ko miye ba, saboda ta fahimci kamar tirsasa sanin damuwarta ne ke haddasa take shirga mata ƙarya.


"Maryama albishir kuwa nake so na miki."


Kwantar da kanta ta yi a ciyar Mama, ta zame ɗankwalinta da nufin ta mata susar kai.


"Ina jin ki Mamana. An dai je a ɗauko Hammad daga School ko? Don ni kam tsoron mitarsa nake."


Murmusawa ta yi Mama, ta ce,


"Mun yi waya da Abbanku yanzun nan, ya ce ya tura Mallam Ya'u ya ɗauko shi."


"Yauwa. Don ni kam tsoron Hammad nake. Rigimarsa yawa gare ta."


Murmushi kawai ta yi Mama. Ta ce,


"Ɗazu Kawunku ya zo, kin sani ai."


"Ehh Mama."


Ta faɗa tana jawo tsoron kalabarta guda, tana gyara tufƙarta.


"Sun yanke shawarar haɗa ku aure, ke da yayanki Deedah..."


Zabura ta yi Maryama haɗe da miƙewa zaune, ta tsura duka idanuwanta a fuskar Mama. Cike da mamakin jin kalamanta.


"Me ya faru?"


Mama ta faɗa, ita ma tana kallon ƴar tata.


"Mama don Allah ki ce min wasa kike ba gaske ba."


"Ta ya zan miki wasa a abu mai muhimmanci kamar aure? Hukunci ne daga kawunku ya yanke shi, na kuma tabbata babu abin da zai sa a canza shi."


Cikin daƙiƙu kaɗan ruwan hawaye suka gama wanke fuskar Maryama, tamkar an ɗebi ruwa an kwara mata.


"Mama me ya sa kawu Imrana zai mana haka? Me ya sa ba zai bar kowa da ƙudirinsa ba? Na tabbata Yaya Deedah na da wacce yake so, yana da wacce yake da ƙudirin aure, kamar yadda ni ma ba ni da ƙudirin aurensa, nake masa irin soyayyar yaya da ƙanwa. Don Allah a bar ni da ƙudirina Mama, a bar ni na fidda gwanina da kaina, wallahi ba na son auren Yaya Deedah."


Ta faɗa a jikin Mama, tana kuka sosai tamkar wacce aka ma dukan tsiya, ta ko'ina jikinta karkarwa yake.


Me ya sa za a mata haka? Me ya sa ba za a bari ta ƙarisa kyakkyawan aikin da ta ɗauko ba? Don me ya sa ba za a bar ta ta zame ma Annur Amrarsa da ya rasa ba? Sai da suka gama shaƙuwa da Annur ne za a mata wannan zaɓin? Yaushe rabon da a yi auren haɗi? Kamar iyayen yanzu sun waye ai, sun daina yi wa yaransu auren dole, saboda sun fuskanci matsalolin da yake haifarwa.


Kuka take mai sauti, mai cike da tashin hankali da neman agaji. Sosai take jin wani irin raɗaɗi da zugi a zuciyarta, tsanar Ahmad Deedah na shiga ta kowanne saƙo da ke cikin zuciyarta.


***


Suna daf da shiga garin Bama suka fara ganin tashin hankalin da ke wakana a garin. Da gawarwakin sojoji suka fara cin karo, wanda ya ƙara tsoratar da su. Sojoji duk training ɗin nasu da komai amma a haka aka karkashe su, aka yasar da gawarwakinsu, wato don ma mutane su gani su ƙara tsorata.


"Shi kenan na rasu su! Na tabbata an gama da su..."


Ya fasa ƙara mai ƙarfi, yana mai fuskantar dreban da duka hankalinshi.


"Ka gani ko? Da alama sun cinye garin baki ɗaya. Sun gama da kowa da ke ciki."


Dakatawa ya yi da mota dreban. Ya ma rasa yadda zai yi da Sans. Kallonsa yake cike da tausayinsa. Wannan babbar jarrabta ce, mai wuyar hayewa. Tun sadda suka kamo hanyar garin Bama Sans ke ba Dreban labarinsa, da duk abin da ya faru tun farkon kiran da Abbansa ya masa.


Kamar da wasa suka ringa jiyo ƙarar mota, da kuma hasken fitilun motocin da suke gabatowa.


Hankulansu ne suka tashi. Dukkanin nutsuwarsu ta gushe. A hankali Sans ya buɗe murfin gaban motar, ya shawarci dreban ma da ya ƙoƙarta ficewa cikin hikima, ta yadda ba za a gan shi ba, duk dayake cewa ba su san ko su waye tafe ɗin ba.


Daga bayan motar suka ɓoye, maƙalƙale da juna suke, ƙirazansu na duka, duniyarsu na juye musu.


Suna jin sadda motar farko ta wuce da ƙara tiiiii! Kamar za ta tashi sama. Ta biyun ce ta ƙoƙarta dakatawa a gefen tasu motar, tare da kashe wutarta.


Sunan Allah suke son ambata amma sun neme shi sun rasa. Tashin hankali suke ciki wanda suka gaza tuna kalmar addua ko guda.


Fincikarsa ya ji an yi Sans, cikin wannan halin ya kalli matashin da ya finciko shi ɗin. Sanye yake da dark glasses, hannunsa riƙe da bindiga ƙarama, gudan hannun kuma ya shaƙure Sans ɗin da shi, yana kallon cikin idonsa.


Kafin ka ce me, wurin ya cike da bataliyar ƴan ta'addan, wanda mafi rinjaye na cikinsu sanye suke da kakin sojoji, da alama mutanen sojojin da suka kashe ne, suka cire kayansu suka miyar a jikinsu.


Dariya wani daga cikinsu ya fasa da ƙarfi. Ya kalli Dreba da ya gama tsurewa ganin yadda ake jijjiga Sans. Bai ankara ba ya ji sautin bindiga, an harbi gefen titi da ita. Cikin tsoro da kiɗima ya ce,


"Don Allah don Annabi ku min rai, wallahi na tuba, ku yi haƙuri don Allah, ƙaddara ce ta shigo da mu. Kar ku mana komai don Allah."


Wani ƙato baƙi-ƙirin mai jajayen idanuwa, fuskarnan tasa ɗaure tamau ya kalli dreban da faɗin,


"Ba a magana a duk inda muke. Duk wanda ya yi ta kuwa furucinsa na ƙarshe kenan a duniya. Zan maka uzuri, ka ƙara kalma guda kawai, ko kalimatushshahada ka yi, wata ƙila ka samu rabo a can."


Matasan da za su kai kimanin biyar suka tulle da dariya, banda wanda ya yi maganar.


Bakinsa rawa yake dreban, baki ɗaya jijiya da jininsa yake jin suna dakatawa da aiki, sanadiyyar harsashin bindiga da ya ji a saitin zuciyarsa.


"Allah, Allah!"


Su ne kalmominsa na ƙarshe, sanann rayuwarsa ta fita.


Ƙara ya saki da ƙarfi sosai Sans. So yake shi ɗin ma su kashe shi. Bai ga amfanin rayuwarsa a daidai wannan lokacin ba.


"Ƙarshenku ba zai yi kyau ba. Sai Allah ya saka ma duk wanda kuka zalunta. Ina kuka kai min iyaye da kuma ƙanwata? Ku faɗa min ina suke? Ina Aunty take? Ta samu abinci ta ci? Yamaira ƙanwata tana ina? Ina Abbuna?"


Kamar zautacce yake sako wannan zantukan, yana ƙoƙarin ƙwace kansa daga hannun wancan matashin, da dukka ƙarfin da ya masa saura.


Wata irin muguwar jifa matashin ya yi da Sans, sai bisa wani ƙaton dutse ya buga kansa da ƙarfi. A take jini ya fara malala daga kan nasa, wanda hakan ya tabbatar musu da cewa ba ya raye.


Barin wurin suka yi su dukansu, amma wancan ɗayan bai tafi ba sai da ya ma Sans harbi biyu a ƙafarsa ta dama, sannan ya masa ɗaya a ƙafar haggu, duk da cewa a tunaninsa ba ya raye, kawai dai yana son ya ƙarisa huce takaicinsa ne.


A nan suka tafi suka bar Sans da ke kwance ba ya numfashi, da kuma dreban da tun ɗazu ya mutu.


***


*This page is too short, I know. A yi haƙuri da zuwansa haka, na so ya zarce, amma Allah bai nufa ba, kuma ina son yin posting ɗin yau, saboda farin cikin wasu bayin Allah. Kun san ko su waye? Aunty Maijidda Musa is among. Basman mai sanyinta ba zan gajiya da ambatarki a pages na book ɗin nan ba. Kina raina, ina kuma jin daɗin comments ɗin ki. Habibaty Queeny, Queen miemie ke ma, kina cikin wanda za na gaisar. Iya wuya ana tare, ina yin ku, ina ƙaunarku fisabilillah🤝*


*Gaskiya dai wattpad ya kamata a ce an koya mana yadda za mu ringa gano Ghosties, mu ringa ganin duk wani mai karanta mana post amma ya kasa kankaro mutunci😎 sai iya ƙwalala ido a karanta, ana jin daɗin abun amma baki ya gaza furta comment, hannu ya gagara dangwala tauraro. Kun ji ni ai ba? Sannunku kun ji.😏*
*Masu votes duk ina gani, ina kuma tsananin jin daɗi wallahi. Ku kuke daɗa ƙarfafa mini guiwa, har nake yin update a kan lokaci😘😍*


Thanks all


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/2, 3:58 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


5⃣3⃣


Wattpad: PrincessAmrah


Kimanin awanni goma sha takwas ya ɗauka a halin da yake ciki. Domin kuwa tun sadda ƴan ta'addan suka masa wannan ta'asar ya yi mummnar suma, wacce in da a gaban wasu ya yi ta, tuni an binne shi ma.


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Abubuwan da suka wakana ne suka hau faɗo masa. Yadda ya ringa sako magana tamkar ba ya cikin hayyacinsa, da kuma sadda aka jefa shi jikin dutse.


Raɗaɗi yake ji tun daga fatar kansa har izuwa cikin kwanyarsa. Ƙafarsa, ciwo take masa mai tsanani, haka ɗayar ƙafar ma, sai dai kuma ba ta kai ɗayar azaba ba.


Wani irin ƙunci yake ji Sans, a zuciyarsa yake fatar mutuwa ta zo masa. Mutuwa ta zo ta ɗauke shi, zai fi jin daɗin hakan, fiye da rayuwar da yake da ita a wannan lokacin.


A ce yau shi ne ya wayi gari babu Abbaunsa, babu mahaifiyarsa, babu kuma tilon ƙanwarsa da ya fi ji da ita a duk duniyarsa.


Yunƙurin tashi zaune ya yi amma ya kasa. Jikin nasa ya masa tsami sosai. Ga ƙishi da yunwa da suke addabarsa. Kuma babu ko halittar dabba da ke gicci a dajin bare ya sa ran ganin bil-Adama. Kusan shida na yamma kenan, rana ta fara ƙoƙarin faɗuwa. Daga inda yake kwance ya ɗago kanshi ya kallo Dreban nan kwance ƙasa babu ko alamar numfashi a tattare da shi. Numfashi ya saki mai ƙarfi, haɗe da sakin kuwwa wacce ta karaɗe dajin, har ana jin echo sound na dawowa, duk da kuwa open place ne.


"Oh Allah! Save me ya Allah!"


Ya runtse idanuwansa. Zafafan hawaye na fitowa daga cikinsu, suna gangarowa bisa kumatunsa.


A nan inda yake ya kwana, kashi da fitsari duk a nan ya yi su. Ba ya iya ko tashi zaune, bare kuma mikƙwa, har ya yi tsammanin guduwa ya bar wurin.


Da asubar fari ya farka. Mutane ya ji a kusa da shi, yana jin saukar numfashinsu.


"Kar ka ji tsoro, mu ba azzalumai ba ne."


Ya ji saukar maganar wani matashi a kunnuwansa.


Buɗe idanuwansa ya yi, ya tsura masa su, tare da taunar duka laɓɓansa.


"Mun zo wucewa ne muka hangi mota, to mu kuma dama ta mu ta tsaya babu mai, shi ne muka yanke shawarar matsowa nan, koda taimakon da za mu samu. To kuma sai muka ga gawar wancan bawan Allah, ga kuma kai a nan, cikin wani hali. Jin alamun kana numfashi ya sa muka yanke shawarar taimaka maka. Wallahi mu ba macuta ba ne."


"Ta ya zan yarda cewa ku ba macuta ba ne? Me zai shigar da ku cikin garin da ƴan ta'adda suka gama mamayewa, suka cinye shi baki ɗaya?"


"Ba shiga za mu yi ba, hangi motarmu ga ta can, fita za mu yi. Muna cikin garin sadda yamutsin ya fara, ɓoye a wani wuri, Allah kuma ya taimaka mana babu wanda ya kama mu. Jin tsit ya sa muka yanke hukuncin fitowa, komai ta fanjama fanjam! Ga shi dai kuma Allah ya taimaka mana mun fito ba mu haɗu da wani hargitsi ba, amma kuma man motar ya ƙare. Ka ba mu damar tamakonka bawan Allah."


Kai kawai ya jinjina musu alamar ya yarda.


Kama shi suka yi su uku suka kai motarsu. Sannan da dabara suka ringa tsotsar man taxi ɗin suna zubawa a tasu.


Ƙarfe tara na safe ta musu a cikin garin Maiduguri. Kai tsaye asibiti suka nufa da shi, take aka karɓe shi Emergency





Likitoci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login