Showing 96001 words to 99000 words out of 201092 words

Chapter 33 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt

ya koma Office ɗinsa.


A reception suka ga Mallam Ya'u zaune yana jiransu. Yana ganin su ya miƙe yana musu sannu. Shi ya karɓi Modu ya saƙalo hannuwansa a ƙarƙashin hannun Modu na dama, ya dafo hannun Modu ɗin ya dafa a kafaɗarsa, suka ci gaba da tafiya a hankali har suka isa bakin mota.


Bayan sun isa ya miƙawa Maryama makullin motar, ita ta buɗe sannan ta buɗewa Modu gidan gaba, Mallam Ya'u ya zaunar da shi, yana yi yana masa sannu.


Shisshiga suka yi cikin motar, Fiddou na tsaye tana ta faman kuka, Mallam Ya'u ya tayar da mota suka bar wurin. Har suka ɓacewa ganin Fiddou ba ta daina ɗaga musu hannu ba. Wani irin ƙunci take ji a tattare da ita, wanda ita kanta ba za ta iya misalta shi ba.


A nan inda take tsaye ba ta san sadda Mahmouda ya tsaya a gabanta ba. Duk ta yi nisa a duniyar tunani har ya shigo da motarsa ya faka, ya fito daga motar ya tsaya a gabanta.


"Fiddou lahiya dai ko?"


Ya ambata cikin wata irin murya, mai nuna zallar tashin hankali, saboda shi a tunaninshi ma ko Modu ne ya mutu, ko kuma ciwon nasa ne ya tsananta.


"Sun tahi da shi, ƴan uwa nai sun zo sun tahin min da Modu."


Ta duƙe a wurin tana kuka sosai, wanda duk wani mai zuciyar imani ya ji shi sai ya tausayawa mata.


"To ai ba kuka za ki yi ba Fiddou. Abu ne wanda yak kamata ki ɗaga hannunki ki godewa Allah, da ya kawo miki dangin Modu, har suka tahi da shi inda suke. A gani na ai hakan zai hiyewa Modu sauƙi, zai samu kula sosai daga wurin dangi nai, wata ƙila ma ya haɗu da wannan Amrah da yake yawan hwaɗin sunanta."


Kanta ta gyaɗa masa Fiddou, cikin sanyin murya ta faɗa masa cewa Amrar ma ba ta raye. Kawai dai sun yi soyayya ne sosai, wadda ita ce ma silar haukacewarsa.


Ajiyar zuciya ya sauke Mahmouda, ya ce,


"Ki daure to ki tashi da Allah de. Kukan naki ai babu abin da zai anhwana miki baya ga ya sakar miki wata cuta, wacce za ki rasa maganinta."


Cikin sanyin jiki ta miƙe a bisa ƙafafuwanta. Sosai take jin jiri na ɗibarta, tana neman zubewa ƙasa ba tare da ta shirya ba.


Komawa ta yi ta zauna a ƙasa, dafe da kanta da ke barazanar fashewa.


"Daure dai ki miƙe in kai ki gida Fiddou. Dole ki ƙoƙarta rangwantawa kanki damuwar nan, Modu dai ya tahi, duk wata damuwa taki ba za ta taɓa dawo da shi ba."


Ya sunkuya ƙasa ya taimaka mata, hannunta na dama ya riƙe ya miƙar da ita tsaye, bai sake ta ba har sai da suka isa gaban motarsa.


Ƙoƙari yake ya buɗe mata ƙofar ta shiga, amma ina, tuni ta sulale ƙasa, ta baje wurin a sume, idanuwanta rufe.


***


Satin da Annur ya cika kwana goma da haihuwa ne transfer ɗin mahaifinsa ta tabbata, inda aka miyar da shi cikin Katsina, Federal Medical Center ɗinsu. Sosai suka yi farin ciki, ko ba komai gida suka koma. Dama rabonsu da gida kusan shekara ɗaya kenan, ko zumunci ba su je ba, saboda rashin wadataccen lokaci. Yanzu kam godiya ya ma Allah, ya kuma yi fatan Allah sa can ɗin ya fi zama alkhairi a kan cikin garin Bama, saboda a wancan lokacin a Bama FMC ɗinsu take, can ne gari mafi girma, mai kwanciyar hankali a duk Borno State.


A falo suke zaune, Suhaila na shayar da Annur suka ji wayar Dady ta yi ƙara. Gaggauta ɗaukar kiran ya yi, hannunsa saƙale da na Momy, wanda ta tallabo Annur ɗin da shi.


Bayan sun gaisa da mai kiran nasa ya ce,


"Zan shigo asibitin ai gobe kafin mu wuce, ban ma karɓarwa Annur takardar haihuwarsa ba. Ga kuma bankwana da ba mu yi ba da sauran al'umma."


Ya ɗauki kusan mintuna bitu yana wayar kafin ya tsinke, ya miyar da wayar ya ajje, sannan ya dubi Suhaila cike da soyayya ya ce,


"Dr. Hamdana ne, young Dr. ɗin nan da nake faɗa miki, wanda bai wuce sa'an ƙanina na uku ba."


Bayan ta daidaita kwanciyar Annur da ya yi barci ta ce,


"Ai yanzu kam ya wuce ƙarami, tunda ya taka matsayin da manyansa ma ba su taka ba."


Tana murmushi cike da tsokana.


Hannunsa ya sa ya kamo haɓarta, ya mata hararar wasa ya ce,


"Babu komai dai, na ji. Ai ni ɗin ma zan zama babban Pharmacist."


"Insha Allahu kuwa. Ina ma mijina fatan hakan, ya zama abun alfahari ga kowa, ga iyalinsa da dukkanin al'umma ma."


Cikin tattausan lafazi ya ɗora idamuwansa bisa kyakkyawar fuskarta, ya ce,


"Ina son kalar addu'ar nan taki a kodayaushe. Sosai take ƙarfafa min guiwa, nake ƙara jin ƙaunar matata na daɗa hauhawa a cikin zuciyata."


Miƙewa ta yi ta ƙarisa bisa ƴar katifar Annur mai haɗe da gidan sauro, ta shimfiɗar da shi ciki sannan ta dawo ga mijinta, ta zauna ƙugu da ƙugu da shi.


"Ba zan taɓa gajiyawa da yi maka addu'a ba mijina. Shin menene amfanin matar da za ta gaza buɗar bakinta ta ma maigidanta addu'a? Bata da amfani a ganina. Ta zama sokuwa, wawuya, kuma ƙatotuwar mai sakaci."


A wannan karon kam sumbatar hannunta ya yi cike da bege, ya ce,


"Ina alfahari da ke, zan kuma ci gaba da yin alfahari da ke har ƙarshen rayuwata, insha Allahu."


Ya ɗaga kanshi ya dubi Nadrah da Saddiqa da ke tsaitsaye suna kallonsu, ba ma su san sun shigo falon ba.


Da hanzari Suhaila ta gaggauta matsawa daga jikin Dady da take, saboda nauyin yaransu da ya ɗarsu a cikin zuciyarta. Ta ce,


"Nadrah me ya sa bakwa sallama ne? In ce ko na sha gargaɗinku a kan ku daina shigowa wuri ba tare da kun yi sallama ba?"


"Momy mun yi sallama fa, har sau biyu ba ku ji ba."


Nadrah ta faɗa tana ɗan ja da baya, saboda ta san halin Momynsu, ba ta da wasa in dai wurin tarbiyya ne.


Rasa abun faɗe ta yi Suhaila, hakan ya sa ta ce,


"Ai da sai ku dakata daga bakin ƙofa har sai kun ji an amsa sannan ku shigo. Ina aiken da na muku?"


Da tsoro ta ce,


"Momy mun faɗa mata, ta ce wai to, goben kafin mu tafi za ta shigo ta kawo miki."


"Good."


Suhaila ta furta bayan ta murmusa kaɗan.


Washe gari da sassafe suka gama shiri, motar da za ta kwasar musu kaya ma har ta tafi, da yake tun da asubah aka fara lodi.


A ƙofar gida maƙofta ne da dama suka zo yi musu bankwana, har da masu kuka a cikinsu, saboda zaman arziƙi da aka yi.


FMC suka fara biyawa, Pharmacy suka tasanma, Pharm IA ya yi bankwana da mutanensa, cike da jin zai yi kewarsu sosai, suka tasanma Amenity, inda za su karɓarma Annur takardar haihuwarsa.


A mota ta bar su Nadrah da Dadynsu, ita kuma ta ƙarisa daga ciki, inda za a bata takardar.


Bayan ta karɓa daidai za ta fita ta ci karo da wannan matar shuwa mai suna Shereefah, tafe da wata yarinya ta goyo jinjirin, wanda da alama Nanny ɗinsa ce.


Da fara'a suka kalli juna, suka gaisa cike da aminci a fuskokinsu.


"Ɗan yaro kana goye? Miye ne sunansa?"


Shereefah Shuwa ta faɗa da murmushi.


Murmushin ta sakar mata ita ma Suhailah, ta ce,


"Sunansa Annur, bari na sauko miki shi."


"Barshi ya yi barcinsa dan Allah. Suna mai dadi, Allah Ya raya Annur."


"Ameen fa. Ya sunan na wajenki?"


Karar sunan nasa take kasantuwarsa haihuwar fari, duk da kuwa ba shi ɗin ne farko ba, a tunaninta wancan ɗin da ya rasu ne farko, amma tunda dai babu shi, dole wannan ɗin za ta yi kara, tunda shi ɗin ne matsayin babba yanzu. Hakan ya sa ta kalli Nanny ɗin, alamun ta ba Suhaila amsa.


"Sunansa Salman."


Yarinyar ta faɗa tana fara'a.


"Masha Allah! Allah Ya raya Salman. Ga shi ba su gaisa da abokinsa ba har za mu wuce."


"Za ku wuce ina? Ba dai garin za ku bari ba ko?"


Ta faɗa cike da zaro idanuwa tana mamaki.


Suhaila ta ce,


"Wallahi fa. Mu dama ƴan cirani ne, aiki ya kawo mu nan, ga shi kuma ya ɗauke mu, ya miyar da mu asalin garinmu."


"Allah sarki! Allah sa hakan ne mafi alkhairi a gare ku. Amma ko sunanki ban sani ba, ga shi bani da lambarki bare a cigaba da zumunci."


Introducing ɗin junansu suka yi, a ƙarshe suka yi musayar lambobin waya sannan suka rabu, ba tare da kowace ta ga yaron kowa ba.


Bayan ta samu su Dady a mota ne ya ce daga nan kuma ɓangaren psychiatric za su nufa, saboda ya ma Dr. Hamdana alƙawarin za su haɗu su yi bankwana, kafin su wuce.


Hakan ce kuwa ta kasance, ɓangaren da marassa hankali suke suka dosa, kai tsaye suka nufi Office ɗin Dr. Hamdana, wanda ke cike da kayan alatu, da na more rayuwa.


Nadrah da Saddiqa suka gaishe shi, sannan Suhaila ma ta gaishe shi da fara'a.


Dr. Hamdana mutumin kirki ne, ƙaramin yaro amma mai matuƙar girmama na gaba da shi. Shi ne the most youngest Dr. A duk asibitin, haka kuma shi ne mutum na uku da ake ji da shi a duk cikin likitocin mahaukata.


Ba su wani jima ba dady ya miƙe, yana miƙewa suhaila da yaranta ma suka miƙe, Dady na faɗin,


"Bari mu lallaɓa Dr. Ka san tafiyar ta mu ba ta kusa ba ce, dole sai an tafi da wuri. Na so ma a ce tun 7 mun bar nan, amma maƙota sukaita bamu shawara cewa kar mu yi fitar nan ta dugu dugu, ta cika hatsari da yawa. To motar kayanmu dai ta yi gaba, na ce da dreban yai haƙuri har gari ya waye ya nunar min da babu abin da zai faru da yardar Allah, ya tafi kawai."


Dr. Hamdana ya murmusa ya ce,


"Hakan ya fi ai. Allah ya kai ku lafiya ya tsare mana ku. Mr. IA please kar a yar da zumunci, a ci gaba da kula da juna, da yardar Allah ni ma ba zan taɓa mantawa da kai da ahalinka ba."


Musabaha suka yi cikin aminci, Dr. Hamdana ya buɗe wata loka ya zaro kuɗi masu yawa, ya miƙawa Saddiqa yana faɗin,


"'Yata ga wannan, a sha ruwa a hanya."


Ƙin karɓa ta yi har sai da ya kalli Suhaila cewa ko ita ce ta hana Saddiqa karɓar kyautar da ya mata? Da fara'a ta ce da Saddiqa ta karɓa, sannan ta karɓa ɗin da godiya a bisa laɓɓanta.


Har bakin mota ya raka su Dr. Hamdana, sannan ya ga sun tashi ya koma Ofishinsa.


***


sai bayan magrib sannan su Maryama suka isa Katsina. Sai da suka fara biyawa suka sauke Hadiza sannan suka wuce gidan su Jiddah, ita ɗin ma aka sauke ta. A lokacin Modu ya jima da yin barcinsa, bai ma san me ke faruwa ba.


Horn ɗin da Mallam Ya'u ya yi ne ya sa mai gadinsu ya gaggauta buɗe musu gate, suka shigo da motar a cikin gida.


Ƙarar motar ya sa Muhammad fitowa da gusunsa, fuskarsa ƙunshe da fara'a ya tarbe su.


Bayan Maryama ta fito daga motar ne ta amsa sannu da zuwan da Muhammad ke mata, ta ce,


"Ka je ka ce da su Mama mun iso, kuma har da mara lafiyan, wai ina za mu kai shi?"


"To."


Ya faɗa haɗe da barin wurin da gudunsa, ya isa cikin falon yana faɗin,


"Mama dama na faɗa miki su ne ba Abba ba. Haka Yaya Maryama ta ce wai sun zo tare da baƙo, ina za a nufa da shi?"


Miƙewa ta yi Mama, ta fara ajje takunta har ta isa harabar gidan, ta inda ake faka motoci biyu da suke da su.


"Barkanku da dawowa. sannu ya hanya?"


Ta faɗa tana kallon Mallam Ya'u da murmushi, sannan ta ce da Maryama,


"Ashe tare ɗin kuka zo."


"Ehh mama, mun tabbatar ɗin shi ne fa, bari mu shiga ciki zan miki bayanin komai insha Allah."


"To madalla."


Ta furta bayan ta zagaya ta inda Modu yake, tana kallonsa da gyaɗa kai, tausayinsa take sosai, yanayinsa da komai nashi abun tausayi ne. Kayan jikinsa babu kyawun gani, ga wani irin zaurin fitsari da yake yi, wanda sai mutum ya kai zuciyarsa nesa zai iya haɗiyar yawu. Sosai ta yaba da ƙoƙarin su Maryama, na yadda suka taho a haka tun daga Maraɗi har Katsina. Tamkar ta zubda masa ƙwalla haka ta ji. Lallai mai rai ba wata tsiya ba ce. Duk a yadda Allah ya yi ka kawai ka gode masa, haƙiƙa ka fi wani. Duk yadda kake ganin kai mai larurin ciwo ne, ɗaga hannu ka godewa Allah, saboda akwai wanda sun fi ka larurin, wasu ga cutar ga kuma talauci da ya musu katutu, wanda ko kuɗin da za su nemawa kansu magani ba su da.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke Mama, fuskarta ƙunshe da tausayin Modu, ta ce,


"Dole inda mutane suke za a ajje shi, gudun kar ya buƙaci wani abu ba a sani ba. In baccin haka ai da sai a kai shi part ɗin can na baya, idan an gyara. Ya yanayin nasa yake? Ina nufin yana duka ko kuma attempting guduwa?"


Sassauta muryarta ta yi Maryama, ta ce,


"Ba ya ko ɗaya gaskiya, haukan nasa fa ba wani mai ƙamari can can ba ne, surkulle ne a kan Amrah, yai ta subbatu cewa wurinta zai je, sai idan bai samu wata maganar kirki ba ne har ya yi ƙoƙarin guduwa, cewa shi zai je da kansa ya nemo ta."


Mama ta ce,


"Ah to in haka ne, bida irinsu ai ba abu ne mai wahala sosai ba. Kenan dai shi ɗin ne Annur da kuke zato?"


Ta ƙarisa maganar da firfito da idanuwanta, cike da mamaki.


"Uhm...shi ne fa Mama. Abin da na ce zan faɗa miki kenan ai idan mun shiga ciki. Ta subbatunsa kaɗai muka tabbatar da cewa shi ne real Annur, wancan ɗin na ƙarya ne."


"Subhanallahi! Lallai akwai damuwa, there's something behind, Allah kaɗai ya bar wa kanSa sani. Yanzu dai a tafi da shi ɗakin Muhammad, shi Muhammad ɗin sai ya kwana ɗakina. Kamar hakan zai yi ai."


"Tunanin da na yi ni ɗin ma kenan Mama. Allah Ya taimaka, Ya ba mu ladar taimakon baki ɗaya."


"Ameen Maryama. Mallam Ya'u ko za a kamo sa a shigar cikin gida?"


"To ranki ya daɗe."


Suka fara ƙoƙarin kama Modu, shi da Mai gadi.


Cikin gidan suka shiga su Maryama, cikin yanayin gajiya ta ce,


"Barin tafi sallah, ban yi ko magrib ba, ga isha na gabatowa."


"To ya yi, bara na kai masa abinci, in saka Mai gadi ya taimaka ya masa wanka, zan nemo masa kaya daga cikin na Abbanku."


"To Mama. Da kau ya ji daɗin jikin nasa, don da gani ya jima bai yi wanka ba. Kodayake Fiddou ta ce wai ta taɓa biyan wasu yara suka masa wanka sau ɗaya, wai yaran sukai ta masa dariya tun daga nan ba ta sake sakawa a masa wankan ba. Na tabbata zai ji sassauci a jikinsa yau. Gobe kuma sai mu saka a masa aski, gashin nan na fuskarsa duka a aske shi."


Tana gama faɗin haka ta doshi ɗakinta, domin sauke farali.


A lokacin da suka kai Modu ɗaki ya farka daga barcin, bin ɗakin yake da kallo sosai, yana tunanin a inda yake, saboda shi ya ma manta da inda za su je, ya manta cewa wai wurin Amrarsa za a kai shi.


Ganin irin kallon da yake bin ɗakin da shi ya sa Mallam Ya'u murmusawa ya ce,


"Kwantar da hankalinka, garin su Amrah ne nan, za ka ganta amma sai ka nutsu, ka yi duk abin da aka ce da kai ka yi."


Bai ce komai ba sai murmushi da ya saki, miyau ya fito masa dalala, duk bisa haɓarsa.


Murmushi ya yi Mallam Ya'u sannan ya fice daga ɗakin, shi kanshi yana mai tsananin jin tausayin Modu.


Yana fita sai ga mai gadi ya shigo da plate ɗin abinci da cokali a ciki, ya ƙarisa gaban Modu da murmushi, yana faɗin


"Na Amrah bada kanka a sare, ka je gida ka ce ya faɗi. In ba Amrah ba sai rijiya, ita kaɗai ce taka, haka kuma kai kaɗai ne nata..."


Kanshi ya ringa jinjinawa Modu, alamun yana jin daɗin kirarin da mutumin ke masa. Murmushin nan bai kau daga fuskarsa ba, sai lila kansa yake, yatsunshi biyu a cikin baki, ɗaya hannunsa kuma a bisa kansa.


"Abinci ne na kawo maka, idan ka ci sai na maka wanka, ka saka sababbin kaya na tarar Amrah sarauniyar mataye."


Bai musa ba ko kaɗan, haka ya ringa cin abincin nan kamar wanda ya tashi daga ciwon yunwa, rabi na shiga bakinsa, rabi na sauka a ƙasa, har abincin ya ƙare.


Mama da kanta ta shigo ta kawo masa kayan Abbah, masu matuƙar kyau, kuma sababbi ne sau biyu ya taɓa saka su.


Bayan ta miƙa su ga Maigadi ta fita, da kanshi ya cire masa kaya, ya ɗaura masa towel ɗin da Mama ta haɗo da shi a cikin kaya, ya ɗaura masa, sannan suka nufi banɗaki.


Sosai mutumin ya dirje shi, saɓi uku ya masa amma duk da haka ruwan kumfan jajur yake, tsabar datti da ya yi. A ƙarshe ya wanke masa kansa sannan ya ɗauraye shi suka fito.


Wani irin sakayau yake ji a jikinsa Modu, shi kanshi yanayin da yake cikinsa ba kaɗan ɗin daɗi yake ji ba. Banda murmushi babu abin da yake saki, haƙoransa sun ɗan yi haske, saboda dirzar da suka sha.


Mai ya shafa masa ko'ina na jikinsa, sannan ya feshe shi da body spray na explore, har kayansa sai da ya fesa ma turare, kafin ya saka masa su a jikinsa.


Take asalin sifarsa ta fito, ya koma real Annur Iqra Al-hussei; mutum mai matuƙar kyau na fuska da na sifa, mutum mai tsantsar ƙwarjini, wanda ba kowa ke iya haɗa fuska da shi ba, tsabar ƙwarjininsa. Mutumin da murmushinsa ke haskaka kyawun fuskarsa, murmushinsa ke daɗa ƙayatar da fuskarsa.


Shi kanshi mai gadi mamakinsa yake. Kyakkyawa da shi, ashe dai yanayi ne kawai ya miyar da shi a halin da yake ciki. Alwashi ya ɗauka a ranshi cewa shi da kanshi zai ci gaba da kula da Modu, zai bashi kulawa ɗari bisa ɗari har ranar da zai bar gidan, ko kuma ya samu lafiya.


"To ka ga yanzu sai ka kwanta ka yi barcinka ka huta, a cikin barcin za ka ga Amrarka ta iso gare ka, ta tabbatar maka da cewa tana cikin aminci, kai kawai take jira."


Bai ko jira ya gama jin maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login