Showing 54001 words to 57000 words out of 201092 words
Chapter 19 - AMRAH NAKE SO BOOK COMPLETE DOCUMENT .txt
kwashe komai ta faɗa wa Mama, sai dai ta ɓoye mata taimakon Annur da take son yi.
Zafafan hawaye ne suka ringa fita daga ƙwayar idon Mama. Tana jin yanda tausayin Amrah ke ratsa duk ilahirin zuciyarta. Take jin tsananin bugawa da zuciyarta ke yi. Wace irin yarinya ce wannan? Wace irin mace ce mai tattare da halayen kirki? Dama akwai irinta a wanann zamanin? Ashe akwai masu kyawawan hali irin Amrah?
"Wannan ita ce damuwata Mama. Dalilin da ya sa kika gan ni cikin damuwa ke nan. Na rasa yanda zan yi da tausayin Amrah. Rayuwarta da mutuwarta duka abin tausayi ne. Akwai manyan darussa a cikin labarin Amrah, wanda saurarensu kawai wani babban ilimi ne."
"Dole ne zaki shiga damuwa Maryama. Dole hankalinki ya tashi. Ina miki fatan kasancewa da irin halayen Amrah, ko da ba duka ba. Idan har kika kasance haka kuwa zan daɗa alfahari da ke, zan ninka gatan da nake gwada miki, zan ci gaba da tutiya da ke a duk inda zan shiga."
Rungumar Mamanta ta yi, cikin kuka ta ce,
"Ina alfahari da ke Mamana. Insha Allahu zan ci gaba da kwatanta halayen Amrah. Zan zamto abar alfahari a gare ki, kamar yanda Maman Amrah ke alfahari da Amrah, tun tana raye har bayan mutuwarta."
Murmushi Mama ta saki a fuskarta, tana jin yanda soyayyar ƴarta ke shiga a duk gaɓoɓinta, ƙaunarta take ji ta ko wane saƙo na zuciyarta.
Suna cikin haka Muhammad ya shigo, School bag ɗinsa ya jefar a ƙasa yana mai ƙirƙiro kuka ya ce,
"Mama yau ma..."
Bai ƙarisa ba Maryama ta dafe kanta haɗe da faɗin,
"Problem boy. Yau ma me?"
"Yaya Maryama ban fa yi masa komai ba ya daken."
Ya faɗa fuskarsa a daƙune, kamar ta ce zata masa wani abu ne.
"Kullum haka kake fa Muhammad. Ban san me ya sa ba sam ba ka ci sunan nan ba. Asalin mai sunan haƙurarren bawa ne, mai kyawawan halaye. Amma kai kam ko kwatantawa ma baka yi, na rasa dalili."
Zama ya yi a bakin gado bakinsa tunzure yana faɗin,
"Ai dama Yaya Maryama ban taɓa ji kin yabe ni ba, komai sai dai ki ce bani da gaskiya."
Dafa kafaɗarsa ta yi murmushi ƙunshe a fuskarta ta ce,
"Amma ai ka san bani da kamarka ko? To duk abin da zaka ga ina maka ƙauna ce ta ja haka. Ko so kake kawai ko yaushe na yita goyon bayanka, bayan kuma ba gaskiya ba ne?"
Janye hannunta ya yi daga kafaɗarsa ya ce,
"Ni dai ban yarda ba. Daga ke har Mama da Abba kuna nuna min banbanci. Ko kaɗan bakwa gwada min soyayyar da ta dace."
Zaro idanuwanta ta yi cike da mamakin kalaman fa suke fitowa daga bakin Muhammad,
"Wace irin magana ce kake haka, Muhammad? Kana da hankali kuwa?"
Tashi Mama ta yi ta gyaɗa kanta, ta kalli Maryama da faɗin,
"Ki fahimtar da shi Maryama. Na kula dai wani abu ne ya ɓata masa rai tun asali. Idan kun gama ki rako shi akwai kyautar da na ajje masa ta musamman."
Murmushi ta saki Maryama, ta ce,
"Mama zaki bar ni da rigimammen yaron nan ke nan. Iyaka na zazzane yaro idan zai min shegantaka."
A daidai fitar Mama ta ce,
"Kun fi kusa ai."
Ta ƙarisa ficewa daga ɗakin.
Juyowa ta yi ga Muhammad da fara'a ta ce,
"In banda abunka Muhammad, kai kaɗai ke nan namiji a gidan nan, ta ya kake tunanin ba zamu ƙaunace ka ba? Duk abin da ka ga muna maka fa muna son ka kasance na gari ne. Ko hausawa sun ce ka so naka duniya ta ƙi sa, ka ƙi naka kuma duniya ta so shi. Idan muka bayyana soyayyarmu a gare ka, baka tsammanin wani abu zai je ya dawo? Abin da mutanen yanzu suka kasa fahimta kenan. Yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke taɓarɓarar da tarbiyyar yaran zamani, wato nuna masu soyayya da gata, a kasa nusar da su abin da ya dace da su. Komai suka kawo kawai daidai ne. Muhammad so kake ka zama sangartaccen yaro?"
Sai a sannan ya fara saukowa, cikin sanyin murya ya ce,
"Amma Yaya Maryama ko yau fa mantawa aka yi da ni a makaranta, ba a je an ɗauko ni ba. Kuma na shigo gida, baku damu da sanin wa ya kawo ni gida ba. Duk ƙaunar ce wannan?"
Dafe kai ta yi Maryama, tana jin haushin kanta na mantawa da ɗauko Muhammad da suka yi. Sai yanzu ta tuna Abba ya kirata a waya ya sanar mata ba zai samu ɗauko Muhammad ɗin ba, kuma drebansa ya tafi ƙauyensu yau.
Cike da damuwa ta ce,
"Yi haƙuri Hammad ɗina, ko kaɗan kar ka ga laifin Abba da Mama. Laifin nawa ne, saboda Abba ya sanar min na biya na ɗauko ka idan na tashi, sai kuma na ji bana jin daɗi ban je lecture ɗin ba. Ka gafarta min ka ji ƙanina?"
Da dan murmushi shimfiɗe a saman fuskarsa ya ce,
"Babu komai, Yaya Maryama komai ya wuce."
"Yauwa ƙanina abin alfaharina. To ya aka yi ka dawo? Ka hawo mashin ne?"
Bayan ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin cire neck tie ɗin uniform ɗinsa ya ce,
"Maman Abdul ce ta ɗauko mu tare, ita ta kawo ni har gida."
Miƙewar ita ma ta yi Maryama, ta ce,
"Wacece kuma Maman Abdul? Ban taɓa jin sunan a bakinka ba."
"Wani yaro ne ɗan Nursery 2. Yana yawan zuwa wurin abokina Khalid ne, a nan na san shi har muka shaƙu. Muna mutunci sosai da yaron. To dama wani lokaci idan mamanshi ta zo ɗaukarsa kafin a zo ɗaukana ina zuwa in gaishe ta, har ta ce zata tafi da ni, ni kuma sai in faɗa mata za a zo a ɗauke ni. To yau kuma sai bata zo ɗaukarsa da wuri ba, ni ɗin ma kuma haka. Muna ta jira sai gata ta zo, ganin duk ɗalibai sun watse ya sa ta ce kawai na zo mu tafi ta sauke ni. Dalilin da ya sa bata je ɗaukarsa ba wai ta shiga yin surgery ne, da yake likita ce. Har ma ta ce min zata zo har gida ta gaishe da Mamana, saboda yanda nake kula da yaronta."
Jinjina kai Maryama ta yi, ta ce,
"Ka dai ringa kula sosai da irin wannan abubuwan. Yaushe ta ce zata zo?"
"Ni dai ta ce min wai zuwa anjima zasu zo, tun da dai ta ga gidan yanzu."
"To shi ke nan, Allah Ya kawo ta lafiya."
Daga nan ta fice daga ɗakin ta koma falo.
***
Zaune yake ya zabga uban tagumi, kwalaben syrup ne jere a gabansa, ga wata irin sigari babba, irin marar warin nan da turawa suka fi amfani da ita.
Damuwa ce shimfiɗe cikin zuciyarsa, wanda har fuskarsa ta gagara ɓoye hakan.
Bai ko tsaya yin diluting ba, kwalbar kawai ya ɗaga ya kai bakinsa, bai sauke ba har sai da ya shanye tas, ko ɗis bai rage ba.
Ajje kwalbar ya yi sannan ya kai sigarin a bakinsa, yana yi yana gyaɗa fuskarsa, cike da ƙunci da baƙin ciki.
"Kar dai maganar boka ce ke neman tabbata. True love ɗin da na faɗa ne ke neman kawo min cikas ko kuwa? Ta ya Dady da kansa zai hau ni da faɗa, saboda abin da ba yau aka fara yinsa ba? Yau na fara jawo hasara a kamfani? Akwai matsala!"
Ya sake fasa wata kwalbar syrup ɗin ya kaita bakinsa. Bayan ya shanye duka ya ajje, yana neman kai sigari a bakinsa ya ji wayarsa na ƙara.
Ɗauka ya yi ya kara a kunne, cikin muryarsa da ta fara canzawa ya ce,
"Hello babe!"
A ɗayan ɓangaren aka amsa da,
"Akwai damuwa my A. Babu kuɗi hannuna kuma ina da matsaloli da dama. Ya za a yi?"
Wata budurwa ce ta yi maganar, wacce yanayin maganarta kawai zai tabbatar wa mutum cewa ita ɗin ma irinsa ce.
"Babe ya kike so a yi?"
Ya furta yana lumshe idanuwansa.
"My A. ka turo min kawai, ko akwai matsala ne?"
Canza wa wayar muhalli ya yi, daga gefen hagu ya mayar gefen dama, ya matse ta da kafaɗarsa sannan ya ƙoƙarta da hannun da sigarin take ya buɗe wata kwalbar syrup ɗin.
"My A. Na ji ka yi shiru, da alama dai akwai damuwa."
"Babu damuwar komai. Ina up ne."
Dariya ta tulle da ita kafin ta ce,
"Har ma sai ka faɗa? Voice ɗinka kawai ya tabbatar min da hakan."
"Na sani ai. Ina zamu haɗu?"
Sai da ta ɗan yi shiru kaɗan, kafin ta ce,
"Dole sai mun haɗu zaka bani? Me zai hana ka min mobile transfer kawai?"
Cikin yanayin slow ya ce,
"Da wasa kike babe, kin san bana fitar da kuɗina a haka nan. Dole na fanshe a jikinki."
"Amma my A. Na ga ka hau up da yawa, ba zaka iya yin komai ba. Gashi kuma ni a matse nake da kuɗin, zamu je wani biki ne Maraɗi. Gobe da sassafe zamu tafi."
Cikin halin ko in kula ya ce,
"Zan miki transfer na 50k yanzu. Amma ki sani, zan fanshe ko ba yanzu ba."
"Babu komai."
Ta faɗa haɗe da tsinke wayar tana dariya.
Yana kashewa ya yi searching account number ɗinta, ya tura mata kuɗin. Shi kuma ya ci gaba da shan kayan mayensa, wanda suka mantar da shi duk damuwar da yake ciki, damuwar da dady'nsa ya saka shi.
Me zaku iya cewa masu karatu? Shin kun hango wani abu a cikin chapter'n nan kuwa? Idan kun hango, menene? Feel free and tell me your expectation. Ni dai na ce bana tunanin komai, what of you?
Na gode kwarai da addu'o'inku. Alhamdulillah! Na ji sauki sosai. Mura dai ce har yanzu voice dina ya gagara komawa daidai. Ku ci gaba da yi min addu'a, ina matukar jin dadin hakan.
Na kokarta yi maku 2k words duk da rashin jin dadin jikina. Don farin cikinku kawai masoyana.
Basman mai sanyinta ina yinki over, ina farin cikin kasancewarki a duniyata, ke din ta daban ce, ba zan gajiya da yi miki fatan alkhairi ba.
Aunty Maijidda Musa kina ina? Hakkun kina faranta min rai. Amrah na kaunarki irin totally din nan, fatan kin san da hakan.
RAZ NOVELLA 1&2 Ina kaunarku fi sabilillah! Kaunar taku a jinin jikina take, ina alfahari da ku, ina kuma yaba maku da comments a kan wannan littafin. Hakan na dad'a kara min kwarin guiwa sosai da sosai. Kun san ina kaunarku kuwa?
Sauran groups da nake ciki duk ina yinku. Ina matukar kaunarku, ina jin dadin kokarinku na yada wannan littafin har ya zagaya inda ban taba tsammani ba.
My dear Kdeey kaunarki a kahon zuciyana take, kin sani kuwa?
Kar dai na cika ku da surutu, sai mun hadu a next page idan Rabbissamawati wal'ard ya nuna mana.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
31
Buɗe idanuwansa ya yi ya sauke su a bisa fuskar Fiddou da ta tsura masa nata idanuwan tana kallonsa ko ƙaƙƙautawa babu.
Da ƙarfi ya fizge ƙarin ruwan da aka dasa masa yanzu, babu wata wata ya diro daga bisa gadon, yana kallon Fiddou da murmushi a saman ƙazamtacciyar fuskarsa mai cike da suma babu kyawun gani.
Murmushin yaƙe ta mayar masa, tana ƙoƙarin miƙewa tsaye da faɗin,
"Ina zaka tai ne Modu? Giɗe koma ka kwanta do Allah de."
Kai ya gyaɗa mata alamar ba zai koma ba yana ƙoƙarin ci gaba da tafiya da ɗangyasasshiyar ƙafarsa, ƙafar wandonsa ɗaya ta gama yayyagewa, tun daga ƙasa har kusan rabin wandon.
Saurin shan gabansa ta yi tana faɗin,
"Modu walle in dai kattai ba zan kai ka inda Amrah ba. Idan kuma baka so in kai ka ton ka tahi."
Duƙewa ya yi a daidai inda yake, ya saki kuka da sauti mai ƙarfi, wanda ya karaɗe asibitin, yana bada wani echo sound har inda babu mutane yana amsawa.
A rikice ta duƙa ita ma, ganin halin da yake ciki ba ƙaramin firgita ta ya yi ba, a tunaninta ko wani abun ne na daban ya same sa.
Mutane ne da dama suka tasan ma ɗakin, ganin mahaukaci a duƙe yana rizgar kuka ya razana su sosai. Suka ringa bin Modu da Fiddou da kallon mamaki.
"Modu da Allah dai ka hwaɗi min abin da akka damunka. Halan wani abu ke maka ciwo?"
"Ba ke ce kike min ƙarya ba? Kullum kina cewa zaki kai ni wurin masoyiyata Amrah amma kina ƙin kai ni. Ni idan baki kai ni ba zan guduwata ne daga asibitin nan, kuma ba zaki sake ganina ba."
Cikin tashin hankali Fiddou ta ce,
"Na shiga ukuna ni Fiddousi! Modu ina zaka tai ka barni? Ko son kake yi in shiga tashin hankali?"
Banza ya mata yana mai ci gaba da kukansa, sai dai yanzu ya rage sautin kukan nasa.
Ɗaya daga cikin mutanen da suka zagaye su ne wani ya tako har inda suke, da alama yana jinyar wani ne a wani ɗakin na daban. A hankali ya dire ƙafarsa a gaban su Modu, ya sunkuya a saitin fuskarsa, da murmushi ya ce,
"Haba abokina! Ya zaka ringa abu kaman ba jarumin maza ba?"
Ɗago kansa Modu ya yi, ya daƙune fuska yana kallon mutumen, a hankali da wata murya kamar mai hankali ya ce,
"Ni ba jarumi ba ne."
Dariya suka ɗauka su duka ɗakin, har Fiddou sai da maganar tasa ta so ta saka ta dariya, sai dai ta danne, sanin cewa Modu baya son dariya ko kaɗan.
Wani kukan ya sake fasawa, kamar ma ya fi wancan na farkon ƙara.
"Ni kuke wa kuka? Ki faɗa masu fa bana so ana min kuka, yanzu zan daki yara, to ni dai na faɗa maku."
Yana faɗin haka kuma ya miƙe tsaye yana murmushi, kamar ba shi ne ya gama hayagaga a ɗakin ba.
"Wai dan ƙarya suka ce Amrah ta mutu. Ni na san Amrah ba zata taɓa mutuwa ta barni ba. Rayuwarta don ni aka yi ta, ni kaɗai. Ban san inda take ba da na gano ta. Na san ita ɗin ma tana can tana jira na, in je mu yi aureee." Ya ƙarisa maganar da janta yana murmusawa sosai.
Yana gama faɗin haka ya fara dafe kansa, jiri na ɗibarsa, ya faɗi ƙasa luuu haɗe da sakin kan nasa.
Ba Fiddou kawai ba, har sauran mutanen wurin sai da hankalinsu ya tashi. Da sauri suka yo kansa, wasu na bubbuga shi a hankali ko zai tashi.
A rikice Fiddou ta nufi nurses station ta kira nurse ɗin da ta karɓi evening, a hanyar dawowarta ne ta haɗu da Mahmouda da wasu ƴan mata guda biyu zasu je ɗakin Modu, sai kuma wannan ɗan sandan guda ɗaya biye da su.
Cikin sakin fuska Mahmouda ya ce,
"Fiddou a gaishe ki."
"Iyi giɗe. Shine kat tahi ka ƙyale mu ko? Tun jiya nit ta tunanin dawowarka amma na ji ku shiru."
"Giɗe ke san na hwaɗa miki Mammata ta rasu, jana'izarta ce ma nittai. Dan shi ne ban samu na dawo jiyan ba. Bawan Allah'nga ma shaidana ne. Na so dawowa to kuma sai mutane sunkai ta zuwa wurin gaisuwa. Ga ƙannena nan guda biyu ma nit taho da su."
Da murmushi ta kalli daka dakan ƙannen nasa, wanda duk girman jikinta sun ce mata kau ban wuri.
"Giɗe mun same ku lahiya? Ya me jiki?"
Ɗaya daga cikin ƴan matan ta faɗa da fara'arta.
"Ina hwa lahiya ga giɗe can ya hwaɗi ƙasa, dan shi ne ma nik kirayi giɗen ceniya da ta shiga ɗaki yanzu."
Da damuwa Mahmouda ya ƙara takunsa har ya isa cikin ɗakin, fuskarsa na nuna zallar tashin hankalin da yake ciki.
Bin bayansa suka yi su duka, har ɗayan ɗan sandan da yake biye da su ƙiƙam, kamar suna masa jagoranci.
Ko da ya je har an cicciɓi Modu an dirar bisa gadonshi, Sister kuma ta koma ta kira likita ta dawo, dan a yanda mutanen wurin suka faɗa mata matsalarsa kamar abun ya fi ƙarfinta.
Dafa kan Modu ya yi Mahmouda, cikin tausayi ya ce,
"Yi haƙuri Modu, ni ne sila, ni ne najja maka wagga wahala da kake cikinta. Damuwar da nake cikinta tassa na kasa controlling temper ɗina, har sai da nik kaɗe ka ban sani ba. Do Allah de ka yahe man."
Ko motsi Modu bai yi ba bare Mahmouda ya sa ran zai farka, ko kuma yana jinsa. Suna cikin haka ne likita ya iso da nurse biye da shi. Hakan ya sa sauran nutanen da ke ciki duk suka watse, har su Fiddou ma a bakin ƙofa suka dakata.
Dudduba shi likita ya yi sosai kafin ya ce,
"Ina ga kamar akwai wata asalin damuwa ne a cikin zuciya tai. Ba wai bankar da mota tai yi mai ce kawai matsala tai ba. Kuma matsalad da ac cikin zuciyatai bata rasa nasaba da taɓin ƙwalwar da garai. Dole sai na ji daga bakin wani nashi ko ina sanin abin da ka hwaruwa da shi."
Cikin gamsuwa da girmamawa nurse ɗin ta ce,
"Bari in kira wacceni da suke tare."
Ta kama hanyar ƙofa, ta ci burki a inda su Fiddou suke, ta sanar mata cewa likita na son ganinta. Tare suka tafi wurin likitan, ita da nurse.
"Giɗe halan ya kuke da Modu?"
Muryar likitan ta daki kunnuwanta tun bata ƙarisa isa kusa da gadon ba.
Shiru ta ɗan yi na wani lokaci tana nazarin abin da zata faɗi. Jin babu amsa ya sa likitan ci gaba da maganarsa,
"Ke ga ga abun gwajin zuciya nan, da shi na auna nagga yanda zuciyatai bata tahiya daidai yanda aka son ta yi. Kuma wannan matsala ko kaɗan bata da alaƙa da wanga kaɗe shi da giɗe ya yi da mota. Sai na tabbatar da komai kafin in san matakin da zan ɗaukar mai, idan ma likitan zuciya ya kamata in haɗa ku da shi sai in hwaɗi mai."
A yanzun ma shiru ta yi dan bata san ta inda zata fara ba. Tsayuwar ta yi yawa ya sa likitan cewa,
"Giɗe biyo ni Office mu yi magana. Ba maganar a tsaya a yi nan ce ba. Ina son taimakon giɗe, wata ƙila idan na san komai har likitan ƙwalwa sai a haɗa ku. Amma hwa yanzu dole a tari matsalar zuciyag ga tun abu bai yi nisa ba."
Yana direwa ya fara takawa zuwa hanyar fita. Ita ma Fiddou binsa baya ta yi.
Har