Showing 27001 words to 30000 words out of 217237 words
sai ya farka bachi ma ba dadi”
Murmushi yai ya katsa kusa da ita yana mai jin son uwargidan har cikin ransa, ya kai hannunsa ya rumgumeta ta baya ya dora kansa saman wuyanta.
“That's right Teema”
Ta yi saurin juyowa ta kalleshi.
“Teema kace fa?”
“Eh ba sunanki ba ne?”
“Amman ai ba haka kake kirana ba sai dai ka ce min Baby ko Madam ko Mom Suhaima”
Dariya yai ya jiyarda ita ya sake rungumeta ta baya.
“To Baby yau yan tsokarna sun motsa ne shiyasa”
“Da wa kake waya?”
“Da Hajiya”
“Amman ka dade a waje fa”
Ya sauke hannayensa daga rikon da yai mata ya saka hannayensa aljihu.
“Ina ta tunanin mutuwa ne, mutuwa kawai ake a yanzu any how abun har tsoro yake ba ni, ina ta tunanin makomarmu ne”
Ya fada yana hade yawun bakinsa domin shi ma yasan karya yai. A take Teema ta bata fuska damuwa ta bayyana a fuskarta jin furuncin daya fito daga bakin mijinta, hakika mutuwa abun tunawa a ko wane dare ko dakika sai dai ba kowa ne ke tunawa da ita ba sai masu imani da tunanin ya goben su zata kasance.
“Allah dai ya saka mun cika da imani, nima abun na taba ni Wallahi”
Ta fada bayan ta sauke ajiyar zuciya. Hannunsa ya kai ya riko hannunta ya nufi hanyar dakinsa da ita.
“Ina Aiman? Suhaima tace sune kawai ba su yi bachi ba”
“Na saka su bachin dole ai, kun zauna gaban tv kamar a gurin za su tabbata”
Hannunta ya saki ya nufi dakin yaransa, a bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon Suhaima da Lubna sai kuma yayan Halimatu wato Namra da Aiman da Adnan, a ransa ya rika kwatatta yadda abun zai burge idan da ace shi Halimatu ta haifawa yaran nan gaba daya musamman Aiman da Adnan domin shi Allah be ba shi yaya maza ba, yan mata biyu matarsa ta haifa masa. Zuwa tai ta tsaya bayansa tana kallon yaran.
“Minene?”
“Ba komai”
Ya kai hannu ya janyo kofar dakin sannan ya nufi dakinsa Teema na biye da shi a baya.
HALIMATU POV.
Karfe takwas na safe kofar shiga dakin da Kabir yake tai min, domin na kwana da shi a raina da na farka kuma sai na ji bana bukatar ganin kowa sai shi hakan yasa ban wani tsaya karyawa ba na nufo asibitin daman can abinci be dame ni balle kuma yanzu da damuwa ta zame min ci da sha, kuma ta zame min abokiyar fira.
Ba ni kadai aka hana shiga ba, har da sauran masu ganin marasa lafiya da masu kawo abinci balle kuma ni da ban kawo komai ba. Muna tsaye a gurin har kusan tara da wani abu ba bar mu mum shiga ba sai dai an bar masu dauke da abinci sun shiga, ni kan sai na samu guri kusa da inda kofar take na zauna, na bawa kofar baya zaman jiran gawon shanu domin ban san lokacin da za a bada damar shigar ba, sai dai bana jin a yau zan wuni ban saka Kabir a ido ba ba dan komai ba sai dan damuwa da halin da yake ciki a yanzu wanda silata ne komai ya afko. Ji nai a dabani da wani hannu mai sanyi da alama mamallakin hannun ya taba ruwa mai sanyi ne ko kankara, ashe mamallakin hannu mace ce ba namiji ba ban fahimci hakan ba har sai da na juyo na kalleta na kuma tabbatar da macece ta hanyar sautin muryarta.
“Kamar Haima?”
Gabana ya fadi har na kasa amsa mata da eh ni din ce ko kuma a a ba ni ba ce, domin mutun biyu ne suke kirana da wannan sunan a duk fadin duniyar nan. Daga Abdulhamid sai Kabir, ba kuma zan ce a gurin Abdulhamid ta samu sunan ba, domin be taba kirana a gabab kowa da wannan lakanin ba, mutumen da be yarda na bayyana soyayyarsa ba taya zai fadawa wata ya taba kirana da wannan sunan a lokacin da na ke budurwa.
“Har na wuce ki na dawo saboda kin min kama da Haima, kuma wannan shirun da kikai ya tabbatar min da cewar ke ce Haima! matar da Kabir ya cika wayarsa da hotunanta kuma matar da aka ce ita yaje siyo ma abinci wannan hadarin ya same shi, wani abun mamaki kuma jiya da kika kira wayarsa sunanki yai appearing da Spacial Haima”
Wani dimmmm na ji kamar an dora min abu akao na kunya da nauyin kalamanta, hakika ni ma mace ce ba zan zo mijina ya kula wata mace ba kuma ba zan jidadi ba, sai a iya zamana da Kabir ban taba daukar hoto daga ni sai shi ba ko kuma ni kadai na tura masa to a ina ya samu hotona wata kila a media ko kuma a gurin wani wata kila kuma ya dauke ni ne a lokacin da nake aiki.
“Shin baki taba sanin Kabir yana aure da yaya ba?”
Ta jefo min tambayar da ban san ta ina zan tattara amsar da mika mata ba har ta gamsar da ita.
“Ya kamata ace na damu da lafiyar mijina a yanzu ko dan saboda yayan mu, amman saboda ke idan na tuno sai na ce masa Allah ya kara, ke ya kamata ace kin fi ni damuwa da shi, ko ba komai kin fini samun lokacinsa kin fi ni samun soyayarsa da kularwarsa, kin fini muhimmanci a gurinsa”
Tana fadar hakan ta fara takawa zata bar ni a gurin da dafin furucinta, cikin kuzari da hanzari na mika sautin muryarta dan isar da mata da abunda bata sani ba.
“Babu wata alaka tsakanina da mijin, abokin aikina ne kawai kuma ni ma matar aure ce har da yaya be kamata ki zarge ni ba”
Juyowa tai ta tsaya tana kallona kamar mai mamakin abunda ya fito daga bakina, a zatona zata yarda da kalamaina ne ko kuma ta dora su a ma'aunin tunani.
“Matar aure? Kina nufin irin auren nan da be hana mai yinsa aikata komai ko? Kina nufin irin ijiyar auren da wasu kan take su aikata alfasha da wasu mazan ko?”
Wani irin abu na ji ya taso min ina iya jure komai a cikin har da kazafin sata ko maita amman ba zan juri a kira mi karuwaba, domin na san illa da kazantar zina ban aikata ba dan haka ba zan yarda wasu su bata min suna ba.
“Ke malama ban san ki ba bana da wata alaka da ke, ko ki iya halsheki ba zan jure irin wadannan kalaman daga bakin kowa ba...!”
“Baki san ni ba ba ki da alaka da ni amman kina da ita da mijina ko? Banza marar sanin ciwon wawuya wacce igiyar aure bata hana ta aikata komai ba....”
Cikin daga muryar take fada min haka, ban san lokacin da na karasa kusa da ita na wanke mata fuska da mari ba, abunda ya janyo hankalin wasu mutanen izuwa gare mu kenan daman tun da ta fara maganar aka fara tsayawa yana kallon mu...
___________
Tofaaaaaaaaa.
Al-hamdulillah yanzu kan Al-hamdulillah na gama komai hankali ya dawo gurin typing.....✍️
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
1️⃣1️⃣
“Ko yar iska ce ni na fi karfin iskanci da Kabir, mutumen da ke daukar the same salary da na ke dauka, mi ya samu mi ya bani na fi karfin abunda kike tunani na fi karfin aikata alfasha da aurena da yayana”
Na fada mata cikin zafin nama bayan na wanke mata fuska da mari, wata matar da ce da ban wayance wacece ita ba ta zo da sauri ta rike matar Kabir din tana kiranta da sunanta.
“Haba Maryam wannan abun da kike ba mutunci ba ne, ai ko da gaske mijinki yana aikata alfahari be kamata ki tsare mace a hanya kina mata wannan maganar ba, ballanta baki da tabbaci akan hakan kamata yai ki fara damuwa da damuwar mijinki a yanzu Kabir yana a halin tausayin a yanzu abunda likito suke fada jinin ya kai har cikin kansa zai rayu ba zai rayu ba haukacewa zai yi ko ya manta komai duk be dame ki ba sai wani abun da ba zaki iya canjawa ba! Haba Maryam”
“Wallahi Anty karuwarsa ce kuma saboda ita wannan hadrin ya same shi, yanzu kuma dan rashin kunya har ta sako kafarta ta zo ganinsa? Haba Anty da wanne zan ji da ciwonsa ko da ganinta”
Ta fada cikin kuka ni kan tuni jikina yai sanyi jin abunda ya same Kabir jinin ya taba kwakwalwarsa, abun ya tsorani sosai kuma ya jefani a cikin wata duniyar tunanin da fargabar yadda gobensa zata kasance. Takawa na fara yi ina tafiya na nufo gate din fita daga asibitin gaba daya ba tare da na sake cewa komai ba, kallo daya za ka min ka fahimci akwai damuwa a tare da kamar yadda tunani ya kawo min ziyara a yanzu. Kar dai ace saboda ya rabe ni hakan ya same shi? Kaddararta ta fara wuce iya ni kawai har ta fara taba yayana da mutanen da suke kusa da ni? Tambayar da na yi ma kaina kenan tambayar da ban san wanda zai amsa min ita ba. Guri na samu kusa da gate din na zauna a saman wani guntun dakali idona cike da kwalla, ban samu kaina a cikin tausayin wani mutum wanda ba jinina kamar yadda tausayin Kabir ya dirar min a zuciya yai min kawaya a ruhi, ya nemi jijiyoyin jinina da jiki ya rike.
“Halimatu”
Muryar Abdallah ce ta hankalto ni har na dago kaina na kalleshi hawaye na min zuba.
“Zama kikai a guri kamar wannan har kina kuka a public? Mutane fa suna ta kallonki”
Cikin wani irin sanyin muryar da natsuwa yai min maganar da sautin da ni kadai zan iya ji da kuma fahimtar kalmomin da yake furta min. Sauke kaina nai daga kallonsa zuwa kallon titi ina ta yawo da ido.
“Abdallah ina tunanin Gobena ne, ya zata kasance? Miyasa abubuwan nan za su faru ta dalilina? Na farko yata? Na biyu kuma abokin aikina? Abunda ya faru da Namra kamar jiya ne, ban sammaci wani abun da zai taba zuciyata kamar haka zai sake faruwa ba, idan wani abun nai nauyi ya sake faruwa da ni ina jin kamar ba zan iya jure ba”
Risinowa yai gabana yana kallon fuskata.
“Share hawayenki zo muje a mota ki min bayani maybe zan sama miki mafita”
Sai na sake dago kai na kalleshi a karo na biyu, a yau Abdallah yai magana ta hankali da nuna kulawarsa a kaina, ko da yake a can baya ma ai yana nunawa sai dai wacan karon ina ganin rashin dacewar hakan saboda akwai igiyar aure a kaina, kuma a baya duk wata magana da zai min ta Aminu ce da abunda ya shafe shi.
“Abdallah zan iya rikon ka kamar dan'uwan? Abokin shawara? Wanda zan labartawa damuwata ya nema min mafita? Dan Allah?”
Sai ya kasa ce min komai, ba dan komai ba dan sai dan ya san inda manufata ta dosa, daga lokacin da zai rike ni a matsayin yar'uwa to babu zancen soyayya ko aure a tsakaninmu, ni kuwa abunda na fi so kenan, domin ban tana yi ma Abdallah kallon so ko kauna ba balle har ta ga kai ga aure! Mikewa yai tsaye ya nufi inda motarsa take, sai a lokacin na lura da inda ya faka ta, tashi nai na bi bayansa ba tare da na share hawayena ba. Na bude front seat ma shiga shi kuma ya tashi motar ya koma da ni cikin asibitin, a daya daga cikin guraren da aka tanada domin likitoci su faka motocinsu ya faka motarsa sannan ya juyo ya kalleni.
“Idan har hakan zai faranta miki rai Halima zan yi, amman ki sani zan cutu domin ba abunda nake so kenan ba, sai dai zan jira har lokacin da zaki fahimci da gaske na ke, fada min minene damuwarki?”
“Abokin aikina yayi hadari saboda ni, kuma yanzu na ji cewar akwai yiyuwar jimin ya tana kansa wata kila ya haukace ko ya manta komai ko ya mutu”
Na fada kai tsaye ina share hawayena. Sosai ya nuna min damuwarsa.
“Subhanallahi miya same shi haka?”
A take na labarta masa komai har zuwa fadan da mukai da matarsa. Na yi zaton ko zai tausaya masa ne sai na ga murmushi a fuskarsa.
“Kin kasa yarda cewar kina da kyau da kan iya jan hankali wasu mazan izuwa gareki saboda Aminu yana yawan fada miki cewar baki da kyau ko? Kina da kyau Halima seriously kina da jikin da ko wane namiji zai so ki kasance a tare da shi, ina tunanin abunda ya ja hankali abokin aikinki kenan har ya kai ga mallakar hotunanki da sakawa sunanki spacial saboda ke din ta musamman ce”
Na yi kasa da kaina ina tuna lokacin da Aminu yake fada min cewar kibar jikina ta masa yawa shi yar siririyar mace yake so wacce ke kamar zata kare, mace da zai nuna mata soyayya ta nuna masa yai zaman jindadi da ita ba zaman tara masa yaya ba.
“Bana son ki saboda kawai wadannan abubuwan da na lissafa miki, no ina fada miki hakan ne saboda ki yarda cewar ke din kyakkyawa ce kuma Allah be rage ki da komai ba”
Maganar da yai ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na fara zuwa, hakan yasa nai kokarin kawarta maganar.
“Taya zan fahimtar da matarsa cewar ni ba karuwarsa ba ce”
Sai da ya danna horn din motarsa kamar wani ne a gaban mu alhalin babu komai a gabanmu sai fulawoyi.
“Ki sakawa ranki sallama for now Halimatu, ki cire zancen cewar saboda ke wannan abun ya samu abokin aikinki, kuma ki manta da zancen fahimtar da matarsa, ki daga musu kafa na wani lokacin idan ya samu lafiya kamin lokacin sai ki je ki ganshi kuma ki fada masa ya fahimtar matarsa sannan kuma ki gargade shi daya cire kansa akan duk wani abun daya shafe ki, Halima kin san abunda nake so da ke?”
Na girgiza masa kai alamar ban sani ba.
“So na ke ki manta da komai da kowa a gabanki ki maida hankalinki gurin aikinki kuma ki kula da yaranki sai kuma zancen Namra shi ma ki jajirce wajen ganin kin kwato mata hakkinta barin wannan maganar zai bawa kanen mahaifinta damar yi ma wata yar ne”
“Amman Mama tace na bar maganar saboda kar na jawa Namra abun kunya idan ta girma”
“Halima ya kamata ki gane wani abu, ke fa uwa ce idan ba ki yi abunda zai kwantar miki da hankali akan yayanki ba to be kamata ki bar damuwa a ranki ba, duk wanda zai nuna miki yadda za ki kula da yaranki a bayanki yake, duk wanda zai damu da abunda ya damu danki ko yarki a bayanki yake, ke fa mutunce ya kamata ki san da wannan, ki yi wani abun da zai zame miki kwanciyar hankali kuma ya zamo abun koyi a gurin wasu matan, bari kashi a ciki baya maganin yunwa hankalinki ba zai taba kwanciya ba har sai kin hukunta wannan mutumen right?”
Na gyada masa kai gaskiya ya fada, ni kaina ina son yin hakan sai dai yadda Mama ta nuna bata so yasa na fara cire rai daga yin abun.
“Zan tsaya miki Halimatu, zan goya miki baya zan miki duk wani abu da kike bukata kuma zan baki kariya i promise you this”
“Zan tattauna da Mama har sai na ji ta bakinta yardar Allah na tare da yardar iyaye, bana son na yi wani abun da zai zamewa mahaifiyata ciwo”
“Yes hakan na kyau, sai dai wani lokacin iyayena suna nuna mana abunda suke gani a kamar zai cutar da mu alhalin ba cutarwa ba ne Allah ya taimake mu”
“Amin ya Rabb na gode Abdallah”
Na fada ina dubansa sai shi ma ya dubuni ido cikin ido wani tsan na ji na rashin jindadi for the first time yau na ji nauyi da kunyar Abdallah ya dira saman kaina.
“Ya jikinki?”
Ya tambaya still idonsa a kaina.
“Al-hamdulillah”
“Ina fatar kin ji sauki sosai”
“Na ji sauki”
“Mashallah. mama tace min kin tafi tafi aiki ashe ganin wani kika zo”
“Na fada mata da ga ganin Kabir zan wuce gurin aiki ne maybe ta dauka na wuce ne, ka biyo da gida ne?”
“Yes na zo na duba jikinki ne kuma ina son nai maganar karatun su Adnan da ke as her mother”
Kallonsa nai ba tare na ce komai ba sai ya cigaba da maganar still idonsa na kaina.
“Ina son canja musu makaranta ne zuwa wacce su Suhaima suke yi idan kin ba ni dama amman kuma kin aminta”
“Aa Abdallah na gode da kulawa ka dawo da su gida, ni zan duba musu wata makarantar dabam”
Ina kokarin kai hannu na bude ganbun motar na fita sai ya danna lock motar ta rufe hakan yasa na juyo ya kalleshi shi ma ni yake kallo da kyau.
“Na fadi wani abun ne daya bata miki rai? Ko na yi wani abun ne marar dadi?”
“Ba ko daya, yayana ne babu ruwanka da su”
“Amman yanzu kika gama fadar cewar zan zama miki dam'uwa? To miye laifi dan na saka su Namra a scul”
“Bana so, yarana ne dan Allah ka kyale su, zan iya kula da abuna zan iya musu komai”
“Ba zan cutar da su Halima kamar ba ki san ni ba”
“Ka kyale ni dan Allah Abdallah bana bukata”
Na fada ina hade hannayena tare da fashewa da kuka.
“Miye abun kuka daga wannan maganar?”
Ya karasa yana unlock din motar, ni kaina ban ga wani abun kuka a cikin lamarin ba, sai dai ina jin a yanzu kamar bana da wata garkuwar shiyasa kukan ya fi kusa da ni. Bude motar nai na fita ina share hawayena.
Na isa gurin aikina cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, yanayin da ba zan iya fadarsa ba, hakika inacikin damuwa bayan ta yarana da tawa yanzu kuma ta Kabir ta hau kaina. Wunin ranar ban iya tabuka komai ba saboda yawan kallon mazaunin Kabir da neka sai na rika ganin kamar yana nan ko kamar zai shigo irin yadda ya saba. Sai dai idan na tuna cewar yana can kwance asibiti sai na ji babu dadi. Ko dan saboda sabo idan abokin aikinka baya kusa da