Showing 138001 words to 141000 words out of 217237 words

Chapter 47 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

189

suna fadin abunda muka samo a school din, kuma su fadi gaskiya cewar kudin yana cikin account ba a hannu ba.
Bayan sun tafi nima na shirya cikin riga da zane na atamfa na saka hijabina, sannan na shiga dakin Mama na fada mata cewar zan tafi kamfanin na nemi alfamar canjin tufafi ko gurin aiki kamar yadda blessed ta bani shawara, daman tun da dare na labartawa Mama abunda ya faru da kuma matar da ke nema, har ta farara min kuiwa yin haka daman tana da complain cewar na daina aiki ba tare da na yi magana ba ban san ko za su aminta su canja min aikin ba.
A yau ban fita ba komai ba a hannuna da sunan kawai Kabir ba duk kuwa da kasancewar zuciyata na raya min na rika masa wani abu kamar yadda na saba, domin tun a lokacin da na daina zuwa aiki na daina kai masa abincin, haka ma take away da nake sakawa a kaiwa Abdallah na daina kasacewar hanya daya ce da gurin aikina a ko yaushe ina bada kudi na ce a kai masa idan 1pm ta yi ko 12,30pm.
Napep din da na tara akwai mutane biyu a ciki ni ce ta uku, a dole sai da ak saukesu inda za su je sannan aka kai no kamfanin wannan karon har bakin gate din kamfanin aka sauke ni, tsabanin da da ake sauke ni kusa da Kabir sai na bashi abincin sannan na wuce, babu irin dubawan da ban yi ba amman ban ga Kabir ba hakan kuma ba karamin haifar min da tsoro da zullumi yai ba, ina ta rokon Allah yasa ba mugun can yai masa wani abun ba.
As usual sai da na gaisa da masu gadin sannan na shiga ciki, kai tsaye reception na nufa fuskarta dauke da murmushi da sauri blessed ta zo ta rumgume ni.

“Oyoyo we miss you”

Ta fada sai kace wani dade muka yi muna aikin tare, ko da yake komai gamon jini ne. A nan fira ta kaure tsakanin na da su suna ta tambayar dalilin rashin zuwana aiki na fada musu sannan suka rika taya ni murna wai blessed ta basu labarin na ci gasa, a lokacin ne nake tambayarsu macen da take zuwa nema sai Rilwal ya ce

“Ai zata zo kullum sai ta zo nemanki a nan”

Na bukaci number wayar da suka ce ta bari tace a kirata idan na zo, sai Rilwal ya nuna min ita a wayarsa, na yi ta karanta number ban gane mai ita ba, sai kawai na zuba numbobin a wayata, ga mamaki sai sunan Suwaiba ya fito, miyasa take nema anan? Ba tasan gidan mu? Kuma tana number wayata idan har son ganina take? Wata matsalar ce? Ko wani abu ya faru da Abdallah? Haka zuciyata tai ra raya min abubuwa kamin na basu amsar cewar na gane mi number, nan suke fada min cewar babu wanda ya shigo a cikinsu daga sarkin girman kan har Yunus din da Tahir, hakan yasa na nemi guri na zauna dan na jirasu, ni kaina na san na yi sammako sai dai na zo da wuri ne saboda gudun na na zo suna tsaka da aiki a hana ni ganinsu tun da komai an kamfanin a tsare yake.
Ban yi minti goma da zama ba naji ana nuna domin sam ban lura da mutane da suke shigowa ba hankalina yana ka ce wayata, ina dago kaina nai yi arba da Suwaiba ta nufo inda nake rai a bace tana tafiya kamar ta fadi abun ka da siririyar mace.

“Kashedi na zo nai miki, ki fita hanyar mijina”

Ta fada cike da masifa tana daga murya iya karfinta, hakan yasa hankalin kowa ya dawo kaina.

“Ki fita hanyar mijina, yafi karfinki”

“Ba ki isa da mijin na ki ba ne shiyasa har kika zo baina jama'a kike min ihu, da ni nake auren Abdallah Wallahi idan na hana shi kallon wata macen ya hanu.... ”

“Ina zan isa da shi kin masa magani kin malleke shi bakar bazawara.... Yar duniya mai bibiyar mazan mutane, aure biyu kika kashe kina bibiyar mijina, marar mutunci kin zubar da yara hudu kin bar ubansu kina bibiyar nawa mijin, dan kawai ba ki san darajarsu ba...... Wani irin karuwanci ne da zaki rika aika masa abinci kullum..... Mijinki ne ko danki?”

Kalmar bazawara bata taba min zafi ba irin yau, ashe akwai ciwo idan aka maka gorin zawarci, a take na ji muzanci ya kamani tace na kashe aure ina bibiyar mijinta ko da karya ta fada wasu zasu gasgatata, na ci mutunci na a bainar jama'a ta gama da ni. Duk yadda na so na ki yin kuka sai na kasa hawaye suka fara min zuba bakina ya kulle gam na rasa me zan ce mata jikina sai rawa yake ina jin kamar na dake ta.

“Securities arrest her...”

Kamar saukar aradu haka muryar Ahmad ta dira a kunnena, da juyo idonw da hawaye na kalleshi yana tafe cikin kamfanin tare da Yunus, a lokacin da Security kamfanin suka nufo inda muke tsaye na yi zaton ni za su rike, sai na ga su kama Suwaiba macen cikinsu ta fisgeta da karfi.

“Ku rufe min ita a kamfanin nan sai ga uban waye mijin naki da za ki zo cikin kamfanin mu kina mana hankali how dare you”

Ya sake fada, a rikice na kalleshi ina hawaye. Sai ya karaso cikin kamfanin yana kallon amsu kallon fadan mu fuska a hade.

“Ku kuma me kuka tsaya yi kuna kallo ana insulting dinta instead of ku yi wani abu kowa ya saki ido fools”

Yana fadar hakan sai kowa yai saurin kama gabansa, shi kuma ya wuce ta gabana ba tare da ya kalleni ba ya bi hanyar da zata sada shi da office dinsa.
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2

*GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


4️⃣4️⃣

Rasa nai abunda zan yi, na bishi nai masa magana ko kuma na zauna ko na tafi gida? Ya Abdallah zai ji idan aka ce wani ya tsare masa mata saboda kuma a kamfaninmu, no ba saboda ni ba ne saboda ta yi hayaniya ne dan haka babu ruwana a ciki.
   Akai akai mutane suke ta kallona, har na soma tsarguwa, tashi nai koma can wani gefe da ba a ganina sosai na zauna, wata zuciyar na fada min cewar naje nai maganar aikina sai dai kuma idan na yi maganar aikin aka koreni ba tare da an gama maganar Suwaiba fa?
  Na kusan awa daya a gurin ina ta tunanin abun ne naje nai masa maganar Suwaiba ko ta aikina, amman ina ruwana da matar da ta ci min mutunci a bainar jama'a, ai kara a kira Abdallah din domin na san ba da saninsa ta zo nan ba.
Ban raba daya biyu ba, aka aiko wata mai sanye da suit kirana, haka ta saka ni a gaba ina baya har muka isa office din Ahmad. A one of visitors chair na tarar da Abdallah zaune, ni kuma sai na tsaya daga bayansa tun da ba a bani izinin zama ba, juyowa Abdallah yai ya kalleni sai kuma ya kawardar fuskarsa ba tare da yace komai ba.

“Look man aiki bake fa zaka tsayar da ni anan for more than 20 minutes, ba kallo office dinka na zo yi ba”

Abdallah ya fada a fusace, hakan yana nuna alamar Abdallah ya dade da zuwa kenan. Da hannu Ahmad yai min alama dana zauna ba tare da ya kalleni ba. Ba musu na zauna a kujerar da ke kusa da Abdallah ina ta kallonsa shi kuma sai yai kamar be san da ni a gurin. After like 5 minutes Ahmad ya kalleshi yace.

“Aiki nake yi ko baka gani ba? So kake na aje aikin na kula ka? Kai da ka zo ganina ba appointment? And you got lucky na barka ka shigo har office dina ka zauna tare da ni, ban barka visitors room ba?”

“Ba kai na zo gani ba, Matata na zo na ji dalilin riketa da kuka a nan”

“Bata fada maka abunda tai ba? Ko a hanya kawai za mu ga mace a hanya mu dauko ta?”

Babu wasa a fuskar Ahmad a yayinda yake wannan maganar, kamar yadda Abdallah ma nake ganin abun ya masa zafi.

“Matarka ta zo nan tana mana ihu na rashin tarbiya tana fada akanka, tana fada da ma'aikaciyarmu ba za mu dauki wannan ba”

“Kai kuma ka rufe ta, saboda gaka hukuma”

Ahmad ya kwanta jikin kujerar yana masawa Abdallah cikin zafin rai.

“Yes ko akwai abunda za ka yi? Kana ta son nuna isa, bayan you are nothing wanda be isa da iyalinsa ba har ya isa yace zai fito waje yai yi takama? It's a shame”

“Family issues ne wannan babu ruwanka a ciki”

Abdallah ya fada yana kokarin danne fushinsa.

“Family in my company? Public place?....”

Ganin abun kamar zai zame musu fada yasa nai hanzarin cewa.

“Na yafe ni tai wa cin mutunci na yafe mata, dan Allah ka barta ta tafi”

Ina fadar hakan Abdallah ya daga min yatsansa alamar babu ruwana a ciki, Ahmad kuma ya tari numfashina

“To ni ban yafe ba...”

Ya fada kai tsaye yana kallona. A lokacin ne Abdallah ya mike tsaye cikin bacin rai ya daka masa tsawa.

“And who are you? Mi kake takama da shi”

Wani shegen kallo Ahmad yai ma Abdallah, mamaki ya kama shi wato a maimakon ya bada hakuri ya karbi laifin matarsa amman sai neman kareta yake, hakan ya kara tabbatar masa da cewar Halima bata da gata domin da tana fa shi da yau ba shi zai yi fadan nan ba wani wanda ya tsaya mata ne zai yi shi.

“Kudi Alhaji......... ko baka gani ba, na isa ne isar ta isa ma matuka, kawai dan kun ga mace bata da gata sai ku yi ta taka ta any how, idan yar wani mai kudi ce ko kuma tana da wanda ya tsaya mata shashanshar matarka bata isa ta taka kofar gidansu ta fada mata bakar maganar magana ba balle har ta shigo gurin aikinta tana kiranta da suna kala kala tana cin mutuncin, so warn your wife for the last time, bilahil'azee idan ta one bad word daga bakin matarka zuwa ga Halima sai a rufeta a cell ba acikin kamfanin nan ba”

Abdallah yayi murmushi yana duba agogon hannunsa, sannan ya kalleni ya sake kallonsa.

“Ba kai ne mutumen da yace idan yarsa ta mutu zaka rufe Halima ba? Ba kai ne mutunen da baka yarda da kaddara ba? Ba kai ka mareta har sai da ta suma ba? Kai duk abunda kai mata ai saboda kana ganin bata da gata ne, yanzu har kana da bakin da zaka fadi haka? Mi ka sani a akan Halima? Baka san komai ba akan rayuwarta fadi tashin da tai ba ka sani ba, sai a yanzu? Tsohon dan iska shiyasa ka bata wando da riga ta saka so that ka rika kallon siraicinta? So kake ka burgeta a yanzu? Shiyasa zaka fara acting kamar wani mutumen arziki... ”

Su suke fadan ni nake kuka, Ahmad be sake cewa komai ba, ya danna dan wani maballi da ke gefen teburinsa, ba a dauki lokaci ba sai ga security kamfanin sun shigo.

“Ku fitar min da shi bana son hayaniya.... ”

Da sauri suka nufi gurin da Abdallah yake saye sai kuma suka saka rika shi sai kokarin masa magana suke.

“Karku taba shi zai fita da kanshi.... Abdallah dan Allah”

Ya fada ina masa magiya, kallo yai ya dauke kai ya juya ya fice daga office din rai a bace, sai security din suka bishi a baya. Karasa matsawa nai kusa da teburin na hade hannayena ina kuka.

“Ka saka a saki matarsa dan Allah, na san ka tsaneni, duk abunda zaka yi Saboda ka musguna min ne ko kuma wani na kusa da ni, idan har ya zama dole sai ka dauki mataki akan abun dan Allah ka hukunta ni ba matarsa, saboda ni komai ya faru...”

Ba tare da ya kalleni ba ya nuna min wata kujera dake can kusa da kofa.

“Je can ki zauna”

Abun ka da mai jiran umarni sai na nufi kujerar na zauna ina kuka a hankali domin har ga Allah ban jidadin da ran Abdallah ya bace ba, kuma ban jidadin abunda Ahmad yai masa ba.

“Idan kin gama kuka ga tissue box kusa da ke ki goge fuskarki, akwai ruwa a fridge”

Yana fadar hakan ya dauki laptop din da yake aiki da ita ya fice ya bar ni a katon office din, ni ko ban fasa aikin kuka ba har sai da nai wanda ya ishe ni na dauki tissue na goge hancina da idona sannan na bude fridge din na dauko gorar ruwa na sha, domin makoshina ya gama bushewa. Bayan na sha ruwa na koma a inda na tashi na zauna. Kalamansa na dazun ne wuka rika dawo min a rai kamar yadda na Abdallah ma suka tsaya min, na rasa ganewa Ahmad ya fara saukowa daga fushin da yake da ni ne? Da har zai ce idan Suwaiba ta sake fada min bakar magana sai ya rufe? Ya bar ni na shigo har office dinsa ya fada min idan na gama kuka na goge fuskata na sha ruwa... Ina tsaka da tunanin sai gashi ya shigo tare da Yunus yana ta murza wani karamin turare a hannunsa, kallona kawai Yunus din yai be ce komai ba ya cigaba da maganar da yake da Ahmad bayan ya gama ya fice wata matar ta shigo da kofin tea guda biyu ta aje a saman teburinsa sannan ta fice.
Daukar dayan kofin yai ya nufo inda nake zaune ya miko min, mamaki ne ya hana ni karbar cup din har sai da ya kalleni. Sai nai saurin girgiza masa kai na mike tsaye.

“A a na gode”

Kallo yai for few seconds sannan ya furta.

“I'm sorry....”

Ya juya yana kurba tea ya nufi teburinsa.

“Be kamata ka bani hakuri ba, duk abunda ya faru laifina ne, ni na ja komai sanadina komai ya faru kuma kamfaninka ne kana damar ka yi duk irin hukuncin da kake so....”

“Akan dora miki laifin kisan Baby Namra da na yi”

Ta tari numfashina, wannan karon mutuwar tsaye nai, da gaske hakuri yake ba ni? Ahmad din ne ko wani dai dabam, na dan juya na kalli bayana na sake kallona.

“Ki yi hakuri dan Allah”

Ya maimaita min da yaren da na fi ji. Har lokacin kallonsa na ke gaba daya kaina ya gama kwancewa, mi ke faruwa ne? haka na tsura masa ido ina ta masa kallon da ban san na minene ba, mamaki kadai ko kuma har da tuannin maganar Abdallah? Da gaske hakuri yake bani ko kuma wani abun yake shirya min saboda na kashe masa ya? Kamar yadda yake zargina?

“I say sorry”

Na hade yawun bakina.

“Ba komai ba, wannan ma yana cikin kaddarata ne”

Ina fadar hakan na juya zan fice daga office din.

“Ina za ki je?”

“Gida”

Na fada ba tare da na juyo ba, idona na cika da hawaye.

“Aikin fa?”

“Na aje”

“Saboda me?”

“Tufafin da nake sakawa be dace da ni ba”

Na amsa cikin muryar kuka, har yanzu na kasa yadda Ahmad ya bani hakuri akan yarsa, har zuciyarsa yake bani hakurin? Miyasa? Taya yanzu ya yarda ba ni na kasheta ba? A take wasikar da na rubuta a jiya ta fado min a rai, ya fahimci ni ce kenan, kuma zuciyarsa ta bude har ya iya yarda a yanzu ban aikata ba, Al-hamdulillah akalla wani abun ya ragu daga bakincikin da yake raina, a yanzu yana kallona a matsayin marar laifi tun da har ya iya ba ni hakurin. Shigowar Yunus ne yasa nai saurin share hawayena sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka nake ba.

“Lafiya?”

Ya tambaya yana kallo da mamaki a fuskarsa. Ban saurari abunda Ahmad ya fadawa Yunus din ba domin har lokacin kokarin tsayarda kukan farincikina nake.

“Biyo ni muje”

Yunus din ta fada ni kuma na juya ina rokon Ahmad amman ko kallona be yi ba.

“Dan Allah ka saki matar can dan Allah”

Ganin Yunus din ya fice yasa nima na bi bayansa, yana gaba ina bayansa har muka isa wani guri, hannunsa ya kai ya tura kofar sai ya bude ya shiga ni kuma na tsaya a waje har sai da ya yi min izinin shiga.
Dan madaidaicin office ne mai dauke da desktops har biyu a teburi daya, sai dan karamin fridge da ac makale a dakin daga gefen ac window ne mai kofa biyu wanda yake bawa mutum damar hango windows din office din Ahmad kamar yadda shi ma zai iya hango na cikin office din idan an bude.

“Kin iya typing ai ko?”

Na gyada kai.

“Yauwa to duk emails din da za a turowa kamfanin nan anan zai shigo wanda kika ga ya dace oga ya gani sai ki masa forward kai tsaye zuwa email dinsa, idan kuma za a aika wani abu to all ma'aikatan mu ke za a bawa ki yi typing sai ki tura, sai dai daga yanzu lokacin tashi aikinki ya canja daga 3 zuwa 5pm, amman ba kamar wacan ba ne nan ana bada abinci saboda zaman da kike”

“Ban gane ba....”

Na fada a hankali cikin sanyayyiyar murya.

“Yanzu nan ne office dinki congratulations”

“Da gaske?”

“Ga zahiri kina gani”

A take idanuwa suka kara cika da kwalla.

“Na gode”

“Oga ya kamata ki yiwa godiya”

“Dan Allah ina rokon alfarma”

“Na san kai ma oganka ne, amman kuna da kyakkyawar fahimta wata kila za ka iya yi masa magana ya ji, dan Allah ka saka ba ki ya saki matar da ya saka a ka kulle”

“Ya sake ta ai, tun dazun mijinta ya tafi da ita”

“Da gaske? Amman cewa yai ba zai barta ta tafi ba”

“Gaskiya tun dazun aka wuce da ita”

Dan murmushi nai na juya ina kallon office din. Shi kuma ya juya fice ya bar a gurin tsaye n rasa abunda zan yi murna ko kuka ko mamaki?
Kasa komai nai a cikin office din sai kawai nai zaune ina ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login