Showing 123001 words to 126000 words out of 217237 words

Chapter 42 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

225

nai kamar ace akwai wani makami a kusa da ni na daba masa a kirji ya mutu a gurin, saboda zafin da maganarsa tai min, taya mutun zai keta min haddi da aurena kuma yana kafiri ina yar musulma sannan yanzu ya dawo yana min maganar aure har da haifar masa yara, saboda kawai ni Halimatu ai komai nawa dabam ne.... Ji nai an haska fuskata hakan yasa na bude ido ashe wayarsa ce ya haska min a fuska ganin ina hawaye yasa shi ce min.

“I'm sorry ban zo nan dan na saka ki kuka ba, zan tafi see you at Children's Day”

Yana fadar hakan ya koma cikin motarsa yai mata key ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye.

“Ba zan je ba, saboda kai ka siyo min ticket din”

Na furta a fili ina ayyanawa a raina cewar ba zanje din ba....



_____________

Wai ashe Abraham yana da team 🤐
Who can guess what will happen next? 🤗

Ni dai ina Team Aminu 😝😝😝
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


4️⃣0️⃣

Hakan nan yau yake sha'awar zuwa gurin aiki da wuri, daman kuma ya tashi ya ji jikinsa sai a hankali so yana bukatar yai aiki da wuri ya dawo gida if possible. And he like to wear a suit today like always sai dai wani lokacin yana saka shadda dan yafi jinsa more comfortable fiye da suit.
  Bayan ya gama shiryawa ya shigo bangaren Hajiyarsa still ya same ta tana aikin hada masa breakfast sai dai yau ba ita kadai ba har da Siyama. As he already knows siyama bata tashi da wuri sai idan makaranta zata je, amman ga a kitchen tare da Hajiyarsa da mai aikinsu har ma da cousin dinsa Khadija wacce kwararriyar banker baker ce. 

“Yau me kuka hadawa haka ne?”

Da sauri dukansu suka juya suka kalleshi domin ba su san da zuwansa ba sai ganinsa da kai a kofar kitchen yana ta kamshin turare.

“Amman Bro you wake early”

Cewar Siyama tana nufo inda yake. Agogon hannunsa ya duba wanda ya nuna masa bakwai da yan mintuna.

“Yeah ina son naje aiki da wuri ne”

“Oh bro i wanted to surprise you.....”

Ta fada tana bata fuska, sai Khadija ta tari numfashinta tana murmushi.

“We can still surprised him dear... ”

Ya kalli Khadija da fuskar rashin fahimta. Sai ta jango masa kujerar kitchen din ta aje bayansa.

“Dan zauna”

Be zauna ba be kuma nuna alamar zai zauna din ba balle har ya furta wani abu. Siyama know him well, he is no nonsense at all, hakan yasa ta hade hannayenta.

“Pls”

Sai da ya kalli Hajiyarsa wace ita ma tai masa alama da ya zauna din sannan ya zauna yana binsu da kallo. Da gudu Khadija da Siyama suka fita daga kitchen din, like 6 minutes suka dawo sai Hajiya ya fita.

“Close your eyes pls”

Be musa ba tunda Siyama ce tai masa maganar, a take ya rufe idon sai ta kama hannunsa yana masa jagora a hankali har suka fita daga kitchen din, gaban dinning area ta nufa shi sannan ta saki hannunsa.

“Now open your eyes....”

A hankali ya bude idon, by surprise yai arba da katon birthday cake mai hotonsa.

“Wow”

Ya furta yana kallon mahaifiyarsa da ke Murmushi kamin ya rumgumi Siyama wacce ke ce masa happy birthday.

“Thank you Blood, Thank you Mom, thanks Sis”

Ya fadawa Siyama Hajiya and Khadija wacce tai masa respond da murmushi.

“So duk kun san yau birthday na kenan, ni na manta sam”

“Taya za ayi na manta ranar da na maifi Ahmad Gwarzo...”

Cewar Hajiya tana murmushi, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya debi cake din ya kaiwa Hajiya a baki.

“I love you Hajiya ta”

One after the other ya bisu ya saka musu cake din a baki har Khadija, sannan suma suka ba shi, daga bisani Siyama ta ciko hannunta da cake din zata shafa masa sai yai saurin rike mata hannu ya murda har sai da ta kai kasa tana ihu.

“Wayyo Hajiya....”

“Gwarzo karka kare min ya”

“Hajiya ba zan bari ta bata min tufafi ba today is special day for me...”

Sai duk suka saka dariya har ita Siyamar sannan ya sake ta ya dauki tissue ya goge hannunsa.

“Yau din nan ko? I very very special day for us, i call your friend on phone and i told him ya saka kowa yai surprise dinka da wani abu each and every person a kamfaninka, so karkaje ka dinga musu fada ni na saka su”

“Kina da hankali Siyama?”

“No sam sam Hankali wala gare ni a yau, la la la and in the laila akwai celebration... ”

Ta fada tana rawa.

“Hajiya yau yarki bata da hankali”

Ya fada sound so serious domin gani yake yau Siyana hauka take ji how zata kira company su tace kowa yai surprising dinsa, and now tana gaya mishi akwai celebration, shi rabon da yai celebration din birthday sa tun matarsa Halima na da rai.

“Tana da hankali she's just celebrating her brother birthday”

Khadija ta fada tana murmushi Siyama tace.

“Louder pls”

“No ina ganinki da hankali Khadija karki biye wannan”

Daga haka ya juya ya fice yana murmushi, sai kuma ya juyo yana kallon Hajiyarsa.

“A saka min cake dina a fridge pls”

“Okay Breakfast fa”

“Zanje office din na san kamin na dawo kun hada sai na ci, akwai wanda nake son meeting da shi a 8”

“Okay Allah ya tsare”

Sai da ya amsa da min sannan ya fice daga falon ya nufa haravar gidan gurin da ake aje motoci. He choose ya black kalar suit dinsa sannan ya shiga.
   Sai ya kusa isa kamfanin sannan ya rage gudun da yake, like always dan kawai ya gani idan ma din ma Halimatu zata bawa mahaukacin nan da be san alakarsu ba abinci, to his surprise yau be ganta ba sai dai mahaukacin na nan a zaune, haka nan kawai ya faka motarsa gefen titi yana ta kallon mahaukacin he just wanted to see idan zata ba shi abinci yau, ko ma bata ba shi ba shi miye nasa a ciki? Yaja tsaki a maimakon yaja motarsa yai gaba sai ya dauko wayarsa ya shiga whatsapp yana duba status din Siyama wacce ta sika status din da hotonsa tana masa kalamaina na kauna irin na yar'uwa da dan'uwanta, sai da ya dora hotonsa a status dinsa ya rubuta happy birthday to me sannan ya shiga duba na sauran yan'uwansa da abokansa, daga lokacin ne n banks dinsa suka shigo sai kuma fb da sukai masa happy birthday.
Ya fi karfin minti talatin a gurin sannan yai ma motarsa key ya karasa office din, hakan nan yaji baya son fita daga motar ma and he don't know why sai kawai ya ciro wayarsa amininsa kuma abokin aikinsa.

“Happy birthday Boss”

“Thank you, Salim ya ganar Inuwa? Kana ganin zai samu zuwa yau kuwa”

“Yes ai ba zai tsaba alkawari ba amman na san yau rana ce mai muhimmanci a gareka, zan masa jagoran komai kai sai ka huta”

“Thank you zan fito amman sai anjima”

“Okay”

Daga haka ya aje wayar yai reverse ya koma hanyar gida, still sai ya sake tsayawa yana kallon mahaukacin na tsawon five minutes sannan ya cigaba da tukinsa.

HALIMATU POV.

Bayan tafiyar Abraham wani tunanin ya fado min a rai, a iya tunani be kamata na kyale shi a haka nan yana ta bibiyar rayuwata ba, ya kamata na kai shi gurin yan sanda su mana tsakani ko ba komai zan samu salama kuma zan fada musu cewar dan fashi ne ko zai kashe ni sai dai ya kashe ni.
Ban sanarwa kowa ba sai dai na kudirci abun a zuciyata, a daren ban yi bachi ba sai pass 12, ina ta tunanin irin matakin da ya dace na dauk domin na san nan gaba kadan iyayena za su bukaci saninsa to sai na ce musu me?
  Da wuri na shiryawa yarana sannan na karya bayan su ma sun karya suka kama hanyar makarantar wacce ta kasance nesa da unguwarmu kadan, yau ban basu kudin tara ba saboda ina son dafa musu indomie tare da Kabir, da kaina na nufi shagon unguwarmu na siyo indomin sai ya rage naira goma ce kawai canji dan haka na bukaci ya bani chewing gum da ita idan ma na karbar na san rigima kawai zata zama tsakamin Namra da Aiman da Amal kara Adnan yana dan daga kafa wani lokacin baya biyesu.
  Sai da na dafa indomie na zuba musu a cularsu sannan na dauko leda na kwashe ragowar indomin na zuba ciki, a gaggauwace na nufi bandaki nai wanka na shirya sai dai hakan be hana ni shafa janbaki da hoda ba har da kwalli kamar yadda na saba,  riga da zane na atamfa na dauko na saka sannan na saka hijab dina ya saka wayata da a jaka na fito ina yi ma su Mama da Inna sallama.
Sai da na karanta addu'ar fita daga gida sannan na fita, ina karasa titi nai sa'a da mai adaidaita babu kowa a ciki bayan na tare na fada masa ya kai ni police station da ke can unguwar kwaza, wata zuciyar na fada min kar ka kai maganar gurin yan sanda saboda gudun abunda zata zame min, amman kuma idan ban kai ba me zan yi? Haka zan zuba masa ido yana ta bibiyata? Bayan na fada min ko na yafe masa idan ban aureshi ba ba zai daina bibiyata ba. Nesa da station din aka sauke ni domin masu napep ko abu hawa basa karasa har gaban gurin, bayan na bashi kudin na shiga ciki, gabana sai faduwa yake kamar marar gaskiya, abunka da wacce bata saba zuwa gurin yan sanda ba. Kai tsaye na shiga ciki har da yar sallama ta suka amsa min wanda na ganin da yar fuska far'a na nufa na fada masa abunda ya kawo ni a gurin, ba shi kadai ba ko su sauran da suke sauraren labarin nawa sai da sukai mamaki.

“Amman kuma ba ki san shi ba?”

“Ban san shi ba ba ni da alaka da shi, kawai dai yace yana so na ni kuma na nuna masa bana sonsa hakan kuma be saka shi ya daina bibiyata ba, and jiya ma sai ga kudi an aikowa mahaifina ina zaton shi ya bada yace a bashi amman shi mahaifin nawa be sani ba, kuma ni ina tsoro kar abun yai nisa ya zame min fitina”

“Kin ce kin taba ganinsa da bindiga?”

“Eh a motarsa ba, ina tunanin dan bashi ne”

“Ko dan kidnapped ba, wannan babban case ne gaskiya, ina ganin abunda ya kamata a fadawa PRo sai ta shiga tai masa bayani”

“No kai ta gurin oga direct zai fi, idan ya hannatawa Pro shikenan, mu sai mu rubuta statement”

Atsakaninsu su uku suke wannan shawarar, kamin dayan ya shiga ciki be dade b ya fito ya ce akwai case din da yake idan ya gama sai na shiga, haka na samu guri a gurin na zauna ina ta kallon wasu mutane da ke shigarda kara da wadanda ake saurarensu suna kare kansu.
Bayan kamar minti talati ya sake lekawa ya fito yace min na shiga, shi yai min jagora ciki har da bude min kofar na shiga sannan ya janyota ya rufe, mutumen da na tarar yana zaune a irin kujerar nan ta office mai lilo, ya bani baya wanda hakan ya bani damar daga kaina saman ina kallon office din, kamin ya kare wayar ya juyo ya kalleni arba nai da abunda ban tana tunani ba abunda ban taba tsammani ba, a take jakar hannuna ta subuce ta fadi, nai baya da sauri kirjina na mugun bugawa kamar zai fito.

“Ya akai?”

Ya tambaya ni fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Ni ban gane ba, tagwaye ne ku, kama ce, ko kuma kai din ne dai?”

Murmushi yai.

“Ni din ne dai, wa kika kawo kara? Ni ko wani?”

“Daman kai dan sanda ne kuma kake fashi da makami?....”

“Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii”

Ya furta tare da saurin mikewa tsaye ya nufo inda nake, kan ya karaso har na kai hannu na bude kofar na fita da sauri jikina sai rawa yake, ina fitowa na nufi gurin kular abincin yarana zan dauka sai dayan yace.

“Kin masa bayani”

“No waya yake, yace naje na dawo, bari na kaiwa yarana abincinsu a makaranta na dawo”

“Okay ba matsala”

Daga haka na samu na fita daga station din, mamaki ya saka ni mike hanya ina ta tafiya ba tare da na tari abun hawa ba, sam hankalina be bani a gafen titi nake ba har sai da nake tsallakawa ba tare da na saurari horn din da motocin ke min ba. Ban ankara ba na ji abu ya buge bugu bana wasa ba, har sai da nai bayabaya na fadi kan kwalbatin da ke gefen titi.

“Ba ki da hankali ana miki horn amman sai kokari tsallaka titi kike kurma ce ke?”

Iyakar kokarin da nai na fita daga kwalbatin ne kamin na dago na kalli mai motar wanda ya rufe da fada babu ko tausayi. Muna hada ido yaja wani bugun tsaki ya koma cikin motarsa da ke bude ko inda nake be sake kallo ba.

“Wawa kai ne mahaukaci tun da baka iya tsayawa ka duba mutane ba, ko tokin be iya ba sai jin kai kamar wani Governor, ko titi na gidanku ne....!”

Be sake ce min uffan ba har yaja motarsa ya bar gurin.
Wani mai acahaba ne ya tsaya yana tambayar idan ban ji ciwo ba.

“Ban jimu ba faduwar kawai nai”

Na fada domin bana jin ciwo komai a jikina.

“Dan Allah ki rika kula idan za ki tsallaka titi irin wadannan ba imani garesu ba”

“Na gode”

Na fada idona na cika da kwalla, lallai a yau na tabbatar Ahmad gwarzo be da imani kuma be da mutunci, taya zaka buge mutum ka wuce ba tare da ka duba lafiyarsa ba, ko da yake ni mai laifi da nai kokarin tsallaka titi ba tare da na duba ba, amman duk da hakan da ace mutum ne mai imani da zai tsaya ya duba idan be jimi ciwo ba, wata kila saboda yaga ni ce yasa yai min haka ko kuwa daman can halinsa haka yake?
Ban bar gurin ba sai da na tari mai napep na fada masa makarantar da zai kaini ta su Namra, wacce ya kamata ace can na fara zuwa kamin na je station din amman saboda gudun kar nai latti yasa na fara zuwa can zuwa da be amfani da komai ba.
Tsayar da mai napep din nai na nufi shagon da ke kusa da makaranta na siye musu pure water shiga har cikin makarantar na kai musu abincinsu tare da ruwan sannan na fito, na sake karbar wani ruwan na Kabir na fadawa Mai napep din inda zai kaini.
Daidai kusa da Kabir ya aje ni na biyashi kudinshi sannan na fita na nufi gurin Kabir din na ciro indomie da ke jakata na bashi sai da na tabbatar ya saka hannunsa ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha, ni kuma na mike na fara takawa da kafar da sai a yanzu nake jin tana min wani irin mugun ciwo, kaina sai sarawa yake ina dan jin jiri kadan-kadan. Cike da karfin hali na karasa kamfanin, ba laifi na gaisa da masu gadin gurin kamar yadda muka saba sannan na karasa cikin kamfanin ina tsinginta saboda zafin da kafar take min idan na taka. Duk wanda ke magana da ni idan ya gan ni sai ya tambaya me ya samu kafar sai na ce fadawa nai kwalbati. Haka na nufi bangaren mu na tura kofar na shiga sai na samu Yunus yana musu wani bayani da ban fahimci me yake nufi ba, har sai da ya gama musu sannan ya juyo yana min bayani.

“Yau dai kin zo late, daman ina musu bayani ne akan yau birthday shugabanku, so yana da kanwa Siyama ta kira ni ta ce tana bukatar kowa da kowa yai masa kyau komai kankantarta, na san ba abu mai yiyuwa ba, domin yawa ma'aikatan kamfanin bata sunansu ba ne shiyasa tace haka, so ni kuma na zabi ku da kuke sabbin dauka ku yi masa haka”

Bance komai ba har yai gama fadar abunda zai fada, ina jin a rain kamar ba zan iya ba, taya zan bawa wanda baya kaunar ganina kyauta, amman kuma ai be san wanda ya shi ba, sai dai ni kuma hankali ba zai kaunata ba matukar nai masa kyautar, ho me ma zan bashi me nake da shi da zan bashi.

“Kamar me za mu bada...?”

Abokin aikina ya tambaya.

“Komai kake da shi zaka iya ba shi, ko biro ne idan kuma akwai mai kudi a cikinku sai ku siyo wani abu a nan waje ku bashi, mu na dai son kamin ya shigo mu yi masa kyautar”

Dukanmu muka amsa da to ni dai ba dan raina ya so ba, wasu suka rika fita suna siyo masa abun da ya samu ban da ni da na rasa abunda zan bashi kuma bana jin zan saka kudi na siya masa komai. Kusan duk a tare muna doshi office din nasa, wanda ban taba zuwa ba sai yau, tun daga muka doshi inda office dinsa yake sai na zama bakauya yadda kaban taba ganin kamfanin ba haka na zama, wata kalar wallpaper ce aka kawata gurin da ita mai wani irin daukar ido da kyau, ga wani uban sanyi ac mai ratsa jiki, sai da muk shiga office biyu ko wane da ma'aikaci a ciki sannan muka isa office dinsa, wanda kanshin air freshener mai dadi ya fara yi mana marhabun, ya kawata office din da hotunansa wani gurin yana tare da mahaifiyarsa wani gurin da Baby Namra sai kuma wanda sukai wani a gurin meeting wani da turawa, tebur biyu ke cikin katon office din daya a yana fuskantar kofar shigowa wanda shine babba, sai kuma karami dayake gefe mai dauke da desktop computer har guda biyu bayan laptop din dake saman babban tebur din, sai kuma wata doguwar durowa mai cike da littafan da kuma numbobin karammawa. A kasa gaban teburin aka umarce mu da aje duk abunda muka kawo masa kusan mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login