Showing 39001 words to 42000 words out of 217237 words
ni a idonsa. Wani lokacin har mamakin yadda Abdallah yake min wasu abubuwan na ke domin an tabbatar da ace shi ne a matsayin Abdulhamid da ya so ni tun ina budurwa da Allah kadai ya san irin chabar da za ayi.
Na fi jin natsuwa da Abdulhamid fiye da Abdallah, wata kila saboda zuciyata ta taba son sa ne, ko kuwa dan ina tausayinsa ne oho, ga shi ya dage sai kai kawo yake, domin idan be zo yau ba, to zai zo gobe tun ina fargabar kar wata rana Abdallah ya tarar da shi har na daina, ko da yake Abdallah ma tun daga wacan ranar da ya min koho wayata ta fashe be sake dawowa gidan ba, kuma be sake gwada kiran sabuwar wayar da Abdulhamid ya siya min ba, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin ya bani damar sakewa da kula Abdulhamid a duk lokacin da yai min sallama.
Ta wani bangaren kuma ina yabon Abdallah sama da Abdulhamid, domin shi mutum ne mai son yara ko na ce mutum ne mai son yayana tsabanin Abdulhamid da ko fuska baya sake musu daman can kowa ya sani Abdulhamid ba a mutum ne mai son yara ba, sai dai ban dauka har da nawa ba ganin kamar ni din ta dabam ce a gurinsa. Yes yana nuna min so da kulawa irin wadanda na rasa a gidan Aminu, shi tun a yanzu ya fara nuna min su sai dai a duk lokacin da muke waya be taba cewa ya yarana ko ya gaishesu balle kuma har ya riko musu wani abun taba. Ba kamar Abdallah ba da har saman jikinsa suke hawa su karbi wayarsa su yi game, rashin sakewa da yarana yana daya daga cikin abunda yake daga min hankalin bayan maganar daina aikina da yai min idan har na amince zan aurenshi. Ya nuna min cewar shi yana da kishin da ba zai iya barina nai aiki ba, kuma yana da halin da zai iya dauke min komai, daga lokacin da yai maganar daina aikina zuwa yau na kasa yanke hukunci kuma na kasa zaba na kasa shawara da kowa, ba dan komai ba sai dan na san duk wanda zai shawarce ni zai ce na daina aikin na yi zaman aure. Na san dole ne Abdulhamid ya ji tsoron naje nai aiki saboda kar na hadu da wani namijin ya burge shi bayan shi baya iya komai, wai da gasken ne baya iya komai din ko kuwa dai gwadani yake ya ga idan zan iya zama da shi? Ko kuma karfin soyayyar da nake masa? Ni dai na san ba dan soyayya kawai zan aure shi ba har da tausayin halin da ya samu kansa wanda na so yin wannan jihadin tun a baya.
Yana yawa fada min sai na ji na ki ji, saboda za ayi ta kananna maganganun akan mu, ganin ni bazarawa ce har da yaya hudu shi kuma saurayi, ko da yake ba irin yaran samarin nan ba ne irin tazuran nan ne da suka dade ba su yi aure ba, amman duk da hakan na san sai yi magana, ban kawo zancen rashin lafiyarsa ba saboda na san ba kowa da ya san da matsalar ba.
*** *** ***
Yau dai na yanke shawara ba zan je aiki ba sai na sake gwada nemawa yarana wata makarantar ko Allah zai saka a dace idan kohin Abdallah ya janye daga jikinsu ko kuma jikina zance tun da ni ce mahaifiyarsu kuma ni ce sila.
A Napep na saka su muka kama hanyar Gwarzo International School, babbar makaranta ce da babu irinta a garin Gusau makaranta ce da ta amsa sunan makaranta kamar yadda na ke jin ana fada babu kamar dalibansu, sai dai makaranta ce mai tsada sosai ba kowa ke iya saka yaransa a makaranta ba saboda kudin da ake kashewa.
Ni kaina na san ba lallai na iya jurar biya musu kudin ba, zan dai gwada ne kawai idan an karbe su sun fara karatun sai na canja musu ni dai burina kohin da Abdallah yai mana ya karye kawai. A lokacin da mai napep din ya faka bakin gate din makarantar na ji wani iri ganin irin manyan motocin da ke kawo yaran makarantar. Sai dai ban yi kasa a guiwa na biya mai Napep din kudinsa na kama hannun yarana muka nufi cikin makarantar, wani abun da zai kara burgeka da makarantar yadda aka tsaurara tsaro domin sai da aka gama bincikamu sannan aka bar mu muka wuce a nan na soma ganin malaman makarantar har da turawa.
Da tambaya na isa office din principal din dake can hawa na biyu, office ne da aka kawata shi da kayan alatu kamar ba a cikin scul ba, guri na samu na zauna daman tun kan na shigo office din sun fada min cewar yana gurin Assembly.
Su Namra suka zauna a a doguwar kujerar da ke kusa da kofa ni kuma na zauna a kujerar da ke kallon teburin principal din. Bayan kamar minti goma zuwa shabiyar aka turo kofar office din aka shigo. Mutumen nan ne da ya kade ni da kekensa yana rike da hannun yarinyar da wacce ta sha kitso mai kyau kuma take tsananin kama da shi, shadda ce a jikinsa ita kuma tana sanye da uniform din makaranta dan guntun skirt ne blue da farar riga sai takalmin makaranta da Scul bag a bayanta mahaifinta, sai wani babbata fuska take da alama wani abun akai mata shi kuma yana ta sham kamshi sai kace wani hege😏
Ni dai kallo daya nai musu daga shi yar sagartacciyar yar tasa na dauke kai shi ko kallon inda muke ma be yi ba.
“Ke tashi ta zauna...”
Fuskata na gabas na jiyo munafukar muryarsa yana yi ma Namra magana wai ta sauka ta bawa yarsa guri ta zauna, juyo nai ina masa kallo uku saura kwata na dakartar da Namra da ke kokarin tashi ta bar yar tasa guri...
“Ke karki tashi, ai da be fi da ba yadda ka kawo yarka a makaranta haka na kawo tawa, dan haka ba zata sauka daga kujera ba tun da kujerar makaranta ce ba da gidan kowa ba”
Yadda kasan ina fada da mutum mutume haka yai min, yana ta lasa wayarsa kamar ba da shi na ke magana ba, ni ma haushi na ji na bawa banza ajiyarsa ina gyara gyalen abayata dake kaina. Muna haka principal din ya shigo, wani abun da zai baka haushi yana ganin mutumen ya fara rawar jiki da shi har da janyo masa kujerarsa ya zauna.
“Ai na san abunda ya kawo ka ranka ya dade daman na san sai Karamar Hajiya ta tsokano mana kai”
Principal din ya fada yana ta washe hauro, da alama dai wannan mutumen yana dan ba shi lashi ne shiyasa ya ke ta masa far'a yana yin kamar be gam mu ba.
“Karamar Hajiya tace kun dake ta”
“Wallahi ranka ya dade bulala biyu ne kawai akai mata ita da yarinyar da sukai fadan”
“Amman kasab ka'idar makarantar nan ba a duka? Then why za ku dake su daga ita har wacan yarinyar?”
“A yi hakuri ranka ya dade dan horo ne kawai ba wai wani abun ba”
“To wannan dai ya zama na karshe”
“In-Sha-Allah ranka ya dade In-Sha-Allah”
“Hajiyata wuce class kinji”
Yarinyar ta dan bata fuska.
“Daddy baka ba ni komai ba”
“Kin san ai bana baki kudi”
“Daddy pls”
Sai kawai ta saka kuka, tsawa ya daka da alama kuma tana tsoron fushinsa ba shiri ta ranta a cikin na kare ta fice daga office din. Sai ta fice sannan principal din ya kalleni.
“Hajiya lafiya dai?”
“Yarana na kawo ina son na saka su a makarantar nan”
“Su duka? Ina mahaifinsu yake?”
Na dan yi shiru na dakiku kamin na amsa masa.
“Baya kusa shi ya ce na kawo su”
“A ka'idar makarantar nan maza suke kawo yara ba mata ba, sannan ba ma karbar yara a irin wannan lokacin saboda an yi nisa da karatu ko wane aji akwai adadin dalibin da ake bukata”
“Dan Allah ku taimaka min zan biya kudin makarantar ko nawa ne In-Sha-Allah”
“Zancen biyan kudin makaranta ai wajibi ne, taimakon ne dai ba zai yi yu ba yanzu”
Rasa nai abunda zan sake ce masa sai na bata fuska kamar mai shirin yin kuka.
“Miya hana su karatu da wuri?”
Mutumen ya tsomo min baki a magana yana kallon yarana.
“Canja musu za ayi”
Na bashi amsa kamar an min dole.
“Saboda mi za a canja musu scul din? Kuma kika kawo su a wannan makarantar”
“Ra'ayi”
Na fada ina mikewa tsaye cike da fusata sai a lokacin ya kalleni domin duk maganar da yake su yake kallo ba ni ba.
“Ya ana magana za ki tashi kuma kika sani ko a taimaka miki... ”
“Bayan ka ce babu a taimakon da zaka iya yi mana? Sai ka ce mu ba kudin za mu biya ba ai kyauta na roka ba, kuma ba wannan ce kawai makaranta ba”
Principal din ya fada, ni kuma na bashi amsa a fusace domin har ga Allah na ji haushi wato saboda ya ga alamar mu ba masu arziki ne kamar wannan ba shine zai wani ce a tainaka mana tun da ya saka ba ki bayan farko ya fada mana ba wani taimako, irin wannan makarantar ma ko yaran ka sun yi karatu aciki wulakanta ka za ayi da yaran. Har principal din ya bude baki yai magana sai mutumen ya daga masa hannu yana lasa wayar da ta zame masa dole. Ni kuma na sako yarana a gaba muka baro makarantar cike da dana sanin zuwan da nai.
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
1️⃣5️⃣
Sai da na sauke su gida sannan na wuce gurin aikina cikin damuwa, damuwar rashin karatunsu da kuma na abunda ya faru a makarantar yau.
Na yi mamakin ganin wani a kujerarta mamakin ba dan kankane ba sai kuma tsoro ya biyo na soma rayawa a zuciyata ko sun kore ni ne kuma? Ko kuma wani abun ne? Ban cewa Emanuel komai ba balle kuma bakon mutumen kai tsaye na nufi office din oga Dahiru.
Sai na fara knocked bayan ya ba ni izinin shiga na tura na shiga. Gaisuwa na fara mika masa a maimakon ya amsa min sai ya kai hannu ya dauki wayarsa ya shiga waya da wanda na ke zaton abokinsa ne domin yanayin firar da yake ya nuna haka, ina tsaye a gurin har yai wayar ya gama sannan ya kalleni da murmushi a fuskarsa kamar zai ce wani abu sai kuma ya mike tsaye ya zago inda na ke ua miko min hannu.
“Congratulations kin hau matsayin Kabeer a yanzu kin samu karin mukami....”
A tsakanin miko min hannunsa da yai da kuma sanarwar karin girman sai na rasa wanne yafi ba ni mamaki, miyasa za a kara min girma kai tsaye bayan akwai waenda suka fini cancantar hawa kujerar Kabir? Da wata manufa yai ko kuwa dai rabo ne ya koka kamar yadda na kowa yake kokawa? Ban ankaro ba na ji na rika hannun nawa yana shaking.
“Congrats Dear”
“Kabir fa?”
Na tambaya bayan na yi saurin cire hannuna daga na shi, ina ta fargabar kar ace min ya mutu. Sai ya juya ya koma kujerarsa ya zauna ni kuma na bi shi da kallo.
“Kabir ya samu tabin hankali, abun nan ya taba shi har cikin kwakwalwarsa, a yadda suka rubuto mana ma an tafi tashi lagos yanzu haka, bayan an bar Kaduna da shi”
Tausayinsa ya kamani ni a lokacin da yake can yana rashin lafiya yana fama da kanshi a lokacin aka dauki position dinsa na aiki a aka ba ni, da ace ba ni ba ce da murna zan hau shi yayinda shi yake can hana fama da kansa.
“Ku kuka cire shi daga aikin?”
“Dole ne wannan ai Halimatu saboda kamfani ne ba aikin gobnati ba, ba za mu iya jiransa har ranar da ya warke ba, ko da ma ya warke ba za mu iya sake daukarsa aiki ba”
Babu tantana idan na sake bude bakina kuka ne zai fito, hakan yasa ban sake ce masa komai ba na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fito daga office din.
“Halimatu....”
Na ji kiransa bayan an fito daga office din, juyawa nai na koma cikin office din ba tare da na amsa ba, sai ya miko miko min wata takardar da ke tabbatar da zamana a position din, karasa nai cikin rashin kwarin guiwa na karba na fito. Na sake dawowa office din mu cike da damuwa ina zaunawa a kujerar da Kabir yake sai hawaye suka ce min sallamu alaikum, babu wani dan 'adam da za ayi ma bushara da karin girma a duniyar ya ji babu dadi sai ni da tawa kaddarar ta zo a haka, ba san abunda ya hanani sukuni da farinciki ba, na kasa samun jindadi da annashuwa, tun ina hawaye kadai har na koma yin kuka mai sauti, Emanuel ne yai ta ba ni hakuri amman sai na ji kamar yana horara min wutar kukan a zuciyata, bayan ko wace dakika biyar fuskar Kabir ce take min gizo, rayuwar da mukai a baya idan zai miko min wata takardar ko ya karba ko ya min wata maganar a cikin har da yawan murmushin da yake min, ina ta jin sautin muryarsa.
Bar bar gurin aikin ba sai da na rubuta takardar resigned ba tare da neman shawarar kowa ba, a lokacin da na aje takadar a office din oga Dahiru baya ciki hakan ya bani damar ficewa ba tare da shan kai ba. Na isa gida da kumburarrin idanuwa saboda kukan da na yi a office, duk wanda ya kalleni ya san bana cikin walwala da nishadi, daga Babana har Mama ba su farinciki da aje aikin da nai ba, ba su fada min ba amman na gani a fuskarsu da kuma yanayin maganarsu. Allah yasa hakan shi ya fi alheri shine abunda suka fada min, ni kuma na amsa da min kamin na taso na baro musu dakin na dawo dakin da nake kwana cikin damuwa.
Kwana biyu da faruwar hakan Abdulhamid ya turo magabatansa aka tsayar da magana, Baba be yi komai ba sai da amincewata kamar yadda shari'a ta shar'anta. An saka lokacin auren saba ga watan Rajab wato watan azumin tsofi. A daren ranar na kasa ganin walwala a fuskar Namra, tun kan nai maganar kanenna suka fara cewa kishi take ni kuwa na san ba kishi ba ne domin har yau Namra bata san cewa mahaifinta ya sake ni ba ita dai tana ta ga ya daina zuwa kuma ba mu koma gidansa ba, tun daga wacan lokacin da ta min maganarsa bata sake min ba, Namra ma ina ta san wani saki balle ta kawo wani abu a ranta ko da yake yaran yanzu wayo ne da su ba kamar mu ba.
Ina daki ina fidda musu kayan bachi ta shigo ta kwanta saman katifar tana ta kallona kamar wata bakuwarta, ni kai na sai da kallon nata ya saka na tsargu duk kuwa da kasancewar karamar yarinya ce.
“Namra minene?”
Na tambaya ina dan murmushi da ban san ma ta ina ya samu hanyar fito min ba.
“Momy aure za ki yi?”
Na gyada mata kai ina karfafa ma kaina guiwa.
“Daddy fa?”
Na dan yi jimm kamin na amsa mata.
“Namra mun rabu da Daddynki shiyasa na dawo nan gidan na zauna, shiyasa Daddynku ya zo ranar yana fada yana cewa sai an ba shi ku”
“Ba za ki sake komawa gidan ba?”
Na gyada mata kai.
“Shi ma ba zai zo nan ba?”
Nan ma na gyada mata kai, sai ta ɓata fuska kan ka ce kwabo hawaye sun fara mata zuba, janyota nai a jikina na rumgumeta ina rarrashinta.
“Namra ai ba daina ganin Daddy za ku yi ba, za ku ganshi lokaci zuwa lokaci, ni kuma kuna nan tare da ni babu wata damuwa”
Kuka tai sosai kamar wacce akai wa bushara da mutuwar ubanta ko tawa mutuwar har wani shidewa take numfashinta na yin sama, ni kaina ban san lokacin da na fara hawayen ba. Daga ni har ita muka kwana kamar marasa lafiya, na kasa farinciki da auren Abdulhamid da zan yi kuma na rasa na rasa dalilin hakan.
Washe garin ranar Abdallah ya sallamo gidanmu, a yawance ya shigo falon ya gaisa da Mama ya shiga ya gaishe da Baba sannan ya shigo dakin da na ke ya tsaya a bakin kofa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ni kuma na kasa kallon inda yake ma balle har na bude baki nai masa magana.
“Am... Yaran nan ya maganar karatunsu?”
Sai a lokacin na dago na kalleshi kwarjininsa ya cika idona sai dai hakan be saka ni dauke kai ko janye idanuwa daga nasa ba.
“Na je Gwarzo ba su karbe su ba, wai sai da ubansu”
“To miyasa ba ki fada min ba? Yanzu idan ban yi magana ba haka za ki zuba musu ido karatunsu ya lalace?”
Sai na ji wani iri kamar ba ni ba, magana yake da ni kamar wanda be taba furta kalma so a gareni ba.
“Kin amince a akai su?”
Na dan kawar da idona daga kallonsa ina girgiza kai alamar ban amince ba.
“Haba Halimatu idan ba ki amince ba ya za ki yi? Ko Aminu za ki maidawa su ki ce ya saka su? Ya kamata ace idan za ki yi abu kina tunani gaskiya, ko da yake har yanzu akwai kurciya a take tare ke yaran ma ai mabiyi da mabiyi ne ba wani dogon tazara”
Sai na ji kamar magana ya fada min a cikin magana, ban yi aune ba na ji yana wata maganar da dariya a sautin muryarsa.
“Idan baki amince ba zan kai karar ki gurin Baba na ce kin hana asaka yara a makaranta”
“Abdallah zan saka su”
Na yi maganar a cikin muryar da ke karantar da mai saurarenta damuwata, sai yai min wani kallon tausayi yai min magana a hankali.
“Zan saka su Halimatu karki damu, karki min musu pls”
Ya roka