Showing 33001 words to 36000 words out of 217237 words
da zan bata ba. Kadan ya rage mamaki ya kashe ni anya Hajara na cikin hankalinta kuwa kuma ta san abunda take kokarin aikatawa? Wai daman da gaske take da take zancen mijinta ya aureni? Ko kuwa dai gwadani take? Idan gaskoya ne ko karya ni ba zan iya auren mijin kawata ba, yar'uwata ma zance domin Hajara ta fi karfin kawa a gurina. Har na isa makarantar nai abunda zan yi na gama na kama hanyar aikina ban daina mamaki ba da kuma jinjina karfi hali irin yana anya irin matan nan suna nan kuwa? Ni sam na kasa yarda da gaske take ma.
*BAYAN WATA DAYA.*
Babu makarantar da ban leka ba nai yawo da takardun transfer su Adnan ba amman aka ki karbarsu a ko'ina, daga private school har na gobnati abun har tsoro ya soma ba ni, a duk makarantar da na kai su sai su kamar za su karba sai kuma su bullo da wani abun, wata makaranta ma ko kallona ba sa yi yadda kasan wacce akai wa wani magani haka nai ta shimlalo a gari neman makarantar da zata dauki su Adnan da Namra amman ina!
Hakan yasa n watsar da zancen karatunsu na maida hankalina gurin aikina duk kuwa da kasancewar bana jindadin aiki a yanzu saboda rashin Kabir ba kuma dan na shaku da shi ba sai dan tuna abunda ya same ni yana ni walwala a cikin office din, musamman da aka kawo wani da zai maye gurbinsa, ko da wasa ban sake gwada zuwa duba shi asibiti ba, sai dai na kan gwada kiran wayarsa kuma bana samu, ta hanyar wani abokinsa da ke aiki a inda nake na samu labarin cewar an kai shi kano a asibitin kwakwalwa saboda abun ya taba hankalinsa, na tauyasa masa ba kadan ba na kuma tausayawa matarsa da duka danginsa musamman da na samu labarin cewar iyayensa duka biyu basa raye, ta wani bangaren kuma ina tausayin kaina domin ban san me gobena ta tanadar min ba ban san abunda zan tarar nan gaba ba.
*Lahadi*
Kasancewar yau ranar hutu ce kamar dai jiya sa ta kasance asabar, dukan mu muna zaune gida har kanena ana ta zancen duniya, yawancin firar da muke ta rashin tsaro da ke addabar al'ummar mu ne da kuma tsadar rayuwa da muke ciki, ina zaune Abdallah ya shigo ya gaishe da Mama da Inna kanena kuma suka gaishe shi ya amsa musu amman bakina be hadu da na shi ba, ba baki kadai ba idona ma ban daga na kalleshi ba balle har na mika masa gaisuwa. Tashi nai ya nufi daki yana rike da hannu Namra waccena lura tana sakewa da shi sosai a duk lokacin da ya leko mu, Mama ta tashi ta bi bayansa suka shiga falon tare, ina nan waje zaune amman hankalina yana can inda suke duk na bi na tsargu sai kace wacce tai wani abun gulma.
Bayan yan mintuna Namra ta fito hannunta rike da chocolate.
“Momy wai ki zo inji Mama”
Na tashi cikin kuzari na bi bayanta, ina shigowa idonsa na kaina kamar daman can rayuwarsa ta takaita akan kallona ne kawai.
“Miya hanaki saka su makaranta”
“Na kai su ba a karba ne”
Na fada ina dan turo baki a shagwabe abunda ban saba ba, kuma ban san dalilin zuwansa a yanzu ba.
“Daman ai ba za akarbe su ba tunda kika bata min rai”
Ya fada yaa ta kallona da idonsa kamar maye, sai a yanzu na fahimci inda zance ya dosa, kar dai kwahi yai min aka ki karbar su a makaranta saboda shi twins ne shi da Abdulhamid.
“Kwahi kai min kenan? Ai ni kwahin ka ba zai kama ni ba”
“Kwarai shiyasa ranar ai kika samu Napep ta kawo ki har gida”
Har yanzu kallona yake yi irin kallon nan kamar ni din tv sa ce.
“To wani abun kika masa kenan?”
Cewar Mama tana murmushi, ni kuma na maida hankali gurin kiran wayata da ke shigowa.
Abdulhamid ne rubuce a screen din wayar, hakan ya saka gabana faduwa ba dan komai na sai dan Abdallah na zaune a falon, kusan tun lokacin da na fito nai bari Abdulhamid be taba kirana da sunan yi min jaye ko sannu ba, ba zan ce dan be ji ba, domin ko last time da Hajiya ta zo ta fada min cewar Abdulhamid ya kawo ta amman be shigo cikin gida ba.
“Hello....”
“Haima”
Gabana ne ya yanke ya fadi jin ya kira ni da sunan da na manta when last ya kirani da sunan.
“Na'am... ”
Na amsa kamar mai koyon magana.
“Kina lafiya?”
“Lafiya Kalau”
“Ina fatar kina gida, gani nan zuwa amman ba zan shigo cikin gida ba magana kawai zan yi da ke na koma”
“To... ”
Ina amsawa ya kashe wayar, idon Abdallah na kaina tana ta min kallon tuhuma, ni kuma na gagara tsayuwa na gagara zama sai yawo na ke da ido kamar marar gaskiya, ba dan komai ba sai dan bana son Abdulhamid ya zo ya tarar da Abdallah, duk kuwa da ban san abunda zai kawo shi ba na san dole daya daga cikinsu ya zargi wani abu. Musamman Abdallah da ya fiye shiga hanci da saka min ido.
#TeamAbdulhamind
#TeamAbdallah
#TeamAminu 😜
#TeamHalimatu
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
1️⃣3️⃣
“Kamar baki da gaskiya Halimatu...”
Sai da na kalli Mama sannan na kalleshi.
“Bana da gaskiya kamar ya? Wannan wace irin magana ce Abdallah?”
Ya dan tabe baki yana ta wasa da hannun Amal kamar ba shi yai maganar ba. Kamar an daki hannuna sai na yi yai min majiyar, ban san lokacin da na saki wayar hannuna ta subuce ta fadi kasa, a take ta watse a saman tedar da ke falon kamar abar da aka taka da mota ko aka sakawa dutse aka daddaka. Subhanallahi Mama ta furta ni kuma na risina a gurin ina kallon wayar ina jin kamar na fasa kuka tuni idona suka cika da kwalla, har ga Allah na tsani na rasa wani abun da na ke matukar so ko yake da muhimmancin sosai a rayuwata, na san phone ce amman ina jin babu dadi domin samun irinta a yanzu ba abu mai sauki a gareni a lokacin da na ke gidanmu dawainiya ta zata min yawa yanzu fiye da, ga kuma zuwan da Abdulhamid zai yi ban san abunda zai kawo shi ba wata kila ma baya son kowa ya san da zuwansa.
“Ya akai wayar ta fadi?”
Mama ta tambaya sai an amsa mata muryata na gargada alamar ina daf da fashe da kuka.
“Ban sani ba Mama a hannu ta zame ta fadi”
“Laa shikenan wayar Momy ta fashe bamu da wayar game”
Namra ta fada tana wani bude baki, Abdallah kam ko dago kai be yi ya kalleni ba sai wasa yake da yatsun Amal kamar be san abunda ya faru ba.
“Momy yanzu da wace wayar za mu rika game...?”
Wani bakin haushi na ji ban san lokacin da na dakawa Namra wacce tai maganar tsawa ba.
“Da wayar ubanki... ”
Sai a lokaci Abdallah ya dago ya kalleni sai kuma ya kalli inda wayar take ba ce min komai ba sai dai fuskarsa ta nuna alamar bachin rai, mikewa yai tsaye yana saa dayan hannunsa a aljihu.
“Mama ni zan tafi, kuma yaran nan a yi kokarin saka su makaranta domin barin su hakan nan ba zai yiyu ba ya kamata a san abun yi lokaci na ta tafiya”
Wata uwar harara na watsa masa saboda haushinsa da na ke ji, wacce be san ma ina yi ba domin be kalli inda na ke ba da Mama yake ta maganarsa, ita kuma tana nanata masa cewar za a saka su makarantar, hannu ya saka aljihu ya ciro kudin da ban san ko nawa ne ba ya aje mata a hannun kujerar da take zaune sannan ya karaso inda na ke duke ina ta kallin wayar da na gagara tattarawa na kwashe ya ce.
“Halimatuuu mu kwana lafiya”
Har na yi kamar na bude baki na aika masa da bakar magana sai kuma wata zuciyar ta hanani ganin a gaban Mama ne da kuma yara. Tare ya fita da Amal da Namra Aiman ma ya bi bayansa.
“Halimatu kina jin yana miki sai da safe amman kika gagara karba mishi miye haka?”
Mama ta fada cikin yanayin damuwa da rashin amsa masa da ban yi ba.
“Mama ba ki kohi yai min wayar ta fadi ta fashe ba”
“Kohin zai saka waya ta fadi har ta fashe? Ai naga ko kallon ki be yi ba kuma ba wata maganar ta bacin rai kika masa ba balle ace, abu ne dai da Allah ya kawo”
Ban sake cewa komai ba na tattara wayar na mike tsaye na nufi dakin Mama na zauna bakin gadonta kamar wacce aka kwashewa tunani a kwakwalwa, babu komai a raina sai bacin ran faduwar wayata, ina zaune a gurin yara suka shigo da yan dari biyar biyar a hannu wai Uncle Abdallah ya basu, ni dai ko kallonsu ban yi ba balle har na karbi kudin na adana musu saboda bakin haushin Abdallah da na ke ji.
Ban yi dabarar na karbi wayar daya daga cikin yan matan gidanmu na kira Abdulhamid ba sai da aka sallame sallar isha'i, a lokacin kuma yan zaman majalisar kofar gida sun soma shimfida tabarsu su zauna. Idan ma nace zan yi magana da shi sai dai na koma ta kofar gidan makotan mu wanda hakan ba zai min dadi ba domin a hanya ne.
Ban yi kasa a guiwa ba na karbi wayar Hafiza na lalabo number Abdulhamid a wayarta na aika masa da kira, kamar jira yake a take tai picking din call din yana rangadamin sallama, bayan na amsa na koro masa da bayanin wayata ta fadi har ta fashe.
“Oh ni na dauka ko kashe wayar ki kai, domin nata kira ban samu ba”
“Wallahi faduwa tai ta fashe screen din ma ya watse gaba daya”
“Subhanallahi garin ya?”
“Ba zan iya fada ba, ni dai kawai tana hannuna ta subuce ta fadi kasa, ka zo ne?”
“Na zo, sai dai ban karaso kofar gida ba saboda bana son kowa ya san da zuwana, dan ki kawai na zo”
“Ka tafi ko kana nan?”
“Na tafi amman na fi karfin one hour a gurin kamin na tafi”
“Ayyah ban jidadi ba”
“Karki damu zan shigo gobe In-Sha-Allah”
“To Allah ya kai mu”
“Amin mu kwana lafiya”
Ba bari na sake cewa komai ba ya katse kiran, ni kuma na sauke wayar ina ta tunanin abunda zai kawo shi gurina ni kadai, wata kila kum zai yi min jajen abunda ya faru ne ko kuma ya bani wata shawarar, ban raba dayan biyu ba Hafiza ta shigo dakin na mika mata wayarta bayan n goge call din domin Bana son ta san da wanda nai wayar. Sai kuma na nufi inda jakata take na bude na dauko dubu biyu saboda ina son siyo man goge baki da Vaseline din mu daya kare. Hijabina na saka ina Kwalawa Namra kira ta zo ta raka domin ta fi sauran natsuwa da abun hankali, sai dai duk yadda nai ta noke noken na fita ni kadai ban samu sa'a ba har sai da Amal ta gan ni ta biyo da gudu tana kuka, a dole na tsaya na rika hannunta sannan na nufi dakin Mama na shaida mata cewar zan je shagon titi na siyo man shafawa da kuma na wanke baki.
“Ba zaki aika kanenki si siyo miki ba?”
“Ina son fitar ne Mama”
“To Allah ya tsare”
Na amsa da amin sannan na kama hanya ina rike da hannu Amal Namra kuma na gefena na hagu dukansu suna sanye da riga da wando ne yan kanti. Cikin tsananin kunya na ratsa kofar gidanmu na wuce saboda taron da maza yan zaman majalis sukai yi. Wanda na san a nan ma ba zan rasa wanda zai yi gulma ta ba, koma na ce gulmarmu yan gidan gaba daya domin mun tara yan mata Masha-Allah, wanenda aka dade ana zancen wai mai kudi suke jira wasu kuma tuni suka fara yi kanena zargin masu nemansu duk na neman auren suke zuwa ba iskanci ne kawai ke kawo su, ni kuma na dade da yin zurfi wajen sanin cewar aure da haihuwa da mutuwa da rayuwa duka na Ubangijin Annabi Adamuna, wato Allah S W T wanda ke rubutowa bawa abunda zai same shi tun gaban bawa ya zo duniya.
Lokuta da dama kan jarabi bawa da abu ba dan Allah baya son bawan ba sai dan gwada karfin imaninsa da kuma aikinsa. Idan na tuna mahaifina da mahaifiyata ina samun kaina a cikin wani kogo mai cike da tausayinsu musamman ubana wanda na san shi mutane za su zaga, kuma shi zai fi kowa shiga damuwa, domin bayan yan dakin Mama akwai na dakin Inna waenda sukansu yan mata ne da suka kasance a karkashin inuwarsa. Gashi lafiyar kafafuwa ma bata wadace shi ba.
“Momy a nan za mu yi ta zama? Daddyn ba zai zo ba?”
Maganar da Namra tai ka katse min zancen zuci da na dade da yin zurfi a cikinsa, gabana ya fadi ba faduwa ta tsoro ko fargaba ba, ba faduwa ta irin amsar da zan bata ba, ko kuma abunda zan mata ta fahimta ba, faduwa dai irin ta ko wace uwa mai yayana yana daya daga cikin dalilin daya hana ni fitowa a gidan Aminu gudun irin rayuwar da yayana za su yi idan bana gidan, sai dai kuma yanzu da suke hanuna kuma ya rufe idonsa daga kallonsu balle waiwayarsu ya rayuwarsu zata kasance? Mama tana yawan fada min ba ko wane namiji ne zai auri da yayana ba, idan ma ya aure ni ba zai yarda na zauna da su ba, anya idan na bar su a gida za su samu kulawar da nake musu fatan samu? Ya makomarsu zata kasance lallai juma'ar da za tai kyau tun daga laraba ake gane ta, indai har yau ba tai musu kyau ba ya gobensu kenan?
“Momy ga fa shagon can, ko ba shagon Takur ba?”
Namra ta fada tana girgiza hijab dina, wani irin numfashi naja na sauke hawayen kam tuni suke wanke min fuska sai dai ban fahimci hakan ba sai da Namra tai min magana ganin ina kokarin wuce shagon da ban san mun kawo ba sai yanzu.
“Eh shi”
Na fada ina share hawayena sannan na karasa gurin shago, sai da ya sallami duka mutanen da suke gabana sannan na mika nawa kudin na fada masa abunda za a bani ya mikon na siya ma Amal da Namra biscuit na rike biyu domin na san indai Adnan da Aiman sun gani sai sun tambaya ina na su? Bayan na karbi canji na juyo tare da yarana muka kamo hanyar dawowa gida. Tunanin dai na dazun ya sake fado min a rai, har na kasa fahimtar shi Aminu ya yafe min su ne gaba daya hakan ya saka ya kwashe har wata daya ba kira ba aike ko kuwa yana jira sai su kara girma ne ya karbe su?
Karar qaraurawar keke na ji kamin na yi kokarin kauchewa tuni keken ta bugeni ni kuma na gibi Namra ni da wadanda suke kan keken muna fadi kasa, saurin tashi nai cike da kunya Allah ma ya tsare ba mutane sosai a gurin da na ji kunya kam. Mutumen da ke rike da keken yayi saurin karaso inda na ke ya daga Namra yana kabe mata jikinta tare da rika fuskarta.
“Cutest ba ki ji ciwo ba?”
Ta gyada masa kai, Amal kam da gudu taje ta dauke chocolate din da ya fadi a gurin dawo inda nake da gudu ta boya.
“Daddy wacan yar yarinyar ta dauke min chocolate dina wanda ban fasa ba”
Wata yar karamar yarinya ce maganar wacce bata wuce sa'ar Adnan ba, kananan kayana a jikina sai dan kwalin atamfa da aka daura mata, a kusa da ita wata matashiyar mace ce tana sanye da abaya wacce na ke kyautata zaton budurwa ce ganin jikinta babu mayafi sai hula mai kyau sai kyalli take kamar an watsa mata kananan taurari a jiki.
“Sannu....”
Ta fada tana dan kawarda fuska kamar tana jin kunya ta.
“Muna ta miki horn amman baki ji ba, har Daddy ya kade ki”
Yarinyar ta fada ita tana kallona.
“Ko kuma ku baku lura ba? A hanyar nan ba dan keke kawai akai ta, at least tun da kun gan ni agefen hanya ai sai ku koma tsakiyar hanyar ku wuce”
Na fada da dan fusata domin har ga Allah na ji haushi kuma ba da yarinyar na ke ba da mahaifinta nake.
“Hey cutest hold this for your Mom”
Da murmushi ya mikawa Namra ledar da ta subuce daga hannuna ta fadi bayan ya kwashe kayan ciki ya saka a ledar. Ni kan ko kallona be yi ba ya nufi inda kekensa take irin kenan nan ce mai tsada sosai ya tashi keken, dogon jeans ne a jikinsa sai yar vest fara ya daure jacket dinsa a kunkurunsa, kana ganinsa ka san irin mazan nan ne marasa kunya domin namiji mai kunya ba zai biyo hanya da vest ba duk dai ban san inda suka fito ba, sai da ya hau keken sannan na daga yarinyar da ke kiransa da Daddy ya dora ta daga gaban keken.
“Kin ga yarinyar ta dauke min chocolate kuma mug dina ya fadi? Sai ya kenan?”
Yarinyar ta fada yana nuna inda Mug din yake sai a lokacin na lura da mug din, da alama yarinyar irin yaran nan masu shegen kodin tsiya da tsiwa, domin har wani juya ido take tana motsa baki kamar wata babba. Babbar kuma wacce ta fi tsananin kama da shi ta hau baya tana dago min hannu.
“Bye..... ”
Ikon Allah su kuma haka suke? Sun buge ni ko sannu babu? Ko ma miya tsayar da ni kallonsu oho, daman can da ganinsu ai ba gidan mutunci suka fito ba. Ni kadai nake ta mita ta a cikin raina har muka iso gida, sannan na karbe chocolate din da Amal ta dauka na yarinyar na jefar, babu irin kukan da ba tai ba na ki na kulata har ta gaji tai bachi.
Washe gari bayan mun gama karyawa na fara shirin