Showing 195001 words to 198000 words out of 217237 words

Chapter 66 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

205

marar kyau har ki sa a fara zargin wani abu, musamman ma Hajiya ta ko Siyama, dan Allah Lims ki bar wannan a matsayin sirrin mu, bana son wani yace zai ga laifinki ko ya tsane ki a yanzu, kina bukatar farinciki ko bana raye, and I'm sure idan ba ki samu a gurina ba Hajiya da Siyama za su ba ki, saboda sun san ina son matata sosai...”

Ya karasa yana sumbatar hannuna. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rumgume shi ina jin kamar akwai abunda Ahmad ya boye min, har ga Allah ba zan daina zargin kaina a kan ciwon Ahmad ba domin a lokacin da be aure ni ba abun ba haka yake ba, why sai yanzu? Ko dai ni din ba alheri ba ce a gurin jama'a? Sanadina ya rasa yarsa, yanzu kuma ace ya zama mijina kuma ta kamu da ciwo?  Ina kokarin tsayar da kukana zancen Siyama da na Doc Nura ya fado min a rai, cewar a daren assabar din data gabata abun ya same shi and a wannan assabar din yana tare da ni ai kuma daga ita ne be dawo ba, hakan na nufin a ranar ne ya kasa kai kansa gida? Kuma a wannan ranar he hold my hand wata kila daga nan abun ya same shi.

“Abu kamar na iska”

Maganar Mama ta dawo min, no wait a daren ma ai ya gaisa da Abdallah, kuma Abdallah zai iya masa wani kofi, indai har ransa ya bace, i can remember ni ma ya taba min a lokacin da ya bukaci na shiga motarsa na ki sai an rasa mai napep din da zai dauke ni, and i lokacin da na auri Abdulhamid ma ya taba min na kasa girki, ya taba min wayata tsage ba tare da ta fadi ba, and yayi ma Abdulhamid ma, tabbas zai iya yi ma Ahmad inda har za a duba ace ba a ga komai ba tabbas Abdallah ne.
  Shine abunda zuciyata ta raya min kai tsaye, domin a wannan ranar Ahmad ya rike hannuna har gaban Abdallah kuma na san hakan ba dadi zai masa ba, secondly the way da ya ba Ahmad hannu su gaisa ba dan Allah bane, how Abdallah zai yi wani murna ya aure ni? Wanin ma wanda ya bukaci na daina aiki a kamfaninsa saboda baya son taraiya mu...
Ban san lokacin da na mike tsaye da sauri ba hankalina yai mugun tashi.

“What...?”

“Ya kamata naje gida ba su san na zo nan ba gashi yamma ta yi”

Kallona yai from head to toe.

“Ji veil din da kika fito da shi Lims, nasa doguwar riga ce amman ina bukatar ki rika rufe min jikina”

“Zan saka next time, zan dawo anjima kadan...”

Na fada ina nufar kofa da sauri sai ya kira ni.

“Hey Lims are you okay?”

“I'm fine”

Na fada ina kokarin kwantar da hankali.

“Okay come here and kiss me”

Dawowa nai na yi kissing dinsa sai ya rumgume ni da dayan hannun nasa.

“I love you”

Ya rada min sannan na sake shi na mike tsaye na dauki purse dita na fice daga dakin. A phone list dina na shiga na nemo numbersa da ke kan gmail nawa na danna masa kira da sabon line na, ringing rai sai da ta kusa katsewa sannan ya daga da muryar da ke nuna be san mai magana.

“Abdallah kana ina?”

Yana jin muryarta ya gane ni ce mai magana.

“Halima.....”

Yayi shiru sai kuma ya amsa.

“Ina gida”

“Wane gidan?”

“Gurin Hajiya”

Kashe wayar nai na nufi hanyar fita daga ward din ina ta sauri kar na hadu da su Mama.



*Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lqmbobin 09137294470 08034236800*
7/21/21, 11:11 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


6️⃣0️⃣

For the first time a yau zan tunkari Abdallah da maganganu a cikin gidan Hajiya babu tsoro ko fargaba a tare da ni, sai dai ga dukan alamu shi din ya kasa natsuwa sai kiran wayata yake ni kuma na ki na dauka domin face to face nake son ganinsa ba ta waya ba, kamin mai napep din ya isa har na matsu, yana saukeni na biyashi kudinshi na buga gate din sai na ji shi a bude, hakan yasa na tura kofar na shiga babu kowa a harabar gidan sai motoci ina ganin motarsa na tabbatar da lallai yana gida kamar yadda ya fada min. Kai tsaye na nufi kofar falon nai knocked sai na ja na tsaya, after some seconds ma sake kwankwasawa. A hankali aka bude kofar Abdallah ne ya fito daga cikin falon ya janyo kofar ya rufe yana kallona da mamaki a fuskarsa.

“Halima lafiya?”

Ya tambaya a hankali kamar mai rarrashin yarinya. A yau da na kalleshi sai na ganshi kamar ba Abdallah ba, duk wata kima da matarta da mutunci da nake ganinsa da ita a yau sai na nemeta na rasa.

“Ina mamakin yadda zaka fada min abunda ba shine a ranka ba, ina mamakin yadda ka tozarta yardar da nai da kai ka watsar da amincin da nai maka”

Karara mamaki da al'ajab suka bayyana a fuskarsa.

“Halima are you okay?”

“No I'm not, me yasa zaka fada min abunda ba shine a ranka ba, akan me zaka ce kana son farincikina bayan ba haka ba ne a ranka?”

Matsowa yai kusa da ni ganin yadda nake daga murya, idanuwana kuma na nuna tsantsar bakin raina.

“Wace irin magana ce wannan? Me yake damunki?”

Ya fada murya kasakasa.

“Kaine damuwata Abdallah, kai ne matsalata”

“What happen?”

“Ka rantse min baka san abunda yake faruwa ba....!”

Murmushi yai ya lumshe ido ya bude.

“Wai wannan banza... Ai...”

“Shi ba banza ba ne mijina ne na sunna!”

Na fada cikin wani irin zafin rai da ban taba sanin ina da shi ba. Sai ya sake yin murmushi.

“Na sani ne ai, har na taya shi murna remember?”

“Yes a ranar ka cije shi a hannu”

“Maye ni ne ko aljani da zan masa wani abun?”

“No amman kai kana da kofi, kai ka yi wa Abdulhamid ya kasa aure, ka taba min ba sau daya ba ba sau biyu ba, Abdallah na sani zaka iya kullatar Ahmad a rai”

“Yes...”

Ya amsa min kai tsaye yana hade fuska kamar ba shi ba.

“Ya fada min zai nuna min matsayinsa a gurinki, kuma ya fada ya cika na sani yayi forcing din ki ya aure ki, he deceive you ba ki san waye shi ba, how could he? Ya aure ki by force and ya holding hannunki a gabana bayan ya san na fi kowa son ki? How dare he?”

“No how dare you....! Ahmad be aure ni ba sai da amincewa ta, abunda kai masa ya nuna baka son farincikina, domin yan'uwansa da danginsa ni zarsu zarga idan hakan ta faru ya kake tunanin zan kasance?”

“Amman Halima ba son shi kike ba, ta ya za ki auri mutumen da ya laka miki laifin kisan kai? Ko kin manta ne? Mutumen daya tashi sakawa a rufe ki gidan yari? Babu kalar maganar da be fada miki ba, Ina son ki Halima kin sani ina da kudurora akanki, i just want you to get a better life, kuma idan mu kai jira na wani lokaci wata kila Allah zai cika mana burinmu”

“Jiran shekara dubu nawa? Jiran ranar da Hajiya za ta so ni har ta amince na aure ka? Ko jiran ranar da Abdulhamid da bakinsa zai roki na aure ka? Ko jiran ranar da mutane za su ga dacewar haka su ba mu shawara aikatawa? Ba so na kake ba Abdallah kana son ka ne, a lokacin da na ke auren Aminu ka sani mijine uban yayana amman kullum sai ka fada min aibinsa, kullum sai ka fada min abunda zai bata min rai saboda na rabu da shi na aure ka, ka sani neman auren matar aure haramun ne Annabi ya hana amman ka nace kana ta min campaign kanka, babu abunda baka min dan na kashe aurena na aureka, wannan dalili ya hana ni auren shiyasa na zabi na aure dan'uwanka domin shi be taba min haka ba, duk kuwa da kasancewar shi ya fara so na kamin kowa, yana sane nai aure amman be taba ce min Halima ki kashe aurenki ki aure ni, Abdulhamid ya fika zuciya mai kyau, domin shi be taba cutar da ni ba, kawai ya kasa aminta da ni ne a lokacin da kaddara ta fada min, and now na sake auren wani ba kai ba, so kake na kashe auren na fito aure ka? Saboda ka cika son kanka kuma ka kasa yarda da kaddara, miye laifin Ahmad idan na aure shi kuma zan samu farinciki a gidansa? Ashe ba farinciki kake min fatar samu ba?”

Na karasa a tsawace hawaye na sauko min.

“Halima kamar ba ke ba”

“Ni ce dai, na zo na gargade ka ne, idan wani abu ya samu mijina...! Ba zan taba yafe maka ba, kuma hakan ba zai saka ya sake ni ba ba zan taba rabuwa da shi ba har a abada...! Domin ni na yarda da abunda ka kasa yarda da shi KADDDARA”

Na kare ina nuna shi da yatsa, sai ya girgiza min kai ya kara matsowa kusa da ni

“Haba Halima kina da raunin tunani, ta yadda idan wani ya kisa miki wata maganar sai ki hau ki zauna akanta, ki rika kokarin samawa wasu farinciki ba kanki ba, yanzu duniya ta wuce wannan kowa kansa ya sani, kamar kin manta waye Ahmad? Miya zai kitsa miki abubuwa a kaina kuma yardar da mutumen da kika gani a jiya sama da ni?”

“So kake GOBE NA ta lalace, so kake mutane su fara guduna suna ganina kamar wata annoba? So kullum nai ta dauwama a bakinciki da damuwa? Na gaji i deserve happiness”

“Shi nake kokarin ba ki, i promise you za ki samu farinciki a tare da ni, dukannin mafarkina da burina akanki ne, Halima ina miki son da wani da'namiji be taba miki shi ba....”

Yana karasa Hajiya ta bude kofar falon ta fito, a yanayin yadda na ganta da kuma yadda fuskarta ya nuna ta ji komai. A gabansa ta tsaya yana kallonsa shi ma kallonta yai sai yai kasa da idonsa.

“Da gaske kai ne silar ciwon Hassan?”

Ta masa tambayar tana masa wani irin mugun kallo, sai yai shiru ya kasa amsawa kuma ya kasa daga ido ya kalleta.

“Ka amsa min? Eh ko a a?”

Ta daka matsa tsawa jikinta har bari yake.

“Eh....”

Tasss ta wanke masa fuska da mari kamar daman jiran take ya amsa mata da eh din, hakan kuma be wadatar da ita ba har sai da ta sake marin dayan baren fuskar.

“Amman baka da tausayi baka da imani Husaini.... Allah ya wadaranka....”

Cikin kuka take mishi wannan maganar, shi kuma har lokacin be motsa daga inda yake ba. Sai kuma ta juyo ta kalleni tana hawaye.

“Fita ki bar min gida, ba ke ba yaya har abada, ko bana raye ka auri Halima ban yafe maka ba.....!”

Ta karasa tana nuna shi da yatsa, a rikice Abdallah ya kalleta ya kalleni sai ya fadi kasa ya rike kafafuwanta ya fashe da kuka kamar ba shi ba.

“Noooooooo Hajiya dan Allah..... Hajiya dan Allah, Hajiya dan Allah.... Hajiya dan Allah.... Hajiya dan Allah...”

Ya maimaita hakan ya fi a kirga yana rike da kafafuwanta yana kallona kuka yake sosai kamar ba namiji ba, sai kuma ya mike tsaye ya rike hannayenta.

“Hajiya ina son Halima Wallahi baki san kudurina ba dan Allah karki shiga tsakaninmu haka....”

A take ta fisge hannunta ta sake wanka masa kyakkyawan mari. A lokacin ne yai shiru ya runtse ido.

“Ka gani ko? Dan Allah ka kyale min mijina.... Ina son abuna”

Na fada ina hade hannayena nima hawaye nake kamar shi, sai ya bude ido ya kalleni kamin ya juya yana kallon mutanen da suka fito daga falon suna tambayar ba'asi, Hajiyar kuma ya koma cikin falon tana kuka. Ni kuma na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fara tafiya ina jin wani abu marar dadi. Sai da na kai gate din sannan na juyo na kalleshi har lokacin yana tsaye a inda yake yana kallona, juyawa nai na bude gate din na fita. Sai da nai tafiya mai nisa sannan na samu napep na shiga ta mayardar da ni asibitin ko da na isa ana kiran sallah magariba, kai tsaye na nufi ward din da Ahmad yake ina isa na tura kofar dakin na shiga, sai na samu Mama da Inna zaune a dakin ga Hajiyarsa da Kanwarsa Siyama da wata wasu mata hudu da ban wayance su ba, sai dai ina kyautata zaton yan'uwan Ahmad din ne, shi kuma yana zaune saman gadon wani kallo kawai yake aiko min wanda ke nuna ba lafiya ba. A sanyaye na shiga muka gaisa da mahaifiyarsa sai ta gabatar da ni a gurin matan, sannan tace min.

“Kin gwangwanin Gwarzo nan”

Hakan yasa na sake mika musu gaisuwa sannan na tsaya a kusa da Inna sai dai a duk lokacin da na kalli Ahmad sai ya dan harare ni kasa kasa, sannan ya sauko saman gadon ya shiga bandaki yai alwala ya fito, Hajiyarsa ta umarce ni da na shimfida masa carpet su kuma suka tashi suka fita tare da bakin. Inna da Mama suka mike tsaye Inna na ce min.

“To mu kan mun tafi Halimatu sai kin dawo Allah ya kara sauki”

“Amin inna sai na zo”

Sai da suka juya sannan ya kawo kunnensa kusa da nawa ya rada min.

“Ki ce musu nan za ki kwana”

Na lake kafada alamar ba zan fada ba, shi kuma ya kware min ido kamar mai yi da karamar yarinya. Sai da suka fice sannan na shiga bandakin nai alwala na fito na zauna bakin gado har sai da ya gama sannan ya tashi ya dawo saman gadon ni kuma na hau carpet din nai sallah, babu komai a addu'a ta sai nemawa Ahmad lafiya da rokon Allah ya tsare min shi. Sai da na shafa addu'ar sai ya miko min hannunsa na hagu, na rika na tashi tsaye sai ya dawo da ni kusa da shi na zauna, sai ya saka hannunsa saitin kwankwaso na yana ta wasa da shi, ya dora gemunsa saman wuyana sai yasa ta bakinsa ya janye mayafin kaina ya sauko kasa, bakinsa saitin kunnena.

“Na fadawa Hajiya ta sa a shirya miki ticket mu tafi tare”

“Amman Ahmad tun da ance ba a ga komai ba why not a yi addu'a kasan wani lokacin iska da kandu suna yin haka fa”

“Ba laifi ya zama iska ba, kin san Nigeria ba mu da irin wannan cigaban yanzu za a iya zuwa a can su yi gwaje gwajensu kuma a gano matsalar”

“No ba na asibiti ba ne”

“How do u know?”

Kamar mai rada haka yake min magana in each word sai ya tsotsi kunnena sannan yake fadarta wani sa'in kuma sai ya busa min iska a kunnen. A kalleshi a natse na ce.

“Baka fada min tun daga lokacin da ka gaisa da Abdallah ne abun ya same ka ba”

Sakina yai yasa hannun nasa ya rike fuskata.

“Ina kika je dazun?”

Na yi shiru.

“Ba gida kika je ba, na sani dominbda suka zo sun tambaye ki kuma Mama tace kin buga mata waya kina kuka, i suspect something fada min ina kika je? Don't lie to me”

“Magana nai da Abdallah....”

A take fuskarsa ta canja.

“As how?”

“Akan ciwon ka ne”

“Oh ya Allah, taya za ki je ki yi magana da shi? Kin san ko tunawa nai akwai son ki a zuciyarsa sai naji kamar na kone, akan me za ki je ki yi magana da shi? Lims why? Is not allowed ya ji muryarki ma ji drees dinki ma, gown ce fa sai mayafi Babe why?”

Ya karasa kamar yai kuka, hakan kadai ya isa ya karantar da ni irin zafin kishin da Ahmad yake da shi, so idan har zan zauna da shi dole nai tsaka tsantsan da rayuwarsa.

“Saboda na san shi yai maka kofi, kuma da na masa maganar ya amsa min da cewar shi din ne, tun da yana jin haushinka na san dole zai maka, shiyasa na ce maka ba na asibiti ba ne, ya yi ma dan'uwansa kuma ni ma ya sha min”

“Ba kofin ya dame ni ba, maganar da kika yi da shi ta dame ni, Allah kadai ya san abunda ya ce miki kila ma yace Halima ina son ki”

Na dan zaro ido.

“Aa be ce ba fada fa mukai da shi”

“Fada did he touch you”

“Oh oh No ba irin wacan fadan ba, fada na baki”

Ture ni yai daga jikinsa.

“Daga ni dan Allah”

“I'm sorry, amman na damu da halin da kake ciki ne”

Ya fada ina kada kafata domin tafiyar abu nake ji kamar ƙuda, ina jijjiga kafar na ji abu ya fado mai nauyi, saurin mikewa nai tsaye sai ganin kunamu nai har uku a inda kafafuwana suke, ban san lokacin da na daka tsalle na dale saman gadon ba ina ihu.

“Ka gani ko? Ya fusata da ni shine yai min kunamu nan”

“Shiiiiiiiiiiii karki bari Hajiya ta ji maganar nan”

Ya fada yana rufe min baki.

“Shiyasa na fada maka cewar ciwon hannunka nan ba na asibiti ba ne, ayi maka addu'a zai fi sai ka mu sauki”

Na fada kamar zan fashe da kuka, jana yai jikinsa ya rumgume.

“Amman kin san yanzu an riga an gama shirya komai Hajiya ba zata yarda a fasa ba, kuma zuwan ma yana da amfani ko ba kuma hakan zai kara tabbatar da maganarki kuma Hajiya ba zata zargi komai ba”

“Amman taya za a samu maganin kofi a asibiti? Ahmad kai tunani mana”

“Okay fine zan yi magana da Hajiya sai nace mata a hada da addu'a hakan ya miki?”

“Eh ni ma kuma za ki rika maka fatiha kafa bakwai kullum da safe a ruwa kana sha idan zaka iya shan yawuna”

“Hmmmm har abunda ya fi yawunki ma zan iya sha, kin san minene”

Ya fada yana shinshinata tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login