Showing 129001 words to 132000 words out of 217237 words
yayi cikina yana zare ido abun be taba, ina baya baya yana cikina har samu sa'ar riko mayafina ya fisge shi gani a gafen titi hakan yasa nai unkurin gudu sai yai nasarar kai mun duka mai shegen zafi, ya kuma rikoni yana kokarin makureni.
“Ni ce ni ce Kabir.....”
Shine kawai abunda nake iya fada cikin ihu da daga muryar, tare da kokarin kwatar kaina amman ina karfin mace da namiji ba daya ba tuni ya samu sa'ar fara makurata, ga ruwan sama ana yi balle a kawo min agaji, ko ma ba a ruwan ba kowa ke shiga lamarin mahaukaci ba ballantana ma gurin babu jama'a sosai.
Kamar daga sama na ji ana kokarin taimaka, sai duka ake kaiwa Kabir ta ko'ina ban san ko waye ba har sai da na samu sa'ar kubucewa daga hannunsa, ruwan dake sauka da kuma makurar da na sha bata hanani gane cewar Ahmad bane, abunda ban tana zato ba, ban tana tunani ba balle har nai mafarki yau yake faruwa a zahiri. Nikam ban tsaya komai ba ganin fadan ya koma tsakaninsu yasa na dauki mayafina da sauri na nufi inda jakata take na dauka tare da kayana na fara tafiya kamar an koroni ko waige inda suke ban sake ba.
Sai da nai tafiya mai nisa sannan na soma tafiya a hankali ina cigaba ta taron Napep, cikin sa'a motar Abdallah ta wuce ni sai kuma ta dawo baya daidai ta tsaya daga can cikin motar ya bude min front seat. Da sauri na shiga jikina har rawa yake.
“Ina kika fito?”
Ni dai ban iya bashi amsa ba domin har yanzu ban gama dawowa daidai ba.
“Ina kika fito...?”
“Aiki”
“Aiki da wadannan kayan? Wando ne fa a jikinki da riga..”
Na dan kalli jikin nawa, ruwan da ya jikani yasa tufafin sun dan kama jikina.
“Karki sake saka su daga yau, idan ba barki ki saka tufafinki na hausawa ba, ki daina aikin”
“Am.... ”
“Ba shawara nake ba ki ba, umarni ne”
Ya fada yana daga min hannu fuskar nan tasa a hade kamar dai ba shi ba.
AHMAD POV.
Hannunsa ya kai ya ciro chewing gum din daga bakinsa sannan ya mike tsaye ya nufi window ya jefar da cingan din yana cigaba da yatsinar fuska.
Ai tun farko be kamata ya ci cingan din ba ko da ba ita ta aje masa ba balle kuma a hannunta ya fito macen da babu ta biyunta a gurinsa gurin tsana. Yawun bakinsa ya tofar a window Yunus dai be ce masa komai ba bayan kallon da ya bishi da shi sannan ya fice.
Haka ya wuni yana tofar da yawu kamar wani mai sabon ciki, yaba ta jin haushin tauna cingan din da yai, daga bisani ya koma jin haushin Siyama wacce ta bukaci ayi masa abun, kamin jin haushin ya koma gurin Yunus wanda yake ganin shi ya biye mata.
After sallah azahar Yunus ya shigo office din yana sanar masa cewar bakinsu sun iso.
“Amman Dahir ya zo”
“No yana kan hanya dai”
“To ya za'ayi communication da su”
“Karka damu da wannan, yanzu dai kaje ka gaisa da su”
After haka ya fice, Ahmad ya bata minti biyar a zaune sannan ya nufi freezer dake office din ya bude ya dauko sweet ya bude ya saka a bakinsa, dan yasan ba zai je can yana tofe tofen yawu ba sai kace mai sabon ciki, idan ma be sha sweet din ba tashin zuciyar da yake ji ba ba zai bar shi ba. Sai da ya dauki rigarsa ya saka sannan ya nufi dakin taro, yana shigowa suka mike tsaye tare da bashi hannu ya gaisa da su da halshen nasara ya fara yi musu barka da zuwa duk kuwa da yasan ba lallai ace suna jin wani abu bayan welcome da kuma gaisuwa ba.
A gurin daya saba zama ya nufa ya zauna, yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu aka turo kofar dakin Yunus ne ya shigo, Halimatu na bayanshi ta tsaya daga jikin kofar har sai dai Yunus din yai mata iso, wani irin bugawa zuciyarsa tai, duk sai yaji ransa ya bace sai dai ba damar ya nuna a gaban mutanen a dole ta sa ya shanye, sai dai yana mamakin abunda ya kawo ta dakin taron. Takawa ta fara yi tana juya yai arba da mazaunanta sai yai saurin runtse idonsa duka biyu, can kuma ya bude dayar yayinda dayar take a makkale ya rufeta, sai kuma yai saurin rufewa yana jan tsaki a ransa. Be bude ba har sai da yaji ta fara magana da su alamar ta juyo kenan sannan ya bude ido, kallo daya yai mata yaga yadda kayan suka karbe ta sai kuma ya dauke kai. Har akai meeting din aka gama be bari ta san yana kallonta ba, ba ma ita ba ko Yunus da ke kusa da shi ba zai iya gano ya kalleta ba ko a'a domin ta kasa kasa yake kallonsa irin na munafukai.
After sun gama ta bukaci fita sa Yunus ya nemi rage mata hanya a take Ahmad yai karaf ya hana shi, yana ta mamakin shisshigi irin nasa, after ta fice ya tabe baki ya tashi tsaye ya face daga kamfanin, office dinsa ya nufa yana kara jin bachin rai na kama shi, zaunawa yai saman kujerarsa ya rufe laptop dinsa sannan ya fito daga office din ya nufi gurin motarsa da sauri, so yake ko da za a sako da ruwan yana gida ko banza yau ai ranar birthday sa ne.
A hankali yake tukinsa, sai dai kamar yadda ya kusan zame masa ibada kallon gurin da mahaukacin nan yake zama a kullum saboda abincin da Halimatu take ba shi yasa shi kallo a yau, yana tunani a yau kam ba zata tsaya ba tun da ta fita tana sauri kuma gashi garin har ruwa ya fara sauka, to his surprise sai ya hangota a gurin tare da shi, at first ya dauka ko wani abu ne mai kama da wasa daga baya ya fahimci kokuwa ce suke wanda be san dalilinta ba.
“Ashe dai itama bata da hankali, daman can ba tai kama da masu hankalin ba”
Ya furta sannan dan karawa motarsa wuta, kamin ya sake kallonsu da kyau ya fahimci dai fada suke, sai kawai ya faka yana ta kallon yadda mahaukacin ya kai mata duka kamin ya hango mahaukacin ya makureta har tana neman taimako. Cigaba yai da kallonsu, har sai da ya fahimci da gaske mahaukacin kasheta zai yi sannan yai unkurin bude motar, a take wata zuciyar ta hana shi, then ya fara tunani ai shi human being ne not like her, ba zai iya kallo ayi kissan kai ba. Cikin sauri ya fita daga motar ya nufi i da suke ya fara dukan mahaukacin ta baya har Halimatu ta samu sa'ar kubuce a hannunsa ta ranta a na kare sai fadan ya dawo tsakaninsu da mahaukacin shi da mahaukacin aka rasa mai hankali kowane kai wa wani duka yake, a cikin rashin sa'a mahaukacin ya naushi idon Ahmad ai take ya ji kalar garin ta canja, be san lokacin da wani karfin ya zo masa ba ya saka kafafuwansa ya buge Kafafuwan mahaukacin ya fadi kasa, a take Ahmad ya ranta a ciki na kare yana dafe da ido daya ya nufi motarsa a rikice ya bude motarsa ya shiga saboda wani azababben zugi da idon ke masa, @360 ya fisgi motar da ido daya da yake gani da shi.
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
4️⃣2️⃣
Da hannu daya yake tuka motar yayinda dayan hannunsa yake dafe da idonsa, wani zafin bala'i idon yake masa ga ruwan da ake kama da bakin kwarya, har baya iya gani da kyau saboda karfinsu.
A dole ya faka motarsa gafen titi, slowly ya dauke hannunsa daga idon da ke masa wani mugun zugi, ji yai idaniyar ta cika da abu mai kauri shi ba hawaye ba kuma ba ya san jini ne har sai da ya duba hannunsa. Jini a ciki kuma shine yake cika masa idon har baya gani da idon daya.
Lumshe idanuwan yai duka biyu yana sauraren yadda zugin yake shigar masa har cikin kansa, a rufe da idon ya saka hannun aljihu ya dauko wayarsa sai a lokacin yai kokarin bude idon daya yana duba iPhone dinsa wacce ta gama daukewa dip, sakamakon ruwan da ta sha, ba wayar kadai ba tufafin jikinsa ma sun gama jika seat dinsa balle kuma wayarsa.
Iskar bakinsa ya bushar yanzu be san yadda zai yi ya kira Doc Nura ba balle yaji idan ma yana gari ko yana asibitin ko gida, daman can a tsarinsa be yarda wani likitan ya duba shi ba sai family doc su, domin ya yarda da aikinsa hundred percent.
“Ba ma ita ce mahaukaciyar ba ni ne mahaukacin, taya zan shigar mata fada? Fadan ma da mahaukaci dan'uwanta? Matar da ta kashe min yarinyar? What's is wrong with me?”
Ya fada yana jin haushin abunda ya aika..
“Bata ma tsaya ta dubani ba fa sai kawai ta gudu, idan ma kashe ni zai yi ita dai ta tsira, mahaukaciyar banza i hate her”
Ya sake fada cikin fusata yana cizon bakinsa. A gurin ya tsaya har sai da ruwan suka dauke gaba daya sannan ya karasa tukin zuwa gida kamin ya isa har wani jiri yake ji cikin kansa.
“Ai I'm human being be kamata ina gani ayi kisan kai ba, shiyasa na taimake ta, amman yanzu na gano matar nan bakincikina take so take ta illatani bayan ta kashe min ya, be m kamata na barta tana aiki a kamfani na ba ai”
Shi kadai yake ta magana da kansa har ya faka motarsa a harabar gidan, yana kokarin bude motar ya fita ya tambayi kansa.
“Ko ma miya kai ni fada da mahaukaci? Da mahaukaci da mahaukaciya suna fada ni mai hankali miya kai ni ciki?”
After ya fito daga motar ya bawa kansa amsa.
“Kaddara.... ”
Part dinsa ya wuce, yana shiga ya fara ziyartar bandakin ya wanke fuskarsa, ya saka tissue yana tare jinin a hankali sannan ya dawo dakinsa ya dauko dayar wayarsa da ke gida yana kokarin kiran Doc Nura.
“Hasara nawa ga saka ni a yau? Ta saka na jika tufafina ga idona daya ga phone dina.....”
Wani irin haushinta ne ya kara cika msa zuciya. Sai da ya tabbatar Doc Nura na aibitin sannan ya canj tufafin jikinsa ya dauko key din wata motar ya fice ba tare da ya leka part din Hajiya ba, domin baya son ya tashi hankalinta.
A asibiti babu kalar dariyar da Doc Nura be msa ba.
“To kai yanzu miya kaika raba fada da mahaukaci? Ai gashi an bak tukuici”
“You make me hate her more”
“Wai wacece wannan?”
“Wata mahaukaciya ce mai ruwan masu hankali”
Ya hada fuska babu annuri can kuma yai murmushi.
“Ita ma fa taji wuya, ba da wasa ya moreta ba”
Dadi yaji tun da ita ma ta ji wuya, but maganar Allah shi yafi kowa shan wuya tunda shi be shi yaja mahaukacin ba.
Bayan Doc ya duba idon ya bashi maganin na sha da shafawa a idon ya kuma fada msa yadda zai kula da ido. After ya dawo gida ya kira shiga part dinsa ya kiran Yunus.
“Yu akwai wani mahaukaci da ke kusa da kamfanin mu, daga hannun dama gurin wani shagon kwano, za ka iya gane shi?”
Sai da Yunus yai tunani sosai sannan ya amsa masa da.
“Yes na gane shi kullum nn yke zama”
“Ka sa a dauke shi a kai shi gidan mahaukata”
“Why?”
“Why? Ya zan baka umarni ka tambayeni why?”
Ya amsa a fusace, kamar Yunus din ba abokinsa ba ne, saboda yau yana cikin zafin kai. Bayan ya kashe wayar yaje gaban madubi yan duba idon, idonsa daya yayi kwancin jini a ciki gaba daya gefen idon ya kumbura, abunka da farin mutun har wani ja gurin yai.
“Ina zaman zamana ta ja min masifa.....”
Ya karasa maganar ta tari sai jini ya biyo baya, daman haka yake yanzu da ransa ya bace sai ya fada tarin jinin sai ciwon kirji.
Toilet ya nufa aman jini yai ba kadan ba, shi kanshi sai da abun ya dan tsorata shi, har yana zargin wata kila saboda ya sha ruwan sama ne abun ya kara hade masa, wanka yai sannan ya dawo dakinsa ya sha maganinsa ha kwanta.
Sai 4:21 ya farka, sallah ce abunda ya fara gabatarwa sannan ya duba idon nasa kamin ya nufi part din Hajiya. Tana ganinsa hankalinta yai mugun tashin musamman idon nasa wanda ta hango jan jini a ciki.
“Miya same ka Gwarzo?”
“Hadarin nan ne da ya taso ina kokarin shiga, mota sai kasa ya shigar min ido”
“Wannan ba kasa ba ne, hannu ne ga kwancin shi nan a idonka, kaga ni ko shiyasa bana son kana zuwa kana dadewa a waje, na sha fada maka da kun gama aiki ka rika dawowa gida, na san halinka da zuciya wata kila kaje ka bugu wani ya rama”
Hannu ya kama yana kokarin zaunawa da murmushi a fuskarsa.
“Haba Hajiya ai na girmi wannan, Wallahi kaddara ce kawai amman In-Sha-Allah ba zai sake faruwa ba”
“Bari na kira Doc Nura”
“Naje gurinsa ya bani magani ya duba idon”
Sam bata yarda ba har sai da ta kira shi da kanta tai magana da shi ya tabbtar mata da cewar ya dubashi sannan hankalinta ya kwanta.
“And daga yau ba zaka je aiki ba sai nan da one week”
Da sauri ya kalli Hajiyarsa yana sakin baki.
“Amman Hajiya kin san idan ba da ni ba wani abun ba zai yiyu ba”
“Doka ta ce wannan”
Ta fada fuskarta babu alamun wasa.
“Yaro ba san ciwon kansa ba, sai idan ana nuna maka abu kace kai ba yaro ba ne”
Rasa yai abunda zai ce mata, ba zai iya karya dokarta ba, kuma ba zai so fashin zuwa aiki ba, zai iya amfani da bakin gilashi ya rufe idonsa.
“Idan an yi magariba ka kwanta karka tashi sai an yi isha'i, zan dafa maka carrot da allayau da wake yanzu suma suna gyara ido”
A dolen dolensa ya amsa mata da okay, ta tashi ta shiga kitchen da zimmar dora masa girkin, shi kuma ya bita da kallo yana ta tunanin randa Hajiya zata yarda da cewar ya girma san ciwon kanshi.
HALIMATU POV.
A hankali na kalleshi, fuskarsa a hade take sam babu alamar wasa a umarninsa. Na sani ba lallai ne su yarda su canja min aiki ba, balle kuma har su yarda na rika saka wasu tufafin na dabam, Ahmad ba zai min wannan lamanin ba, ko a da balle a yanzu da ba san yadda na baro shi da karfi ba, ba laifi ya nuna kulawarsa tun da har ya taimaka min ba dan shi ba wata kila da yanzu na zama gawa, domin ba kadan Kabir ya makure ni ba.
Tunanin nake ta yi ni kadai ina shafa wuyana da har yanzu ciwon yake min.
“Amman za su iya cewa ba za su yarda na daina saka kayan ba”
“Sai ki daina aikin”
“Idan na daina aikin da me zan kula da kaina? Kamin na samu wani aikin abu mai wahala, kuma ka san bana da mai taimakona a yanzu sai Allah”
“To sai ki samu miji ki yi aure, ki rike Namra da Amal Aiman da Adnan kuma ki maidasu gurin Babansu.....”
Kai tsaye ya fada min maganar nan ba tare da ya kalleni ba. Wani irin kallon mamaki nai masa, ban yarda daga bakinsa kalaman nan suke fitowa ba, sam ban yarda Abdallah na ne ba, taya zai min wannan maganar me yake nufi da ni? To sai ki fitar da miji ki yi aure...... Kalmarsa na ta maimaita min kanta a cikin kaina.
“Kalmar ka ta min nauyi Abdallah, tana kokarin rikecewa, ban gane komai ba”
Ajiyar zuciya ya sauke ba tareda ya kalleni ba ya ce.
“Har gobe ina sonki, har gobe ina kishinki, har gobe ina tausayinki ki saka wannan a zuciyarki, kuma wannan kaddara ta ce zan mutu da sonki.... Na sani kuskure ne na so matar yayana bayan ya rabu da ita, sai dai sonki ya dade a zuciyata tun kamin ki auri dan uwana, kin riga kin lalata komai Halima, Hajiya ta min katanga tsakanina da ke....”
“Har da aurena....?”
Na tambaya murya na rawa, idanuwana kuma suka soma aikinsu.
“Taya kike tunanin samun farinciki a auren da uwa bata so? Dan'uwa baya so? Da wane irin ido za mu kalli al'ummarmu? Zan mutu da kaunarki Halimatu wannan ita ce kaddarata.....”
Ban taba jin abu marar dadi irin na yau ba, Abdallah be taba fada min wata bakar magana ba irin yau, gaba daya sai na nemi farincikina da kuzarina na rasa, wani irin bakinciki ya cika min zuciya.
“Sauke ni a nan”
Na fada ina kawarda fuskata, ba musu ya faka motarsa gefen titi ni kuma na bude na fita, ina jikin babu kwari kamar na fadi. Key yai ma motarsa ya kara gaba ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye.
“Shiyasa ya daina kula ni? Miyasa na auri Abdulhamid tun farko? Miyasa tunani be bani Abdallah ba sai a yanzu? Miyasa kaddara take min haka? A lokacin da ya kamata ba jidadi sai wata matsalar ta saka ni a gaban? Gaba daya ban san jindadi a rayuwata ba....”
Na fada ina fashewa da kuka, ruwa na ta dukan kaina. Kasa na fara tafiya daman tazarar dake tsakanin inda ya sauke ni da gidanmu babu nisa sosai, tun ina tafiya ruwan na sauka da karfi har suka rage, ban daina tunani da kuka ba. Ruwan da ke saukowa ya taimaka min da ya hana a gane ina hawaye saboda yana dukan kaina. A lokacin da na shiga gida kowa yana daki ya fake, kai tsaye na nufi dakin Mama, ban saba shiga ba sallama ba amma a yau haka na shiga babu sallama mana ma iya kallon wake falon waye baya ciki.
Dakin Mama na shiga na cire tufafin jikina na dauki zanenta na daura, tana ta kallona da yadda nake motsa jiki babu kuzari.
“Lafiya kike yau kuwa?”
“Nima ban sani ba, ko lafiya nake ko ba lafiya nake ba”
Na amsa mata ina hawaye.
“Miya faru”
Juyowa nai na kalleta.
“Mama