Showing 36001 words to 39000 words out of 217237 words
zuwa aikina, kanwata Husna ta shigo wai na zo falon Mama ana kirana, ta gwarin guiwata na nufi falon Mama ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata, na shiga falon da rabon ido dan ganin mai kirana sai naga Mama ce kadai a falon hannunta rike da farar leda mai rubutu da zanen wayoyi a jiki.
“Mama ke kike kirana?”
“Aa Abdulhamid ne yana waje saka hijabinki ki masa godiya waya ya kawo yace a baki”
Ta amsa min cikin rashin jindadi da walwala. Dakinta na shiga na dauko hijabi na nufi kofar gidan. Sai na same shi cikin farar motarsa zaune yana danna wayarsa, farin gilashin motar na kwankwasa da zimmar ya bude min na gaishe shi kuma nai masa godiya sai na ga ya miko hannunsa daga can cikin motar ya bude min motar da alama so yake na shiga ciki na zauna. Haka kuwa akai na shiga uncomfortable na zauna sannan na mika masa gaisuwa be amsa min ba kuma be kalleshi ba har lokacin taba wayarsa yake.
“Yau ba zaki je aiki ba ne?”
“Zanje ina cikin ne aka ce kana kirana”
Sai a lokacin ya dago ya kalleshi a natse. To je ki karasa shirinki sai na kai ki. Kallonsa nai har na bude baki na ce masa a a sai kuma na tuna da abunda ya faru da ni a lokacin da nai gardama da Abdallah ban sani ba shi ma ko yana da kohin kar ya min na kasa samun abun hawa.
“To by the way na ga waya na gode sosai”
“No no no never mind je ki shirya kawai”
Ya fada yana dauke idonsa daga barin kallona, ni kuma na fita daga motar na shiga cikin gidan na karasa shirina sannan na shiga falon Mama dan mata sallama kuma n karbi wayar da har yanzu bana jin murnar siya min ita da yai. Wani kallo tuhuma Mama tai min sai duk na ji babu dadi a take shikan shikan rashin natsuwa suka bayyana a jikina da kuma fuskata.
“Ina kyautata zaton Abdulhamid be san Abdallah na zuwa gidan nan ba, kamar yadda yau din ma nake kyautata zaton Abdallah be san Abdulhamid ya zo ba, sai dai ke kin sani kuma ina tunanin kin san daidai da rashinsa, na dade da fahimtar cewar Abdallah yana son ki ko dan saboda kulawar da yake nunawa yaran nan, sai dai abunda ban sani ba kuma nake son sani a yanzu shi ma Abdulhamid son ki yake yi?”
I find it so difficult na amsa mata, ni kaina a yanzu ban sani ba iyakar abunda na sani Abdallah na so ko be fada min ba ya nuna min balle kuma ya fada min tun a lokacin da igiyar auren Aminu take kaina, ba zan iya shaidar abunda ya kawo Abdulhamid a yau ba, domin bana da tabbaci yana so na har yanzu kamar yadda zuciyata ya kasa goge shi a raina, ko kuwa dai tausayine kawai a tsakaninmu.
“Dukansu yan'uwna junane Halimatu kin sani, bayan yan'uwanta ta jini ma su tagwaye ni a ciki daya suka fito a rana daya kuma a mahaifa daya, mace daya ta raine su uba daya ya haife su, karki aikata abunda zai zame mana matsala ni da mahaifinki domin uwar data haifi mahaifinki ita ce ta haifi mahaifin Abdallah, mahaifin Abdallah da mahaifinki uwa daya uba daya suke karki lalata alaka Halimatu”
“Ban kira Abdallah na ce ya zo nan, zuwan Abdulhamid a yau ma bana da masaniya sai da na ganshi”
“Ba shi nake kokarin fahimtar da ke ba, ki sallami daya daga cikinsu saboda gudun abunda zai iya faruwa a gobenki, idan kuma dukansu ba ki ra'ayinsu to ki sallame su duka shi ya fi alheri Allah ya tsare a dawo lafiya”
Ya miko min ledar sannan ta mike tsaye ta fice ta bar a falon tsaye, ji nai kamar a san saka gatari an sare duk wata gaba ta kuzari da ke jikina. Kamar wata marar lakka haka na fito daga cikin gidan na nufi inda motarsa take na bude na shiga shi kuma ya tashi motar muka hau hanya.
“Ban jajanta miki kan abunda ya faru ba, na yi hakan ne saboda na baki lokaci ki huce bacin ranki, kuma bana son wata magana ta shiga tsakanina da ke a lokacin da kike idda, ko da ko gaisuwa ce, amman yanzu ina jin I'm free to name what ever i want daga gareki saboda kina da yanci”
Ban ce masa komai ba ina ta kokarin maida hankalina gurin titi amman na kasa, magaganun Mama sun tsaya min a kai.
“Ban jidadin abunda ya faru ba, Aminu kuma be yi miki hallaci ba amman mai hakuri yana tare da nasara, kuma kansa yai ma na san wata rana zai yi nadama ya gane cewar yayi kuskure a lokacin da ke din kin masa nisa”
Still ban ce masa kuma ba, hakan kuma be hana shi cigaba da magana ba.
“Jarabawa ce ta rayuwa, you know wani lokacin Allah yana jarraba bayinsa da abubuwa daban dabam, kamar yadda ya jarrabe ki da miji kamar Aminu ni kuma ya jarabe ni da cutar da na kasa samun maganinta har yanzu, wanda hakan yasa har bana son kawo tunanin aure a rayuwata....”
Juyowa nai na kalleshi a take zuciyata ta cika da tausayinsa.
“A da na sadakar na cire rai daga samun lafiya, kuma na aje duk wani abu na neman magani, amman daga lokacin da na ji cewar Aminu ya sake ki sai na nemi duk wannan abun na rasa, na ji cewar a yanzu ya dace na nemi magani kuma na nemi aurenki ko da ba za ki so ni ba, ba dan komai ba sai dan na faranta miki kuma na cika burina a kanki, ban sani ba ko akwai soyayyar Abdulhamid a zuciyar Halimatu ko a a, idan ma babu zan yi kokarin samawa idan kuma akwai sai na kafafata na ingantata”
Ya karasa daidai lokacin da ya faka motarsa a ma'aikatarmu sai ya zauna daidai yana dubana da fuskarsa ta tausayi.
“Na san za ki mamaki jin irin wannan maganar daga bakina kai tsaye kuma a karon farko da na ziyarce ki, daman abunda na ke son mu tattauna kenan a jiya, saboda ina son nai mata sha daya ne idan ma hadiye zuciya zan yi na mutu na san makomata idan kuma dama za ki ba ni nan ma na san makomata, ni dai har gobe ina son ki Halimatu kuma ina alakanta abunda Aminu yai miki da rashin aurenki da nai ta hanyar kin yarda da shawararki ta cewar na aureki na cigaba da neman magani za ki yi hakuri da ni a haka, ko kuma ki jira ni na nemi magani amman duka na ki yarda, na san da cewar Allah ta rubuto hakan zai faru amman komai yana da sila....”
Jimmm nai na dan wasu mintuna sannan na ya cigaba.
“Wata kila zuciyarki ta raya miki cewar na cika son kai a yanzu ko? Kina da gaskiya ba ko wace mace ce zata auri namiji irina ba, shiyasa ban gwada neman kowa ba sai ke ban taba saka son wata mace a raina ba sai ke kuma har gobe ke ce a raina Halimatu, zan iya baki damar yin shawara matukar kika ji za ki iya aurena a haka, ko kuma ki jira har na samu lafiya zan fi kowa farinciki, idan kuma kika ji ba za ki iya ba nan ma ba zan zarge ki ba.... ”
“Zan shiga office na gode”
Shine kawai abunda na fada na share hawayen da suka fara min zuba tun a lokacin daya fara maganar.......
Anya Halimatu zata iya zabe tsakanin dan'uwa da dan'uwa?
Anya zata iya zaba tsakanin mutuwa da rayuwa? Domin auren namiji irin Abdulhamid mutuwa da rayuwa ne.
A ganinku waya dace ta zaba?
Ina labarin Aminu ne?
Ko ya Kabir yake?
Shi kuma Abdallah haka yake da an bata masa rai sai kohi 🤣🤔
#TeamAminu
#TeamAbdulhami
#TeamAbdallah
#TeamHalimatu
#ZawarcinHalimatu
#Gobena
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
1️⃣4️⃣
A bakin gate din gidan ya tsaya da kekan Namra da ke gaban keken ta sauka, sannan Barra ta sauka suka nufi yar karamar kofar gate din sukai knocked mai gadin ya bude musu suka shiga sannan ya budewa Ahmad gate din gaba daya ya shiga da keken ciki. Katon gida ne plate mai dauke da shuke shuke gaban gidan kamar bayansa yake domin za kai tai kallon fuskar gidan amman ka gagara gane kofar shiga har sai idan an nuna kama ka, daga fentin kofar har fentin gidan har mayan motocin da ke harabar gidan duka farare ne tasss, irin farincikin nan mai burgewa da dare da rana kuma ya kawata maka ido idan kuma ya hadu da hasken rana sai ka dauka ba a Nigeria kake ba.
Bangaren da aka faka motocin ya nufa ya sauka daga kan keken ya kai hannunsa ya bude gareji ya saka keken ciki sannan ya maida garejin ya rufe, sannan ya soma tafiya cikin wani irin taku da ba na sarauta ba kuma bana kasaita ko ci da kai ba, sai dai duk wanda zai kalli yadda yake dora kafarsa a kasa zai yi tsammanin tausayin kasar yake ko kyamarta, wata kila ma a iya fassarashi da mai nuna isa da dagawa.
Zagayawa yai can baya inda ya sama kamar dabam da gidan kofarsa ma a can baya take, tun kan ya karasa ya saka hannunsa ya kwance daurin jacket din dake kugunsa, sannan ya kai hannunsa ya tura kofar ya shiga. Sanyin ac ne da hasken garin gulub tare da dadadden kamshi suka fara masa lale marhabun, katuwar plasma kuma na ta aikinta, remote ne farkon abunda ya fara dauka ya canja channel din daga Al Jazeera zuwa Tvc news. Sannan ya nufi hanyar dakinsayana shiga ya rana jikinsa da tufafin da ke jikin nasa ya daura tawul, a take farin fatar jikinsa da siffarsa ta zati ta bayyana, cikin wani irin ya na saka su a washing machine sannan ya shiga ya bawa jikinsa hakkinsa sai da ya tabbatar komai na jikinsaya wanku sannan ya fito ya shirya cikin wata farar shadda mai kyau da haske zanen jikin shaddar ma abun kallo ne balle kuma aikin da ke jikinta.
Wani tsadden turare ya dauko ya saka bayan ya saka wani a cikin jikinsa da vest din da zai saka. Murmushi yai yana kallon kansa a madubi, shi kansa ya san yayi kyau balle kuma da ya dora hular da ta dace da shaddar. Sajen fuskarsa ya kwanta gwanin sha'awa har wani shining yake.
Wallet dinsa ta fara ziyartar aljihunsa kamin makulin mota da sababin kudade su biyo baya, sannan ya dauki agogon hannunsa ya saka, for the second time ya sake duba kansa agaban katon madubin da ke dakin madubi da mutun zai iya ganin har kasansa da takalminsa. Cike da annshuwa ya fito daga dakin zuwa falonsa sai ya duba agogon hannunsa sannan ya zauna a saman manyan cushion din ya kalli labarai na yan mutuna kamar mai jiran ciron lokaci domin tsadadden agogon hannunsa na nuna 9pm ya mike tsaye ba tare da ya kashe tv ba ya fice daga falon.
Bangaren mahaifiyarsa ya nufa wacce ta zame masa dole a duk lokacin da zai fita ko da zuwa nan da kofar gida ne sai ya sanar mata, hakan ya saka cousins dinsa da yan'uwansa and friends suke kiransa da Mommy's Boy domin har time take ba shi na fita da dawowa matukar ba aiki zaije ba ko wani lalurar na dabam wanda ita ma kanta ta san mai muhimmanci ne, duk da kasancewarsa ya girma har ya haifi ya mace yar shekara tara bata daina masa haka ba, shi kansa ya saba abun ya bi masa jiki idan ya fita be sanar da ita ba sai ya ji kamar ya aikata wani babban zunubi, ita ce abokiyar shawararsa kuma abokiyarsa domin komai zai yi sai ya sanar mata ko da ko abun be taka kara ya karya ba, hakan yasa take sanin ko wane sirrin na zamantakewar aurensu, domin a cikin dabi'un daya sabunta da su a gurinta ko dankwali ya siyawa matarsa sai ya siya mata kuma sai ya fada mata tun kamin ya siya din, idan kuma ya siyo zai kawo mata ta fara gani ta zaba ko ta canja masa tukuna ya kaiwa matarsa.
Ya shiga falon da fuskarsa da annuri kamar sabon ango, daman can yana da irin fuskar nan ta samarin aljanna wadanda zaka gansu kullum fuskarsu kamar suna murmushi ko da kuwa ba murmushin sukai ba ga haske fuska da haiba, ga natsuwa da kwarji kamar wani Zaki.
Hakimce take saman kujera sanye da wata holland yar ubansu wuyanta ya ji zinari kamar yadda hannunta ke amsa amo a ko wane motsi da tai, kallo daya za kai mata ka karanci sifofin da ke fuskar mahaifiyar sune a fuskar dan, kamanni na hanci baki da kuma ido a siffa da sura da hallita irin ta da'namiji kuma Ahmad Gwarzo kamar yadda mahaifiyarsa take kiransa.
“Momy barka da dare.... ”
Ta juyo cike da isa tana kallonsa, irin kallon nan na farinciki da kaunar uwa ta ga danta.
“Barka da Gwarzo irin wannan shiri haka ina zuwa?”
“Zance zanje mana Mom”
A yayinda kalmar zancen ta dira a dodon kunnenta sai ta za me mata kamar wata mummunar kalamar marar dadin jin, annushuwa da ke fuskarta ta sai ta gushe murmushin kamar na dole. Dauke kai tai kamar ba ita ya bawa amsar ba ta maida dubanta gurin plasma.
“Bari na je kai na saba alkawari tace na zo 9”
Ya fada yana shirin juya daman can tun da ya shigo be zauna ba.
“Karka wuce 10pm”
Ta fada bayan ta kalli agogon zinarin da ke jikinta fuskarta babu alamun wasa. Juyowa yai kamar zai ce wani abu sai kuma yai murmushi ya juya ya fice. Ita kuma ta bishi da kallo tana jin kamar ta hana shi tafiya zancen, Hajiya Uwani irin iyayen nan ne da ke kishin matan yayansu musamman Gwarzo da bata hada shi da kowa ba a duniya, ba tun ba ta saba kashe masa aure ta kan saka shi ya saki matarsa idan zamanta a gidan be mata ba ko ma ta sake ta da kanta wani lokaci, wasu matan ma da kansu suke neman fita idan suka ga matsuwar ta musu yawa, ba dan kuma babu arzikin ki akwai shi har na zubarwa amman haka take bi ta takurwa matan da Ahmad Garba Gwarzo yake aurowa har sai ta fitar da su a gidan, Hajiya Uwani na da wani irin hali da ba san mutanen Kano da shi ko ma na ce mutanen Gwarzo domin daga ida har mijinta yan asalin karamar hukumar Gwarzo ne, wannan dalilin ya saka daga abokan Ahmad har ita kanta Momy da duka familynsu suke kiran dan nata da Gwarzo.
Juwuriyya ce mace ta tara da Ahmad ya aura kuma ita ce mace da ta jajirce a wajen zama da shi har tai nasarar haifa masa ya mace wato Namra, duk kuwa da irin kin son haihuwar da Hajiya Uwani take yi, ta jure duk wani cin zarafi da muguwa daga uwar mijinta saboda kawai ta zauna da Ahmad, kuma ta zauna da shi ra rayu da shi na tsawon shekara biyar kamin tai hadarin mota ta rasu. Hajiya uwa bata yarda danta ya cire kudi mai yawa da sunan yi ma mace hidima idan ma yayi ta kan rage tace ta yi yawa, haka ta ke juya duk matan da Ahmad take aure kamar waina tana kishin matan Ahmad sosai.
Latest Benz ya shiga White color daman duk motocin da suke gidan farare ne, sai dai kawai sunanyensu da kudinsu su banbanta, tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate ya fisge motar kamar domin shi kawai akai titin GRA ring road.
in time ya isa kofar gidan Alhaji Yunusa Dan-Gaske, kamin ya danna horn ya ka kai hannunsa ya dauki iPhone dinsa da ke cikin motar ya kira Zainab.
“Hello Ina kofar gidan”
Ya fada kamar wani dan sarki sannan ya danna horn aka bude masa gate din ya kunna kai a harabar gidan..
HALIMATU POV.
*Bayan sati biyu...*
Sati daya nai ina raya ko wane dare da sallah da salatin Annabi, na mikawa Allah zabina a tsakanin zama a gida nan ba tare da aure ba da kuma yin auren, domin ni ba dan Abdulhamid ba da ban kawo maganar aure a kusa ba, a da na yi planning akan na cigaba da aikina na rike yayana har zuwa wani lokacin domin ban shirya fuskantar wani kalulen zaman aure ba a yanzu saboda wahalar da na sha a gidan Aminu, sai dai yadda Mama da Inna suka tsaya kai ta fata wajen ganin na cire wannan burin a raina yasa na sassautawa kaina, ga kuma rokon Allah da nai sai ya saka min son auren a raina fiye da lokacin da nakr budurwa ma. Na roki Allah ya zaba min a tsakanin yin auren a yanzu da kuma hakura da auren har na wani lokaci, amman ban roki Allah ya zaba min a tsakanin yan uwa guda biyu ba wato Abdallah da Abdulhamid, a iya ganina da fahimta Abdulhamid ya fi Abdallah cancantar aure a yanzu domin shi be taba auren ba gaba daya a rayuwarsa, kuma ni ya so tun a lokacin da nake budurwa yanzu kuma da auren ya mutu ya dawo min. Ko ba komai ya hade kwadayinsa na furta min kalmar so ko cancantar zama da Aminu be taba fadin wata mummanar kalma akan Aminu ba, duk kuwa da irin sanin da yai na irin zamantakewar auren da muke da halayensa, be taba daga waya ya kira ya fada min wani abun marar dadin ji ba, idan har ya kirani sai idan wani babbab dalilin ne ko kuma idan mun gadu da shi a gida. Tsabanin Abdallah da yake yawan fada min abubuwan da Aminu yake aikatawa a waje bayan yabon surata da yake da nuna yana sona tun daga lokacin da ya dawo daga kasarsa ya saka