Showing 117001 words to 120000 words out of 217237 words

Chapter 40 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

194

fata da ganin kamar wata rana zaka daina, da nai haihuwa ta biyu sai na fara karaya, daga lokacin ne na dauka cewar aurenka yana cikin mummunar kaddarata, domin zama da mazinacin namiji ba abu ne mai sauki ba, kullum ina cikin fargaba, kullum ina cikin addu'a, kamin wani lokaci sai alakar auratayyarmu ta canja, na kuma maka kamar bakin maciji, idan nai kwaliya ina jiran ka dawo ka yaba min, ba zaka dawo ba sai tsakiyar dare, a maimakon idan ka kalleni kace na yi kyau sai ka fada min cewar siraran mata suna can suna can waje suna jiranka, a gabana kake yabon wasu mata a wayarka ko a tv saboda kawai na ji zafi, bayan ka san a lokacin da ka aureni ba haka nake ba, kyau jikina na daya daga cikin abunda ya dauki hankalinka har ka zo gurina ka nuna kana son aurena, a gidanka halitta ta canja Aminu saboda yayan da na haifa maka yasa jikina ya bude, halitta ta tashi daga budurwa zuwa matar aure, na bar iyayena na bar yan'uwa da kowa nawa na koma gidanka cikin yan'uwana da zama, amaimakon ka tausaya min ka mutunta ni sai na zama abar wulakantawa, kai ka yi min mahaifiyarka tai min yan'uwanka su yi min, ka dinga fada kana cewa na haifa maka yara da yawa zan tsofar da kai, hakan yasa na fara tunanin planning, kace na ciki kiba kai ba haka kake son mace ba ka fi son siririya, babu irin kudin da ban kashe ba akan nai slimming amman ban samu sa'a ba duka ka san saboda me? Saboda na faranta maka saboda na gyara rayuwar aurena, wani lokacin idan na unkura sai na ji kamar ba zan iya fita na bar yayana ba, hakan yasa na yarda aurenka yana cikin kaddarata, wasu akan jarabesu da kiyayyar uwar miji, ko yan'uwansa, wasu kishiya wasu mijin wasu yaya wasu rashin abinci wasu rashin lafiya, to sai aka jarrabe ni da abubuwada yawa, da gangan kake kin siyo mana abu mai dadi ko na marmari wanda za mu ci mu jidadi saboda kawai ka musgun min, ka dauki karan tsana ka dora min saboda kawai na aureka na haifa maka a yaya, a ranar da na tambaye ka 2k ka hana ni a ranar na ga alert dinka na turawa wata 30k+ ka tuna....?”

Tun da na fara naganar yake hawaye har na kai aya, be iya bani amsar tambayar ba ko kallona sai ya kasa yi. Hannu na saka na share hawayena ba tare da sun bar zuba ba.

“A kowa ce rayuwar aure akwai kalubale, na sani shiyasa na jure zama da kai a wacan lokacin. Amman wani abun mamaki a lokacin da kake ki na kaka nuna min kiyayya a lokacin ne Abdallah ya nuna yana so na, bashi kadai ba a duk inda na shiga maza basa dauke ido a kaina amman nawa mijin....”

Kasa karawa nai saboda kukan da ya ci karfina.


“Na yi miki abubuwa da yawa Halimatu, a lokacin ina jin kamar ke din matsala ce a rayuwata, ban gane muhimmancin ki ba sai bayan na rasu da ke, duk abunda zan fada miki a yanzu na san ba yarda za ki yi ba, amman Wallahi zuciyata babu wanda take mamari take kauna sai ke, na aikata babban kuskure na rabu da nai da ke, amman ko a wacan lokacin ina son ki Halima, kawai dai sherin zuciya ne da na shaidan. Amman a yanzu na canja Wallahi duk wani hali marar kyau nawa yanzu babu shi..... ”

Sai a lokacin ya kalleni ya sauko daga zaunen da yake ya risina gabana.

“Ki dubi girman Allah ki yafe min, ki duba yayanmu ko dan su ki yafe min, ni da Hajiya duka mun yi nadama, Wallahi babu daren da bana kukan rashinki Halima....”

“Kana son na yafe maka?”

Yayi saurin gyada min kai jikinsa har rawa yake kamar ba shi ba.

“To ka maka dan'uwanka a kotu, ka tsaya da kafafuwanka har sai ka kwatowa yarka yancinta......”

Ina fadar hakan na mike tsaye ina share hawaye na kauce daga gabansa na fara tafiya....

“Idan nai hakan zaki yafe min ki dawo ki zauna da ni da yayana?”

Juyowa nai na kalleshi.

“Wata kila dai zan iya yafe maka na goge sunanka daga bakar takardar da na rubuta shi, amman zancen zama aure a tsakanin ni da kai wannan har abada ne, sai dai wata mai sunana amman ba ni ba....”

Ban tsaya jiran abunda zai fito daga bakinsa ba na nufi dakin da su Amal suke, har a lokacin Mama da Hajiyarsa suna dakin a zaune, kusa da Amal na karasa na zauna ina tambayar Aisha wayata.

“Yaya Abdallah ya zo nan”

“Eh mun gaisa da shi”

Na fada ina yin kasa da idona saboda jan da sukai.

“Halimatu ayi hakuri da rayuwa, mun san mun yi kuskure mun laifi amman a dubi girman Allah a yafe mana wallahi yanzu Aminu yayi nadama
......”

Kaina na daga na kalli Hajiyar Aminu wacce ke maganar murya kasa kasa kamar za tai kuka, sai na kalli Mama nace.

“A nan za ki kwana? Ko ni zan tsaya na kula da ita?”

Sai Hajiyar Aminu tai karaf tace.

“A a ni zan kwana nan kuje ku hutarwarku”

Jin hakan yasa na mike tsaye nai musu sallama na fice. A daren ranar kasa bachi nai saboda tunanin rayuwar da nai a gidan Aminu, tabbas na fuskanci kalubale wanda ba ko wace mace ce zata iya jurewa ba. Da asuba bayan na yi sallah na dora da karatun qur'ane, misalin shida da yan mintuna na sha ruwa na koma bachi, bayan begen Abdallah da zuciyata ta kwanta da shi har da mafarkinsa sai da nai a bachin nan nawa na safe. Kiran waya ne ya farkar da ni duk kuwa da kasancewar bakuwar number ce hakan be hana ni dauka ba. Tun da sallamar matar ta daki dodon kunnena na gane mahaifiyar Aminu ce, ita ta fara miko min gaisuwa ni kuma na amsa mata da ina gajiya. Ta fada min wai kar a dafa komai tasa an kawo musu daga gida, ni dai da to kawai na amsa mata na aje wayar.
Misalin tara na shirya na cikin bakar abaya kamar yadda na fi son sakata a duk tufafina na fita da zimmar idan na bar gidan Abdallah na je asibiti, so nake na tafi na bawa Abdallah hakuri kuma na fada masa labarin mutumen nan, and i got lucky na tarar ya shirya cikin kananan kaya na shirin zuwa office. And wani karin farincikin kuma shi ya bude min kofar da kansa yana rike da mug.

“Ina kwana?”

Na gaishe shi ina murmushi sai ya amsa min fuskarsa ba yaboba fallasa.

“Ya kai?”

“Zan iya shigowa magana nake son yin da kai.....”

Daga can bayansa na jiyo muryar Suwaiba tana da fada.

“To wannan abun ya wuce gona da iri, ya zama iskanci da cin fuska, kuma Wallahi ba zan dauka ba ke bakya ma jin munya bibiyar kanen tsohon mijinki... Kai tirr Halima kin yi abun kunya.... ”

Da muryar da na san zata iya jiiyoni na ke fada masa cewar.

“Ka ce tai hakuri na san babu dadi, amman babu abunda zai yanke alaka a tsakaninmu...”

“Muje waje mu yi maganar”

Shine abunda ya fito bakinsa, bakin nasa nake ta kallo kamin nai backwards na fita daga falon, wanda hakan ya bashi damar fitowa ya janyo kofar ya rufe.

“Ya kai....”

Yan yatsuna na fara murzawa sai hawaye.

“Daman na zo ne na baka hakuri akan abunda ya faru..... ”

“Ai na ce miki ya wuce ko? Ni ban rike ki da komai ba tun wacan karon na ce na yafe miki”

“Ba shi ba, akan duka abubuwa da nai maka”

“Na yafe miki Halimatu....”

Na kalleshi cike da kaunarsa wacce ta mamaye qalbina take taraiya da numfashina a yanzu, kai na gyada masa alamar gamzu.

“Kuma ina son ma fada maka wani abu....”

Sai yai hanzarin katseni.

“Bana son jin komai a yanzu pls”

Na sake gyada kan a karo na biyu ina hade yawuna.

“Amman magana ce mai muhimmanci akan maganar fyaden..... ”

“Oh Please haba dai bana son jin komai a yanzu”

“Shikenan, zan jira har zuwa lokacin da kake son ji, zan tafi amman dan Allah ka rika daukar wayata idan na kiraka kuma ka rika min reply idan ka ga sakona pls dan Allah”

Be ce min uffan ba har na juyo na fara tafiya, sai jin mutum nai a gafena yana takawa tare da ni.

“Dan Allah Halimatu ki cire komai a ranki, ki nemi aiki ko wata sana'a zaki iya tallafawa kanki ki rage damuwa kin ji? Ki cire kowa a ranki”

Tsayawa nai na kalleshi.

“Babu kowa a raina a yanzu, na cire komai na fahimci komai, babu wanda yake cikin raina Abdallah sai kai....”

Kallon mamaki yake min is like kamar be yarda da ni ba, juyawa yai ya kalli bayansa kamin ya nuna kansa. Ni kuwa na gyada masa kai cike da kuzari, can ya busar da iskar bakinsa.

“Ya rabb, wato baki daina shayeshayen nan da na ce ki daina ba ko?”

Na matso kusa da shi ina girgiza masa kai.

“Ban sha komai ba Wallahi a hayyacina nake”

“No Halima ba zata fadi haka a hayyacinta ba, ko dai damuwar nan ta dawo miki ko kuma kin koma ma shaye shayen”

“Wallahi ban sha komai ba”

Na fada ina masa magiya kamar zan fasa kuka.

“Shikenan ki tafi gida”

“Zan tafi duk abunda ka ce zan yi Abdallah”

Kamar umarninsa nake jira sai na juya da sauri na fice daga gidan.



AHMAD POV.

Glass cup ne a hannunsa yana kurba lemun a hankali, while idanuwansa suna watching plasma but his heart is one where else. Yana jin tsananin damuwa da kadaici a rashin Baby Namra da Matarsa da kuma mahaifinsa a rayuwarsa, sai dai his try be strong for him mother and his sister Siyama, domin su kadai suka rage masa a yanzu, he feels like da ace mahaifinsa yana raye da abubuwan sun masa sauki, kamar yadda da ace Baby Namra tana nan wata kila da be shiga damuwa haka ba damuwar da ke taba lafiyarsa ta taba rayuwarsa, he missed his wife his father his daughter. Be dawo daga duniyar tunanin Gobensa ba har sai da Hajiya ta soma magana da shi ayayinda take zaune saman sofa Siyama na kasa tana matsa mata kafafuwanta.

“Dazun Laraba ta kirani tace wai dan Allah a taimaka mata a dauki danta aiki a kamfaninku...”

A hankali ya juyo ya kalleta.

“Ai ba irin su muke dauka ba, yan boko, kuma kin san Attahiru ba wani boko yai mai zurfi ba, idan ma yayi ba zai wuce secondary school ba”

“To a duba masa dai haka nan tunda har ta roka sai a samu inda aka laba shi”

“Hajiya ki dai fada mata masu ilmi muke dauka saboda kamfanin a yanzu yana bukatar gogaggun.....”

Be marasa ba ya fara tari da sauri ya aje lemun hannunsa ya ciro handkerchief dinsa ya tari jinin da ya fito daga bakinsa. The white handkerchief din ya bawa Hajiya da Siyama damar ganin jinin da kyau, daga Hajiya har Siyama sai ka rasa wanene hankalinsa ya fi tashi...

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Mi zan gani haka?...”

Cewar Hajiya. Sai yai murmushi yana nuna mata cewar ba komai ba ne.

“Habo na ke yi, daji ne ya kamani da mura ba wani abu ba”

“Brother yaushe ka fara haka?”

Siyama ta tambaya hawaye na sauko mata, kallonta yai he know he can't hide anything from her domin karatun likita take kuma ta fi kowa sanin waye dan'uwanta.

“Can we talk private?”

Hajiya tai saurin amsawa tana girgiza kai tana kuka.

“No I'm your mother be kamata ka boye min komai ba, how do you expect your own mother to live after you death? How? Ku kadai kuka rage min daga kai sai wannan”

Ta nuna Siyama hannunta na rawa tana fashewa da kuka. Da sauri tashi yai ya koma gabata.

“Wallahi Hajiya ina shan magani kuma i believe zan ji sauki, duka duka ban hi sati da fara wannan tarin jinin ba, kuma na ga different doctors sun bani magani ina kan sha”

Siyama ce ta taso ta zo bayansa ta rumgume shi ta fashe da kuka.

“Please Brother we love you..... ”

He feel so hopeless, so emotional but a haka yake kokarin ganin ya zama very strong for them.
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


3️⃣9️⃣

Tun daga lokacin da Hajiya ta lura da halin da danta yake ciki bata sake yarda ta barshi ya zauna shi kadai ba indai yana gidan to yana falo tare da ita ko kuma yana harabar gidan suna fira, a ganinta sakewarsa zai taimaka masa fiye da kadaicewar da zai yi shi kadai yana tunani da saka kansa a damuwa.
  Kamar yadda ta saba masa after dinner suna zaune dinning ta dauko masa zancen aure domin shi ne abunda ta fi son taga yayi a yanzu ko zai rage masa damuwa har ma ya kawo masa farincikin samun wata haihuwar.

“Tun kwanan baya na maka magana akan aure kace zaka yi tunani ba ka ce min komai ba”

Ya kurba ruwan da ke gabansa kadan yana dan murmushi.

“Hajiya bana son zancen aure a yanzu”

“Saboda me? If saboda ni ne zaka iya zama a wajen gidan nan da matarka, and ba zan cilasta maka auren Ikilima ba, sai ka dauko budurwa da kake so ka aura”

“No ba wai Budurwa ko bazarawa ba, a halin yanzu mace bata gabana, ni ban ki na mutu a haka ba”

“Saboda me? Ni bana son ganin jikanka ne? Ku kadai Allah ya bani ai zan so ku yi aure ku yi juri'a da yawa ba kamar ni ba”

“Kawai ina ganin kamar idan na sake haihuwa rasata zan yi, ni kuma bana son abunda zai sake kasani a damuwa yanzu”

Hajiya ta yi murmushi.

“Baka da karfi zuciya sai kace ba namiji ba”

“Hajiya ba zaki san abunda nake ji ba, babu wanda zai shiga a irin halin da nake ciki a yanzu ace be samu kansa a damuwa ba”

“Yes dole na ka damu an sani ai, amman ka rika sassautawa rayuwarka, ita daman rayuwa tana tafe da kalubale kala kala, wani mai sauki wani mai wahala, sai dai duk halin da zaka shiha ka rika tunawa akwai wadanda suka fika shigarsa, idan arziki ne akwai wadanda suka fika, idan talauci ne da damuwa akwai wadanda suka wankeka suka shanye, kai mata kawai ka rasa sai ya kuma uba, akwai wata macen da na gani na ita tana da uwar a raye uba a raye dukan ya'yanta suna nan, amman kalubalen rayuwar da ta shiga ko kan akaifarta baka shiga ba, tun daga lokacin da na ji labarin matar nan abun ya tsaya min a rai”

“Indai har tana da kowa a raye mi zai saka ta a damuwa”

Har Hajiya ta bude baki ta fara labarta masa labarin Halimatu sai ga Siyama ta dauko fuskarta dauke da damuwa taja kujera ta zauna tana fadin.

“Ni kam i don't think zanje gaskiya”

Ahmad ya kalleta.

“Why? Saboda Baby bata nan? Mu da Hajiya za mu je kamar yadda muka saba a kowace shekara”

Yana fadar hakan ya mike tsaye ya bar dinning table din ya nufi hanyar da zata fitar da shi daga falon zuwa part dinsa. Hajiya ta kalli yarta cikin kwarin guiwa tace.

“Idan ba mu karfafa masa ya manta da komai ba, taya za mu taimaka masa wajen tunawa da abunda zai tsaya masa arai, a kowa ce shekara shi yake bada kaso 50 a cikin dari na wannan wasa da ake na children day, 25% daga kamfaninsa ne, 25% daga makarantarsa ne, sauran al'umma da kamfanonu su dauki 50%, taya mutun zai yi wannan aiki kuma ya kasa halarta taron da yake talarta duk shekara, saboda kawai yarsa ta rasu sai yace ba zai je ba”

“Nifa ban ce kar yaje ba”

“Shi kike nuna masa mana saboda babu Baby Namra sai ya kasa jurewa ya nunawa duniya yana cikin damuwar rashinta har yanzu, ya kamata ki karfafi dan'uwanki shiga irin abubuwan nan zai rage masa damuwa, ko a lokacin dq Baby take raye wannan children game din yana cikin abunda tafi so fiye da komai a rayuwarta,to yanzu dan bata da rai kike tunanin mahaifinta ba zai je ba?”

“No Hajiya ina jin ba dadi ne, kusan every year tana cikin mutanen da suke bada award wa wadanda sukai nasara, kuma tana zaune tare da shi....”

Ta karasa tana fashewa da kuka, Hajiya ta tashi daga kujerar da Siyama take zaune tana rarrashinta.

“Haka Allah yake ikonsa, haka na rasa mahaifinku a lokacin da nafi tsananin bukatarsa, amman da nai hakuri sai komai ya wuce, na koma ina farinciki kamar ba ni ba, idan muka yi hakuri sai ki ga Allah ya sauya mana da wani abun na daban”

Siyama ta rike hannun Hajiya tana ta kuka, haka take a duk lokacin data suna Baby, domin ta zame mata kamar kawa kusan abubuwa da yawa a tare suke duk kuwa da kasancewar ta girma sosai amman ta dauke ta kamar kawarta.


Magani ne first abunda ya fara sha a lokacin da ya shiga part dinsa sannan ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa, ya fi karfin 30m ruwan na dukan kansa sannan yai wanka ya fito daure da towel, zuwa yai gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa. Ba rama kadai ba har bakin rai mutuwar Baby Namra ta kara masa daman can dariya ba babinsa bace balle yanzu da yake jin abune mai wahala wani abun dariya ya kusance shi balle har yai ta, a nan ma ya dade yana kallon kansa kamin ya saka kayan bachi ya kwanta.

Da wuri ya farka saboda akwai abunda yake son yi a office, ko da ya fito part dinsa cikin shirin zuwa office ya fito ya shiga part din Hajiyarsa 7:13am. A kitchen ya sameta tana hada musu breakfast, tana da mai aikin amman ta fi ra'ayin girka musu da kanta musamman shi da tasan ba ko wane abincin yake ci ba, gashi da kyama komai tsaftar mace idan hankalinsa ba kwanta ba sai yace ba zai ci abunda ta dafa ba.

“Yau da wuri ka tashi gashi ban gama hadawa ba”

“Akwai abunda nake son yin a office

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login