Showing 63001 words to 66000 words out of 217237 words
masa haka. Baby Namra ce ta fito daga bedroom dinta tana masa oyoyo.
“Daddy sannu da zuwa”
Ya mika hannunsa ya rikota.
“Yauwa darling y scul?”
“Fine Daddy wannan Name sake din tawa ta tafi”
“Yeah Momy ta zo ta dauketa did you miss her”
“Yes Daddy”
“Ke da kika ce ba ki sonta?”
“Yanzu kuma na ji ina sonta, daddy za ka kai ni gidansu?”
“Ban san gidansu ba”
“Pls daddy”
“I'm serious”
Ya fada yana kara gyara mata zama a jikinsa, har cikin ransa yake jin son yarsa fiye da komai a rayuwarsa, musamman idan ya tuna cewar bata da mahaifiya a raye.
“Idan kin je makaranta ki tambaye unguwarsu sai a kai ki”
Wannan karon Momy ce take maganar.
“Wane class take Momy?”
“4 tace min kamar 4 kamar 3 na manta dai ki bincika”
Da sauri ta gyada kai tana murmushi.
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
*Gaba daya littafin nan Sadaukarwar ne ga Zainab A Baba💖*
2️⃣2️⃣
AHMAD POV.
Wayarsa ce tai ringing, da gangan ya ki duba wayar ya ga mai kiran balle yai deciding idan zai dauka ko ba zai yi picking ba. Babu kira mai muhimman a gurinsa kamar na Hajiyarsa sai kuma na kanwarsa da yarsa su ne kadai mutanen da suke da muhimmanci fiye da komai a rayuwarsa, yana girmama kiransu yana mutunta bukatunsu, kamar yadda yake martaba su. As long as yana tare da Hajiya ko yana cikin gida, duk wanda ya kira shi sai idan yaga dama zai daga kiransa kowa shi a duniyar nan kuwa.
“Ba wayarka ce ke ringing ba?”
Cewar Hajiya ganin be daga ba duk kuwa da ta san halinsa na kin son call, ya fi son sako fiye da kira.
“Ita ce wata kila wane ni bana son amsawa yanzu”
“Ko dai yan matan ne ke kira?”
Kallonta yai da murmushi a fuskarsa.
“Kowa da bukin zuciyarsa, Allah na tuba wace mace ce zata wahalar da kanta yanzu na son dan Hajiya?”
“Hmmm ai yan matan yanzu shegen wayo ne da su, yanzu sai su tatse ka tass baka sani ba”
“Hajiyata, kin kasa gane cewar ni ba yaro ba ne, ka ci abinci? Me ka ci? Yaushe zaka dawo, karka wuce minti talatin a waje, da sauransu na yara ne, Hajiya ni babban mutum ne a yanzu tun da har Daddy ya kirani nai min wasiyar kula da ku, kuma cikin ikon Allah da iyawarsa na iya rike gidan nan da kula da ku da tafiyar da komai na kamfani yadda ya dace ya kamata ace kin fahimci cewar dan ki ba yaro ba ne a yanzu”
Murmushi tai Murmushi mai sautin irin na su na manya.
“Har gobe kai yaro ne Gwarzo, maza ai ba wayo ne da ku ba, ba komai kuke ganewa ba sai na nuna muku”
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya kalli Baby Namra.
“My Love je ki dakinki bari mu yi magana da Hajiyarki ko?”
“Okay Daddy”
Sai da ta sumbanci kumatunsa sannan ta haye sama, shi kuma ya bita kallo kamin ya ciro wayar tasa da ke ringing yai picking.
“Yusuf ya akai?”
“Lafiya kalau, oga ya gida ya family?”
“Fine go straight to the point”
“Oga maganar vip ne”
“No ya dai kusa ka san kace baka son sai abu yai gab a fada maka, shiyasa na tuna maka”
“I think kudin shekara ya kamata mu fara biya na wata wata nan yana confusing dina, ka lissafa na shekara nawa ya kama zan turawa abokina number ka sai ku yi magana”
Be jira Yusuf din da ya kira wayar ya kashe ba, balle har ya saurare abunda zai fada ya kashe wayar, yana kallon Hajiyarsa zai yi magana ta tari numfashinsa.
“Har yanzu ba a daina biya Vip din nan ba? Shekara nawa Gwarzo? A yanzu ka gama maganar cewar ka girma, ni nasan abunda na ke ai na san waye kai”
“Ba haka ba ne Hajiya, abunda kika kasa ganewa freedom din danki, Hajiya kin kasa bari na yi komai kamar ko wane namiji, kin ki aminta na zauna a gidan kaina, kin hana auren duk yarinyar na kawo, ko fita nai idan na wuce ka'idar da kika ba ni sai kin nuna bacin ranki ko kuma ki nuna min hankalinki ya tashi ba ki san inda na ke ba, duk yadda nake son na fita na fira a waje na wuce 9 ko na kai 10pm sai ki ce min ba haka ba.
Exclusive City, a nan na hadu da Halima, a kujerar da nake biya a yanzu a gurin na same ta zauna, kin sani Hajiya every week muna zuwa gurin mu sha iska, and ta taba fada min ita take biyan gurin ko da bata zo ba, and after mun yi aure ita ta cigaba da biyan gurin, duk yadda na so na cigaba da biya sai ta hana ni, she once told me na bari sai idan bata da rayuwa sannan na cigaba da biya, and nai mata alkawari daga lokacin da na auri wata macen ba zan sake biya ba, alkawarinta nake kokarin cikawa Hajiya gurin nan yana da muhimmanci a gareni saboda mahaifiyar Namra, ko rai aka bata mata a gurin take zuwa tai kuka, idan kika mata wani abun a gurin take zuwa ta zauna tai bacin ranta ta gama sannan ta kira tace idan na taso daga office na biyo ta nan na dauke ta, wani lokacin kuma da kaina nake zuwa nemanta a gurin, ni kaina a yanzu ko anjima ko wani lokaci na kan je can na zauna kuma na samu natsuwa kamar tana raye... ”
Ya yi shiru idonsa tab da kwalla, uffan Hajiya ba ta ce ba har ya mike tsaye ya saka wayar aljihun shaddarsa da ya zuba hannayensa aljihu ya nufi upstairs. Wani irin abun na rashin jindadi ke masa yawo a zuciya, haka yake samun kansa a duk lokacin da ya tuna da matarsa Halima, wacce yake yawan fada mata cewar daga ita ya gama so, mace da yake ganin babu mai hakurinta da kirkinta a duniyar nan.
Ajiyar zuciya ya sauke sau uku zuwa hudu sannan yaja wani dogon numfashi ya busar a bakinsa. Ya kai hannunsa ya murda kofar dakin Baby Namra ya tura ya shiga ciki. Agaban plasma take zaune rike da drawing book da pencil a hannunta tana drawing wani bird da ake nuna a kids channel. Daga bakin kofar ya tsaya yana kallonta zuciyarsa fal da kaunar yarsa, sannan ya karaso kusa da ita yana ayyana abubuwa da dama akan rayuwarsa da nata.
‘Ko da na ayi aure zan yi ne kawai saboda ke, saboda ni da ke mu samu kulawa amman ba dan zan taba son ko wace mace a duniyar nan ba’
Kanta ya shafa yana murmushi kamar yadda ita ma ta dago ta kalleshi tana murmushin.
“Daddy what”
“Ba komai”
Ya fada yana cigaba da kallonta, ita kuma ta maida hankalinta gurin tv ta cigaba da abunda yake. Wayarsa ya ciro ya nemo number Rayyan.
“Rayyan”
“Ranka ya dade”
“Yusuf ya kira ni wai kudin wata sun kare, na ce masa za ku yi magana akan na year sai ka bashi zai fi”
“Okay amman ban gane Yusuf din ba”
“Wanda yake Exclusive City, kudin Vip nake nufi”
“Okay ina da number shi ai bari na kira shi yanzu”
“Okay ya fada maka ko nawa ne na shekara sai na bashi”
“Consider it done”
Daga haka ya yanke wayar ya cigaba da kallon abunda yarsa take zanawa.
HALIMATU POV.
daga karshe na yanke shawarar fadawa Abdulhamid gaskiya, na san duk yadda zai ji zafi da tashin hankali ba zai kai kamar lokacin da abun ya faru ba, kwana biyun nan na lura yana cikin damuwa wata kila saboda abunda Abdallah yai masa ne a kwana baya duk da be fada min ba amman ni kaina na lura da hakan, abunda zuciyata take yawan fada min idan ban fada masa gaskiya ba, idan ya ji a wani gurin ba zai ji dadi ba ba kuma zai fahimce ni ba. Amman kuma ta ina zai ji? Wa zai fada masa bayan babu wanda ya san wannan sirri daga ni sai Allah sai kuma kawata Hajara?
Doyar da nake ferayewa na aje na rike wukar kamar ita ce zata sama min mafita.
“Zan fada masa gaskiya, ina jin kamar ba zan samu peace of mind ba idan ban fada masa ba, ina jin kamar na ci amanarsa ne”
Ni kadai nake magana da kaina a kitchen kamin na aje wukar na wanke hannuna saboda wayata da na ji tana ringing. Cikin hanzari na nufi inda wayar take, a lokacin da na kai hannu na dauki wayar sai na kasa picking din call din ganin number mai kiran duk kuwa da ba suna, Aminu ne na san ba wata magana mai dadi zai fada min ba, wata kila haukansa zai min ko kuma ya min gargadinsa na iska da ya saba, sai da ya jera min four miss calls sannan na daga, nai masa shiru tare da hade rai kamar yana a gabana.
“Hello Halima”
“Ya akai?”
Na tambaya ina kara hade fuska kamar ance yana ganina.
“Sai an yi wani abun zan kira? Alaka fa har yanzu bata yanke a tsakaninmu ba saboda yara”
“Babu wata alaka a tsakanina da kai Aminu, kuma bana fatar wata alakar ta sake kulluwa a tsakaninmu, wacan da mu kai a baya ma ka dauka cewar labari ne”
“Ta wuce labari Halimatu tun da har kika haifa min yara hudu, maza biyu mata biyu Al-hamdulillah, yanzu ma kira nai na tambaye lafiyarsu, kuma na ji idan akwai abunda suke bukata idan zan taho musu da kaya sai na siyo musu”
Duba wayar nai dan tabbatarwa idan har number Aminu ce da gaske ko kuma a a. Kamin na maida wayar a kunne na ya kira sunana ya kai sau uku cikin tausasshiyar murya kamar ba shi ba.
“Lokacin da nake gidanka ma baka damu da tambayar lafiyar yayanka ba, sai yau? Ko kunya baka ji ba? Yarana ba sa bukatar komai daga uba irinka Aminu, mahaifiyarsu ta ishesu kuma zata iya yi musu komai, karka sake kirana domin ni matar wani ce a yanzu”
Ban jira abunda zai ce ba na yanke wayar, mamaki fal a zuciyata wanda ya kasa boyuwa har ya bayyana a fuskata, sake duba wayar nai a karo na biyu, neman dalilin kiran Aminu na ke a wannan lokacin na rasa? Me yake so? Ko kuma na ce mi yake kokarin aikatawa? Me zai saka ya tambayi yaransa? Gaba kaina sai ya kulle har na girkin na gama ban raba dayan biyu ba, ko dai Aminu yana da wata manufar akan yaransa ko kuma yana shirin lalata min aure ne.
Abdulhamid be shigo ba sai bayan sallah magariba, na masa sannu da zuwa kamar yadda na saba na raka shi har daki na hada masa ruwan wanka domin na san wanka ne abunda mijina yafi bukata a duk lokacin da ya dawo daga gurin aiki. Kamin ya fito na jera masa abinci da ruwa mai sanyi sannan na fiddo masa da jallabiyarsa, da kaina na karbi karamin tawul din na natse masa jiki sannan na shafa masa mai sannan ya saka gajeren wando ya dora Jallabiyar sama. Zaunawa yai ni kuma na soma zuba masa abincin ina ta kallon yanayinsa kamar yadda na lura da kwana biyun nan ya fiye kallona.
A tare muka soma cin abincin kamar yadda muka saba sai da na tabbatar ya kusa koshi sannan na fara bijiro masa da maganar.
“Hubby Akwai wata magana da nake son mu yi mai muhimmanci....”
Tarar numfashina yai.
“Ya jikinki....? Na manta dazun da muka tashi ban tambaye ki ciwon marar ba”
Wani dif na ji numfashina yai dogon zango, kamar wacce zata suma sannan ya dawo min kamar an jefo shi.
“Na ji sauki, akan hakan ne nake son mu yi magana”
“Uhm ina jinki”
Yadda yai maganar da yadda ya fuskance ni sai ya saka ni tsoro da fargaba kwarjinisa duk sai ya cika ni, har na kasa furta komai.
“Ina jinki”
Spoon din hannuna na aje na kama hannunsa na rike na saka idona cikin nasa.
“Ban san yadda zaka dauki abunda zan fada maka ba, ban san ya za ka ji a zuciyarka ba, ban san wani irin kallo za kamin ba, za ka iya cigaba da zama da ni akan kaddarar da ta same ni ko a'a, ban sani ba iyakar abunda na sani shine bana da kwanciyar hankali idan ban fada maka.....”
Idona ne ya cika da hawaye sai nai saurin kawar da fuskata daga barin kallonsa.
“Me kika aikata?”
Yawun bakina na hade na sake kallonsa a karo na biyu sannan na ce
“Ban aikata komai ba, darajata aka taba....!”
“Ban gane ba”
Shiru nai na kasa cewa komai sai hawaye na ke shar kamar ba gobe, shi kuma bayan kallona babu abunda yake.
“Zaka iya tuna lokacin da ka tafi Abuja karbar wasu takardu? Ka bar ni ni kadai?.....”
Cikin natsuwa irin ta masu gaskiya na zayyana masa komai, ba natsuwa irinta ta masu kwanciyar hankali ba, kallon kallo muka ko yi ma junanmu akuya kallom kura, idona na hawaye ina kallonsa, yayinda shi ma yake min kallon da ban san na minene ba, yarda ko akasin hakan ko kuma tausayi? Sosai nake Kallona na kasa dauke idona daga kansa, so nake ya fada min cewar ya aminta da ni tausayi da kulawa da kauna nake son gani a fuskata, so nake na ga idonsa sun cika da hawaye saboda mu yi kukan a tare mu yi jumamin a tare.
Be ce min komai ba, be kuma daina kallona ba, be nuna min wata alama ta yarda ko akasin hakan ba, ban tsinka jimami a idonsa ba balle har na iya hararo tausayi a zuciyarsa.
Ni din ce da kaina na tsargu na mike tsaye na bar masa gurin, ina jin zuciyata na min wani irin zafi kamar zata fashe, idonuwana kuma suna ta min yaji saboda hawaye daya hana ni gani daidai. Dakina na dawo na kwanta saman gadona na mika hannuna na janyo fillo ya dora kaina dayan hannun kuma na rika shafa gadon da shi kamar ban san abunda nake ba, kwancin ya gagareni sai na sauko na zauna a kasa na dora kaina a saman gadon.
Uwa ce ni, amman a yau ji nake kamar ace akwai wata uwar a kusa da ni ta rarrashen ta fada min komai zai wuce, ina son naji wata kalma mai dadi ina son na ji an fada min cewar wata rana zan yi dariya wata rana zan yi farinciki, ina ma a ce Mama ta san da maganar nan da ita kadai zata iya ba ni hakuri ita ce kadai zata taya ni mu yi kuka tare kamar yadda nai da Namra.
“Kaicon ki Halimatu? Wace ƴa ce za a yi mata fyade kuma ayi ma uwarta? Nai kukan yata kuma nai nawa? Yau kenan ya gobena zata kasance?”
Mikewa nai tsaye ina kara magana da kaina kamar wata tabbabiya.
“Ya isa shikenan komai ya wuce, abunda ya faru ya riga ya faru ba zan iya canja shi ba, ba kuma zan iya goge shi ba, shikenan ai kaddarata ce wannan”
Ina kaina nan na fadi kasa zaune na fashe da wani irin kuka da ban san ta ina hawayen ke fito min ba. Na kan yi kuka har na samuwa natsuwa ko kuma na samu sukuni amman a yau sai na nemi natsuwa da sukunin na rasa, kukan ya ko ya tsaya min kamar yadda hawayen ma ce min sallamu alaikum. Wani kalar sara na ji kaina na yi idonawa har rufewa suke saboda ciwo, har kuma lokacin hawayen ba su daina min zuba ba. Karfin hali nai na tashi na shiga kitchen na dauko flask din na hadawa kaina tea da cup nai ta feta har ya sha iska sannan na kurba kadan, wani abun mamaki sai na kas hadewa kamar wacce tasha wani abun mutuwa, kuka ya subuce min.
‘Ke fa uwace Halimatu, idan Namra ko Amal ko Adnan ko Amir suka shiga damuwa gurinki za su zo, ke za ki sama musu mafita, so be a strong woman....’
Shine abunda zuciyata yake fada min, kai na gyada ina karfafawa kaina kuiwa sannan na shiga bandaki nai wanka har kan nawa da ke ciwo sai da wanke dan kaiwa na samu salama. Daure da tawul na fito na nufi gaban madubi na zauna ina ta kallon kaina, hawayen idona be daina zuba ba kamar yadda ruwan kaina suke zuba. Ina jin motsin shigowar Abdulhamid gabana ya yanke ya fadi, daga jikin kofar dakin ya tsaya yana kallona.
“Amman Halima ba su bar wata alama da za a gane cewar yan fashi sun shigo gidan nan ba? Ba su fasa komai ba? Ba su dauki komai ba? Ba su harbi kowa ba? Kuma duk a unguwar nan ba su shiga ko'ina ba sai nan? Kuma ba su zo ba sai ranar da bana nan?”
Ta cikin madubin na aika masa da kallo sai murmushi ya bayyana a fuskata, still hawaye na sauko min.
“Wacce zan fara amsawa a cikin tambayoyinka?”
“Halima babu yadda za ayi 6arawo mai makami ya shigo gidan nan be bar wata alama da zata nuna cewar ya shigo ba, and if gaskiya ne miyasa ba ki fada min tun farko ba sai yanzu, and miyasa kika yi kokarin zubar da cikin? Ba ki fada min ba sai da kika fara gano cewar na gane halin da ake ciki shiyasa kika kirkiri wannan? Na kasa yarda cewar ke ce Halima!”
Wannan karon juyowa nai na fuskance shi.
“Ni din ce dai Abdulhamid, ka yi tunani iya yadda zuciyarka ta kawo maka, Halimatu ce! Karka damu wannan din ma yana cikin kaddararta, na yarda wani sabwar kaddarar ce ta fuskance ni kuma ta bude min sabon shafi, na shirya karbar ta da hannu biyu, na sani bakinciki baya taba dawwama, kamar yadda jindadi ba ya dawwama, ko dai bakincikin ya tafi ya bar ni, ko kuma ni na mutu na bar shi, kuma gaskiya a duk inda take gaskiya ce zata bayyana ko da bayan raina...”
Takowa yai ya karaso kusa da ni ya dafa ni ya tayarda ni tsaye ya kalle ni da idonsa da ke zubar da kwalla.
“Saboda ina kaunarki na aureki, har ga Allah na yarda da ke..... amman zuciyata ta kasa natsuwa da wannan, duk wani kuduri da nake da shi akanki