Showing 87001 words to 90000 words out of 217237 words

Chapter 30 - GOBE NA Compelet Book by Khadijah Candy.txt

24 Sep 2025

192

daga kai na kalleshi.

“Shi aure yana da rayuwa da mutuwa kamar mutum da rayuwa, idan lokacin mutuwarsa yai babu mahani, kuma abu kalilin kan iya sakawa ya afku ko ya mutu, ko da dalili ko babu, dan haka ki sawa rayuwarki sallama ki dauka cewar ajalin aurenki a gidan Abdulhamid ne yai”

Da sauri na dago na kalleshi, jin magana mai dadi da kwantar da zuciya da samar da natsuwa daga bakinsa, tun kan na furta ya fahimci cewar aurena ya mutu. A take na share hawayena ina gyada masa kai alamar na gamsu.

“Saki nawa yai miki?”

“Daya ne Baba daya yai min”

Na furta muryata na rawa, sai Mama tai karaf ta ce.

“Amman me kika masa mi ya hada ku?”

Kamin na ce komai ba Baba ya daga mata hannu.

“Ba yanzu ba, tashi ki je ciki ki huta, Allah yai miki albarka”

Ban san lokacin da murmushi ya kubuce min ba, kaunar mahaifina ta kara cika min zuciya, ya famshe ni daga tambayar da ban san mi zan fada a matsayin amsa ba.

“Madallah da kai Baba, ina ma ko wane uba kamar kai yake? Madallah da uba irinka, madalla daka zama jigo ga Halimatu....”

Na fada ina hawaye cike da shaukin sonsa, Hafiza ce ta taso daga bakin kofar da take zaune ta zo da gudu ta rumgume Baba tana kuka tana fadin.

“Ina kaunarka Baba Allah kara maka lafiya”

Dariya yai ya tashi tureta daga jikinsa ya tashi zaune. Ni kuma na dago na shiga dakin Mama. A dare Mama bata iya hakura ba har sai da ta ji dalilin mutuwar auren, ni kuma ban boye mata komai ba cikin har da fyade da kai min da abubuwan da suka faru, sai dai ban yarda na fada mata cewar Abdallah na ke zargi ba.
Na ga rashin jindadin mutuwar auren a fuskarta, daman wace uwa ce zata zo auren yarta ya mutu? Balle Mama da take daukar abu ta saka a rai, su Salma da Hafiza ma da suke yan mata ba su yi aure ba abun ya dame ta balle kuma ji ace aure na biyu ya mutu. Sai dai duk da hakan ta nuna min zama da Abdulhamid din ba mafita ba ne sakin ya fi tunda har yana zargina. Da yamma Su Adnan suka dawo daga islamiya, ganina suka hau murna kamar wacce suka shekara ba su gani ba, ganin na kai har bayan i'shai yasa Namra ta fara tambaya wai nan zan kwana.

“ A nan zan kwana, yanzu na dawo kenan sai illla ma shaa Allahu”

Wani irin tsalle ta daka ta dire tana murna ta kama hannuna ta rike.

“Momy da gaske?”

Na gyada mata sai ta kara rumgume ni tana ta murna.

“Yeee mun huta Momy ta dawo”

Iya murnar da yata take na ganina a kusa da ita ya isa da tabbatar da cewar yarana sun yi marmarina duk kuwa da suna zuwa su ganni ko na gansu idan bukatar hakan ta kama, sai dai ko wane d'a yana bukatar mahaifiyarsa a kusa da shi, amman ni na bar su na auri Abdulhamid, a yau ya saka min da haka! Da tunanin abun na kwana a zuciyata har safe.

Washe gari Baba ya kira ni a dakinsa ya tambaye ni abunda ya faru, a nan na tsige masa tun daga biri har wutsiya, a ganina shi mahaifina ne be kamata na boye masa komai ba. Shi ya ba ni shawarar zuwa asibiti na sake yin gwajin hiv dan tabbatarwa. Ban yi wata wata ba na shirya na tafi gurin gwajin. Ban dawo ba sai yamma domin daga asibitin na wuce gidansu kawata Hajara, a lokacin da na labarta mata mutuwar auren sai ta fashe da kuka kamar an mata mutuwa.

“Wannan wane irin abu ne yake ta bibiyarki Halimatu? Tun farko sai da na ce ki auri Abban Ikram da yanzu duk wannan abun be faru ba kika ki”

Kai na girgiza mata.

“Wallahi sai ya faru, abunda Allah ya rubuta ya samu bawa babu mahani, na yarda da wannan”

“Allah sarki Halimatu, ga ki da tauhidi ga yarda da kaddara, Allah ya yaye miki wannan abu da yake bibiyarki”

Ta fada cikin kuka ni kuma na amsa da amin. Bayan sallah magariba na koma gida, sai na tararda tsakar gidamu cike da kayana na daki, alamar Abdulhamid ya aiko min da su kenan kamar yadda yai alkawari, mama ce take labarta min cewar a gurin kawo kayan har da mahaifiyarsa wai tai ma baba bayanin komai, wata kila shi ya turo ta dan ta wanke shi kar a ga laifinsa, wata kila kum ita ta saka kanta a tunanin ba zan fada musu gaskiyar lamarin ba, mama ta fada min har da cheque din kudi ta bawa baba ya ki ya karba, hakan kuma ba karamin dadi yai min, domin bana bukatar komai na Abdulhamid a yanzu.

Da kaina na shiga na fadawa Baba result dina cewar ban daukr da shi, yayi murna matuka dai kuma ya sake ba ni shawarar zuwa wata asibitin na sake yin gwaji. Ban watsar da shawararsa ba, na tafi kusa asibiti uku ana min gwaji result na fada cewar bana dauke da cutar, daman can ni hankali na be taba tashi akan hakan ba, ko da Abdulhamid ya fada min ban ji komai a raina kuma ban san dalilin hakan ba. A dakin da na bari cikina na koma da kaya na jera komai kamar wacan karon, a nan kam gaskiya na ji babu dadi sosai domin a takure na ke duk kuwa da kasancewar gidan ubana ne amman gidan yawa ne, ba irin gidan nan ne na masu kudi ba da za a ce kowa da dakinsa.
Ranar da na cika kwana uku da dawowa sai ga Aminu ya zo kofar gidan ya aiko da siyayya wai a bawa yaransa kuma yana kiransu, an fada min haka yake musu a yanzu duk bayan kwana biyu ko uku, ni kau na rasa dalilinsa na yin hakan bayan dacan ba haka ya saba ba. Be san ina cikin gidan ba na sani tun da ba kowa ya san aurena ya mutu ba, na san yana cikin mutunen da za su yi murna da mutuwar aurena domin ya sha fada min a lokacin da nake gidabsa cewar babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina. Fita yai da da su yai musu waya siyayyar ya hado musu da kudi sannan ya dawo da su suka shigo gida suna ta murna.
A daren mun dade muna tattaunar maganar yadda a yanzu hankalinsa ya dawo gurin yaransa, abunda ya bawa kowa mamaki a gidan mu, Mama ta karkarta min hankali da wata maganar wai ko shine mutumen da yai min fyade.

“A a mama ba Aminu ba ne, na san siffar Aminu ciki da waje, yadda yake idan ya saka tufafi kanana kaya ko manya kuma yadda yake mu'amalarsa, da shi ne da tuni zan gane, ko kadan wannan mutumen be yi min yanayi da Aminu ba, idan har shine dole zan gane, kuma me ma zai saka Aminu yai min haka, mutumen da baya kaunata, wanda ya kasa hakuri har ya dawo ya saki ni ta waya ya sake ni fa, mutumen ya wulakanta ni Mama Wallahi ko sunansa bana son ji”

“Ai saboda kiyayyar da yake miki na ke zaton haka, saboda ya jefa ki a matsala ki kasa zaman auren”

“Ko ma wanene ina rokon Allah ya bayyana min shi”

Na furta ina hawaye zuciyata cike da kuna, Mama ta amsa da amin. Mun dade muna fira a dakinta, cikin har da zancen Abdallah tana cewa da ma shi na aura ita tun farko shi ta so na aura amman na ki ni dai ban ce mata komai, saboda ban taba fada mata cewar Abdallah yayi ta neman na kashe aurena na aure shi ba....


AHMAD POV.


Tarin takardu ne a gabansa da laptop yana ta aikin cika wannan cire wannan saka wannan, aikin daya taru masa ne na satin daya shige wanda be be yi ba yake yi yau ganin yau assabar ce babu karatu.
Mug din coffee na gefensa lokaci zuwa lokaci ya ke dauka ya sha. Be tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah azahar sannan na fito daga garden din
ya shiga part dinsa yai alwala ya nufi masallacin dake unguwar, after sun yi sallah ya shigo gida, as usual ya nufi part din Hajiya, yar aikinta kawai ya samu a falo hakan yasa ya nufi dakinta tun kan ya karasa ya jiyo muryarta ita da abokiyarta suna fira, har ya juyo da zimmar ya fasa shiga sai kuma ya juya ya shiga da zimmar ya tambaya iya Baby Namra.
Sai da ya gaishe da abokiyar Hajiyar sannan ya kalli Hajiya ya ce.

“Hajiya ina Baby?”

“Bata nan, wannan mahaifiyar Ikilima ce, Hajiya ga danki nan ko da yake ai kin san shi”

“Na san Gwarzo ai tun ba yau ba”

Cewar matar tana dariya, shi kuma ya saci kallonsa ya sake kallon Hajiya ya ce.

“Ina taje Hajiya?”

“Gidansu kawarta Namra”

Kansa ya daga sama ya saka hannunsa ya dafe.

“Oh Hajiya kin san na ce miki kar a kaita can, matar nan ba mutunci ne da ita ba wata kila ma kallon banza zata mata, shiyasa duk bibiyar da take min ban yarda na kai ta ba”

“To ina ruwan yara da lamarinku, ta sha mun kai tana son zuwa can sai a hana ta? Su fa yarane babu ruwansu da wannan, kuma dazu ta fada min cewar Momyn kawarta ba a gidan take ba”

“Hajiya dan Allah ki aika a dauko ta, ni dai bana son abotar nan, bana son yawan fitar nan da take Wallahi”

“Zan aika amman sai da yamma, abincin ka yana part dinka”

Be sake ce mata komai ba ya juyo ya baro jikin kofar, sai a yanzu yake mamaki no wonder yau weekend kuma bata zo ta dame shi ba, da yanzu tana nan ta saka shi gaba da hana shi aikin nan tace sai su yi game ko ya fita da ita kamar yadda ya saba mata every weekend. A dayan bangaren kuma yana ta ganin karfin halin Hajiya na zon hada shi aure da bazawara dan shi dai kam ya raya a ransa ba zai taba auren bazawara ba.

“Allah kadai ya sani wata kila ma yarta bata da miji, miye na wani zuwa gidan iyayen mai son yarki a yi maganar auren da ke”

Ya fada yana kokarin zama sai jin haushi yake kamar ance masa zancen aurensu ya kawo ta.



HALIMATU POV.

Washe gari ya kama Saturday babu scul sai islamiya, dan haka na tashi da wuri na gyarawa yarana suka tafi makaranta, har Amal a yanzu tana son zuwa islamiya duk wani kuiya da son jiki yanzu ta daina shi ganin babu ni a kusa da ita. Around 12 suka dawo daga islamiyar suka cire uniform suka saka kayan gida na zuba musu shinkafa da wake da akai a gidan, sai Amal ta murje ido ta kanne kafadarta ita sam ba zata ci wake ba, daman can na san Amal is not fan of wake da shimkafa amman na dauka ta canja ganin bana nan, a dole na tashi na dora mata indomie da kwai. Ina cikin kitchen din ta zo ta same ni ta rike rigata tana tabe baki.

“Momy za ki goyani”

Dariya yai ina mata kallon Mamaki.

“Wato kin ga Momy a banza ko? Amal kin fa girma yanzu ya kamata ki daina wani abun, yanzu ba kamar da kike ba”

Bata fuska tai tana kokarin kuka. Kanwata Salima tai dariya ta ce.

“Kin ganta nan wallahi dole sai an goyata a cikin gidan nan, ko dai Namra ta goyata ko wani a cikin gidan nan idan ba haka ba sai ta shige cikin daki tai ta kuka tana kiranki, yanzu kuma kin dawo dan haka ki yi ta goyon abarki daman can ke kika saba mata”

Dariya nai na kai hannu na dauke na dorata a bayana, ina kokarin kwance dankalin kaina na goyata da shi na ji Sallamar Baby Namra wato kawar Namra yar mutumen nan marar mutunci, da kuzarinta ta shigo da far'a har da yar ledarta a hannu. Gaba daya yan matan gidan mu suka hau yi mata oyoyo suna ta murna da zuwanta da alama dai sun saba da ita ba kamar yadda na ke tunani ba. Ita ma da far'a take ta gaishe su daya bayan daya sannan ta nufi dakin Mama inda ta san su Namra suna can.
Ni dai ina goye da Amal ina dahuwar indomie sa gata ta shigo tare da Namra, Namra na nuna min ledar hannunta.

“Momy kalla turare da chocolate Hajiyarta ta ce ta kawo mana”

“Eyeee lallai kun gode”

“Laaaa Momy Good afternoon”

Ta fada tana mamakin ganina

“Ykk ya makaranta?”

“Fine”

Sosai yarinyar take kama da mahaifinta, sai dai ita tana da far'a da son mutane ba kamar shi ba. Kana ganin fuskarta ita da Namra ka san suna murna da ganin junansu, daman kwana biyu nan suna da damuna da maganar zuwa gidan ni kuma na banzantar da maganar sai ga ta a yau ta zo. Amal ma sauka tai daga bayana ta bi bayansu.

Ina sallame sallar la'asar Adnan da Namra suka shigo tambaya wai za su je waje su yi wasa, har ta bukaci na bata kudi ta biya kudin lilon da ake kusa da mu su biya su hau, ban musa musu ba na dauko jakata na ciro naira hansin na mika mata suka fita da gudu har suna rigengen. Wani irin faduwar gaba ne ya same ni sai na ji kamar na kira su na ce su dawo, gaba daya na ji babu dadi, ban kuma san dalilin hakan ba, zuciyata tai ta bugawa da karfi kamar zata fito tsabar faduwar gaban da nake, a take na soma ambaton Allah, sai dai ban wani damu ba ganin yamma ce na san shaidanun aljanu ma suna saka haka. Bayan na gama azkar na dauko wayata na shiga YouTube in duba wasu videos har biyar da rabi tai sannan na fito tsakar gidan kamar yadda muka saba zama na zauna cikin ya'uwana. Sallama akai mana muka amsa sai yaro ya shigo yace wai ana kiran Baby Namra direban ta ne ya zo daukarta. Kamin mu ba shi amsa Adnan ya shigo gidan da gudu har ya faduwa wasu yara na biye da shi jikinsa duk kasa ya fado kaina.

“Momy Namra Namra....ta fada rijiya..... ”

Ban san lokacin da na ture shi ba na mike tsaye na daki kirji idanuwana a waje.

“Wace Namra?”





*Jiya na yi 5k words yau kuma na yi 5k+ words 🤔 wace addu'a kuka min ne?🙄 Pls ku ba ni ita nai ma Halimatu ta koma gidan Abdulhamid 💔😪*
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy


2️⃣9️⃣

“Baby Namra....”

Jin maganar tasa nai kamar daga sama, ban san lokacin da na doshi kofar fita da gudu ba, har sai da Inna ta riko ni.

“Tsaya ki saka hijab dinki”

Sai na koma cikin gidan da gudu na shiga dakin Mama ban tsaya neman hijab na janyo zanen da nai arba da shi a saman gadonta na lufe kaina kamar wata tsohuwa na fito hankali a tashe. Yan mata gidan mu na biye da ni, rijiyar da na sani a unguwar mu na nufa sai Adnan yace min ba ita ba.

“Momy ba ita ba, rijiyar malam ya'u”

Tsayawa nai cak jin ya ambaci rijiyar da na manta when last a dibi ruwa a cikinta, rijiyar da ake cewa har ma sha ruwa akwai a ciki.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, miya kaiku gurin rijiyar malam ya'u”

Sai na maida dubana gurin Salma wacce tai maganar.

“Namra ce ta ce muje can mu yi wasa”

A nan ma kallon Adnan nake, kamar wacce bata da makoma haka na zama, jikina yai sanyi ga uban sara da kaina ya soma yi. Tafiya nake ina jin kamar ana mayarda ni baya ina tafiyar ina jin kamar ba kasa nake takawa, sam ban lura da babu talkami a kafafuwana ba sai da na isa bakin rijiyar kafafuwana suka taka sanyin ruwan da ke gurin. Leka rijiyar da nai ma sai da wani jiri ya kama ni saboda hudunta da kuma dadewarda tai ba a bude ta ba. Wasu mazan unguwar mu ne suka shiga ciki suka daukota a yanayin da na ganta na sam abu ne mai wahala ta rayu, ta ji ciwo a kai a fafafuwanta ma ta samu rauni hannunta har zubar da jini yake.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Shine abunda kawai na iya furta na saka hannu biyu na dauke, abun ka da marar karfi ga kuma rashin kuzari na tashin hankali sai na fadi a gurin tare da ita, har sai da kanena suka zo suka dauketa ni kuma na bi bayansu hankali tashe, har na isa gida kuka nake ina jin mutane na tambayar ko mi ya kai su can, garin ya suka fada a wannan tsohuwar rijiyar, sam ni kam ba tambayar ce a gabana yanzu ba ceto ran yar mutane ne a gabana. Muna shiga gida na dauko hijabi da jakar kudina na saka takalmi na muka nufi titi ni da kanena kusan rabin unguwar suna biye da mu wasu na fadi bata da rai wasu na tambayar yadda abun ya afku. Napep muka shiga kai tsaye muka nufi asibitin fmc, mun tararda mutane da yawa a emergency kuma sai mu ka yi rashin sa'a babu likitoci da yawa kasancewar yau Saturday. Sun karbe ta domin duk wanda ya ganta a dole ya tausaya mata, sai dai duk da sun karbe ta din hankalina be kwanta ba na kasa zaune na kasa tsaye, zuciyata ta na ta raya min cewar bata da rai ganin tun da aka cirota daga rijiyar bata motsi bata numfashi ga raunukan da ta ji.

“Anty ki zauna”

Salma ce ta dafa ni tana fadin haka, sai na girgiza mata kai ina kuka domin ba zan iya ba.

“Ko ki kira yaya Abdallah...”

Salma na fadin haka zuciyata ta raya min yes na kira shi maybe he can help, jaka na lalaba ban ji wayata ba sam ban lura da jakar kudi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login