Showing 174001 words to 177000 words out of 217237 words
ya dannen shi yana kokarin kwantar musu da hankali.
“Ku kwantar da hankalinku, zata samu sauki likita yana ciki yana dubata”
Mama ta gyada kai hawaye na sauko mata.
“Dukanta su kai?”
Inna ta tambaya.
“Ban sani ba tukuna sai likitoci sun gama bincike su”
After like 40 minutes Dr Nura ya fito daga dakin ya nufo inda suke. Ahmad sai kallonsa yake ya kasa tambayar komai.
“Ba wata matsala a yanzu nan da awa uku zata farka”
A hankali Ahmad ya cikawa bakinsa iska ya busar, ya Lumshe ido ya bude sannan ya mike tsaye ya bi bayan Doc Nura. Mama da Inna da Husna kuma suka nufi dakin da aka wuce da Halima.
“Ka tabbatar babu wata matsala Doc”
Bayan sun shiga office din Ahmad yake tambayarsa domin gani yake kamar ya boye ne ganin iyayenta. Sai da Doc Nura ya zauna sannan ya amsa masa.
“Babu wata matsala, abunda aka buga mata akan ne ya mata nauyi shiyasa hankalinta gushewa, amman babu wani matsala”
Ba zai iya zuwa dakin ya zauna ba bayan Mama da Inna ya san suna ciki kuma zuciyarsa ta ki aminta ya tafi ya barta cikin asibitin sai kace bata da kowa ko kuma bata san kowa ba, so he decided ya zauna a office din Doc Nura yai jiran awanin da Doc yace zata farka, da kansa ya kira Hajiya sanin cewar zata kirashi idan an yi magariba be dawo gida ba.
“Hajiya yau ba zan dawo gida da wuri ba”
“Why?”
“Lims ta samu matsala ne”
“Wacece lims?”
Runtse ido yai ya bude sai a lokacin ya tuna da Hajiya fa yake waya, duk da ba kunyarta yake ba domin ta zama kamar friend dinsa amman duk haka ita bata san yana kiran Halima da Lims ba duk kuwa da irin yadda sunan da yai mata ya bi bakinsa, duk da haka be kamata ya fadi haka a gaban Hajiya ba.
“Halima i mean”
“Subhanallahi matsalar me ta samu?”
“Kanta ya bugu da wani karfe muna asibiti yanzu haka, so ba zan bar asibitin ba sai ta farka”
“Allah sarki, babu matsala Allah ya bata lafiya”
“Amin thank You Mom”
“Se ka dawo”
Ya sauke wayar yana murmushin jindadim yadda Hajiyarsa ta amince a take ba kamar yadda take masa ba a da, ko kuma dai dan yana Halima ne oho.
HALIMATU POV.
Ba zan iya kiran bachin da nai da suma ba, ba kuma zan iya cewa ban suma ba, sai dai abunda na sani hankalina ya bace na dan lokaci a lokacin da aka saka min abun da, sai dai ina jin hayaniyar da suke kamar cikin mafarki kuma kamar a wata duniyar, har dauko ni da akai aka saka ni a mota zuwa asibiti har shigowa asibiti duk ina ji sai dai ba ji irin na mai rai ba kuma bana iya bude idona balle nai motsi, hakan ne ya tabbatar min da ba suma nai ba domin wanda ya suma baya sanin abunda ke kansa, sai dai daga lokacin aka suka min allura sai hankalin nawa ya tafi ban farka ba sai da aka sauko daga sallah magariba.
Na farka cikin rashin kuzari yawun bakina ma ba dadi kamar wata mai ciki, ba na wahala ne kawai ba wata kila har da yunwa domin ko karin safe ban yi ba.
“Sannu Halimatu”
A hankali na daga kai na kalleta wacce ita kadai ce a dakin, sai ya gyada mata kai alamar gamsuwa, sannan na maida idona gurin kofar da aka turo. Ahmad ne ya shigo hannunsa rike da ledodi tun da muka hada ido yake sakar min murmushi har ya aje ledar yana fadin.
“Ga kayan marmari na gani a gate na riko muku”
“Allah ya saka maka da alheri”
“Amin, ya jikin nata?”
“Al-hamdulillah yanzu ta bude ido”
“Okay, Baba babu ruwan shayi ko?”
“A a babu su yanzu kam, ga dai tuwo nan da aka kawo”
“Shayin dai zai fi, ko zaki kira gida ki ce a kawo mana ruwan zafin in yaso sai na karbo kayan tea nan waje, Doc yace idan ta farka a bata tea”
Da to Inna ta amsa sannan ta tashi ta fita daga dakin, kamar jira yake ta fice sai ya nufo gadon da nake kwance ya kwanto da fuskarsa daf da tawa.
“Na ji tsoron sosai da na ganki a galabaice dazun, na dauka ba za ki yi saurin farkawa haka ba, ya jikin naki”
Kamar mai rada yake min magana sai kallon cikin idona yake kamar zai cinye ni, kai na gyada masa alamar na ji sauki.
“Wani gurin na miki ciwo?”
Na girgiza kai.
“Can you talk?”
Nan ma dai kan na gyada.
“Then say my name”
“Ahmad... ”
Na fada cike da nauyin baki, murmushi ya sakar min.
“That's my girl”
Ya fada yana kara kashe murya sannan ya mike tsaye ya nufi inda nake zaton bandaki ne ya bude ya shiga sai gashi ya fito rike da karamin bokoti ya nufo inda nake, sannan ya dauko daya daga cikin ruwan gorar da suke saman drawer wadanda nake kyautata zaton shi ya siyo su ya bude daya.
“Za ki iya tashi ki wanke bakinki?”
Haka nan na unkura ba dan ina jin karfi ba na tashi na zaune na tara hannuna yana zuba min ruwa ina kaiwa a baki n kuskure na zubar, sannan na soma wanke fuskata.
“Ji yadda suka saka pretty face din nan na ki ya rame”
Ni dai ban ce komai ba, ko ban duba madubi na san na rame domin na ji fuskar tawa ta zurma. Yana aje ruwan ya dauki bokitin ya maida sannan ya nufi kofar fita yana.
“Bari na fara yin magana da Doc kar na baki wani abun ya saba doka”
Da kallo na bishi har ya fice kofar bata rufe ba aka sake turo ta Mama ta shigo tare da Mama Ramatu.
“Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode maka”
Shine abunda take fada har ta iso inda nake ta zauna bakin gadon tana kallona fuskarta da murmushi.
“Ya karfin jikin Halimatu?”
Cewar Mama Rahamatu sai na amsa mata da Al-hamdulillah.
“Kina jin wani ciwon a yanzu?”
“A a”
Na fada ina kallonta babu komai a cikin idanuwa sai son mahaifiyata da kaunarta. Likitan nan ne ya shigo tare da Ahmad ya tambaye ni jiki na fada masa bana jin komai sannan yace a bani abinci na ci sannan a bani magani. Ahmad da kansa ya dauko ayaba ya mikawa Mama yace ta ba ni, ita kuma ta rika barewa tana saka min a baki ina taunawa a hankali har na koshi.
“A saka miki tuwo?”
“A a cikina ya cika”
A nan ma shi ya ballo maganin ya mikawa Mama ta bani na sha.
“Mama rumgume ta, idan mutum ba shi da lafiya yana jindadi a rumgume shi”
Ya fada yana kallona, Mama ta amsa da to tana dan kallonsa kamar yadda nima nake mamakin maganarsa sai kace wata karamar yarinya zai ce a rumgume ni, Mama ta kara haurowa kan gadon taja ni jikinta ta rumgume, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba sai na ji natsuwa ta sauko min har na Lumshe ido.
“Am Baba daman ina son na fada muku wani abu, na yi magana da lauyana zai saka kara akan abunda akai wa Halima so i think ya kamata ku sani”
Ba shiri na bude ido na dago na kalleshi kamar yadda Mama ma take kallonsa.
“A a idan su idonsu ya rufe sun aikata abunda suka aikata, mu be kamata mu yi haka ba, ba a taruwa a zama daya, akwai zumunci mai karfi a tsakani, da mahaifin Abdallah da mahaifin Halimatu”
“Amman su basu san da zumuncin ba ne suka aikata abunda suka aikata?”
“Hankali da tunani ba daya ba, kuma ba a biye son zuciya kamar yadda tai”
“Ba ki ga yadda sukai mata ba? Zata iya rasa ranta fa sanadin haka”
“Tun da Allah yasa ba a rasa ran ba hakuri shi ya fi, amman shiga kotu a yanzu zai kara lalata zumunci ne kuma ka jawa Halimatu bacin suna a cikin dangi”
Wayarsa ce tai ringing kamar yana nema sai kawai yai picking call din ya fice daga dakin, a lokacin ne Mama ta dube ni cikin yanayin damuwa tace.
“Karki ba ri a kai matar yayan mahaifinki kotu, ita ma uwa ce a gareki, na sani da margayi yana da rai wata kila da yanzu kina can gidansa zaune yana kula da ke, inda yana raye da duk abubuwan nan ba su faru ba, idan kika bari aka saka Hajiya kotu saboda abunda tai miki Abdallah ba zai taba ganin farinki ba, ko dan shi kadai be kamata ki bari akai Hajiya kotu ba, domin zai kara lalata zumuncin ne, idan hankali ya gushe hankali ne yake dawo da shi, ki masa magana kar ya kai abun nan kotu dan Allah”
“In-Sha-Allah zan yi magana da shi Mama”
“To Allah ya miki albarka”
“Amin”
Tun da Ahmad ya fita ban sake saka shi idona ba sai washe gari da safe, misalin bakwai da wani abu. A lokacin ina zaune a dakin ni kadai domin ba sa barin kowa ya shigo da safe sai yamma ta yi. Ya shigo hannunsa rike da kwandon dake dauke da kulolin har kala uku dayan hannunsa kuma rike da filas din ruwan zafi.
“Ina kwana....”
Na mika masa gaisuwa sun kamin ya karaso, be amsa ni ba kuma be min murmushin daya saba ba har ya aje kayan.
“Ga breakfast in ji Hajiya”
“Ina kwana?”
Na sake mika masa gaisuwa a nan ma be amsa ni ba.
“Ya jikinkin na ki?”
“Al-hamdulillah”
Daga haka be sake ce min komai ba sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. Kallonsa nai yanayinsa da yadda yai min sai ya sa na ji babu dadi.
“Kai hakuri na ja maka ba.....”
Kamin na karasa ya tari numfashinta.
“Ba ki ja min komai ba, ni na ja miki duk wannan abun daya same ki, ba ina fushi ne saboda abunda ya faru ba, kawai ina mamakin hali irin ba ku ne, taya za a ci zarafin mutum kuma ya hana a bi masa hakkinsa? Su ba su san da zumunci ba ne suka wulakanta ki? Har marinki fa aka ce yar sanda ta yi aka fito dake waje babu mayafi babu wulakancin da ba su muku ba, kin san abunda nake ji a zuciyata?”
Kai na girgiza masa.
“Babu wanda ya mare ni, kuma ba mu fito cikin gidan ba sai da mayafi, duk wanda ya fada maka tsabanin haka karya yake”
“Kanwarki ta fada min kuma baza tai karya ba, kina boyewa ne kawai”
Shiru nai ina tunani a cikin duka kanena babu wacce zata iya fadar haka sai Hafiza.
“A ina ka ganta”
“Na kira wayarki ta dauka, ita ta fada min komai”
Na yi shiru domin bana son karyata kanwata a gabansa, ko ba komai gobe ba zai sake ganin girmanta ba, balle har ya yarda da ita.
“Idan hankali ya gaushe hankaline yake dawo da shi, ita ita ta aikata kuskure mu be kamata mu aikata ba, ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin ni ce silar batar danta”
“Amman miyasa ke kadai zata zarga? Ya akai ta san da maganar ma? After na fada miki wa kika fadawa?”
“Saboda bata so na, kuma ta fada tana tunanin na dauke Abdulhamid ne ko kuma na saka an dauke shi saboda zai yi aure, kuma saboda ya ki zama da ni, tana tunanin ni an saka Abraham ya dauke shi saboda na dauki fansa”
“Amman ba ita kadai ba har wannan Abdallah.... ”
“Abdallah ba zai taba min haka ba, i trust him, ba da sa bakinsa Hajiya tai min haka ba, ba zai taba bari ba, balle har shi yai min, kiyayyar da Hajiya take min a yanzu ta samo asali ne ta dalilin soyayyar da Abdallah yake min”
“Miya hana ki aurenshi?”
Ya aiko min da tambayar kai tsaye, kallonsa nai ina kokarin kawarda da hawayen da suke son zubo min.
“ A wacan lokacin Abdallah ya nuna min soyayya ne ta hanyar da be dace ba, shi yake yawan kawo min labarin abunda Aminu yake, yana son na kashe aure na na aure, wanda a musulunce haramun ne, domin Annabi yace baya tare da wanda ya so matar wani, ko ya zuga matar wani dan ta kashe aure ta ko da kuwa shi din zai aureta, a lokacin da aurena ya mutu, sai Abdulhamid ya fito so na bayan kuma Abdallah yana so na, amman shi Abdulhamid be san Abdallah yana so na ba, Abdallah kuma be taba sanin cewa na yi soyayya da Abdulhamid a lokacin da ina budurwa ba. A lokacin ina jin tsoron abunda ya kashe min aure kar na sake fada mishi, da kuma ganin da nai Abdallah yana so na tun ina a gidan wani sai nake ganin kamar idan na aure shi, aure ba zai dade ba hakan yasa na take aurensa na auri dan'uwansa, daga lokacin sai mahaifiyarsa ta fara kina, ashe Abdallah ya fada mata yana so na, sai take ganin kamar ni na ja hankali Abdulhamid ne na aureshi saboda na batawa Abdallah, saboda babu wanda ya san mun yi soyayya da Abdulhamid saboda a boye mu kai a wacan lokacin ya hana na bayyana soyayyar, wanda ban san dalilin hakan ba wata kila saboda ba shi da lafiya ne yana tsoron soyyayyar mu ta bayyana sirrinsa, a jiya ina jin tana fadar cewar na lalata zumuncin da yake tsakanin Abdallah da Abdulhamid, ban san iya abunda ya shiga tsakaninsu ba, kuma na san saboda ni ne, komai bana yinsa daidai, yanzu ma idan aka kai Hajiya kotu saboda ni Abdallah ba zai jidadi ba”
Dan murmushi yai ya tabe baki
“Kamar dai Abdallah nan yana da muhimmanci a gurinki”
“Yes, ya taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon, ya rike yayana kamar nasa a lokacin da ubansu ya guje su, kuma mijin dana aura wato Abdulhamid ya nuna min baya bukatarsu, duk son da Abdulllah yake min be tana neman yin lalata da ni ko sau daya ba, mi zai saka ba zai zama mai muhimmanci a gurina na”
“Duk da haka dai abunda mahaifiyarsa tai miki ba ki cancanci yayanta ba, kuma ya nuna karara bata kaunarki, domin abunda tai miki makiyi ne kadai zai iya yinsa, zai iya zama silar ajalinki da baki farka ba a yanzu yaya kenan? And tell me taya za ki auri yaya uwa daya uba daya twins ya sake ki, yanzu kuma ki yi tunanin auren kane? A addinance ba haramun ba ne, amman a al'adance haramun ne, so pls ki manta da zancen auren Abdallah for now”
Da kanshi ya tashi yaje ya hada min tea ya miko min, har na karba zan kai baki sai yai saurin dakatar da ni.
“Tsaya tsaya muji”
Ya karba ya kurba kadan.
“Yana da zafi ba ri ya sha iska”
Ya fada yana kura min ido.
“Ji nake kamar ace da aurena abunda nan ya faru, zan kyale Hajiyar for now, amman shi dan sanda da yar sandar da ta mareki sai na hukunta su”
Kallonsa nai na dauke kaina.
“Akwai damuwa karara a fuskarki”
“Idan na ce babu damuwa a tare da ni a yanzu na yi karya”
“Don't be afraid i will by your side, you will be safe”
Kallonsa nai sai ya sakar min murmushi.
“I will surprise you idan kika ji sauki kika koma aiki, a gaban kowa da kowa and i hope you won't disappoint me”
Ya fada sound so serious.
ABDALLAH POV.
A yanzu Abdallah yana jin ba shi da babban makiyi kamar Ahmad, daman can Allah be hada jininsu ba balle kuma yanzu da ya zama sanadin tashin ciwon Hajiya sakamakom fada mata da yai Abdulhamid yana gurin Dss, ya san duk wanda dss ta kama yana aikata wani mugun abun ne, be tana zargin dam'uwansa da aikata wani mugun abu ba, a yanzu ma ba zai iya zarginsa ba domin ba a fadi abunda yai ba, be zama lallai dan yana abota da Abraham ace aikinsu daya ba, sai dai kalamar da Ahmad ya fada cewar shi ne sanadin zuwansa dss din ya fi komai tsaya masa a rai.
Lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya yana kallon mahaifiyarsa wacce ke kwance an daura mata mata drip a hannu sai sharar bachi take. Mikewa tai tsaye yana kallon dakin kamar wani bakonsa sai ka ce ba dakin Hajiya ba. Sam be jidadin abunda Hajiya tai ma Halima ba da ya san haka za tai da be fada mata komai ba, a dayan bangaren kuma yana tunanin ko a wane hali yanzu Halima take ciki? Har ya dauko wayarsa kamar ya kirata sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ajiyar zuciya ya sauke a hankali zuciyarsa na sosuwa da kalaman da Ahmad yai masa, yana mamakin wai a yau har wani zai nuna masa isa da Halimatu,shi ko zai nuna masa cewar be isa ga Halimatu ba, dan murmushin takaici yai.
“Mahaukaci, marar tunani, mayaudari”
Ya furta murya kasa kasa, yana jin a ransa ko da shi ba zai auri Halimatu ba tun da Hajiya tai musu shamaki to ko Halimatu bata dace da auren banza mutum kamar Ahmad ba, mutumen daya gama wulakanta ta yai mata kazafin kisa, yanzu kuma ya dawo yace son ta yake dan bashi da kunya. He know shi kadai zai aureta ga rike tsakani da Allah babu wata kyama, babu tunanin komai a ransa, ba dan Hajiya ta shiga tsakaninsu ba wata kila da yanzu ya aureta ta haifa masa da namijin da yake ta mamari, yake ganin kuma zai iya samu idan ya aureta domin ita ta haifi both maza da mata ba kamar matarsa Suwaiba ba da ke haihuwar mata.
*** *** ***
Wasa wasa aka kwashe sati daya kullum sai an sakawa Hajiya drip duk da bi ta rame kamar ba ita ba. A ranar hankalin Abdallah ya tashi sosai ganin halin da mahafiyarsu take ciki, kusa kullum a gidan yake wuni domin shi yake kuka da ita, a yau ma sai da ya tabbatar bachin Hajiyarsa yayi nisa sannan ya kama hanyar gidansa da tunani kala kala.
Yana isa harabar gidan su Inteesar suka zo da gudu suka tare shi kamar yadda suka saba, sai ya fito daga motar yana murmushin karfin hali ya rika hannunsu suka nufi cikin falon.
Ko da ya shiga Suwaiba na zauna a falon, ta kashe dauri sai