Showing 81001 words to 84000 words out of 217237 words
saurin gyada kai.
“Haka ne”
“To ai danki ya baro kyau tun ranar haihuwa, ga shi dauke da kwaryar alheri sai kuma ya bari ta fadi ta fashe”
Hajiya Zuwaira ta yi masa kallon rashin fahimta. Sai yai yar dariya ya gyara zamansa.
“Na san baki fahimta ba, wato tauraruwar danki sakaina'u ce, irin wannan tauraruwar bata iya haske har sai ta hadu da yar'uwarta mai iya daukar nauyinta, ma'ana mai taimaka mata ta haskaka, da danki zai hadu da taurari dubu idan be hadu da wannan tauraruwar ba gasri to abu ne mai wahala ya iya haskaka ya daukaka yadda yake so, daman ko wane dan'adam yana da tauraruwarsa to ita ta danki haka take”
“To amman Malam.... ”
Sai ya daga mata hannu.
“Wacece Halima?”
“Matar da ya saki ce ita ce uwargidansa”
“To ita ce mai wannan tauraruwar gasri, tauraruwa ce mai tsananin haske da kaifi gaske, tana haska ko wane irin tauraruwa, ban ce dan ki ba zai arziki ba, amman da ace yana tare da ita ina mai tabbatar miki ko matar gobna bata ita ta nuna miki yatsa ba”
“Amman Malam ai can baya tare da ita kuma yana al'amuranshi”
“Amman ya kai kamar haka?”
Ta girgiza kai alamar a'a.
“To kin gani, zai iya samun mai irin tauraruwar amman abun ne mai wahalar gaske”
Hajiya Mairo ta ce.
“To amman Malam dole sai Aminu ne kawai idan ya aureta zai yi arziki ko kuwa idan wani ya aureta shi ma zai iya yin arzikin?”
“Sosai kuwa ai kowa ta raba zai yi arziki, ita daman haka tauraruwar take”
Cikin damuwa Hajiya Zuwaira ta ce
“Yanzu babu yadda za'ayi tauraruwar tasa tai haske? Kenan dole sai da ita?”
“Akwai mana, amman aiki ne mai wahalar gaske kuma za a ci kudi”
“Karka damu indai har za a samu biyan bukata ba matsala”
“Za ki siye sa daya, da fararen balbelu uku sai fafaren kaji bakwai, sannan za a biya masu aiki 30k”
Murmushi Hajiya tai.
“Wannan ai ba wata matsala ba ce, sai dai ba zan iya siyowa ba zan dai bada kudin sai ka siyo komai da kanka, sai dai ba ka fada mana nawa za a biya ka”
“Ni sai bukata ta biya sannan za a biyani”
A take a gurin ya lissafa mata kusan dubu dari biyu da za a bada na kayan aiki, sai ta karbi account dinsa da zimmar idan ta koma gida zata turo masa, bata bar gurin ba sai da ta aje masa 10k na shan ruwa. Har suka dawo ita da Hajiya Mairo ba su daina mamaki da jinjina lamarin ba.
Ba ma kamar Hajiya Mairo domin ita nata tunanin dabam.
ABDALLAH POV.
Tun daga lokacin da suka samu matsala da Suwaiba ta canja masa, ya lura da hakan a dabi'unta da halayyarta da kuma yadda take mu'amalantarsa a yanzu.
Shi kau iya kokarin da yake na ya fahimtar da ita ne ta daina ganin laifinsa ko kishin Halimatu, a iya ganinsa shi be ga dalilin wannan kishin da take ba, be san abunda zai saka ta ji haushi dan yayi ma yar'uwarsa alheri ba, tun da ita ma babu abunda ya rageta duk wani abu da take bukata yana yi ma kuma yai ma yan'uwanta, sai dai duk bata ga na kowa ba sai na Halimatu. Duk yadda take kokarin avoiding dinsa shi kuma kara shige mata yake yana nuna kamar wani abu na bacin rai be taba shiga tsakaninsu, daman can haka yake idan yai fada da ita kokarin mantawa yake saboda kullum auna tunaninta yake yana ganin be kai na shi ba, a ganinsa mace mai rauni ce kuma ba komai suke iya tsayawa su yi tunani ba, duk yadda abu ya zo musu haka suke karbarsa shiyasa shaidan yake yin galaba akansu. Idan har ya ce zai rike ta a ransa zata iya shiga matsala, matukar ya rike bacin ran mutun a zuciyarsa sai wani abun ya faru da mutun domin yana da kofi, idan har ka bata masa rai za ka ga daidai ba, shi kansa har mamakin kansa yake wani lokacin abu yake kamar wani maye.
sai da yai shirin office saf sannan ya nufi dakin matarsa yana kamshi turare mai dadi. Yana shigowa ta wani dauke kai be damu ba ya karasa kusa da ita ya kama hannunta ya sumbata.
“Zan tafi office sai na dawo”
Bata ce masa koma ba, shi ma kuma be jira ya ji wani abu daga gurinta ba, daman be yi tsammanin ta fada masa wani abun ba ko da Allah ya tsare ne ba tun da fushi take da shi, ba kamar da ba da har bakin mota take rakoshi. Daga gidanshi gidan Hajiya ya nufa as usual daman sai ya biya ya gaisheta yake wucewa office, ko a dawowa ma idam time be kure masa ba sai yayi mata sallama yake dawowa gida. Ya dauki Hajiya kamar wata abokiyasa yana jindadin fira da ita sosai duk wano sirri na shi ko shawara ita ce, kamar yadda ita ma ta fi shakuwa da shi fiye da Abdulhamid.
Ba kasafai Abdulhamid yake zuwa da safe gaishe da Hajiya ba, wani lokacin sai da rana ko dare, wani lokacin ma sai ya wuni be shigo ba sai dai yai mata waya. A kujerar da mahaifiyarsa take zaune ya zauna yana mika mata gaisuwa.
“Lafiya Kalau ya aka tashi ya yaran”
Ta amsa masa fuskarta da alamun magana.
“Abdulhamid”
Daman haka yake masa he can't say Abdulhamid ina kwana saboda yana jin age mate dinsa ne, tun da yake a rayuwarsa be taba bude baki yace wa Abdulhamid ina kwana ko ina wuni ba, sai dai ya kira sunansa.
“Likita ykk”
“Lafiya kalau”
Ya amsa yana kallon yanayin Hajiya da kuma shi kansa Abdulhamid din.
“Lafiya wai?”
“Lafiya kalau wai Halimatu ce tace ta gaji da zama da shi saki take so.... ”
Ji yai kamar an zuba masa ruwan sayi a kai a take tsigar jikinsa ta tashi.
“Saki?”
“Eh”
Hajiya ta amsa masa.
“Why?”
Abdulhamid ya daga kafadunsa alamar be san dalili ba.
“No dole akwai wani abu, akwa abunda kai wa yarinyar nan Abdulhamid haka nan kawai Halimatu ba zata ce ka sake ta ba, i know who's her”
Hajiya ta tabe baki tana fadin.
“Ni nace dai ko ta gaji da zama da kai haka nan ne ba”
“No bana tunanin haka duk dai na san matsalar ce tai haifar da komai, amman wata kila tana jin kunyar kan ta ne akan abunda ya faru”
Cewar Abdulhamid, a take Abdallah ya gyara zamansa yana girgiza masa kai.
“idan har akan matsalar ne be kamata ta saka kanta cikin damuwa ba, matar da zata bar yayanta ta bar aikinta ta yarda ta aureka bayan kuma ta san irin lalurar da kake tare da ita, be kamata dan wani abun ya same ta ka barta ta shiga damuwa ba, and she told you ba su yi raped dinta ba, miyasa ba za ku yarda da ita ba?, Abdulhamid Halimatu kamar amanace a gurinka kuma matarka ce ka zaunar da ita ta nuna mata baka da matsala da hakan kuma ta kwantar da hankalinta, Abdulhamid yarinyar nan.... ”
Be karasa ba Abdulhamid ya tari numfashinsa.
“Halima ba yarinya ba ce, yaranta hudu ta san me take yi. She told me babu wanda yai forcing dinta ta aure ni and now she want divorce”
“Ai sakin ma shi ya fi alheri”
Abdallah ya juyo ya kalleta cike da damuwa.
“No Hajiya ke kika haifar da wannan matsalar kika saka Abdulhamid ya rika ji a ransa kamar an yi raped matarsa, and now kina kokarin ki karfafa nasa guiwa ya sake ta haba Hajiya be.... ”
“No tun kamin ayi wannan abun i suspect something, and yes na kai ta an mata hiv test and the result din positive, maybe dai tana jin kunyar kanta ne.... ”
Da mugun mamaki Abdallah yake kallon dan'uwansa.
“Don't tell me you don't trust your wife...? Why all the insult bro? Taya za kai ta ayi mata hiv test? Kasan halin da za ta shiga?”
“Ba zaka fahimta ba ne Abdallah, ni na san abunda yake nan, and matar nan yanzu har shaye-shaye take fa, na ga kwalaben maye a dakinta, and wani lokacin zan tarar tana ta bachi kamar wacce ta mutu, idan ta farka idonta har canjawa yake”
Kamar an saka scissors an yanke jiyojin jikinsa haka ya ji, be taba jin tausayinta irin yanzu ba, yana jin da ace shi ne Halimatu ta fada masa cewar ba'ayi mata fyade ba babu abunda zai hana shi yarda da ita, even if an yi mata fyaden ma zai iya zama da ita a haka.
“Akwai abunda yake faruwa a tsakaninku Abdulhamid, wanda ba ka son mu ji kuma ba lallai ne sai mun ji ba, amman ka dubi girman Allah ka ji tausayin yarinyar nan, ace har ta fara shaye-shaye amman kake maganar sakinta? Abunda ya same ta kaddara ne miyasa ba zaka nuna mata hakan ba? Rashin lafiyarka ma ka nuna mata zaka nemo magani, i promise you zaka samu sauki soon...”
shiru Abdulhamid yai for a while kamin ya sake bude bakinsa ya ce.
“I think rabuwar shi ya fi alheri a tsakaninmu dukan mu za mu samu kwanciyar hankali”
Wani irin kallon Abdallah yai masa.
“Ta auri mutunen da be cancanta ya zama mijinta ba, Abdulhamid ban yi tsammani haka daga gareka ba... ”
“Ba ka fahimta ba ne Abdallah tun kamin wannan abun ya faru Halima tai ciki, kuma ta zubar da shi ba tare da na sani ba....”
“Ciki? pregnant.... Ciki?”
Ya maimaita har sau uku, sai kuma yai saurin mikewa tsaye ya nufi window falon ya tsaya a gurin yana shafa kansa, gaba daya zuciyarsa ta gama narkewa da tausayin Halimatu yanzu kam. A hankali ya busar da iskar bakinsa yana sauraren yadda Abdulhamid yake labarta abunda ta fada masa da kuma kin yardar da yai da ita. Lumshe ido yai ya bude, so yake yacewa dan'uwansa Halimatu tana da gaskiya amman taya? Shi kansa ba shi da hujja, iyakar abunda yai imani da shi, shi kam ya yarda da Halimatu ko da bata kafa hujja da komai ba, and ya san idan har Halimatu za ta aikata zina to zata aikata ne tun a lokacin da take gidan Aminu. Juyowa yai ya kalli dan'uwansa.
“Amman ka yi magana da ita? Abdulhamid ko da da gaske Halima ta aikata haka ta cancanci ka zauna da ita, macen da zata bar yayanta, ya bar duk wani abu mai muhimmancin a gareta ta yarda ta aureka da matsalarka ta gama maka komai, kama yai ka tambaye ta ka bincike ta wata kila ta iya gane wanda yai mata wannan abun sai a bincike shi amman duka ba ka yi wannan ba sai kawai ka juya mata baya? And now kana maganar ka sake ta? Ka yi convince dinta ka nuna mata sakin ba mafita ba ne a gareta, ta shiga damuwa da yawa, Abdulhamid, Halima deserve a happiness”
“Ya isa haka Husaini wuce ka je gurin aikinka”
Hajiya ta fada a tsawace tana daga masa hannu. Ya gyada mata kai yana hade wani irin abu daya tsaya masa a kahon zuciya. Ko minti biyu be kara cikin falon ba ya fito ya shiga motarsa, Halimatun dai ce ta tsaya masa a rai ya kasa rika ko da sitiyarin motar har na tsawon lokaci ba yi wata halitta da yake tausayi a duniya kamar Halimatu ba. How he wish shi ne a step din Abdulhamid da ya nuna mata soyayya da kauna ya rumgumeta har sai ta manta da duk wani bacin rai a duniyar nan. Ya dade a gurin kamin ya tashi motarsa ya danna horn a bude nasa gate ya fita da motar, titi ya hau yana tunanin inda zai je direct asibiti gurin aikinsa ko kuma gurin Halimatu? He need to talk to her, sai kuma wata zuciyar ta ce nasa no, kuskure ne yai magana da ita a yanzu, ba zata fahimta ba, son da yake mata ma yana jin a ransa cewar ya aikata baban zunubi kuma yana jin kamar ya ci amanar dan'uwa, wannan kadai ya saka shi a damuwa. And maybe idan yai magana da ita ta fahimta ta daina zancen sakin, he can talk to her as her brother wata kila ta fahimta.
Haka yake ta sake sake a ransa, daga karshe ya yanke shawarar kiranta a waya, sai dai kuma idan ya kirata a waya dan'uwansa ya ji he may think something else... But yes he can talk to her as Abdulhamid brother as his best friend, as her husband best friend. Har cikin ransa baya son ta rabu da Abdulhamid saboda ba mafita ba ne a gareta, and idan ta rabu da shi yanzu zuciyarsa kan iya bijiro masa abunda ba mai yiyuwa ba ne akanta. Wayarsa ya ciro ya aikawa Abdulhamid sms.
“Can i talk to her? As your brother”
Immediately yai masa reply.
“Yes i trust you”
The truth word break his heart sai yaji ina ma be tambaya ba. But yes mace ta bukaci saki a gurin miji ai ya kamata yan'uwansa su ji daga gareta su ji dalilinta. Sai da ya saita natsuwarsa sannan ya dauki hanyar gidan Abdulhamid yana ta tunanin a irin halin da zai samu Halimatu. Zuciyarsa sai raya masa take kar yaje, ya faka motarsa a bakin gate sannan ya fito ya tura kofar gate din ya shiga cikin gidan. Ya dade tsaye a kofar falon sannan yai knocked. For like five minutes ta bude kofar suna hada ido, idonsa ya cika da kwalla wani irin tausayinta yake ji yake kamar ya dauke ta ya hade ta manta da komai.
“Abdulhamid ba ya nan”
“Gurinki na zo”
Sai ta saki kofar falon shi kuma ya turo ya shigo cikin falon ya zauna a kujerar da ke kusa da kofar falon. Daga inda take tsaye fuska babu annuri ta ce
“Ina jinka”
Sai ya nuna mata kujera alamar ta zauna, ba musu ta zauna a kujerar da ke nesa da shi sosai, after ta zauna ya soma magana a natse.
“zan yi magana da ke as Abdulhamid brother, Abdulhamid ya zo mana da magana marar dadin ji daga gareki, b zan iya nanata maganar ba amman ina fatar ba haka zan ji daga bakinki ba.... ”
Bata ko jira ya karasa ba ta dora da nata.
“Haka yake ko ba zancen saki ba?”
“Amman Halimatu wannan ba mafita ba ce a gareki and... ”
“And what? Idan ya sake ni mutuwa zan yi?”
Kasa ce masa komai yai, gaba daya ta canja a tsaye take kamar ba ita ba.
“Be kamata ki canja rayuwarki ba akan abunda ya same ki, kowa ya san kaddara ce, ki tattara komai ki aje a gafe ki barwa Allah labarinsa, dabi'un da kika dauka yanzu ba za su kai ki ko'ina ba and mijinki yana son ki yana cikin damuwar abunda ya same ki....”
“Babu abunda zaka fada min da zai saka na canja kudirina Abdallah, bana son jin wata magana daga gareka ko wace iri ce, let it go can't hold me back anymore, duk abunda ya faru ai kai ka janyo you try to act innocent, da ba ka aikata min abunda ka aikata ba, da yanzu komai be faru ba, na rasa gane wane irin mutum ne kai Abdallah na kwarai mai son taimakona da yarana, ko kuma mai son ruguza rayuwata?”
Still now be iya ce mata komai ba, gaba daya jikinsa ya gama sanyi, be fahimci inda zancen ta ya dosa ba. Ita kuma bata fasa fayyace masa komai ba.
“Mutumen da yai min fyade be rage komai a zoben hannunka ba, na danna na cige ina ta boye abu saboda na samu natsuwa a zaman aurena, amman Abdulhamid ya masa yarda da ni, ba zubar da cikin nai ba zubewa yai saboda tashin hankalin batan Namra, amman yana ganin kamar na aikata alfasha da wani ne na zubar da cikin, shin idan na fada masa dan'uwansa ne ya aikata ya kake tunanin zai ji?”
Rumtse idonsa yai da mugun karfi ya fisgi kansa kamar ba shi ba. Be taba jin magana daci ba irin wannan, ba a taba munana masa zato ba irin wannan, amman a maimakon ya ga laifinta sai tausayinta ya kara rufe shi, tausayin da be san daga ina yake ba, gani yake yanzu kanta a chushe yake, bata fahimtar komai da kyau kuma tana da raunin tunani.
A lokacin da ya bude ido sai ya ji kamar ba a duniyar nan yake ba, maganganunta na ta maimaita kansu a cikin kunnuwansa. Zoben hannunsa ya kurawa ido, kokarin tuna inda ya tsiya zoben yake a office right! Wani mai kawo musu kaya ya kawo rings even though shi ba masoyin zobe ba ne ya tsiya daya ya saka saboda zoben ya masa kyau. Yes he remembers at first ma mai alphabet H ya dauka sai kuma ya ga rashin dacewar hakan then ya canja to A mai sunansa. Magana ya fara yi tana rabe masa hawaye na sauko masa.
“Na san kin san ina son ki... Na fada miki... Kuma... Kin san haka.... Amman soyayyarki.... Bata taba saka min sha'awarki ba.... Ban tana jin sha'awar na rika hannunki ba daidai da minti daya Halimatu..... Indai har dan jikinki ne.... Zan bukace ko a lokacin da kike gidan.... Aminu.... Ko a lokacin da kike zawarci.... Ba yanzu da kika auren dan'uwana ba.... Wallahi ban tana aikata zina ba.... Zuciyata bata taba raya min akanki ba..... Kullum burina da fata na aurenki ne.... Saboda ki huta ki samu kwanciyar hankali.... Tausayi kike ba ni Halimatu... Yana daya daga cikin dalilin da ya saka nake daukar dawainiyar yaranki..... Da ke kanki... Na ke damuwa da damuwarki..... Yes i love you.... I do love you..... I love more i did before... Amman yanzu duk wannan ya wuce saboda kin riga kin auri dan'uwana twins brother na..... And yes na so na aure ki saboda na samu da namiji ko ba komai hakan zai kara min kaunarki.... Amman yanzu duk wannan ya wuce.... ”
Lumshe ido yai ya bude har lokacin yana hawaye.
“Idan har zan miki fyade, ba zan bar wata alama da za a gane ni ba, bazan shigavgidan makotanku har a kashe wani da ni ba saboda kawai na biya bukatar da zan tashi a gaban Allah