Showing 42001 words to 45000 words out of 217237 words
kuma ya samu domin ban iya masa musun ba sai gyada masa kai da nai alamar na amince.
“Thank you”
Ya furta sannan ya fice daga dakin ni kuma na hade wani abu marar dadi da ban san ko minene ba na rumtse ido.
*** *** ***
A satin suka fara zuwa makaranta, daga uniform har Littafai da school bus da ke zuwa daukarsu da komai Abdallah yai, aikina kawai wanke musu uniform shi ma ba kullum ba domi kanena ne suke wankewa su goge musu, bangaren abinci na samu sauki sosai domin a makarantar ake ba su na safe da kuma na karfe sha biyu daya da rabi kuma a kawo su gida. Tun daga lokacin ban sake saka Abdallah a ido ba da na kira wayarsa nai masa godiya ma kin dauka yai.
Wata rana muna cikin fira da Abdulhamid na ke masa zancen yarana akan tafiyar da zan yi na bar su a gidan.
“Amman za su rika zuwa suna ganina a gidanka”
Na fada ina karantar yanayinsa.
“Haka ne”
Ya fada yana hade yawu, ni kuma na ji wani iri, be karfafa min guiwa ba kuma ba ce zai hana su zuwa ba, a ranar har muka karkare ba mu tattauna wani abun arziki ba. Misalin goma na dare na shigo gida, dakinmu na wuce kai tsaye sai na samu dukansu sun kwanta a saman katifa sun yi bachi har Amal da bata bachi da wuri. Ido na kura musu ina ta kallonsu kamin na zauna na kai hannuna na safa su, ina ta jin su kamar wasu marayu zan auri wanda baya farinciki da zuwansu a gidansa ga mahaifinsu har yau be leko ko ya turo a duba lafiyarsu ba, gaba daya ma sai na ji kamar na fasa auren kuma babu dama. Shinfida nai musu na kwantar da su a inda nasaba kwantar da su Amal kuma na rumgumeta mu kai bachi rumgume da juna. Tun daga lokacin wata irin shakuwa da kauna ta kara shiga tsakanina da yayana ba ma kamar Amal da take karama, har ta kai ko laifinsu bana son a gani dana ji kukan daya daga cikinsu sai na ji babu dadi. Ban sanarda kowa zancen auren ba sai ana sauran sati biyu ciki kuwa har da aminiyata Hajara, a ranar da ta sallamo gidanmu ta nuna min bachin ranta sosai har take labarta min wai mijinta ya fara gina gida mai part biyu saboda ni da ita.
“Hajara ba ki da hankali”
“Babu wani rashin hankali Halimatu, abokiyar zama tana da dadi ko da dan yau da gobe, kuma ko Abban Afra be aure ki ba zai karo aure saboda akwai son karin auren a ransa, ba ki san kudirinmu ba, ba ki san iya abunda muka shirya akanki ba”
“Wai ba ki ma kishin mijinki?”
“Wallahi ban taba jin kishi akan ki auren mijina ba, na san waye mijina za sama miki rayuwa mai kyau irin wacce kika rasa a gidan Aminu, kuma zai rike yaran nan da muhimmanci ko ba komai ai hakan zai bawa Aminu haushi tunda abokinsa ne”
“Wallahi ni ba zan iya ba Hajara, taya zan yi kishi da yar'uwata?”
“Ba zaman kishi za mu yi ba, zaman yan'uwa za mu yi”
Duk yadda tai ta kokarin convince dina na yarda da ita sai na kasa, ni kallon marar tunani ma na koma yi mata, a ranar dai mun sha fira sai da yamma ta tafi. Washe gari sai ga kawata Sa'adatu na yi mamakin ganinta ba ni kadai ba har da kanwata Hafiza domin ni dai na san ban fada mata cewar zan yi aure ba, rabona da ita ma tun a lokacin da ta fada min cewar za tai tafiya tafiyar da Hafiza ke labarta min cewar da Aminu tai yi ta. A al'adar ko ma na kira shi da dabi'a bana iya cin fuskarka mutum a kusa da shi kamar yadda na ke saurin yarda da mutane, komai mutum yai min zan shanye na mai da komai ba komai ba. Haka muka zauna muka sha fira da ita daman a gidan babu wanda ya san akwai wata alaka tsakaninta da Aminu daga ni sai Hafiza, hakan yasa Inna da Mama suka sakar mata fuska kamar yadda suka basa tun ina budurwa.
Sosai ta nuna min rashin jindadin mutuwar aurena da Aminu da kuma tambayar wai da su Namra zanje gidan sabon mijin nawa ko a'a.
“Ya ce na je da su, ni kuma na ga kara dai na bar su a gida tun da sun fara sabawa da nan din”
“Eh kuma kin yi tunani, tun da na ji ance saurayi ne wanda za ki aura”
Na kalleta da mamaki.
“A ina kika ji?”
“Hmmm Halimatu kenan, ai abun duniya baya boyuwa ballantana ma kin san wannan babban sakamako ne Allah yai miki Allah yasa dai kyakkyawa ne kamar yadda kike kyakkyawa kin san ke fa matar manya ce”
Murmushi nai tare da canja mata fuska, hakan yasa ta hade duk wani zancen da ke kunce a bakinta tai min sallama ta wuce har da mikawa su Amal 2k ni dai ko rakiya ban mata ba.
Duk yadda kawaye da yan'uwa suke ba ni kayan gyara da tsima jiki kin sha nai sanin mijin da zan aura, dan haka ba zan sha abun da zai zo ya dame ni ba ko ya zame min matsala. Sai dai bana nunawa kowa sanin cewar babu wanda yasan da matsalar Abdulhamid sai ni. Daga ni har shi ba mu tsara yin wani event ba, dama ni ba budurwa ce shi ne dai ya kamata yai hakn kuma be yi ba, wata kila saboda shi ma din kansa ya san be cika cikakakken ango ba ko kuma dan baya da son hayaniya ne oho.
Ranar da aka daura aurena da Abdulhamid sai na kasa farinciki kamar wacce akai ma auren dole, wata kila saboda na san irin mijin da na aura ko saboda zan tafi na bar yayana ko kuwa saboda dan'uwan Abdallah na aura wanda ya saka ce min komai akan hakan har yanzu. Duk wata murna ta iya fuska ce da hakora amman bata kai zuci ba, gaba daya ma neman son Abdulhamid nai da ke zuciyata na rasa, da na tuna cewar baya son yarana sai ji kamar bana bukatar zama shi, duk kuwa da kasancewar be fito kai tsaye ya fada min ba amman alamu ya nuna haka. A wunin ranar da akai wunin biki Amal na biye da ni duk inda zanje, ba Amal kadai ba har da Namra Aiman da Adnan ne kawai ke ta sha'aninsu su kan fito basu kula ba, Amal har wani sabon kuka ta tsira ba tare da am mata komai ba. Tun da magariba kanena Zayyanu ya karbe ta ya fita da ita da Namra saboda ya dauke musu hankali kar su ga tafiyata.
Inna da Mama sun min huduba kamar yadda su kai min a farkon daren da za a kai ni gidan Aminu, sai abun ya dawo min sabo ina ta hawaye kamar bakuwar aure. Baba ma ya min tasa bayan wacce yake ywan min tun daga lokacin da aka saka ranar auren. Ban san abunda ya hana jin bana son tarewa a ranar ba sai naji kamar ace sai nan da kwana biyu zan tare. Motoci da Abdulhamid ya turo na daukar amarya motoci ne amsu kyau da tsada, ba mota daya ko biyu aka kawo ba, motoci da yawa aka kawo na daukar amarya da kawayenta ni kaina abun har mamaki ya ba ni sai ka ce wata budurwa, ko da yake a gurinsa auren fari ne dole abokai da yan'uwa su yi masa kara.
“Hafiza ga yayanki dan Allah ki kula min da su, na san kowa yana kula da su yadda ya dace amman zan kara tunatar da ke ne saboda na san halin yara da cin rai, ta bangaren makarantar su a kula min da su dan Allah”
Haka na fadawa Hafiza kanwata wacce muka fi shakuwa, ina jin wani abu ba dadi kamar ina bar mata wasiya. Dafa ni tai tana karfafa min kuiwa.
“Karki damu Yaya Halimatu za'a kula da su In-Sha-Allah, Allah dai ya baku zama lafiya da hakuri, idan kika cire komai a ranki sai ki ga kin saba kamar can baya”
“Na gode Hafiza”
Misalin tara da yan mintuna aka kai ni gidan Abdulhamid da ke can bayan science, har muka isa kafata ta taka cikin katon gidan mai kyau ban daina jin kewar yayana a raina ba, ba ma kamar Amal sarkin takuwa yau ko a jikin wa zata kwana oho...
AMINU POV.........✍️
___________________________
To fa Halimatu za a fara sabuwar rayuwa, Allah bada zaman lafiya.
Anya dai ta kyautawa Abdallah kuwa? 🙄😏
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_
By Khadeeja Candy
1️⃣6️⃣
Milk shadda ce a jikinsa sai farar hula, fuskarsa na ta sheki kamar shi ne angon ga wani kamshin tutare da yake mai sanarda zuwansa tun kamin ya iso. Abu biyu ne babu a tare da shi walwala da sai kuma yar ramar da yai kadan. Da sallama ya shigo falon Hajiyarsa sannan ya zauna da bismillah, kamin ya mika mata gaisuwa daga inda yake zaune. Sai ta amsa masa tana ta kallon yanayinsa yanayin da ya sauya masa tun sati biyu da suka gabata.
“Hajiya ta sai yanzu ake karyawa?”
Ya fada yana kallon kofin tea da ke hannunta.
“Aa yau da dumamen tuwo na karya sai yanzu na ke shan tea”
Be sake cewa komai ba ya maida hankalinsa a gurin tv da ke kunne.
“Ba kaje aiki ba yau ko kuma ba a aikin ne yau?”
“Zan je yanzu, Suwaiba na kai gidan Abdulhamid, daman ta matsa min tun kwanaki baya tana son zuwa na hana ta sai yau dai na kai ta”
Har lokacin da yake maganar be kalli gefenta ba. Yana shirin mikewa tsaye ta ce.
“Jiya Mal Dalhatu ya zo nan”
Da sauri Abdallah ya juyo ya kalleta jin ta ambaci mahaifin Halimatu.
“Mi ya kawo shi?”
“Yace yana ta son ya zo yai mana godiya be samu dama sai yau saboda yanayin jikinsa”
Dan murmushi yai ya kawardar fuskarsa.
“Baba Karami akwai karfin hali, miye abun godiya a ciki ai yi wa kai ne”
“Yi wa kai ko kashe kai? Akan me za ka dauki nauyin irin wannan dawainiyar haka? Ya fada ko ruwan da aka sha a gurin wunin nan kai ka kawo su”
Cikin muryar da ke bayyana rashin jindadinta tai masa maganar hakan kuma ba karamin mamaki ya ba Abdallah ba, domin be taba ji ko ganin ta hana su yin wani aikin alheri ba musamman abunda ya shafi yan'uwa.
“Akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka dauki nauyin hidimarta? Har da wani daukar yara ka saka su makarantar kudi ina ruwanka ba su da uba ne?”
A karon farko ta yi masa maganar a tsawace tana dire kofin tea da ke hannunta da karfi.
“Ban yi dan wani abun ba Hajiya, a gaban ki Alhaji ya bar mana wasiyar taimakon yan'uwa da mabukata, kuma tun ba yau ba idan za ayi biki a gidan Baba Karami mu na yi masa abu mai nauyi saboda mun tashi mun ga Alhaji na yin haka kuma ya mana wannan wasiyar, ba hidimar aure kawai ba har abincin da za su yi ke da kanki kin sha daukar abu daga nan ki aika musu balle kuma mu da muke jininsa”
“Ba alheri na ke hana ka yi ba, wannan karon ka yi alherin ne a gurbin da be kamata ka yi shi ba, akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka nuna mata kula har da duniyarka”
“Hajiya idan Halimatu ta auri Abdulhamid kamar ni ta aura, ni da Abdulhamid duka daya ne kuma.... ”
Hannu ta daga masa.
“Na fika sanin wannan kai da shi duka ni na haife ku, ina magana ne kawai akan abunda yake bayyane ni na san Abdulhamid ba son Halimatu yake ba, ita ta janyo ra'ayinsa ba kuma saboda kowa ba sai dan kai”
“Haka ya fada miki?”
“Ba sai ya fada min ba, ni na san waye ďana, be taba zo min da maganar wata mace ko son yin aure a wannan yanayin da yake ciki ba sai a wannan lokacin, mutumen ma da neman lafiyarsa ya saka a gabansa? Rana tsaka ya zo min da zancen auren nan idan ba ita ta nuna masa ba taya za ayi ya kawo wannan tunanin a ransa? Kuma ya rasa mace aure sai Halimatu bazawara? Mai yaya hudu yana saurayinsa bayan kuma ba iya komai yake ba Allah yasa dai tsakani da Allah zata zauna da shi”
Murmushi Abdallah yai ganin yadda Hajiyarsa take ta bude wuta.
“Ban da abinki Hajiya Abdulhamid ai ba yaro ba ne da zata nuna masa hakan ya yarda idan har ya san baya son ta ko kuma zai cutu”
“Ko dai minene Husaini be dace Halimatu ta auri Hassan ba bayan ta san kana sonta ban goyi bayan Abdulhamid ya auri Bazawara ba a aurinsa na fari na kyale shi ne kawai saboda na lura da ra'ayinsa na son yin haka kuma bana son na karya masa guiwa saboda ya dade yana mafarkin aure be samu ba, kuma na tabbatar shi kansa be san kana son ta ba Wallahi ba zai aure ta ba, amman ita ai ba yarinya ba ce ya kamata tai tunani indan har ba zata aure ka ba to be kamata ta auri dan'uwanka ba, ko da kuwa shi ya nuna mata son da gaske sai da ta fasa aurenku duka, Hassan ya ji da wanne yayanta guda hudu ko kuma lalurar da take gabansa? Da gangan tai wannan saboda ta bata zumunci kuma ya batu”
Abdallah ya shafa kansa tare da hade yawu sannan ya kalli Hajiya a raunana ya fara magana muryarsa kasa kasa.
“Jikina yana yawan ba ni haka, ina yawan jin cewar kamar Halimatu ta jayo soyayyar Abdulhamid ne ba shi ya kai kansa ba, sai dai zuciyata ta kasa yardar da hakan, tun daga lokacin da kika fada min Abdulhamid ya zo miki da maganar auren, ko wane dare sai na lalubo na ga ko zan hango wani abu da zai saka na zargi Halimatu amman Wallahi Hajiya na kasa ganin laifinta, a maimakon haka sai tausayinta ya kara kamani saboda na san Abdulhamid ba kamar ni ba ne baya son yara a rayuwarsa, ko da ma yana son yara ba zai kaunace su a lokacin da yake saurayinsa ba ita kuma take a bazawara ta zo masa da yara, ga mahaifinsu be kula da su ba, and yan gidansu gaba daya mata ne mazan uku duka kanane da ba su yi wani wayo da za su iya kula da tattalin kanensu ba, balle ma yayan yayyu, abu ne mai wahala ta samu mai kula mata da yaranta yadda ya dace”
“Can ta matse mata ina ruwan wani? Ita yarinya ce da ba zata yi tunani ba kamin ta aikata abu? Ni Wallahi da tausayi take ba ni amman yanzu na natse ko ganinta bana son yi, ba dan kuma komai ba sai dan wannan wawanci da ta aikata, ni Wallahi bana son Abdulhamid ya auri bazawara kuma bazawarar ma wacce dan uwansa yake so kuma ita ta san hakan amman ta yarda”
Wannan karon wani dogon numfashi yaja ya sauke.
“Hajiya akwai wani kuskure da na aikata a can baya, wanda na ke tunanin wata kila saboda shi Halimatu take son hukunta ni kuma na cancanci haka”
“Haba Husaini wani irin laifine da zai saka ta auri dan'uwanka saboda kai? Ni ban ga cancanta aurenta da Abdulhamid ba Wallahi na san waye ďana”
“Hajiya na yi kuskuren furtawa Halimtu cewar ina sonta a lokacin da take da aure, tun da na dawo kasar nan na ganta sai ta ga ta canja min kamar ba ita ba sai Allah ya dauki son ta ya saka min a rai, a lokacin na yi ta kokarin ganin na haka zuciyata abunda take son cusa min amman na gagara, Wallahi Hajiya har ta kai idan zan kwanta ko ina wani abun sai tunaninta ya fado min a rai, musamman da na samu labarin yadda mijinta yake da kuma irin yadda take hakurin zama da shi, a lokacin shaidan ya yaudare ni kuma yayi galaba a kaina zuciyata tai ta nuna min cewar Halimatu bata dace da auren Aminu ba, ni ta dace ta aura a lokacin akwai good understanding tsakanina da ita, hakan yasa na fara nuna mata irin halayen mijinta da abubuwan da yake marar kyau, daga lokacin muka fara samun matsala da ita, a lokacin ne na fada mata kai tsaye cewar ina son ta.... ”
Shiru yai for few seconds ya shafa fuskarsa sannan ya sake sauke numfashin a karo na biyu.
“Na fada mata zan iya aurenta idan har zata iya kashe aurenta ta fito, kuma na yi ta aikata abubuwan da nake sa ran za su iya zama silar mutuwar aurenta, Astagafurullah ....Abubuwa da yawa Hajiya har ta fara fada min bakar magana tana min kallon wani shaidani yes ni kaina a ynzu ina jin na aikata ba daidai ba, amman a wacan lokacin sai na kasa gane hakan duk da na san bata dace da auren Aminu ba amman ai he dace na yi sanadin mutuwar aure ba ko?”
Hajiya ta gyada masa kai. Sai ya maida kansa kasa yana taba agogon hannunsa
“Yes i know... Kuma na san shi ya janyo min wannan matsalar a yanzu, so ko da ma ita ta janyo soyayyar Abdulhamid batai laifi ba inda dai ta hukunta ni tai i deserve it, and Abdulhamid ya fi ni bukatar aure a yanzu saboda yana a situation din ba ko wace mace zata iya aurensa a yadda yake ba sai mai hakuri da jajircewa kamar Halimatu”
“Babu wanda ya san da wannan matsalar sai mu, sai kuma ita a yanzu waya sani ko ta gagara zaman ta fita ta tona mana asiri kuma ta bayyana ma duniya halin da Hassan yake ciki bayan a da yana cikin rufin asirin Allah? Na fi tausayin Hassan fiye da kai na dade ina jiran zuwan ranar da zan ga Hassana yayi auri yana rayuwa ta farinciki kamar kai kamar kowa, amman na bana farinciki da auren nan, saboda yayi auren